Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
buqata a wurin zane.
Sai da suka ware kyakkyawan wuri a cikin parlourn sannan suka ajiye kayayyakin.
Zafaran kam wayarsa ya dauka suka fara zagawa lungu da saqo na gidan, video ya fara dauka da wayarsa har suka gama zaga ko'ina.
Dawowa sukayi parlour, Zafaran ya zauna ya fara shirin sa, videon ya kunna ya mayarda hankalinsa cikin kwarewa da fasaha ya fara bin tsarin gidan dallah dallah yana zanawa.
Sun dauki kusan awa daya har da mintuna arba'in zafaran na aikin zanen kafin ya fitar dashi tsafff, babu wani lungu ko wata kwana da take a cikin gidan wacce zafaran bai fitar ba.
Fahad kuwa tunda zanen ya fara fitowa ya tsurawa wuri ɗaya idanu a cikin zanen tsawon lokaci har aka kammala fitar da komai dake wurin.
Murmushin da ya zamo masa kamar dabi'a yayi yayinda yake tsaka da bincike a duk wani aiki da zai yi idan ya hango nasara.
"Na kammala" zafaran ya fada yana qara gyara zaman allon da takardar zanen ke kai.
"Good job mr. Zafaran me ka fahimta a wannan aikin namu"
Tsawon sekonni zafaran shima yana kallon zanen tsappp "babu abunda na gane gaskiya, wallahi da wannan dama an gayawa jami'an bincike na farin kaya".
"Hummm, man zafaran kenan. Kasan me?" Bai jira amsawar zafaran ba yaci gaba da faɗin "Turab fa yana gidan nan!"
Ba zafaran ba!!! hatta su leeyana dake zaune jugum-jugum sai da suka girgiza da jin wannan zancen.
"Taya turab yake zaune gidan nan tsawon kwanaki fahad?"
"Gaskiya ya-Turab baya gidan nan ya-fahad, Wallahi Ni da kaina da kuma mai gadi ba inda Bamu bincika ba a gidan nan ciki da wajensa babu shi babu mafarin sa"
"Akwai inda baku bincika ba leeyanah"
"Ina ne wurin?"
"Bani zanen zafaran" cewar Fahad yana miqawa zafaran hannunsa alamar ya bashi.
Ciro zanen yayi ya miqa masa, shikuma ya mikawa leeya.
"Nanne baku bincika ba" ya fada yana nunawa leeya dan wani guntun gini a cikin zanen kamar Piller, kamar kuma step. A cikin step din an fitarda wata ƴar qaramar shafaffiyar kofa wacce idan mutum bai kula ba ma zai iya rantsuwa bango ne.
"Ya-fahad nan a bangon gefen bedroom ɗina ne"
Ba bango bane muje ki nuna min wurin"
Gaba ta shige su kuma suka rufamata baya, basu tsaya ko'ina ba sai gaban step din.
"Ka gani bango ne fa"
Murmushi kawai yayi yana shafa wallpaper da aka yi ado da ita a wurin.
Daga cikin window bedroom ɗin ta ya saka hannu har can gefe sai da yaji hannunsa ya sauka akan handle.
A hankali ya fara mirdashi har sai da ya buɗe, nan da nan kuwa kofa ta wangale sai ga wani daki ya bayyana daga cikin bangon step din.
A wurin kuma saboda ba'a so aikin yayi two colour ne yasa aka shafe kofar kamar bango sannan aka saka wallpaper kalar bangon dakin gaba daya ya sajeh da ko wane bango.
Daga ciki aka fitarda handle wanda sai ka saka hannunka ta windown bedroom dinda ke kusa da bangon sannan kake iya kamo handle din kofar, idan ka bude kuma kofa ce zata bayyana.
Hakika duk wanda yake rayuwar Turai wannan ba baqon abu bane a wurin sa.
sai dai idan baka sani bane zai zamo baqo a wurin ka.
Sosai mamaki ya kusa kashe duk wanda yake wurin har zafaran da ya riga ya san irin haka, amma bai yi tunanin har Nigeria ana aiki da irin wannan gini ba.
Wata kofa suka ga fahad ya nufa ita ma ya buɗe ta, madaidaicin daki ne da baza'a kirashi babba ba kai tsaye, haka kuma baza'a iya kiran dakin qarami ba domin gado biyu ne a dakin sai set daya na kujeru. Sai wardrobe da kuma toilet gefe.
