BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   56 / 61

165K to 168K   out of 180.4K words

uku tana lumshe idanun ta, hawaye taji sun sakkomata itama, kamar an dauremata harshe haka taji domin ta kasa cemasa uffan sai shine ya katse shirun da faɗin "ki sauko down ina main parlor ina jiranki yanzu kinji"

Baki ta bud'e cikin jin kunya da shagwa'ba tace "ya-turab akwai mutane da yawa fa.......!

"Yes to meye..!? And ke ba matata bace....!?" Ya fad'a cikin halin Ko in kula.

"Gaskiya nidai a a!"

"Okay bara nazo Ni, ki jirani gani nan"

Da sauri tace "no please, gani nan zuwa dan Allah karkazo.....!"

Murmushi yayi yana yanke wayar bayan yaji abunda ta fad'a.

Juyowa tayi da niyar neman ɗayan su ya rakata.

Ba'ki sake suke binta da kallo tsantsar mamakin irin wannan kyau da Allah ya bata, a ransu suna qara jinjina wayo da dubara irin na ammin leeya, yanda ta baiwa 'yarta kariya cikin dubara.
Domin da ba dan haka ba Allah kadai yasan halinda leeya take daidai wannan lokaci.

Daga cikin tunanin da suke ne sukaji qarar camera da alama pictures ake yi mata, aikuwa khulud ce ta shigo dakin ganin duk sunyi suman tsaye yasa ta ciro wayarta ta fara yimata pic's wannan qara da camera keyi idan ana daukar hoto shine ya karkato hankalin su badariyyah da suka faɗa duniyar tunani.

Har rige-rigen ciro wayayunsu suke wajen son daukar ta hoto....!

Ba wacce bata yimata hoto ba a cikinsu, wasu su yimata su kadai wasu kuma su had'a da kansu suyi salfie.

Ringing din wayar ta taji a karo biyu da sauri tayiwa zohal rad'a a kunne, alama sukayi wa meenal da ta matso kusa.
Banji me suka gayamata ba sai gani nayi sun fita dakin su uku.

A hankali suke sauka kan step gab da zasu shigo parlourn ne meenal da zohal suka juya suka tafi sakamakon ganin turab da sukayi shi kadai ba tare da abokansa ba kamar yanda sukayi zato. kenan ita ma leeya tazo ita kadai,,,,,! Haka yake nufi.

Jiki a sanyaye ta zauna gujerar da ke fuskantar wacce yake zaune.
Kansa na qasa yana daddana waya yayi kamar baisan da zuwanta ba.
Sai da suka dauki tsawon mintuna biyu a haka kafin ya daga kansa ya fara magana kamar bayason yinta.

"Ke yarinya kin shigo ba zaki iya gaida ni ba sannan bazakiyimin Allah ya kyauta aure ba kho.......? Bama wannan ba, yau za'a yi walima kinsani ko? To motocin da zasu dauke ku suna hanyar zuwa ba jimawa, ku shirya komai da wuri duk da ba wani shiri zakuyi ba domin na gayamuku akwai komai a can.
And..........yarinya dan Allah shawara nazo muyi, duba da yanda kikayi kyau haka tubarkallah a hakan kike so muje walima kowa yana kallonki ....? ai sai bakin mutane ya kamaki aimin asara, shiyasa nake so mu yanke shawarar duk wani programme da za'a yi ki dinga saka mayafi kamar yanda kike dha.......! Ya kika ji shawarar tawa......?" Ya qarasa maganar cikin sigar tambaya.

Numfashin ta ne ya tsaya chakkk ya daina tafiya.! Ko wace ga'ba ta jikinta ta daina aiki, motsi ma ta kasa yi lokacin da ta d'ago ta kalleshi da nufin tayi magana bayan da ya qarasa maganar da yake.
Amma me...? Maganar ta ce ta maqale lokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskar sa da kuma shigarsa.
Duk da bataga wannan tsadadden murmushin nasa ba domin kansa a soke yake da alama yana wani abu mai muhimmanci a cikin wayarsa da ya 'kura wa idanu.

Wani irin fitinannen kyau yayi, shadda ce a jikinsa kalar sararin samaniya, ko makaho ya lalubi shaddar yasan an kashe mata maqudan kudi, balle mai idanu da yake ganin komai.

Sumarsa ta kwanta luf, hakama sajensa da yaji gyara kamar yanda larabawa suke, qasa ne da d'an yawa sai saman da ya kasance kadan ya kwanta sosai

Fuskar sa cike da annurin da ya qara bayyana tsantsar kyau da Allah ya bashi.

