Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
yayi mata take ta juya inda fridge din yake.
Da ta dawo ma bai kula ba sai jin alamar na'ura yayi a gefensa.
Hannu ya saka zai kar'ba sai kuma yaga kofuna biyu, cikin mamaki yakebinta da kallo fuskar sa ta kasa boye farin cikinsa yace "qalbie kinji sauqi, masha Allah. Alhmdullillah Allah ka qara bawa matata lafiya"
Tana murmushi tace "to ka karbi ruwan mana"
"Zo ki zauna ki qarasa ladarki" ya fad'a yana nuna mata cinyarsa tare da kashe mata ido daya.
Janyota yayi ya zaunarda ita ya bude bakinsa ya rufe ido, ganin haka ya saka ta gane abunda yake nufi nan take kuma ta dinga bashi ruwan har ya qoshi.
"Kamanta da robot fa"
"Ba fa robot ne sunan wannan ba, kowanne a cikinsu yanada suna. Ita wannan sunanta Clara"
Aikuwa yana fadin haka ta gyara tsayuwarta tana kallonsu.
Leeyana ta maimaita fad'ar sunan "Clara....."
Tana ji leeyana ta kira sunanta ta juya ta tafi gabanta tana miqamata kofin.
A wannan karon leeyana bata ji tsoronta ba ta karbi kofin tana murmushi.
Martanin murmushi ta mayarmata itama tare da juyawa tabar wurin.
"Clara tana da saukin kai ba kamar sholeen ba"
"Kana nufin kace har a cikinsu akwai masu sauqin kai akwai masu wuyar kai"
Dariya ta bashi Sosai yanda tayi maganar "wai wuyar kai" hakan ya sakashi darawa tare da cewa "kwarai ma kuwa, yanda kikasan mutane haka suke"
"Ikon Allah" ta fad'a tana tallafe ha'ba.
"Babynah kinyi kyau sosai wallahi kin ganki, gskiya ina qara godewa Allah da yayimin ni'imar samunki leeyana, wallahi kayan nan sunyi kyau amma meyasa baki kirani na tayaki shiryawa ba"
"Banyi tunanin kana kusa bane, abunda ya saka na jiyo alamun ka ma shine lokacin da zaka kira Clara"
"Okay tau ki tashi muje ayi breakfast kho...?"
"Yawwa sweet dan Allah ka kira min su mum na gaida su Wallahi har nayi kewarsu ina so naga mummah na"
Baki ya taɓe tare da cewa"su kewa manya aikuwa bansan ranar da zaki gansu"
Baki ta bud'e zatayi kuka da sauri ya rufe bakin"kin manta nayi alqawarin bazakiyi kuka ba indai inada rai da lafiya, dan Allah karki soma dan wallahi bazan jura ba"
''Yayana to ka kirasu na gansu yanzu''
"Yanzu kuma sweetheart kin manta yanayinsu da namu ba daya bane, mu yanzu safiya ta waye..... Su kuma Yanzu ne suke shiga bacci"
"Eh, kuma fa haka ne........! Nidai wallahi sai ankirasu" ta fad'a cikin rigima irin Tata.
"Naji zankira, amma dai zaki bari muyi breakfast Koo.......?"
"Ni bana jin yunwa...." Cewar ta tana juya masa kai gefe....................✍🏼
49.
_____________"haba dai uwargidan ya-turab, kiyi hakuri mana muyi breakfast just in minutes fa, wallahi zan kirasu koda karfe ukun dare ne a Nigeria yanzu....!"
Jin yayi rantsuwa ya sakata d'an sake fuskarta kadan tace "promise....!" Tana d'aga yatsarta daya.
Ganin haka yasa ya riqo hannun nata gaba daya yace "I promise you dear, can we go...!?"
D'aga masa kai tayi alamar ehh. Tamke fuska yayi sosai yace "bana so ana daga min kai idan nayi magana"
Ganin ransa ya soma ɓaci ya saka ta dan sunkuyar da kanta qasa tana qara shigarda kan nata cikin qirjinsa, "kayi hakuri na daina"
"Hummm ni bakyamin laifi ai, koda kinayi ma na yafemiki tun Kafin kiyi, kuma ki tashi muje Yanzu. Nifa da nine banyi breakfast ba bazan damuba, amma wlh duk na damu da ya kasance kece bakiyi ba"
"Allah sarki mijinah, to muje" ta fad'a tana qoqarin miƙewa.
Jinta kawai tayi jikinsa ya d'aga ta sai daining area. Haka ya kira clara da sauran robot dinsa sukayi sarving dinsu. A baki ya dinga bata harta qoshi.
duk yanda tayi yaci yace "a'a" sai ta qoshi tukunna.
