BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   3 / 61

6K to 9K   out of 180.4K words

budurwa kukan me kikeyi kefa budurwa ce ki daina kuka kar leeyana tayi miki dariya kinji, ammin ki zata tashi kuma in Allah ya yarda bazata dokeki ba, kantane yake ciwo shiyasa kika ganta kwance a nan. kuma yanzu da anyimata allura zamu je gida da ita kinji budurwar amminta"

Abbie yayi maganar yana shafa bayan Aleena, shima badomin ransa na yimasa daɗi ba kawai dai dauriya yakeyi domin hankalin yayansa ya kwanta. leeya kuma na zaune kusa da Ammi tana cigaba da hawaye, shigowar doctor tauƙir fawizz ce ta katse komai hankalin su duk yadawo kansa.

Isowa yayi a gaban Abbi sannan ya miƙa masa guntuwar takarda mai dauke da sunan allurorin da ake buƙata

"Hamraz waɗan nan sune allurorin da muke buƙata kuma gashi babu su a hospital ɗin nan saidai idan ka fita cj Chemist, anan bayan layin kaɗan"

Da "tohh" Abbi ya amsa shi kafin ya juya wurin ammi ya kalleta kaɗan sannan ya juya ya fita.
Bai ɗauki lokaci ba ya dawo da allurorin, cikin Sa'a kuwa koda ya dawo ya tarar ammi ta buɗe idanunta, amma tanata haki kamar wacce tayi tseren gudu. Da sauri Abbi ya iso wurin ya dafata sannan yace "yajikin naki faheema?"
"naji sauki" ta faɗa da kyar tana hade kalmomin kamar mai koyon magana.

'"Tau Allah ya ƙara sauqi"

"Ameen" tafaɗa tana miƙewa kaɗan zata jikina da ginin ɗakin. cikin hanzari abbi ya isa ya tallafa mata ta jingine bayanta sai sannu yake jeramata. Juya yayi zai fita ɗakin domin ya kaiwa doctor tauƙir fawizz allurorin da ya siyo.

sai yaji ammi ta kirashi da sunansa na asuli wanda rabon data kirashi da irin wannan sunan aƙalla yakai shekaru ashirin harda dadi.
Juyowa abbi yayi fuskar sa fal da mamaki yayin da su leeya ke chan rakuɓe gefe daya.

Sai yanzu hankalin su yaɗan kwanta tunda sukaga ammin su ta buɗe idanun ta, kuma har tayi Magana.

Karasowa yayi kusa da ita ya zauna yana fuskantar ta,
Domin a yanda yaga takira sunansa yasan ba magana bace ƙarama, kuma yasan tanada muhimmanci sosai tunda yaga haka.

"Hamraz dan Allah wata alfarma nake nema a wajenka, nasan abune mai matuƙar wuya. Amma kayi kodan yayan mu hamraz.
wallahi har ga Allah banajin zantashi daga jinyar nan, kuma sau da yawa Allah yana nunawa bawa alamomin haka, Nima inajin alamar bazan tashi daga jinyar nan ba"

Ammi ta faɗa da kyar tana tari a hankali, sai da tarin ya ɗan saketa sannan taci gaba da faɗi "kayiwa Allah hamraz ka taimaka min kadubi alƙawuranda mukayi a tsakanin mu kaduba girman soyayyar mu hamraz kasada leeyana da Aleena ga mahaifana.
Hamraz ka nema min gafara wurin mahaifina!! kuma dan Allah na roƙeƙa kacigaba da kula da leeyana itama,
kada kabarta ta bayyana fuskar ta ko ta cire wannan mayafin a har sai lokacin da muka ɗiba ya cika, kasan komai, kasan itama da kanta zata iya cutar da kanta idan ba Wannan mayafin a fuskar ta.
kuma dan Allah hamraz alfarma ta ƙarshe danake nema kayi min shine kasada yayan mu da iyayena da kuma yar uwata ina ƙara jaddada maka wannan maganar ne saboda karka manta, hamraz ka nema min gafarar iyayena ta faɗa da mugun karfi har sai da su Leeya suka ƙaraso wurin da sauri. Idanun ta sunyi jaaa sosai kamar gauta ta kalli gefen da yaranta suke ta ɗaga hannu da kyar tana murmushin karfin hali tace "budurwa Allah ya muku albarka ya hada fuskokin mu a aljanar sa maɗaukaki, leeyana ki kula da............."