“Tabarakallah fii ahsanul khaliqin, wa ja‘alahu min ibadika as-salihīn.”
Ta fad'a a ranta kamar yanda Annabi ya umurta idan kaga mutum mafi kyau da tsari.

A ranta tana ci gaba da fadin, "shin wai mutanen da suke gani inada kyau basu ta'ba ganin ya-turab bane, wallahi da mutane zasu ganshi da ba wanda zai qara kallona a matsayin mai kyau, ya-turab Allah ya sa ka more kyawunka........."


Zancen zuciyan ta ne ya maqale lokacin da taji muryar sa ta daki kunnuwanta.
"Ke yarinya ki daina kallona haka mana,,,,,, kin ga d'an kyakkyawa kho, kinaso ki qaremin kyau da wannan kallon naki......!
To Ni fa ban gama aure ba kar kallon nan ya saka kyauna ya qare inje neman aure ace baza'a bani ba......" Ya yi maganar yana dariya.

Taɓe baki tayi zatayi kuka yayi saurin isowa gaban ta "haba dai kyakkyawar ya-turab, dan Allah karkimin asarar ruwan hawayen nan naki masu tsada, taya zan jure ganin irin haka daga gareki. Kiyi hakuri kinji"

Cikin muryar kuka tace "ba kai bane kace baka gama aure ba....!"

"Ke rufamin asiri kinji" wanda yake da ke zaice bai gama aure ba, hmmmmm kiyi hakuri kinji wallahi turab mallakinkine ke kadai in sha Allah, wata bata isa ta sami gurbi a zuciyata ba, turab na kine ke kadai" ya fad'a tare da manna mata Peck saitin d'an qaramin bakinta.

"Har a cikin gidanmu....?" Ta fad'a tana zare idanun

"Har abun da yafi haka zamuyi a cikin gidanku idan kuma kina musu ki sake yin magana ki gani"

Mikewa tayi da sauri ta fita parlourn tana dariya, shikuma ya saita muryarsa yanda zata iya jiyoshi yace "karki manta ku shirya da wuri wallahi motocin na hanya".

Da qarfi ta amsa masa da"tho...." Shikuma ya juya ya fice daga parlorn.

Fitarsa keda wuya Aunty Rafa'at da sauran mutane suka shigo Domin ganin amarya.
A cikin 'yan kwanakin wata shaquwa ce sosai ta shiga tsakanin Aunty Rafa'at da leeyana, Leeyana jin Aunty Rafa'at take kamar yayarta wacce suka fito ciki ɗaya da ita.
Itama Aunty Rafa'at a 'bangaren ta haka ne domin duk abunda mace zata buqata a wurin yayarta ta baiwa leeyana damar hakan.

Zaune a bedroom leeyana ce tana feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi, sai Aunty Rafa'at kuma tana saka kayan su Arfah ta Aamir a trolly.

"Aunty na gayamiki yace ba sai anzo da komai ba fa, yace an tanadi komai a can"

"Ai kayan matarsa kawai ya sani bai san namu ba, sannan kayan nan ba nawa ba ne na Aamir da Arfah ne...., na kammala shiryawa kinga Mutane da dama sun tafi motarmu kawai ta rage, zohal da meenal duk suna parlour tun dazu"

"Nima na gama shirin Aunty muje...." Leeyana ta fad'a tana saka takalma.
Ba wani shiri tayi ba domin komai nata yana can a Abuja hatta kayan da zata saka idan lokacin walimar yayi.

Fita sukayi suka tarar da drivern da zai daukesu yana jiransu.
Suna isowa suka shiga gaba d'aya suka d'au hanya.

Da misalin ƙarfe hudu na yamma aka fara gudanar da waleemar daurin aurensu.

Sosai leeyanah tayi wanka na ji da gani, lifaya aka yafamata malt colour da kuma rigar roba ta ciki mai dogon hannu kalar golden da yafi yawa a cikin lifayar da ta saka.
Fuskar ta kuwa tasha kwalliya mai tsananin kyau da tsari domin bazakace hannune ya zana ba, duk wanda yazo wurin walimar idan yayiwa leeya kallo daya sai ya qara fiye da haka, wasu har ba sa son dauke idanunsu daga kanta.