Shigarsu cikin dakin ya qara tabbatar musu da turab yana ciki domin kuwa da mayen qamshin turarensa suka fara cin karo.
Wani madaidaicin Centre carpet mai taushin gske aka shimfida tsakiyar dakin, babu wata kwalliya ko ado a cikin dakin iya carpet din ne kawai sai kuma mirror.
Shigowa sukayi gaba dayan su, babban abin mamaki kuwa dukansu wuri daya ne suka tsurawa idanu da alama wani abun suke kallo.
Sallayah ce shimfiɗe a gefe sai cazbi da kuma waya dake kan sallayar da alama mamallakin kayan baije nesa ba.
"Masha Allah, kagani ko zafaran na san akwai wani private part a gidan nan, Nima wallahi shekaran jiya na gano irin wurin nan a gidana. Nasan gidajen mu duk iri ɗayane amma wallahi banyi tunanin wuri daya aka ware aka fitarda private part ɗin nan ba, kaga ko a gidana daidai nan aka fitar dashi ba bambanci, shiyasa na buqaci kaimin zane ka fitarda gidan nan naga ko zan iya ganowa a wane bangare akayi dakin cikin ikon Allah kuma munyi nasarar ganowa ba tare da munsha wahala sosai ba, yanzu sai mu jirashi kawai nasan yana toilet" fahad ya faɗa yana zama kan daya daga cikin kujerun da ke dakin.
Zafaran yayi murmushin jin dadi yace "gashinan kam Allah ya bayyana mana shi sai ya zo naci masa mutunci saboda me zai 'buya anan ba ci ba sha, sannan kuma baya ɗaga kiran kowa" cewar zafaran yana qoqarin kai hannunsa ga wayar da ke ajiye a gefe.
Tsugunawar da zai yi ya dauki wayar ne karafff idanunsa suka sauka akan mutum kwance cikin jini, amma jinin ba mai yawa ba iya kansa ne a ciki da kuma wasu sauran sassa na jikinsa.
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, fahad kaga abunda na gani" zafaran ya fad'a yana nuna wurin da yatsarsa cike da tashin hankali.
Da gudu suka isa kofar toilet inda suka hango wani mutum da suka kasa gane waye shi daga nesa. Sai da suka iso gaffff da shine suka fahimci ashe turab ne.
Kamar fahad zai fashe da kuka saboda tsananin tausayi yace"ya subhanallah, zafaran yanzu turab ne ya dawo haka, ɗan gayu mara son kazanta, mutum cike da kyankyami. Yau shine a haka ji yanda gashin kansa ya hargitse, ga sajensa duk ya cika masa fuska, ba wanka, ba wanki. Jin yanda kayan jikinsa suka yi. Fuskar sa duk tayi baqi ta jeme a cikin kwanaki hudu kacal, yanzu da bamu zo ba bamu san iyakar abun da zai faru ba zafaran........" Zafaran yayi saurin katse fahad da faɗin;
"Wallahi fahad turab baya numfashi!"
Cikin Matukar tashin hankali suka rugo gare shi aguje har su leeyana dake gefe.
Sunansa suka fara kira da karfi amma ko yatsunsa bai motsa ba balle su saka ran zai musu magana.
"Fahad don girman Allah a kira mum a sanarmata uwa ce fa. Inada tabbacin yanda baya d'aga kiranmu itama baya d'aga kiranta, gashi yanzu chajin wayar ma ya qare ta dauke saboda yawan kiran da ake yimasa idan ta kira wayar ba samu zatayi ba ji kaga yanda turab dinmu ya dawo" zafaran ya fad'a cike da damuwa.
"Ka kwantarda hankalinka zafaran ni yanzu tsorana kar turab ya rasa ransa a wannan yanayi da yake, kasan yanda za'a yi........?muje da shi asibiti tukunna idan muka kaishi asibiti sai mu kira su mum da papu mu sanarmusu, inaga yanzu ba amfanin saninda zasuyi tunda muma bamusan abunda yake damunsa ba"
Garaff.....!
sukaji qarar rufe kofa, da sauri kowa da yake wurin ya duba.
"Leeyana ce!"
"Fita tayi?
"Wallahi nima bansan fitarta ba, sai bayan ta fita ne naji qarar kofa"
Sosai zafaran da Fahad sukayi qoqarin fitar da turab daga dakin har suka sakashi cikin mota suka tafi dashi asibiti.
