BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   59 / 61

174K to 177K   out of 180.4K words

[{BAYAN WATANNI UKU}]
*SPAIN*~~~~
_____Kwance take ta kanannad'e a cikin blanket, tunda zai je sallah yake tada ita amma ta kasa tashi. Yasan mafi yawan lokuta idan tana period haka take a maimakon ta bud'e baki ta gayamasa cewar bata sallah.

Fita yayi daga bedroom din ya nufi prayer-room, ya dade sosai yana yimusu addu'ar qara samun farin ciki da zaman lafiya mai dorewa kafin ya dawo bedroom din da ya barta.

Da mamaki yake bin ko'ina da kallo, shi dai yasani idan tayi irin haka, ya tabbatar koda zai dawo sallah zai tarar ta tsaftace jikinta, sannan ta gyara ko'ina a duk ɓangaren da suka kwana a gidan.

A mamakinsa sai ya tarar tana nan yanda ya barta.

Cikin sanyin murya irin tashi yake kiranta "wife ki tashi gari ya soma wayewa kinji, nasan kina period ne kho...? Toh nagane.
ki daina jin kunya ki tashi ki tsaftace jikinki ki dawo kici gaba da kwanciyarki, zankira su sholeen su gyara komai in yaso muje wani bangare ki kwanta ki huta.
Bata d'ago ba, haka zalika ko motsi baiga alamar tayi ba.

Bubbuga gadon ya fara yi tun yanayi a sannu har ya fara bugawa da qarfi amma ko kezau batayiba, babu kuma wata alama da ta nuna taji bugun da yake.

Bargon ya d'aga yana kiran sunan ta "wife wai meye haka ki tashi mana" ya fad'a lokacin da yake yaye bargon daga fuskar ta.
Da mugun sauri ya d'aga bargon gaba ɗaya, hankalin sa a masifar tashe ganin yanda take.

kwance take ta kanannad'e jikinta wuri ɗaya sai karkarwa take haqoranta na sama na karo da na qasa.

A hankali ta dago idanunta da sukayi jajir saboda tsananin ciwo tace "ka gafarceni hub,,,, ban gayamaka ba wallahi kwanaki biyar kenan yau shine na shida ina fama da zazzabin nan, banyi niyar gayamaka ba nasan xakace sai munje asibiti, nikuma a duniya babu inda na qie jinin zuwa kamar asibiti shiyasa nayi shiru ban gayamaka ba.
a zatona zan sami sauki da magungunan da nake sha. Amma yanzu inajin ciwon nan yaci qarfina da yawa"

A fusace ya hau kan gadon ya ɗora kanta akan cinyarsa ya fara magana Cikin tsawa "ke wace irin mace ce haka leeyana, me yasa kike qoqarin yimin wasa da ranki da kuma lafiyar ki, duk da bakya buqatar zuwa asibiti ya kyautu ki zauna da ciwo a jikinki. Wannan shine abunda bazai taɓa yuwa ba saboda haka ki tashi muje na shiryaki yanzu mu tafi hospital.

Idanu ta zazzaro.

ganin bai bata damar musawa ba ta gimtse bakinta.
Cikin azama ya kinkimeta sai toilet, a hankali ya sakata a koman wanka, shiya yimata wanka da kansa ya shiryata cikin wata doguwar riga mara nauyi, ko kadan rigar bata kama jikinta ba rigar ta zauna sosai yanda bazata takura mata ba.

Ɗaukar ta yayi da kansa ya sakata a mota ya kira driver yazo ya tuqasu, shikuma ya zauna back sit yana tallafe da ita.

Wata tsadaddiyar asibiti suka nufa wacce turawan koria suka bud'e ta, kuma kafff Birnin Spain itace babbar asibitin Kudi da aka fi sani lungu da saqo.

Tun a gate na hospital din aka fara tarbar su, hannu bibbiyu aka karb'esu bayan shigarsu ciki.

Wani qaramin gado aka kwantar da ita aka saka wasu labule aka killaceta kafin a kammala cika mata Form, wannan yana daga cikin wani abun birgewa da Asibitin ke yi.

Basu dauki lokaci ba aka kammala komai kafin aka shiga da ita inda zasuga doctor.
Tare suka shiga da turab ya zauna kusa da ita a kan wasu kujeru biyu da suke fuskantar likita.

Cikin nutsuwa likitan ya fara tamabayarta da harshen turanci domin basa jin hausa ko kaɗan.

"Me kike ji a jikinki, ma'ana menene abunda yake damunki wane yanayi kikeji.......?"