Tana qoshi itama ta fara bashi abaki har sai da ya qoshi shima.
"Muje to akira mum dan Allah"
"Oh ni jikan mainah na haɗu da rigimammiyar mata" ya fad'a yana talla'be ha'ba.
Kukan shagwa'ba ta saki harda hawaye tana bubbuga qafa"nice ma rigimammiyar mata, to ai nima ina da wayar ba'a buqatar kiran naka bara naje na kirasu da wayana"
Fizge jikinta tayi daga nashi ta tashi fusace zata wuce bata ankara ba taji bakinsa cikin nata.
Kissing dinta ya farayi deeply har suka koma zaune gaba ɗaya yana romancing dinta cikin kwarewa.
Tsawon mintuna sai qarar numfashinsu akeji. Murya a kasalance cikin yanayinsa da ya fara changerwa yace "Ni banyi komai dakeba, naga kinyi fushi ne, wannan ce hanya mafi sauqi da zan baki haƙuri saboda haka kiyi haƙuri kinji....ke ba rigimammiya bace my one..."
A hankali ta d'aga kanta dake kirjinsa ta shafa sumar kansa tana murmushi tace "naji kuma banyi hakuri ba"
"Subhanallah...dan Allah mana" ya fad'a yana marairaice fuska.
"Bazanyiba gskiya.....!"
"Saboda me qalbie...?"
Kamar zatayi masa kuka tace"to bakai bane tun ɗazu fa ina roqon ka akan ka kiramin mahaifiyata amma ka qie, kuma kace can Nigeria yanzu dare ne so kake koda zaka kira sunyi bacci kho"
"Lahh yanzu akan wannan. Ki tashi muje parlour na kirasu da system ma nasan zaki fi jin daɗin ganinsu a babban screen"
"Muje to.....!" ta faɗa tana miqewa.
Shima miqewa yayi da nufin ya bita, lokacin kuma har leeya ta fara tafiya.
"Tho malama ki jirani kho..."
"Ka sameni kawai bazan iya bin shiriritar tafiyar ka ba.."
"Ikon Allah, Princess nine mai shiririta idan ina tafiya..? Wai ko kin manta soja ne ni, harfa yaqi ina yi, shine zakice ina shiririta idan ina tafiya. Nidai ki jira ni kawai"
"Naqi bazan jira ba d'in..."
"Shikenan kije, ynzu za'a mayarmin dake nan kinga remote ɗin su sholeen da Clara kho, derbesh ma zan saka ya d'akko min ke domin shine namiji acikinsu, kuma duk yafisu rashin mutunci"
"Robot....!.." ta fad'a a fili tana dafe kirjinta.
"Kwarai kuwa robot zan kira su dawomin dake har gabana"
Tana tsaye ta kasa ko motsi Allah yasan tana tsoron wadannan robot bada wasa ba..... ita ko acikin film bata cika ganinsu ba ma balle su saba........"
Tana cikin zancen a zuciyarta ne taji qarar na'ura alamar ya kirasu kenan.
Aikuwa da mugun gudu ta isa ta fad'a jikinsa tana sauke numfashi "miji.....! dan Allah kayi hakuri dauke ni da kanka muje Please, Ni ko ganinsu bana so inyi yanzu dan Allah ka kirasu kuma kace basai sun zo ba"
"Nayi hakuri, muje kar su mum suyi baccinsu" ya fad'a lokacin da yake direta bayan sun iso main parlor.
Fita yayi daga wurin ya shiga wani d'aki ba tare da ya furta komai ba ya dawo inda take kusa da ita sosai ya zauna yana bude system dinsa.
Ita kuwa ta zuba masa idanu tana jiran sakamakon.
*NIGERIA*
kwance take akan sofa ta lulluɓe rabin jikinta da blanket sakamakon yanayin sanyin da ya shigo.
Murmushi take Sosai ta kafe wayarta da idanu tana daddanawa da hannayenta biyu cikin sauri da kwarewa a typing da alama dai chat take.
Dariya sosai take harda 'kya'kyatawa. Mamakine ya rufeta sosai har sai da ta dakatar da dariyar da take. Ga qatoton screen ɗin wayarta ya bayyana video Call ake kiranta.
"Rabeen jiki..." Shine abunda saving ɗin number ya numa lokacin shigowar kiran.
Ido ta zaro waje da matuqar farin ciki har hannunta na rawa wajen picking call din sa.