bata ƙarasa faɗar abunda take niyyar faɗaba wani wahalallen tari ya turniƙeta, numfashin ta na fita da wani irin ƙarfi.

da sauri abbi yayo kanta yana dafata tare da kiran sunanta,
zumbur ya miƙe aguje ya fita waje.

fitarsa wajen keda wuya yayi karo da doctor tauƙir fawizz.
Riƙoshi doctor yayi da sauri domin yaga kamar ba'a hayyacinsa yakeba ''hamraz ince dai lafiya na ganka haka a ƙiɗime meyafaru?"

cikin wani irin yanayi Abbi ke nuna ƙofar ɗakin tare da janyo hannun doctor tauƙir fawizz ya ƙasa furta komai, da azama ya biyemasa suka shiga ɗakin.
Hatta doctor tauƙir ya tsorata da yanayin ammi kafin ya isa gare ta ya fara aunata,
kiran sauran nurses yayi tare dayiwa Abbi da yaransa iznin da su bashi waje ya dubata.

leeya kam tunda taga ammi a wannan yanayi take kuka har yanzu yayinda hawayen aleena suka ƙafe kafff, kuka kawai takeyi ba hawaye abun tausayi.

janyesu Abbi yayi daga ɗakin ya fita dasu waje sai addu'a yake a fili da ɓoye yana ƙiyasta irin rayuwar da zai shiga idan ya rasa matarsa.

A can bangaren su doctor tauƙir kuwa dubata ya fara yi kafin ya cire zoben da ke hannunta ya miƙawa ya nurse ɗinda ke kusa dashi sosai "kije ki kaiwa mijin wannan matar zoben nan" yayi maganar cikin bada umurni.
Fita nurse ɗin tayi da zoben a hannunta, tana fita kuwa duk suka rugo kanta banda Aleena da zazzaɓi ya rufeta sosai saboda kukan da tasha.
Nurse ɗin na isa batace musu komai ba duk da ganin su da tayi cikin damuwa.
miƙawa abbi zoben tayi ba tare da tace masa komai ba, Abbi kam a yanzu ba zoben bane damuwarsa, damuwarsa itace matarsa bai ko kula matar ba yaci gaba da kai kawo da yakeyi a harabar Wurin.
Leeya da ta lura saita miƙa hannu ta karbi zoben ta sanya shi a cikin silin gashinta ta haɗe da wani ta daure shi tamau yanda bazai fita ba.................




004
Karɓar zoben da tayi yayi daidai da fitowar doctor tauƙir fawizz daga dakin yana gyara zaman glasses ɗinsa,

Ni leeyana: gabana ne ya fara duka uku-uku. Yayin da naga doctor tauƙir ya nufi abbi fuskar sa ba walwala. Ƙara matsowa nayi domin sanin halin da ammin tamu take ciki, isowarta wurin yayi daidai da lokacin da doctor ya dafa kafadar Abbi tare da zaunar dashi kan wata kujera dake wurin, nikuma na ƙaraso dafff da wajen kamar wacce aka cillo.
Isowata wurin yayi daidai da maganar doctor tauƙir fawizz dayake cewa:
" Hamraz sai dai hakuri kasan ita duniya ba komai bace, tamkar kasuwa ce wacce zamuci mu koma, nasan kaima da kanka kasan hakan saidai ma kagayawa wani, duniya aro akabamu batamu bace, komai yana tafiya da lokaci, kuma ba wanda zai wuce lo..."

Doctor tauƙir Bai kai ga ƙarasa maganar ba abbi ya tari numfashinsa a ƙiɗime yace "doctor meyafaru da faheema dan Allah kada kacemin fahima ta mutu meya faru dan Allah?"

Abbi ya faɗa hawaye na gudu a fuskarsa, kamar ƙaramin yaro.

cikin alamu tausayawa dr. Tauƙir fawizz ya ce da abbi hamraz:"
"Hamraz sai hakuri faheema is no more!, haƙiƙa Allah ya ƙarɓi faheema wata ƙila ma tun baku fita a ɗakin ba, a lokacin da muka shigo muma".

Jina, motsi na, ganina, nutsuwata, hankalina ɗiffff komai ya ɗauke daga gareni, sharafff najini a ƙasa daga nan ban sake sanin abunda ke faruwa ba.

Shuɗaɗɗun sa'anni da faruwar haka,,,,,,,,


"Ta farka naga kamar ɗan yatsan ta na motsi"
Muryar wata mata danake kyautata zaton makwabciyar mu ce naji Muryar ta a kunnuwana kamar daga sama.