Itama cikin harshen turanci ta fara masa bayanin abunda ke damunta tsawon kwanaki biyar.

"Inajin ciwon kai mai tsanani, ina yawan jin qishi, kuma ina yawan ganin juwa wani lokacin ma sai na dafa bango nake iya yin tafiya"

"Okay, kina yawan jin yunwa"

"A'a" ta bashi amsa a ta'kaice.

"Kinajin d'and'ano idan kika ci abinci"

Jijjiga masa kai tayi alamar bata ji "ko kaɗan banajin dandanon komai ruwa kawai nakesha naji dad'i"

Rufe file din da ke gabansa yayi bayan ta qarashe maganar.

Wani belt ya d'an kad'a nan da nan sai ga wasu nurses mata biyu sun shigo office din.

'dayar ta janyo kujera mai kamar gado ta ajiye gaban leeya, d'ayar kuma tana murmushi tace "madam ki hau nan yanzu zamu dawo mintuna goma".

Zama tayi kan gadon suka bi ta wata kofar daban suka faɗa wani daki.

Turab kam sanin yanda tsarin manyan asibitocin suke ya saka yayi gum da bakinsa yana jiran sakamako.

Cikin mintuna goma kuwa basu dad'a ba suka dawo, nurses d'aya ce ta fara shigowa da takardu a hannunta ta ajiye gaban doctor sannan ta juya inda ta fito.

Hannu likitan ya miqa masa yana murmushi haɗe da takardun da nurse din ta shigo dasu.

"Congratulations sir-turab, amarya tana dauke da juna biyu tsawon sati takwas"

Wani irin wuntsilowa yayi daga kan kujerar da yake zaune, hakan kuma yayi daidai da shigowar leeya da kuma nurses din da ta fita dasu amma a wannan karon kam ba bisa gado suka dawo ba da qafafunta take.

Da sauri ya rungume ta tsamm kamar wani zai kwacemasa ita.

"You are pregnant my wife, Allah yayi miki albarka, ina matuqar sonki da qaunarki, Allah ya nunamin ranarda zaki haifi wannan cikin lafiya matata, Allah ya baki lafiya. Alhmdullillah ya Allah"

Ya fad'a ƙwallah na taruwa a idanunsa har ya kasa kwatanta irin farin cikinda yake ciki a wannan lokaci.

Likita da kuma nurses kam kallonsu kawai suke cike da sha'awa domin basa jin komai da yake fadi sakamakon da hausa yake magana.

Dawo da hankalinsa yayi ga likitan bayana ya zaunarda leeya akan kujera.

Bayani likitan ya masa da yanda ya kamata a kula da ita da kuma irin abincin da ya kamata ta dinga ci da wanda bai kamata ta ci ba a ka'idance.

Cike da farin ciki suka koma gida turab kam hatta drivern da ya daukoshi sai da ya gayamasa wannan abun farinciki, ai kuwa kamar jira yake ya koma gida ya fara kiran mutane yana sanar musu.

Leeya kam duk kunya ta kamata tana qara godewa Allah da yasa ba Nigeria suke ba da rufe kanta zatayi a d'aki.

Mum ya kira ko kunya babu ya sanarmata, mum ta gayamasa ai tuni aka kirata aka gayamata. Yayi mamaki sosai amma mamakin nasa ya ragu tunawa da yayi ya sanarwa mutane da yawa kafin mum.
Anan kuma ya sami labarin ai 'yan uwan nasa duk basa nigeria, zafaran da Aleena suna Mexico amma kuma 'yan uwan zafaran din sun nemi ya dawo taraba, idan cikin Aleena ya isa haihuwa nan suke so su ajiyeta har sai ta haihu sannan su rad'a wa yaro suna, idan anyi suna kuma sai 'yan uwanta suzo su dauketa sai anyi kwana arba'in sannan a mayarda ita gidan mijinta haka al'adar su take.

Lokacin da turab ya gama jin zanjen mum yayi ajiyar numfashi sannan yace "ikon Allah, mum kowa da irin nasa amma ina na taɓa ganin anyi irin haka"

Mum ta bashi amsa da faɗin "kasan kowace qabila tana da al'ada irin ta ta, to su kuma waɗan nan wannan shine al'adar su tunda har suka gayamana. Yanzu dai suna Mexico kuma nasan idan lokacin haihuwar yayi dole zasu koma chan taraba"

"Mum kuma naji kince wai sai an rad'a wa yaro suna"

"Eh sunan da sukeso su dinga kiran yaron, sunada damarda zasuyi haka ai, sannan kuma muma zamu sakawa yaro sunanda mukeso. Idan suka tashi su dinga kiransa yanda suke so, muma mu kirasa yanda muka saka masa"

Cike da al'ajabi turab yace "shikenan mum, Allah ya sauke su lafiya, shima fahad ya gayamin sun je India. Kuma ya gayamin wata mai fita ne watan zohal. Ina tunanin shima bazai dawo ba sai ta sauka"

"Saboda me?...." Mum ta tambaya da mamaki ganin yanda familyn zohal din suketa shirye-shiryen bikin ta idan ta haihu.

