Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
dake sarqafe da nasa hannun.
Mum da khulud ne suka zo inda yake, mum ta shafa goshin sa hawayen ta na qara guda kamar fanfo tace"Allah ya baka Lafiya, Allah ya tada kafadun ka, ya saka ciwon nan ya zama kaffara a gareka".
Hannunsa ya fara dagawa a hankali har saida yakai daidai idanunta ya shafe mata hawaye yana girgiza mata kansa.
Khulud kam kamar jira take tana ganin haka itama kuka mai sauti ya kufcemata, da sauri Aleena tazo ta janyeta suka fita daga dakin.
Papu yazo ya masa ya jiki shima, komai da papu yake yi sukuku yake yinsa domin tunanin halin da turab ya shiga ya hana masa gudanar da lamarinsa kamar yanda yake.
Ta ido fahad yayi wa zohal alama, haka tazo itama tayi masa ya jiki sannan ta koma ta zauna, duk abunda suke leeyana na zaune ko motsawa batayiba, kuma tanajin duk abunda suke fad'a amma ko kallon wurin batayi.
Aleena da khulud ne suka dawo dakin bayan Aleena ta rarrashi khulud akan ta daina kuka.
Basu tsaya ko'ina ba sai gaban gadonda turab yake.
Sannu da jiki suka yimasa, amma da kansa kaɗai yake iya amsa musu domin oxygen ne a hancinsa. Komawa sukayi suka zauna kowa na saqa abunda yake saqawa a ransa game da leeyana da kuma sauyawarta cikin ɗan qaramin lokaci.
Zafaran kam har qaryata kansa yake wai leeyanahr ammice ta mayar da Rayuwar ta haka ba tausayi ko kadan kamar ba musulma ba, ai ko wanda ba Musulmi ba idan yaga ɗan uwansa a irin wannan yanayi dole ne ya tausaya masa balle turab da yake dan uwanta na jini, kuma yayanta da-ɗin daɗawa kuma mijinta.
A rayuwar Fahad bai taba ji a ransa ya tsani mutum ba sai a wannan lokaci, kusan yanayi daya suka shiga da mahaifinsa dad ƙarami. Shi dad yana gani ta dalilin leeyana ne d'ansa ke kwace cikin matsananciyar jinya.
Kowa da yanda yake kallon leeya a wannan lokaci. Shikuma turab yayi duk yanda zai yi domin su haɗa idanu amma taqi yarda samm.
Mintuna biyu da suka wuce ba wanda ya qara fadin komai kuma ba wanda ya qara kula kowa a cikinsu, sai dad ƙarami ne yake tambayar turab jikinsa akai akai Har bacci ya daukeshi, saida dad ƙarami ya fahimci yayi bacci ne sannan ya daina masa sannu.
Miƙewa leeyana tayi fuskar ta a hade kamar bata taba bud'e bakinta ba da nufin dariya.
Tafiya ta fara yi d'ad'd'aya kamar wata basarakiya, kowa dake wurin ya zubamata na mujiya domin suga iya gudun ruwanta.
durkusa tayi da gwiwoyinta gabansa har ya kai ba wata tazara sosai a tsakanin su, hannuta ta saka kan qirjinsa, sannan ta ɗora kanta saitin zuciyar sa ta kawarda kanta daga fuskar sa cikin muryar kuka take fadin "nasan bakajin lafazin bakina, saboda halin jinya da kake ciki. Amma hakan bazai saka in fasa furucin zuciya ta ba, saboda nasan ba kalamaina bane ba, zuciyata ce take kai sako ga zuciyarka" numfashi mai qarfi ta jaa saboda kukan da ke shirin zo mata taci gaba fadin "a gaskiya zuciyata tana sonka!!!! Kuma ta kasa daina sonka ya-turab" Huuuhhh ta furzarda wata iska mai zafi. "Ina fargabar zan iya tsintar kaina a cikin halin da kake ciki, koma fiye da haka idan har aka rabani dakai. Dan Allah....... Ina roqon alfarmarka, ka daukeni a matsayin abokiyar rayuwar ka, dan nima na rayu! Nayi qoqarin cireka araina ganin baka sona, amma abun ya gagara, ina fargabar abunda Zai faru dani idan na rasaka. Na kasa danne abunda ke zuciyata. Saboda kaine burin zuciyata Wallahi ina matukar kaunar ka ya-turab! Na rokeka ka qaunaceni koda quarter ne a cikin tarin qaunar da nake maka" Leeya ta qarashe maganar ta da wani kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, musamman Wanda akayi dominsa.