A hankali na fara bude idanuna dake lulluɓe cikin mayafi, ji nayi an kamani tare da taimakamin na jingina da ginin da har yanzu ban tantance inda nakeba.

Sunana naji ankira, A hankali Na ɗago kaina danake ji kamar zai tsage saboda tsanin ciwo na kalli matar da take miƙo min ruwa.
karɓar ruwan nayi na kai saitin bakina na ɗan ɗaga mayafin kaɗan na saka ruwan a baki nasha. Sai kuma a lokacin na samu damar da zan iya juya idanuna ko zan gane inda nake, gidan mu ne aka dawo dani!!
sainake ɗaukar komai kamar a mafarki kafin na fara kalle-kallen ƴan tsirarun mutanen da ke tsakar gidan namu kowa na faɗar albarkacin bakinsa, ina baza idanuna ko zanga ammi da abbinmu da ƙanwata.

Saidai wani abu danaji ya ƙara girgizani matuƙa ta yanda a wannan lokaci banmasan irin yanayin da nashiga ba,
wasu matan unguwar mu ne su huɗu da suka juyamin baya ma'ana suna zauna a ɗan nesa dani sun juyamin, a hankali nakejin maganar tasu na duka a kunnuwana tamkar sauƙar aradu.
Daga Nan banƙara sanin inda kaina yake ba sai da dare ya ɗan fara yi, kamar dai ɗazu motsin da naji ne ya tayardani,
saidai a yanzu ba a gidan namu nake ba, idan na fahimta daidai gidan wata ƙawar amminmuce, mama hujra ƙara dubawa nayi dakyau domin gasgatawa ko gidan ne da gaske.

Da gaske kuwa gidan ne domin Ni a nawa mamaki banyi tunanin ƙara shigowa gidan ba, saboda kwata-kwata mijin mama hujra baya ƙaunata saboda kawai mayafin da nake yafawa a fuskata.
A yanda yake faɗa muddin inaso in shigo gidan saina cire mayafina nikuma bazan iya ba shiyasa nadaina shigowa gidan gaba ɗaya. Sai gashi yanzu na ganni a gidan, gabana ne ya yanke ya faɗi sakamakon tunawa danayi da maganar da matan nan sukeyi ɗazu.
Nan da nan naji gaba ɗaya tsoro ya rufeni don ina shirin tambayar mama hujra, kuma ina tsoron amsarda zata fito daga bakinta.

maganar da tayine ta dawo dani daga duniyar dana lula.
Sannu kawai mama hujra ke jeramin kafin tace"sannu leeyana, ki tashi ga ruwa can na sakamiki a kewaye kiyi wanka kizo kici abinci kinji".

kai kawai na gyaɗamata sannan na buɗi baki da kyar nace mata "ina Ammi na da Abbi da Aleena?"
Miƙar dani tayi tsaye , Ni kuma sai Binta nake da idanu ina saurarar abunda zatace,,
"duba can, ga aleena can kwance bata jin daɗin jikin ta" mama hijira ta faɗa tana nun wani ɓangare na gidan da hannunta.

Dubana nakai inda take nunamin aleena nagani kwance shimfiɗe tanata rawar ɗari, abunda yaban mamaki shine ba wani ɗari da har zatayi rawar sanyi, dayake rabon da ayi muna ruwa yau kwana biyu kenan sai dai yayyafi can ba'a rasaba.

Da gudu na kwashi jiki domin na isa ga ƙanwata naji abunda ke damunta, domin ganin ta a halin nan shafff ya mantarmin da damuwa ta, duk da ban gasgata maganar da nakeji tana min yawo a kwakwalwa ba.

"Kiyi a hankali mana leeya jikinki ba kwari fa kinga ma ko yanzu idan ban riƙeki ba faɗuwa zakiyi"

kallonta kawai nayi domin da gaske bana jin kwarin jikin nawa, a daddafe nashiga kewayen na watsa ruwa na ɗaura mayafina domin na saba da yin haka ko a gidan mu.

fitowa nayi koda na iso kofar ban ɗakin mama hujra na tsaye tana jiran fitowa ta, ina fitowa kuwa ta kamani har muka isa kan tabarmar da ta shimfiɗa mana.

Kallona na sake kai ga Aleena wacce ke duƙunƙune har yanzu kamar yanda na barta ɗazu.