"yana so su sami kwararrun likitocin karɓar haihuwa basai ta wahala da yawa ba. idan ta sauka Lafiya ko kwana ɗaya bazasu qara ba zasu biyo flight su dawo"

"Ikon Allah, yaran nan kunada abun mamaki, da alama dai kaima irin haka kake so kayi"

"Eh wallahi mum kamar kinsan abunda yake raina kenan"

"To bara kaji, wallahi mamanta ummasalima bazata yarda ba, ko Aleena ma da kyar da sudin goshi aka samu tayarda shima dan yana al'adar su ne, saboda haka ka fitarda ranka tun wuri"

"Naji, dama ban saka raina duka-duka ba, amma fa anan zamu yi rainon cikin sai idan ta shigo watanta sannan zamu dawo"

"Ko ma dai menene idan ba so kake ta biyoku spain ba"

"Bama zata biyomu ba mum zamu dawo, kedai kice kina kewar d'iyarki ne kuma bakyaso ki fad'a"

Haka suka ci gaba da fira cikin raha har ya bawa leeya waya sukayi waya da mum sosai duk da suna yin wayar lokaci zuwa lokaci.



_______*A bangare d'aya kuwa.
Sayyid ya tsaya sosai ganin rayuwar id da mahaifiyar sa tatafi daidai.

Inda ya dage sosai ya saka mahaifinsa ya basu gida, wani Makeken gida mai martaba sarkin suleja Muhammad Safwan al'adal ya bawa mahaifiyar turab. Sannan ya ginawa turab qatoton mall da babu kamarsa.

Shikuma sayyid ya gina musu gida iri daya kuma a unguwa ɗaya, babu abunda ya bambanta gidajensu.
Kuma ya saka mai martaba ya nema musu aure. Aka saka bikin nasu lokaci guda nan da shekara daya mai zuwa.
Dalili kuwa shine zasuje aikin hajji sannan kuma sayyid zai wuce jidder ya wakilci mahaifinsa wani taron gaggawa da za'a yi kuma taron zai dauki tsawon watanni shida shiyasa aka saka auren a shekara ɗaya.

Da reemah rabil akayi engaging din sayyid shikuma id da Khulud, kuma sosai suke qaunar junansu.



*****
Bayan wasu kwanaki.


SPAIN.

Zaune take kan cinyarsa hannunsa riqe da rubber bowl yana bata abinci a baki.

Ruwa ta d'akko zata sha da sauri ya ajiye bowl din ya d'akko ya bata.

Cikinta ya girma sosai sai da kyar take iya tsugunawa. Kuma idan ta zauna bata iya tayarda kanta daga zaunen.

"Inaso na kwanta" ta fad'a tana murmushi.

"Muje na rakaki tho, cikin nan kam yana wahalar min da babynah Allah dai ya rabaku lafiya"

"Ameen honey, amma ba dai baby ba sai dai maman baby kho"

"A'a ni a wurina har yanzu baby ce"

"Wallahi dear cikin nan yana bani tsoro ji girmansa fa....... kuma har yanzu akwai watanni biyu gaba"

"May be basamude zaki haifa ma na, ko kuma mai qarfi sosai kamar jarumi hantaru"

Kwa'be fuskarta tayi sosai.........! mai neman kuka an jefe shi da kashin tumaki.

"Ɗan Allah kiyi hakuri karkimin kuka wasa nake ba kamar jarumi hantaru zaki haifa ba ai"

Kukan ta saki a shagwa'be tana faɗin "ai gwara jarumi hantaru da basamude menene ma basamude irin mutanen nan masu tsawo kho...?"

Daga Mata kai yayi yana gimtse dariyarsa sanin yanda takeji idan aka ce ɗan ta babba ne ko kuma dogo a cewar ta sai ta wahala wajen yin naquda.