Da mugun d'oki ta amsa wayar ko sallama batayiba tace "ya-turab mutanen Spanish ashe dai baku manta damu ba"
Dan murmushi yayi kawai yace "autar mum kin wuni lafiya? Dah na dauka kinyi bacci ai..., ashe kina nan baki kwanta ba har yanzu"
Bakin khulud har kunne ganin ya-turab ya ɗan sake mata tace "ina nan ya-Turab banyi bacci ba tukunna ina amaryarmu"
Kallon gefen da leeya take yayi yaga itama system din ta kurawa idanu sai washe baki take ganin Khulud a gabanta kamar su rungume juna ba qaramin dad'i hakan yyi mata ba.
Juya kan system din yayi yanda leeya zataga komai dakyau. Cike da kewa da farin ciki suka gaisa gaba dayansu, sun dauki tsawon mintuna goma kafin leeya ta tambayi khulud.
"Ina mum da papu, wallahi ina kewar su sosai"
"Aikuwa dai sarkin kewa, su mum suna nan lafiya qalau wallahi. Ba'a jima ba da na ji motsinsu down stairs bara na duba idan suna nan sai na basu wayar kho"
"da kinyi agaji wllh domin idan bangansu ba yau fiffike zanyi sai Nigeria kinga nan ko goman safiya batayiba balle dare yay min akan hanyata"
Turab ya kalleta yana dariya yace
"nifa har naga kin jima baki wuce Nigerian ba na ga iyakar kewa, ke mai iyaye kho"
Taɓe baki tayi zatayi kuka, yanda tayi ta bakin idan ka gani zakayi tunanin yarinya ce ƴar shekara huduj, sosai abunda tayi ya birgeshi yana kallon dan qaramin lips dinta yana murmushi yace "menene kuma my princess, me akayimiki, gayamin naji kinji waya taɓa matar yaya guda"
Kamar zata ɗan yi kuka tace"to ba kai bane ba yaya ina magana da 'yar uwata zaka sakamin baki"
"To ba kai bane ba yaya ina magana da 'yar uwata zaka sakamin baki" ya kwaikwaya kamar yanda tayi maganar da qaramar murya yana dariya.
D'an naushin nan ta masa irin na love tana shirin kuka ya shafa fuskarta yana qoqarin had'e bakinsu wuri ɗaya.
"Ummmm, ummmm, ya-Turab baku katse kiran ba fa, naga kuna batun ku fara (L) a gabana" Khulud ta fad'a tana qoqarin kumshe dariyarta.
"Ke banason raini ki kaiwa mum wayar ko na 'ba'b'ballaki wallahi" Turab ya fad'a kamar ba shi yake dariya ba yanzu nan.
"A ina zaka ganni balle ka babballaki, Lallai ma ya-Turab kanada abun mamaki, daga abun arziki, ina naga abun alheri ya zama na tsiya, saboda kawai na tuna maka karka saki layi agabana shine abun wani babballawa" Khulud ta fad'a a zuciyar ta, a fili kuwa cewa take "yayan mu Allah ya baka hakuri, mum kam kamar an bata wayar angama kuyita kallon juna sai safe"
'kwafa yayi yana jijjiga kai kafin ya kawarda kansa daga kallonta. Leeya kam idanunta na kyam akan screen ɗin system din tana jiran ganin mum, cikin hakan ne bata ankara ba kuma sai dariyar mum da papu sukaji.
Turab bai san yayi kewar iyayensa ba sai da yaji muryoyinsu suna dariya duk da ba wannan ne farkon tafiyarsa mai nisa ba amma yayi kewarsu sosai a wannan karon.
Cikin murna da farin ciki suka gaisa da mum da papu gaba dayansu sai farin cikin ganin 'ya'yansu suke. Sosai hakan yayiwa su mum dad'i.
"Tau nakira mum hankalin ki ya kwanta kho..?" Turab ya fad'a lokacin da suka kammala wayar gaba d'aya.
Rungume shi tayi tana dariya tace "eh hankalina yayi rabin kwanciya, ka cika ya zama ya kwanta gaba d'aya Please"
"To ya zanyi na cika hankalin ya kwanta gaba d'aya"
"Ka kira ya-zafaran mu gaisa dasu suma..."
"Ke wai baki san dare bane yanzu a wajensu ko dan kina ganin rana tarrr anan"
"Nidai wallahi ba ruwana ka kira kawai idan kuma ba haka ba zanci gaba da barin hankalin nawa tsaye tsaff ko zama ba zai yi ba balle ya kwanta"
Murmushi yayi kawai yana jijjiga kai, number din zafaran ya lalubo normal call ya kirashi, sai da wayar tayi ringing sai biyu ana ukun ya dauka, bai ma jira jin abunda zafaran zaice ba ya riga shi fadin, "idan matarka tayi bacci ka tayarda ita ku hau online gimbiya ta na buqatar yin waya da ita video call.....!"