Hotuna kuma ta sha su babu adadi kamar ba ranar dainawa.
Ummasalima kam abu nasu, darduma, da chazbi da kuma Kur'anai ta raba, a cikin wata jaka madaidaiciya wacce ke dauke da hoton amarya da angonta a kyakkyawan yanayi.

Ita kuma mum da qawayenta kamar su mummy-neesah suka raba turmin atamfa da kuma turaren tsintsiya da robar dabino, suma a cikin jakar su, jakarsu mum ta bambanta da irin wacce ummasalima ta raba, domin tasu mum bata da hoto sabanin tasu ummasalima da ta kasance mai hoto.

Lapia qlw aka kammala taron walima, su mum da wasu tsirarun mutane suka dawo suleja.
Leeyana da Aunty Rafa'at da sauran yaran gidan da suke tare kuwa suka wuce masaukinsu domin kuwa gobe idan Allah ya kaimu jirgin sassafe zasu bi zuwa Greece gudanar da lunch.

Ba yanda turab bai yi ba akan aunty Rafa'at ta barsu su ga juna da leeyanah amma 'kememe ta hana hakan, duk da ya san address din gidan da aka saukesu a abuja hakan bai saka shi ya je ba domin yasan ba bari zatayi yaga matarsa ba tunda har ta gayamasa.

Washe gari kuwa tun ƙarfe bakwai na safe suka dau hanya.
Sai misalin ƙarfe biyar na yamma suka isa babban birnin Greece United State.

Nan ma masaukinsu suka wuce babu 'bata lokaci domin qarfe takwas na dare akeso a fara taron.

Direct wurin da aka tanadarwa leeya domin shiryata suka wuce.
Da kanta ta zabi kalar kayan da take so.
Ba su dauki tsawon dauki ba aka kammala komai, sai Aunty Rafa'at ce takira turab ta sanar masa.
abokan turab dake ƙasar Greece su sukayimasa hidima sosai wajen zirga-zirga da amare domin shima yana can ana gyara shi.

Leeyana tayi kyau sosai fiye da tunanin mai hasasowa, Ni a ganina alqalamin bazai iya fassara muku irin fitinannen kyau da tayi ba, ball gown ta saka fara sol irin wacce turawa suke sakawa idan sukazo shagalin aure.
Fara ce sosai har tana dallare idanu.
Qasan ta ya bude sosai inda aka ru'banya ta tayi wani irin cika daga qasa idan tana tafiya sai kaga tana wani bubbud'ewa kamar rafah, kama kuma fiffike.
Samanta kuma d'an simple ba wani ado sosai bead kawai akayi adon dasu kalar maroon da suka qara fito da rigar ya zama kamar sarqa.
Gashinta kuwa angyara mata shi sosai aka yi packing dinsa tsakiyar kanta, sannan aka saka roberline aka qara kwantarda shi.
Farin net aka yafa mata har ya rufe fuskarta daga gaba, daga bayan ta kuwa ya sauka har qasa yana jaa da qasa idan tana tafiya ko tana tsaye.
Hannuta da yaji kunshi kuma rige take da flowers masu matukar kyau da kamshi abun sai wanda yagani.

Turab ma haka yasha wankansa cikin suit farare tasss kamar yanda nata yake, wankansa ba laifi gskiya. Kana gani kasan an narka nera ba kadan ba.

Haka ma su zohal da sauran families da sukazo sunyi wanka naji da gani abun ma baya misiltuwa.

Haka akayi wannan taron shima aka gama hankali kwance, turawan greece da suka halarta kam sunsha mamakin ganin waɗan nan mutane wai a Nigeria suke.
Ko kusa basu kawo za'a iya samun kalar fatar leeyana a Nigeria ba, shikuma turab sun zata daga Arabian counties yake.

Yauma kamar jiya ana kammala taron aunty Rafa'at ta tusa 'keyarta gaba, turab kamar yayi ihu domin a yanzu kam ya gane tsaff indai ba wurin programme suka had'u da leeya ba baya ganinta yanda yakeso, ko wurin programme ɗin kuma babu time da yawa sakamakon mutane.

Washegari ma haka suka wuce Portugal inda suka gudanar da dinner dinsu cikin aji da wayewa, sosai qasar tuwara ta dauka, baramma Nigeria da kullum suna social media jiran ganin kyakkyawan ango da kyakkyawar amaryasa da ake ta posting kullum duk wani event da akeyi.

Daga Portugal kuma babu 'bata lokacin suka wuce Egypt don su gudanar da taron Arabian nights da za'a yi.