Suman tsaye kafff mutanen da ke dakin sukayi, baramma fahad dake ji kamar ya shaqeta ta mutu. To a wane mizani zasu daura leeyana. Dama tana sonshi amma ta wahalarda kanta kuma ta wahalar da shi. Gsky lamarin nan nasu akwai ban tausayi da izza da al'ajabi, ga tarin jin kai.
Miqewa tayi zata tafi while tana ci gaba da kukanta, ji tayi an qara kwantarda kanta a qirjin nasa. Hannunsa daya ya saka ya cire oxygen din da ke bakinsa, dayan hannun kuma ya kwantar da kan leeya lif a qirjinsa yana shafa gefen fuskar ta.
Mamaki bai ida kashe su fahad da sauran mutane ba sai da suka ji turab yana magana da muryar nan tasa mai cike da kwarjini lafiya qalau take fita kamar ba shi bane ke ciwo.
"Ko da zan sha wahala fiye da haka, zuciyata ba za ta taɓa janye miki ba. Kin cika rayuwata da haske da farin ciki a duk lokacin da wani zai ambaceki kusa dani, kuma burina na ƙarshe a duniyar nan bai wuce na kasance tare da ke ba, kasantuwa ta har abada. Ina son ki da zuciya ɗaya, so domin Allah ba don kyawunki ko dirinki ko wata sura ta jikinki ba, halattacciyar soyayyar ki da Allah ya sanyamin a zuciya.
Na sha wahala sosai saboda ke, bana tunanin akwai kalmar da zanyi amfani da ita wajen sanardake leeyana wallahi kece komai nawa, kuma duk irin tashin hankali da tsanani dana shiga akanki ba zai hana ni faɗin yadda nake ji ba. Soyayyarki ta canza ni, ta sa na fahimci ma’anar rayuwa. INa roƙon Allah ya sanye miki halattacciyar soyayya a zuciyar ki akaina leeya. Ina sonki ina kuma qaunarki dan Allah kar ki qara nisanta kanki dani kinji Please" ya fada yana qara qanqameta jikinsa.
Gyaran murya sukaji anyi daga bayansu, cikin sauri leeya ta miqe ya sake janyota, a wannan karon kusa dashi ya zaunarda ita kan gadon da yake kwance.
"Sai dai su fita su bamu wuri ba ke zaki fita ba, idan kika fita wazai kula dani" turab ya fada yana daga muryarsa don suji abunda yake fadi.
"Ga mum nan zata kula da kai, ga kuma ya-fahad nan da ya-zafaran" leeya ta faɗa tana ci gaba da qoqarin tashi kusa dashi, har ga Allah ita dai kunya takeji.
"Mum zata kula dani kika ce? To idan mum ta kula dani wazai kula da pa? Zafaran da fahad kuma ina zan iya dasu waɗan nan gardawa, amma dan Allah karki gayamusu kinji, kinga sirri muke kho"
Da sauri ta daga kanta ta kalli inda fahad da zafaran suke tsaye,.fahad kam sarkin zuciya ya cika fammm, domin yanaji duk firarsu.
Kujera ya janyo yazo wurin da turab ke kwance ya ajiye sannan ya zauna. sheqeqe yake kallonsa yace"tho sabon mara kunya butulci zakayiwa mum, da can data kula dakai wata mai kular ka samowa pa, shine dan amarya ta karɓe ka zakazo kana mana surutai. Yanzu bakinka ya kere na kowa a wurin nan, amma mintuna goma da suka wuce iya kanka kake iya motsawa ko zarahin yin magana baka da sai yanzu ne zakazo kana cika mana kunne da surutai"
Murmushi turab yayi yace " dad ku bazakuzo muyi firar ba sai dai ku koma gefe daya meyake faruwa"
"Son, ai mune ya kamata mu tambayi abunda ke faruwa" cewar dad qarami.