Bai jira cewar sa ba kuma ya katse wayar ya koma online. Zafaran kamar bazai zo online ba ba dan ya dauki mintuna kafin su ka ga saqonsa ya yi musu sallama "hi nice couples" ya tura musu da saqon wannan.
Da sauri leeya ta bud'e sakon ta danna musu kira, cikin matuqar farin ciki leeya ke kallon qanwarta "budurwar ammi kin manta da yahyah leeya kho..?" Cewar leeya tana murmushi amma idanunta tapp suke da hawaye.
"Yahyah-leeya taya zan manta dake Ni kuwa, wallahi ki tambayi broth O ma kiji yanzu muke zancenku, Ni ina ma tunanin da wuya idan 'yan Spanish basu mayardaku aljanu ba, da kukazo kuna leqon asirin mu, Domin fa yanzu muke zancenku wai sai ga kiran wayanku abun akwai mamaki gsky" Aleena ta fad'a tana washe baki.
Leeyana ma bakin take washe wa suka gaisa kafin ta miqawa turab system, Aleena kuma ta miqawa zafaran suka gaisa.
A cikin zancensu ne Zafaran yake bawa turab labarin kwanan nan zasuyi tafiya zuwa taraba wato asalin garin iyayensa.
Da mamaki turab yace "taraba dai zafaran....?"
"Eh wallahi, grandnee na ne sukace sai ankawomusu amarya sun ganta"
"Allah yasa dai karsu nunawa qanwata wariyar launin fata"
"Bazasu nuna ba ai, saboda muma muna da musulmai a familyn mu amma gskiya basu wuce hud'u ba, kuma tunda momynah ta rasu suka rage nunamin qiyayya akan nafita addininsu na shigo wannan. Suna gani sun quntatani idan suka ci gaba da nunamin qiyayya shiyasa suka sassauta.
Yanzu ma sun sami labarin nayi aure shine suka takurani akan sai na kawo musu amarya sun ganta kuma itama na gayamusu musulmace kaga babu wata wariya da zasu nunamata in sha Allah"
Cikin gamsuwa da maganar da zafaran yayi turab yace"okay, tau Allah ya kaiku lpia ya mayar daku lafiya"
"Ameen ya rabbi, amma dawowa ba yanzu ba tun da na sanarmusu she's pregnant suka kafe akan saina kawota Ni ina tunanin ma bazasu bari ta haihu anan ba kasan yanda qabilar mu take fa"
Turab da mamaki yace"waye mai ciki kuma"
Zafaran ya ɗan shafa kansa yana dariya Yace"matata mana, me kake tunani nifa ba ragon namiji bane wallahi kaima ka matsa ka qara qaimi"
Cikin jin kunya leeya ta tashi zata bar wurin turab ya riqota har tana fadowa kan jikinsa, ta zaune suka dinga sheqiyanchi ko kunyar matan nasu basa ji sukuma kamar su nutse saboda kunya.
Haka sukayi sallama cike da kewar juna, "nasan yanzu zakice sai an kira Fahad kho"
"Eh mana my love Wallahi nayi missing bestina Please ya-Turab dan Allah mana" tayi maganar tana marairaice fuska.
Dan jan hancinta yayi "kinganki kho, tho bazan kira ba"
"Haba yaya dan Allah.......!"
""To shikenan kinga ma baki kula ba harna kira ringing take ki shirya"
Ko rufe bakin sa baiyiba yaji alamar sun daga kiran, fahad ne zaune sai zohal dake kwance ta dora kanta akan cinyoyinsa, suma da system suke aiki hakan yasa call din nasu yafito so well.
Cike da nutsuwa suka fara gaisawa gaba dayansu, leeya da zohal kamar su rungume juna saboda murna sun jima suna wayar kafin sukayi sallama. Dare yayi sosai a Nigeria ba kamar spain da suke qarfe tara na safe ba yanzu.
Rufe system din yayi yana cewa "my princess angama komai koh...?"
"Eh honey, ina godiya sosai Nagode Allah ya barnin kai jarumina"
"Ameen ya rabbil ibaddd, ki tashi muje na shiryaki zamu fita yawo yau"
Har wani ihun murna take domin tun shigowar su garin ya qawatata matuqa, har Allah-Allah take taji ranar da zaice su fita yawo.