Wani Asibitin kudi mafi kusa suka kaishi, cikin ikon Allah kuma suna isa aka karbeshi emergency domin duk wanda yayi tozali da turab dole sai ya tsorata ganin yanda yake ba ya da wani bambanci da gawa.
Sai da suka gama cika ko wace takarda da za'a cika kafin suka kira gida suka sanardasu, cikin mintunan da basu haura hamsin ba su mum da kuma Khulud suka sauka asibitin.
Duk irin karfin halin mum da kuma juriya da Alkunya irin ta tata sai da tayi kuka kamar ranta zai fita ganin halin da turab ya ke ciki.
Bayan mintuna ashirin da zuwansu mum sai ga papu da dad qarami sun iso.
Zaman jira suka fara yi domin tun zuwansu ba wani bayani game da turab, abu kamar wasa har aka shafe Awanni bakwai ba amo ba labari.
Dad qarami kam kamar zai yi hauka, haka kawai yake bala'in son turab, sosai mutane suke jin mamakin wannan iri so da dad qarami ke yimasa saboda duk yanda yakeson ƴaƴansa na cikinsa baikai quarter na son da yake yiwa turab ba. Qaunace kawai da Allah ya sakawa dad qarami tun lokacin da turab ya fado duniya.
Cikin matukar fushi dad qarami yace "Kagani ko justice Khattab, wannan shine babban kuskuren da nake gudu ya faru, Khattab kana sane da cewa ciwon turab ne ya tashi wanda muke matuqar kiyaye faruwar hakan tun yanada shekaru shida a duniya, wallahi idan turab ya rasa ransa bazan taba yafemuku ba daga kai har wannan yarinyar leeyana. Duk yanda akayi ta kasa fahimtarsa ne shiyasa abun ya zauna masa arai. Kuma da take muguwa sai taki sanarwa mutane da ciwon, Wallahil Azeem da tasan irin matsalar da ke tattare da hakan ta bata 'boye mana ba"
Mum kuma hawaye na zuba daga idanunta ta amsawa dad qarami da fadin "baban twins kadaina aibatamin 'ya Wallahi leeyana ba muguwa bace, da ka san irin abubuwan da ya dinga mata a baya da bakaga laifinta ba saboda ta hukunta shi, kuma wannan da tayi shine daidai yanzu zai gane karatun ai, gobe ko cemasa akayi ya wulaqanta wata bazai yiba domin wannan abun daya faru......"
"Dakata dan Allah hajiya fanaya" dad ya katse ta da tsawa ta hanyar daga mata hannu alamar ta tsaya din "d'anki ne fa na cikinki yake halin rayuwa ko mutuwa, amma har kike yaba wata banza wacce itace sanadiyyar fadawar sa halin da yake ciki, lallai. Kiyi abunki wallahi da ba dan a asibitina kika haifi yaron nan ba da na ce ba ke kika haifeshi ba"
"Eh din ka fada mana baban twins, kace bani na haifi turab ba mana, kuma wallahi leeyana ba banza bace a wurina, uwa daya ta haifenu ta raine mu tare da uwarta. Kamar yanda nake jin Khulud haka nake jin leeyanah da turab, wallahi da za'a tona...... soyayyar leeyana tafi yawa a zuciyata bisa ga yaran nan"
"Ba ke kika haifeta ba amma kike jin soyayyarta fiye da yaronda kika haifa da cikinki hummm....... tirrrr da ke wallahi"
"Baban twins kanada bakin da zaka gayamin haka, kai ba d'an d'an uwanka kake yiwa wannan ba, ai kaima yanda kake son d'an d'an uwanka fiye da yaranda ka haifa haka nima nakeson ƴar ƴar uwata fiye da yaranda na haifa. Kaga anyi one one kenan sai dai ace tirrrr damu gaba ɗaya".
"Mum, dad don Allah kudaina wannan gaban duniya.... gaban mu ƴaƴanku kuma. Wallahi wannan abun da kuke shine babban abun kunya domin yanzu ba lokacin yinsa bane. Wannan da kuke yaqi akansa da shine a kwance emergency fiye da awanni takwas. Da wannan cece kucen da kuke da ma ace addu'a kuka yimasa. Idan Mala'ikun karbar addu'a suna kusa kuma shikenan za'a karba, dan Allah ku daina wannan domin ko qananan yara bazasuyi irin abun nan da kuke ba haba dan Allah". Fahad ya faɗa cikin kuka.