"mama dan Allah ina so in tambaye ki nasan bazaki rasa sanin abunda zan tambaye ki ba dan Allah ki taimaka ki gayamin gaskiya"

Dafa ƙafaɗata mama hujra tayi kafin tace "zan baki ko wace amsar tambayar da zakiyimin idan har na santa in sha Allah karki damu kinji, amma kafin nan sai kinci abinci kin koshi sannan ki kwanta kihuta, idan kin tashi sai muyi magana,
yanzu ina jiran Adamu, (wato mijin ta) yadawo inada wasu kuɗi dana bashi ya ajiyemin idan yanada su ya bani sai nakai budurwa Chemist ayi mata allura"

Mama hujra tayi magana tare da janyo kwanon abincin gabana sosai.

"Lah-lah-lah hujra mezan gani haka wannan yarinyar ce a gidan nan yau? Waike hujratu meyasa kikeda kunnen ƙashi ne, wannan yarinyar kika janyo a cikin gidana,
To wallahi bazata saɓuba. wannan aljanar yarinyar bazata zaunamin a gida ba zaɓi uku gareku daga su harke da kika kawosu a gidana, kodai ta cire wannan mugun mayafin nata mai kamada fatalwa sannan tagayamin dalilin sakashi da takeyi,
ko kuma ta tashi ta fucemin a gidana, ko kuma ku tashi gaba ɗayanku ku ficemin daga gida" cewar Adamu mijin mama hujra dayake shigowa gidan yanzu.

Ɗa gowa mama tayi a raunane kafin ta fara magana cikin kuka tace "haba Adamu kaji tsoron Allah, wallahi a ko ina maraye abun tausayawa ne. ka duba kagani fa duka yau ko kwana ɗaya ba ayi ba da rasuwar iyayenta ba gaba ɗayan su,
ka tausayawa waɗannan yara ciwon hawan jini ya kashe mahaifiyarta lokaci ɗaya yayin da mahaifinta kuma zuciyarsa ta buga dalilin mutuwar matarsa, nan ya faɗi ya mutu shima.
Akwai waɗanda za'a tausayawa ne daya wuce waɗannan yara du-du-du shekarunsu nawa saboda Allah baibamu haihuwa ba bawai yana nufin bamusan zafin yara bane.
Dan Allah Adamu kayi hakuri muzauna da yaran nan mu ingantamusu rayuwa tunda kaga basuda kowa, ka duba ƴar ƙaramar can zazzaɓine ya rufeta tun kafin abun ya faru gashi har yanzu tana fama dashi. Yaran nan marayune Adamu, kada ka manta manzo (s.a.w) yana cewa "kafaɗa daya zamu jera da wanda ya rika maraye riko na hakika zuwa gidan aljanna, Adamu bazakaso kazama cikin Mutanen da Annabi zai yi alfahari dasu a ranar tashin alkiyama ba"

Cikin hanzari Adamu ya ƙatseta da faɗin yimin shiru wallahi kafin ranki yayi mummunan ɓaci, ai bansan haka kika iya yin wa'azi ba da na dinga rakaki mumbari, kuma injiraki har ki gama.
Ai wadannan yara ba abun tausayawa bane waya sani ma ko muguwar yarinyar nan ce ta kashesu da siddabaru irin nasu na mayu, nidai wallahi na rantse da Allah bazata zaunamin a gida ba kinji na gaya miki, idan kuma kina musu kibari naje na dawo na sameta a gidan nan"

Adamu ya faɗa yana shura takalma tare da barin gidan.

"Mama da gaske ne abunda naji kina faɗi wai Abbin mu ya rasu!!? Da gaske ne mama, dan Allah ki sanardani, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un Ashe abunda naji matan nan suna faɗi gaskiya ne mama kiyiwa Allah ki tadani daga mafarkin da nake, don Allah mama kice komai ƙaryane, mama ki karyatani dan Allah kice ƙaryane Abbi da Ammi basu mutu ba,
kai ina. Mama!! iyayenmu suna sonmu ko ke kin san da hakan , kinsan duk inda zasuje damu suke zuwa, su Abbi bazasu barmu su tafiba"

zabura tayi daga inda take zaune ta nufi inda Aleena take kamar wata zautacciya.
Dariya ta farayi while hawaye na zubowa a idonta kafin ta yaye zaninda Aleena ke lulluɓe dashi tace "ƙanwata kitashi muje gida su Ammi na can suna neman mu, nasan kema baki yarda sun mutu ba ko Aleena ?Ammin mu bata Mutuba sai taga aurenki kho ƙanwata, ki tashi muje, kinsan kinyiwa Ammi alƙawari idan kikayi aure ga ɗakinki ga nata, budurwa ki tashi muje mu ki cika alkawarin ki da kika dauka, Ammi bazata mutuba saitaga aurenki in sha Allah ki tashi kawai muje gida"