"Eh masu tsawon nan ne samudawa mana....... sosai fa, inagayaki shi basamude ko qaramar yatsar qafarsa ta fimu tsawo mu duka biyu idan aka hada"

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, amma Lallai ya-turab bakada tausayi wallahi, shine kuma kake cewa na haifi basamude. Allah ya kiyayeni wallahi"

Yana shirin magana yaji qarar wayarsa dake hannun leeya alamar kiransa ake.

Miqamasa wayar tayi ba tare da ta duba mai kiran ba.

Cike da farin ciki yayi accepting Call.


"Alhmdullillah" ya faɗa bayan yayi sallama an amsa masa bayyannen farin cike ne cike da fuskarsa ya kuma faɗin "masha Allah, me aka samu.........! Allah ta'alah ya raya mana akan sunnah,,,,,,,,,,tho Allah ya kaimu muma zamuzo ayi biki damu in sha Allah..........., ba wasa ba zamuzo wallahi gudan bestinmu ta haihu kuma muqi attending suna, Ameeen ya rabbi" turab ya fada yana fadada murmushin fuskar sa zuwa dariya bayan ya katse wayar......................✍🏼




























Ep.50_END.....🥳🥳🥳







________________da murmushin da bai gama gushewa daga kan fuskarsa ba ya kalleta da faɗin "gskiya sai kin bani tukuici kafin na gayamiki wannan daddad'an labari"

Ita kam tunzuro baki tayi.......! shi har ya manta da abunda tace masa. Bacci fa tace tana ji, har zai tsaya wani shiririta, alhali yasan tana jimawa baccin bai zo ba.......

Shine yanzu ta samu yazo shine yakeso ya koreshi.




"Wallahi idan na haihu bacci zan yi har sai an manta dani tunda wannan Babban cikin ne yake hanani bacci"

"Ohh sorry my princess ai zakiyi bacci sai ma kin gaji wallahi, kuma ba wanda zan bari ya tadaki har sai kin gaji kin tashi da kanki....., yanzu dai kibani tukuici na gayamiki abunda nakeson gayamiki"

Cikinta ta kalla tana shafawa tace
"na baka tukuici wannan....!"

"Wannan ai nawane tun tuni ma,,,,,,bani wani abun"

"Na baka wannan........" Ta fad'a tana nuna masa ɗan mitsitsin bakinta.

Dariya yayi sosai ya d'an ja bakin yace "na karɓa"

"To gayamin.....!"

"Zohal ta haihu fa yanzu nan fahad ya kirani ya sanardani ta sami 'yarta mace mai kamada ke"

"Whattt......!!!!, bestie....." ta fad'a kamar zata kifa Saboda batada wani nauyi duk cikin ya karɓe komai.

"A hankali dai madam kar ki min asara" cewar sa yana tallafo ta jikinsa.

"Hub....Dan Allah mu koma Nigeria yau, can't wait to see my bestie with our precious baby gurl"

"Yaushe zamu tafi Nigeria tho"

"Yau mana babe..." Ta fad'a cikin shagwa'ba

"Uhmm lallai kho, to suma su zohal din basa nigeria suna India sai nan da kwanaki biyu, nima ina tunanin komawarku a kwana na uku. Idan akayi biki damu sai mu dawo nan"

"Muyi me anan ya-turab"

"Ki haihu mana"

"Tabbb wallahi bazan iya ba, nifa idan na koma Yanzu ba abunda zai mayardani idan ba haihuwa nayi ba, Ni kunya ma nakeji ana ganina da wannan tulelen ciki"

Dariya mai sauti ya kece da ita yana qara jin soyayyar matarsa na ratsa jini da 'bargonsa.

"Yanda kikeso haka za'a yi mai girma da daraja a fadar turab"

Dariyar jin dadi tayi kafin tace"muje mu fara shirin tafiya kho, ai baccin ma ya tafi"

"Inahhh.......! Ai baki isa ba wallahi sai munje kinyi"

Rigima ta saka masa akan bazatayiba da kyar ya samu tayi baccin.

Kwanan su biyu a haka, leeya kam kullum tana qara narkewa turab dinta shikuma sai faman biyemata yake, washegari ya kama laraba kuma a sannan ne suka shirya tafiya.

Tun a daren yau ya shirya musu komai na tafiya da kuma sauran abubuwan da zasu buqata na haihuwa.

kama daga kayan babies da kuma ita kanta wadanda basa tunanin a samesu a Nigeria.

Tashin hankalin daya shine yanda zasu je gida Nigeria da leeya a haka, shi wallahi yana matuqar tausayinta yanda cikin nan ke wahalar da ita, idan ta jima zaune qafafunta su kumbura suntul, dha ɗin daɗawa kuma idan ta jima zaune bazata iya tashi da kanta ba har sai an tallafamata saboda nauyin cikin.