Dafa kafadarsa papu yayi yana masa murmushin karfin hali domin shi kadai yasan yanayin da yakeji agame da halin da babban d'ansa mafi soyuwa a ransa yake ciki.
Yace"ka barsu fahad, idan basuyi hankali ba duniya ce zata saka suyi ba sai ance suyi ba, duk akan mutum daya ne ake wannan,.wata qila ma ya barmusu duniyar su huta, wata qila kuma yana shirin barin duniyar ne. domin halin da turab yake ciki ba wanda zai iya saka ransa da zai tashi yayi rayuwa kamar yanda yake dha"
"In sha Allah turab zai tashi papu, kuma yaci gaba da tafiyarda rayuwar sa kamar dha ka saka ran haka"
"Allah ya yarda fahad, Allah yayi muku albarka ya qara hada kanku"
"Ameen" fahad ya faɗa yana qoqarin zama.
Mum da dad ƙarami kuma jikinsu ne yayi sanyi sosai, duk suka fara jin kunyar abunda sukayi.
Sallamar Aleena ce ta rasa wurin ita da zohal da kuma leeyana.
Isowa sukayi suka gaisheda kowa dake wurin, zama Aleena tayi kusa ga dad qarami domin ita shine mahaifinta. Kuma shima yana jinta sosai kamar ƴar da ya haifa da cikinsa.
Ita kuma leeyana ta isa ga mum ta rungume ta tare da fashewa da kuka.
"Mum dan Allah ki yafe min amma wallahi bazan iya zama da....."
Tun kafin ta qarasa mum tace "nasan bazaki iya ba leeyana kiyi hakuri kinji, wallahi idan na isa da shi dole sai ya sauwaqe miki kije ki auri wanda kikeso kema kiyi rayuwar ƴanci ,kwantar da hankalin ki idan har turab ya tashi an gama komai" mum ta fad'a idanunta na cikowa da ƙwallah.
Dalili kuwa shine ta gayawa leeyana hakanne kawai ba dan tana da tabbacin zata iya saka turab ya sauwaqe mata ba, a iya qin yarda dashi da tayi ya sakashi wannan ciwon.
idan aka sakashi ya saketa kuma wane hali sukeda tabbacin zai faɗa.
Duk firar da suke ba wanda bai ji su ba kuma ba wanda bai ji kalaman da leeya ke fadi ba, haka zalika ba wanda bai ji abunda mum ta faɗa ba.
Sosai mamakin leeya ya kashesu, musamman ma zohal da taga sauyawar leeyana lokaci ɗaya. Wanda ba a haka suka fito gida ba, tana ganin tsantsar butulci a cikin kwayar idon leeyana.
Leeyana kuma cikin wani irin yanayi da suka kasa bambance farin ciki take ko bakin ciki ta buɗi baki zatayi magana. Sai ga likita ya karaso inda suke ba alamar fara'a a fuskar sa ko kaɗan yace "su waye suka kawo Turab k. waasib?"
"Gamu nan" su fahad suka faɗa da sauri gaba dayansu duk suka miqe.
"Ok good, Ina mahaifinsa?" Likitan ya kuma tambaya.
"Gani nan" dad qarami ya fad'a yana qarasowa gaban likitan.
"Dr. Mahad Barka da aiki, nine mahaifin turab. Koda muka iso kuna ciki da shi Allah yasa abun da sauqi, Saboda naga an dauki lokaci sosai" cewar dad qarami yana miqawa wanda ya kira da Dr. Mahad hannu.
'Dan sake fuska mutumin yayi shima ya miqa masa hannunsa sukayi musabaha yace "Dr gahees WAASIB ashe yaron ɗan mu ne kho ?"