Da hanzari ta shiga toilet tana qoqarin rufewa ta ganshi ya biyota.
Zare idanu tayi tana shirin magana ya saka yatsarsa yana rufe mata baki tare da jijjiga mata kai.
Zip din rigarta ya fara zugewa har ya kaishi qasa, ya rage kayanda ke jikinta basuda yawa, tafukan hannunta ta saka ta rufe fuskarta ta lokacin da taji ya mayarda da ita naked, shima yayi naked ya fad'a cikin koman wanka ya janyota itama ta fad'a kan jikinsa.
Saida sukayi romance sosai kafin yayi mata wanka shima yayi wanka ya nad'ota cikin towel kamar wata baby ya ajiye ta akan bed.
Tana kwance ta kasa ko motsawa harya shirya cikin qananun kayan da suka yimasa kyau matuqa.
Blue armany jeans ya saka anyi layi uku na fari daidai gwuiwoyinsa. Sai kuma keymoni short fara tasss mai dogon hannu, sai wata arninyar top da ya saka saman kayan.
Turarukan sa masu qamshi ya feshe jikinsa dasu, duk abunda yake tana jinsa tayi lamo kamar mai bacci.
D'aga ta yayi zaune kafin yakaita gaban mirror, da kansa yayi mata make up so simple bayan ya shafeta da lotions. Irin kayanda ke jikinsa sak ya saka mata sai dai nata na mata ne daga yanayin sharp din kayan. Farin gyale jessy ya ajiyemata yace "my one rolling ne kadai ban iya ba kiyi da kanki nasan ke zaki iya yi"
"Nidai bazan yi ba ai tunda kai ka fara ya kamata ace ka qarasa da kanka"
Magiya yayita yimata akan ta daura Jessy din amma fur ta qie,,,,,! ganin suna cin lokaci ya saka shi janyo wata cabinet drawer ya fito da rolling pin kalar jessy din wato fari.
"Ki gyara da kyau na daura naga ko zan iya"
Juyomasa da kanta tayi sosai yanda zaiji daɗin roller ma ta gyalen.
Sosai ya bada himma wajen ganin rolling din ya fita yanda yakeso.
"Ki duba kiga ko yayi miki" cewarsa yana juya kujerar da take zaune gaban mirror.
Baki sake takebin fuskar ta da kallo, ganin ko ita da take mace idan tayi wannan ai sai an yaba mata balle ma ace namiji yayi.
Mamaki ya hanata faɗin komai sai tashi da tayi ta rumgumeshi tsamm ta manna masa kyakkyawan Peck a kumatu.
"Kinyi kyau my angel"
"Allah kaima kayi kyau sosai hub..., kar 'yan matan Spanish su kwace min baby.." ta fad'a tana dan langwa'be kai.
"Humm, kar ma ki bari wannan yayi tasiri aranki domin turab nakine ke kadai"
"Allah koh qalbie.....?"
"Eh sosai nakine ni, Ni akayiwa ke, kema ke akayiwa ni. Mun hadu babu rabuwa"
"Allah yasa haka Honey, muje"
"Ina zamu fara zuwa....?" Cewar turab yana tuqa mota bayan sun fito gidan.
"Inaso muje gidan namun daji first, daga nan kuma naje gidan tarihi da al'adu na qasarnan, sannan kuma inaso muje asibiti aqallah guda biyu muyi sadaqa, sannan muje gidan abinci.........."
Tayi jimmm kamar mai tunani daga nan kuma bata qara cewa komai ba.
"Umhumm, ina jinki sai ina"
"sai muje mall"
"And them...?"
"Sai.....sai......sai mu dawo gida".
Laquto kumatunta yayi yana dariya yace"naji nabi ya shugabata"
Dariya sukayi gaba dayansu lokacin da suka qaraso bakin wata asibitin gwamnatin dake qasar.
Kamar yanda leeya tace haka turab yayi, kuma duk inda ta fad'a sai da sukaje sosai ya kashe kuɗi kamar ba gobe.
Haka suka tattaro suka dawo gida a gajiye.
Damansu ɗaya duk sallahr da akayi suna tsayawa suyi har lokacin sallar isha da yayi suna waje basu dawo gida ba acan wurin yawon shan iskansu sukayi.
A matukar gajiye sukadawo leeyana da jan qafafu ta shigo parlon gyalenta a hannu da kuma waya da handbag.
sai turab ne ya shigo da kaya niqiqi bayan ya kira robot dinsa sun taimaka masa.
Da taimakon sa tayi wanka shima yayi wankan suka shirya cikin kayansu na bacci masu masifar kyau suka kwanta.