A kan cinyoyinsa ta kwana a cewarta bazasu yi bacci ba kar suyi missing morning flight din da zai tashi karfe 7:45am agogonsu na can. Domin morning flight ne kawai zasubi su isa gida da wuri.


Shine tace bazasu yi bacci ba suna nan zaune har sai lokacin tafiya yayi karsu makara.

Amma gashinan a zaune wasai ba bacci, ita kuwa fara baccin ta zuwa yanzu taci mintuna fiye da arba'in.

Dariya yayi yana shafa sumar kanta mai tsananin taushi da qamshi, wacce ta bajeta a kan cinyoyinsa.

Magana ya fara mata a hankali cikin kunnuwanta "qalbie kinga kho, da wannan baccin naki kin saka munyi missing flights.....Tho kici gaba da baccinki tunda haka Allah ya qaddara ba yau zamuyi tafiyar ba"

Yanayin yanda ta miqe zaune yasan da ace ita kadaice abun sai yafi haka, kafin ta gama tantance gaskiyarsa tuni idanunta sun kad'a sunyi jajir da kwanciyar ƙwallah a cikinsu.

"Meyasa baka tasheni ba ya-Turab, wallahi na saka rai da tafiyarmu yau....! Har mafarki ma nayi mun tafi wallahi, Saboda me zaka barni ina yita bacci dan Allah. nidai baka min adalci ba gaskiya" ta fad'a har wata rawa muryarta keyi.

Wayarsa ya nuna mata "qarfe biyar da kwata fa wasa nake miki garin ma bai idarda wayewa ba na miki haka ne kawai dan ki tashi muyi sallah idan mun idar mu fara shirin tafiya"

Miqewa tayi da kyar ya taimaka mata suka shiga toilet tayi wanka tare da alwala, shima wankan yayi ya d'auro alwala sannan suka dawo bedroom.

Kaya ya saka mata sannan ya zuro jallabiya ya tayarda sallah. Sosai sukayi Addu'oi bayan kammala sallarsu.

"Ki kwanta ki huta kinji, Bara naje na fitar mana da kayayyakin mu sannan muyi breakfast"

Wani lallausan murmushi ta sakarmasa tana gyada kai, har ya juya zai tafi ta kira sunansa.

"Ya-turab....!"

"Na'am" ya amsa mata da mamaki jin yanda ta kira sunansa da kuzari.

"Ina sonka yayanah, dan Allah karka barni kaji Please, wallahi ina matukar kaunar ka, qauna irin wacce ban taɓa yiwa wani hallita makamanciyarta ba bayan mahaifana da Yar uwata sai kuma kai mijinah, qauna da soyayyarka daban suke a zuciyata, dan Allah kar ka manta dani da irin soyayya ta a gareka ko bayan babu ni"

Sosai maganar ta tayi tasiri a zuciyarsa, cike da sanyi jiki ya dawo har kan bed din da take kwance ya shafa gefen fuskar ta.

Ance sumbata a koshi tana nufin alqawari mai girma da babu abunda zai iya karyashi face wanda ya aikata ya cika alqawarin.

Irin haka ce ta faru da leeya da kuma turab, kafin ya furta komai sai da ya sumbaceta a goshi sau biyu sannan ya fara magana.

"Dan Allah qalbie ki daina irin wannan zantuka, taya zakiyi tunanin ni turab zan iya rabuwa dake kuma inada rai da lafiya, wallahi ko kusa haka bazata taɓa faruwa ba,,,,! ko a cikin mafarki naga haka wallahi da gudun jirgi zan qaryata domin nasan ba gskiya bane.
Kuma bazan mata dake ba, ba kuma zaki mutu ba in Sha Allah muna tare, kuma tare zamuga tsufa in Allah ya yarda.
Ina sonki irin sosai din nan more than words can describe....!"

Lumshe idanunta tayi har ga Allah taji dadin kalamansa, har ta kasa samun kalma ɗaya tak da zata gayamasa da ita domin shima ta sakashi farin ciki kamar yanda ya sakata.

"Ki yi bacci kin ji, amma fa na mintuna talatin kawai, suna cika zan ta da ke mu tafi"

Rufe idanunta tayi kamar yanda yayi fatar gani sai kuwa baccin gskiya yazo.











NIGERIA.
K.WAASIB MANSION.

Sosai aka shirya komai na tarbar su, musamman mum da ta qagu taga 'yarta.

Komai an shirya mata na haihuwa ita da qanwarta duk

59 / 61