"Eh wallahi Dr. Ai nayi tunanin bazaka iya tuna ni ba domin anjima ba'a haɗu ba"
"Haba dai, aikuwa babu abunda ka qara wanda ban sani ba ajikinka dr. Gahees, amma meyasa kuka bar yaron nan har ciwon nan yaci qarfinsa. Wallahi da ba'a yi gaggawan kawoshi asibiti ba da zai iya rasa ransa cikin mintuna talatin a wannan lokaci. Shin me kuka yimasa da zafi haka. Yanzu haka zuciyar sa ta kumbura sosai. Kuma ya zubarda jina. Sannan kuma hanyar da ke sada iska daga waje zuwa cikin hancinsa su fitarda numfashi ta toshe Saboda qaba da kumbura da zuciyarsa tayi. Ina tabbatar muku da yaronku bazai iya numfashi da kansa ba a yanzu. Sannan tunda muka shiga dashi emergency bai motsa ko yatsarsa ba balle yayi motsi. Munyi iyakar qoqarin mu amma abun yaso ya gagaremu. Akwai wata allura da akeyiwa masu irin ciwonsa a lokacin da suka kai limit din nan na halin rayuwa ko mutuwa cikin sekonni. Kuma munyi masa ita awa daya da rabi alurar take dauka zuwa qasa, bata haura haka face mutum bayada rayuwa gaba ɗaya. Amma idan akayi Sa'a cikin mintuna biyu ko uku allurar zata farkarda mara lafiya. Wani kuma mintuna talatin, wani awa daya, kai wani zata iya tayardashi a minti daya kacal. Wani kuma sai awa daya da mintuna talatin. Amma daga zarar ya haura hakan mutum bai motsa ba to he's no More! Ya mutu kenan kuma mun gwada wannan allurar ga danka turab"
"Dr Yanzu turab ya mutu kenan!!?" Mum ta tambaya cikin matukar tashin hankali.
Kamar yanda tayi haka dad qarami yayi shima, saidai nashi bai kai nata ba domin kuwa shi namiji ne sannan kuma babban Dr. Bazai yanke hukunci batare da yaji abunda likitan zai fadi ba.
"Dr. Da aka gwada allurar wane sakamako ta bada" cewar papu.
"Yawwa Alhaji, gaskiya sai dai mu godewa Allah domin kuwa da akayimasa allurar mintuna shida kawai ya dauka ta fara masa aiki kuma ya farfaɗo. A yanzu haka munyi masa allurorin da zasu saka zuciyarsa ta daidaita kuma ta sache da kumbura da tayi. Amma fa har yanzu baya iya controlling numfashin sa sai da muka saka masa oxygen. Sannan muka daura masa drip da zai hana shigar zazzaɓi bayan wannan, har kuma ya sami bacci.
Saboda haka yanzu zaku iya shiga ku ganshi"
Jikinsu duk yayi sanyi da jin halin da turab yake, wai turab. Wannan shine abunda yake faman yawo a kanunsu, ko a mafarki basu taɓa tunanin turab zai iya fadawa wannan hali ba hummm rayuwa kenan.
Da sallama dauke a bakin wasu daga cikinsu suka shiga dakin, ganinsu kuma ya saka sauran likitocin da ke kansa suka fita suka basu wuri.
Ga wurin zama amma ba wanda yayi yunkurin zaunawa ganin yanda turab ya ke. Jikinsa har wani yellow yayi saboda tsanin jigata da yayi.
Leeyana kam zamanta tayi har da dora kafa daya akan daya, haqiqa leeyana ta sauya daga kawo Turab asibiti zuwa yanzu, domin lokacin da ya 'bata ba'a ganshiba kullum cikin damuwa da tunani take, amma kuma a yanzu sai saɓanin hakan take nunawa.
Sun jima tsaye akansa mai addu'a yanayi, mai zubarmasa da ƙwallah nayi.
A hankali ya fara bude idanunsa yana kallon kowa, ba wanda ya kula da ya buɗe idanunsa sai ita! Kuma idanunsa na haduwa da nata ta masa wani irin kallo da ya saka shi zabura kamar zai fado daga kan gadon.
Hakan ne ya mayarda hankalinsu gareshi. Ganin ya farka ya saka dad qarami zuwa wurinsa da azama.
Ya jiki ya fara masa, shikuma yana daga masa kansa alamar yaji sauki.
Zafaran da fahad ne suka qaraso gareshi, zafaran kamar mace tuni kuka ya kwace masa yana shafa kan abokin nasa.
Ganin haka ya saka turab ya lumshe idanunsa sannan ya juya kansa gefe ya daina kallon gefen da zafaran yake.
"Nagane abokina, bakaso ina kuka ko to kayi hakuri ka juyo garemu na daina kukan kaji" zafaran ya fad'a still hawaye na tsiyayo wa daga idanunsa, shima ya fadi hakan ne kawai saboda turab din ya juyo.
Shi kuma turab da yaji abunda zafaran yace a hankali Cikin rashin kwarin jiki ya mayarda fuskarsa wajen su yana qara matse hannun zafaran da fahad