Hmmm abun sai ganin idanu, domin duk taron da akayi a baya bai kamo qafar wannan ba, duba da yanda larabawa, da turawa, da hausawa, da kuma manyan celebrities na fadin duniya suka halarci wannan taro.

Sosai aka darje kudi, turab da abokansa sun saki bakin aljihu kudi kamar nan ake 'kera su, haqiqa duk talakawan da suka halarci taron kakarsu ta yanke saqa domin a cikin mintuna kadan za'a fara lissafinsu a sahun masu dukiya.

Sunsha wanka har ba'a cewa komai, kunsan larabawa da ado,,,,, haka suka zage suka shirya leeya cikin adon farin zinari da jauhari, wallahi ganin farko zaka iya yin rantsuwa da Allah kace daga duniyar aljannu leeya ta fito duba da tsanin kyau da ado wanda ta sha.

Mafi yawa daga wurin sai da suka dinga suma ana tada su idan sukayi tozali da ita.

Tayi kyau sosai kamar watah d'an daren goma sha biyu, haka nan kake ji kamar ka sacheta ka gudu idan ka tsuramata idanu.

Yanzu ma haka an kammala Arabian night kuma kowa ya dawo masaukinsa washe gari zasu koma nigeria gaba daya su sake shirin tafiya spain honeymoon.

Leeya ce kwance kan sofa idanunta a lumshe tana murmushi, zakayi mamaki sosai idan ka kalli fuskar ta wani irin nishadi take fuskar tana kyalli kamar tauraruwa.
Mamakin ka zai tsaya chakkk idan ka lura da yanda take sakin murmushi haqoranta na bayyana ga kuma wayarda ke ma'kale a kunnenta kana gani kasan fira take.

"Please jarumata........! dan Allah kisan yanda zakiyi wallahi na kasa bacci ne ina matuqar son ganinki"

"Kayi haquri T-heart, Wallahi ba yanda za'a yi kuma kaga gobe ne tafiyar mu idan bata bari muka haɗu anan ba ai dole mu haɗu Nigeria"

Cikin kwantarda murya da rarrashi yace "dan Allah..........! My precious kinsan yanda zakiyi ki fito yanzu nan zanzo, koda bamuyi magana in ganki kawai ya wadatar da zuciyata, kinga zan sami peace of mind idan kuma na sami kwanciyar hankali shikenan zan iya yin bacci kinji Please matata"

Yanda yayi maganar ya bata matuqar tausayi yasa tace "to shikenan bara na sanarwa da aunty zakazo yanzu"

"Kinsan bazata bari ba wallahi"

"Hummm zata bari in sha Allah, Nima zan saka baki sosai akan haka, kasan ba kai kadai kake so ka ganni ba. Nima ina so na ganka jarumina"

"Tau shikenan my favorite Dan Allah kiyi qoqari idan ba so kike ki rasa angon ba"

"Rufamin asiri idan na rasaka ai nima rasani za'a yi"

"Tau Bama fata, ki je kinji my gurl"

D'aga masa kai tayi kamar yana ganinta, da wayar a kunnen ta ta wuce ta shiga bedroom inda aunty Rafa'at ke zaune da su zohal, da Aleena, khulud, meenal da badariyyah da kuma su Airah da Aneesa da twins.
'ya'yan aunty Rafa'at Arfah da Aamir kuma suna bacci.
Sukuma suna ta fira wasunsu na shirya kaya, gobe zasu koma nigeria.

Shigowa tayi da sallama a bakinta, cike da nutsuwa ta zauna gaban aunty Rafa'at.
"Amarsu har an gama firar" zohal ta fad'a tana gyara kwanciyarta itama yanzu suka rabu da fahad.

"Ai ke zancewa haka, wai ta wace hanya kika shigo nan. Nidai nasan tare na barku da Fahad?"

Zohal na dariya tace "ta hanyar da ake shigowa mana, ina zaki sani kina nan kina soyewa"

Taɓe baki leeya tayi kawai tana kai dubanta ga Khulud domin yanzu sunfi kusa da Aleena ganin shekarun su zasu zo ɗaya tace "khulud ina Aleena ko sun tafi?"

"Ba su jima da fita ba ai, amma bata kofarnan nan suka bi ba ta waccan hanya suka fita" Khulud ta fad'a tana nuna mata wata hanyar daban.