Aleena da zafin ciwo ke cinta ido kawai ta zubawa yayar tata yayinda itama hawaye ke zuba a idanunta.

hujra ce ta iso wajen tare da rungume su baki ɗaya tana rusa kuka. haƙiƙa duk wani mai zuciyar tausayi yaga wadannan bayin Allah a wannan yanayi dole ne yaji tausayin su matuƙa.
Sake komawa Aleena tayi kwancen da take saboda ita kaɗai tasan abunda takeji yayinda leeya ta sake miƙarda ita sannan ta duƙa a gabanta,cikin dauriya da karfin hali, ta fita da kyar ta saɓata a bayanta ta saka zani ta ɗaureta tamau.

badan tanada tabbacin zata iya goyata ba kawai itama tayi hakan ne saboda tarasa abunda zatayi a yanzu komai ya kunce mata aka, tana shirin juyawa mama hujra ta riƙeta idanunta sharkaf da hawaye tace
"ina zakije leeya kigayamin inda zakije nasani, yanzu ba kamar da bane, yanzu bakuda mai kula da ku leeya kunrasa gatan ku babu faheema babu hamraz ba dangin faheema babu na Hamraz balle ku sami sauƙi dan allah kigaymin inda zakije nasani, ko kuma ki ajiyemin budurwa a gidan nan kafin musan tayi tunda kinga Adamu ke ƙaɗae yace bada itaba"

Cikin ƙarfin hali leeya ta fizge daga riƙonda mama tayi mata sannan ta fice gidan, tana fita gidan sai tayi hanyarda zata Kaita gidansu, dama can layin nasu ba'a fiye samun mutane ba a irin wannan lokaci da duhu yaɗan fara yi.

banke kofar gidan tayi da wani irin karfi da batasan tanada shiba, turus tayi sakamakon ganin okene zaune a tsakar gidan yanata rizgar kuka kamar shi akayiwa mutuwar, yana ganin leeya da gudu ya taso tare da rungume ta suka yita kuka gwanin ban tausayi, saida suka ɗauki lokaci Kafin leeya ta iya tambayar okene.

"Okene da gaske Ammi da Abbi sun mutu, da gaske mun rasasu,
shin da gaske zuciyar Abbinmu ta buga bayan Ammin mu ta mutu? dan Allah okene ka ƙaryatani kace duk ƙaryane, ko kuma kace nasamu taɓin hankali ne shiyasa nake faɗin haka"

Janye jikinta tayi daga na okene kafin ta nufi hanyar tilon ɗakinsu ta shige tana ta kuka tare da kiran Ammi da Abbi,
fitowa ta kuma yi ta ajiye aleena sannan ta koma kofarda zata sadata da shagon Abbinsu.

Kai komo ta farayi tsakanin ɗakinsu da kuma shagon na Abbinsu, har saida ta gaji sosai okene yayi kokarin hanata amma ta kasa hannuwa har ya kyaleta ya zubawa sarautar Allah ido.

Da dai ta fahimci cewa da gaske ne ba abbi ba ammi sai ta sami wuri daya ta zauna tayita kuka kamar ranta zai fita.

Batasan lokacin da okene ya zagayo ta gabanta ba ya durkusawa da gwiwoyinsa ƙasa yana ta kuka gami da harɗe hannayensa biyu alamar roƙo yana magana cikin matsanancin kuka kamar mahaifiyarsa ce mai rasuwa.

"Leeya dan Allah kiyi hakuri, idan kinyi imani da Ubangiji ke kashewa ya raya kiyi hakuri leeya, sau dayawa idan na biku islamiyya inaji ana yimiku wa'azi dangane da mutuwa da tawakkali. leeya Meyasa zaki karaya kina cikakkiyar musulma, meyasa leeya!? Idan har kin yarda Allahn da ya baki iyayenki shi ya ƙarɓesu dan Allah ki ajiye hankalinki ki daina kuka kiyi musu addu'a susami rahma da dacewa kinji leeya Please. Nima gobe zanje Church kuma saboda nayimusu addu'a kawai zanje kema ki dage kiyi kinji na rokeki"
Okene ya ƙarasa maganar yana ƙara fashewa da kuka.


Jikin leeya yayi sanyi likis da jin abunda okene ya faɗa shida yake ba musulmi ba yayi imani da

3 / 61