Aleena tun da sukazo mijinta yake zuwa yana daukar ta idan sun dawo masaukinsu sai ya jira ta idan ta gama fira da 'yan uwanta sannan yazo, kusan wuri daya suke domin da gidan da aunty Rafa'at take da nasu gida biyu ne a tsakani, fahad da zafaran na turab shine ya zama cikon na uku, ba sa da wata tazara mai yawa tsakanin su.

"Aunty ya-turab ne yakeso ya gaida ke ga wayar" cewar leeya tana miqawa Aunty Rafa'at waya.

Cikin sanyin murya yayi mata sallama ta amsa suka ɗan gaisa sannan ya fara rokonta akan buqatarsa.
Da kyar da sudin goshi ya samu ta amince da zuwan, aikuwa kamar jira yake yana ganin ta amince ya zuro jallabiya kawai ya fito.
Da qafa ya karaso gidan domin basuda nisa ko kadan.

Knocking suka fara jiyowa da sauri suka kalli juna suna dariya. Khulud da sautin dariyar ta yafi na kowa tashi da sauri ta gimtse bakinta cikin matuqar tsoro Sakamakon ganinsa da tayi fuskar sa daure tamau da alama ya gane shi sukeyi wa dariya.

Wata gigitacciyar tsawa ya daka musu hatta aunty Rafa'at sai da ta ɗan ji tsoro.
Leeyana kam ta tsorata matuqa domin yanzu ya fito asalin Turab din sa da ta sani a baya wannan mai tsanani da tsakura, mara tausayi, mara sakin fuska, mara sauqi da kuma rashin son raini.
Har saida fuskar sa ta sake dawomata a baya lokacin da ya sami su Airah na rawa a parlor wanchan lokacin.

"Dan uban ku wa kuke yiwa dariya?"

Shiru ba wanda ya amsa sae wata zufa da karkarwar da suke saboda tsoro.

"Ba magana nake ba kun wani zubamin ido kamar baku sanni ba"

Baki na rawa meenal tace "dan Allah ya-turab kayi hakuri wallahi bazamu sake yin irin haka ba"

Ko kallon ta baiyiba sai ma qoqarin qarasawa yake gaban khulud, ya shaqo wuyan ta ya sake dakamata uwar tsawa "bazaki gayamin abunda kk yiwa dariya ba koh, Ni sa'an wasankune da zan shigo wuri kuymin dariya? Ga mahaukaci kho?"

Jijjiga kai kawai Khulud keyi hawaye na faman gudu tanaso tayi magana amma tsoro ya hanata faɗar komai, shikuma wannan ne babban abunda ya tsana wai yana tambayar mutum bazai bashi amsa da baki ba sai da kai.

"Bazakiyi magana ba" ya fad'a a hasale yana shirin kaimata duka, da sauri leeya ta shiga tsakanin su tana kuka sosai.
A rikice ya ajiye khulud ya janye leeyana amma ta turje.

Cikin murya mai bayyanar da tsantsar fushi yace "zo muje...!"

Itama da karfi take magana cikin muryar kuka tace "bazan je ba, ka haɗamu mu duka kayi mana abunda kaso..... Duk wadannan yara da ka gani saboda kai sukazo fa, ai koda wani zai quntata musu bana tunanin akwaika ciki. Nasan idan har zaka iya taba wata a cikinsu akan wannan karamin abu, to nima zaka iya taba Ni, idan har basu chanchanci ragowataba, to nima banason ragowar saboda haka ka barni na zauna a cikinsu ba inda zanje"

Da ido ya jefa musu wani kallo aikuwa da saurinsu har suna hardewa suka fita bedroom din.

Zaunar da ita yayi, sannan ya durqusawa kusa da ita. "Ki gafarceni rankishidade, bada niyya nayi hakan ba, wallahi nima inaso na yakice wannan halin amma na kasa zanyi qoqari naga na zama yanda kikeso kiyi hakuri kinji sarauniyata"

Goge hawayenta tayi sannan ta ce "tom shikenan na hakura amma dan Allah kar ka sake irin haka"

"Bazan sake ba in sha Allah, karki damu kinji"

"To kuma menene na durkusawa" ta fad'a a shagwa'be.

"Kin taɓa gani bawa yayiwa uban gidansa laifi kuma ya bashi hakuri a tsaye ai hakan bazai yiwu ba gskiya"

"To kuma shine bazaka tashi ba"

"Kin ce in tashi ne rankishidade"

Hannu ta saka ta rufe fuskarta tana jin kunyar sa sosai wallahi, wani lokaci ma har bata iya boyemasa haka, shikuma yanaso ta daina kunyarsa shiyasa yake

56 / 61