Murmushi turab yayi a karo na biyu kafin ya dafa gadon sosai ya miqe zaune ya jingina da bango, tari yayi a hankali sau biyu sannan yace "dad leeyanace duk ciwona, yanzu kuma ta dawo gareni. Wallahi kaso chasa'in na abunda nakeji ya ragu"
"Ungo nan mara kunya, kai bakasan duk iyayenka ne ke wurin nan ba" mum ta faɗa tana watse masa hannu.
"Na karbi zagin dear mum, amma ai kune kuka haɗa auren kunyar me zanji. Yawwa dan Allah mum kwananku nawa a asibitin nan?"
A ganin mum kamar tambayar raini ce kawai turab yayi mata, amma shi bil-haqqi yayi mata tambayar harga Allah bai sani ba.
Tunawa tayi koda aka kawoshi hospital din nan baya numfashi, ba kuma yanda za'a yi ya iya ganewa tunda yana halin ciwo.
"Bamu kwana ba, yanzu ne zamu kwana in sha Allah"
Zaro idanu yayi sosai ya d'an marairaice yace "mum ku koma gida Please gobe sai kuzo da safe, dan Allah ku tafi angode da jinya Allah ya biyaku na sallameku sai gobe da safe kuzo"
Zafaran da Fahad kamar su naɗa masa duka sukeji, wato gayen nan yanaso ya musu wulaqanci kho, zai gane ai. Kuma Allah yasa bashi kaɗai akayiwa aure ba balle ya kurantamusu.
Fira sukaci gaba cikin nishadi har aka kira sallahr isha, ana bashi kula sosai lokaci zuwa lokaci. Dad ƙarami da Papu daga fita sallah suka wuce suleja.
Mum da Khulud kuma suka wuce gidansu dake nan cikin abuja. Idan baku manta ba a can baya na sanarmuku da su mum da papu abuja ne Asalin mazaunarsu, khulud ce ta saka suka dawo suleja da zama. Saboda haka basu zarce ko'ina ba sai a gidan nasu.
Leeya da turab kuma sun sha fira sosai, har suka raba dare suna labaran nishadi kamar ba su ba. Tun suna saka ran dawowarsu mum har suka fitarda ran domin kuwa su mum sun dauki maganar turab da gaske sanin likitoci sun gargadesu a karo na karshe akan rayuwarsa. Shi yasa duk abunda ya faɗa jiki na rawa ake aikawata.
Sai cahn dare gabanin asuba ya farka daga baccinsa, idanu ya tsuramata yana tunanin meye ma qarshen zancensu a daren jiya. Shidai yasan labari kawai take bashi shikenan sai yanzu da ya farka ya ganta a haka.
Kenan bacci yayi lokacin da take bashi labarin, "Allah sarki" ya furta a fili ganin yanda take.
"Kenan zaune ta kwana" ya faɗa yana shafa bayanta.
"Ki yafemin kinji, Wallahi dana san wannan wahalallen bacci zakiyi da na baki gado na zauna kan kujera.
Blanket din da ya rufa dashi ya sauke ya rufa mata domin sanyi ya fara sauka, yana rufa mata kuwa yaji ta sauke numfashi. Addu'a yayi sannan ya tofa mata shikuma ya tattakure jikinsa ya saka hannunsa tsakanin cinyoyinsa ya mayarda bacci.........................✍🏼
47.
____________sai da aka fara kiraye kirayen sallahr asuba ne Dr. Mahad ya shigo dakin, mamakin ne ya kusa kashe shi.
"Kenan akan yarinya nan ne ya shiga wannan tashin hankali....?"
Murmushi yayi a bayyane ganin yanda kwanciyar tasu take, kana gani kasan ba'a shirye suka kwanta ba.
Abun ya birge Dr mahad sosai, wayarsa ya ciro ya fara yimusu video.
Ganin yanda leeya ke zaune ta dora kanta kan gadon da yake kwance, shikuma ya cire blanket dinda yake rufe da shi ya sakamata.
Kwance yake a takure duk ya du'kun'kugune wuri daya, kana ganinsa kasan matuqar sanyi yakeji.
Sai da Dr ya gama yimusu video sannan yadan bubbuga gadon a hankali yanda iya leeyanah ce kawai zataji, baya ma so ya tada turab.
Tashi tayi tana murza idanun ta har ta bud'e su gaba d'aya.
"Lahhhhh wai bacci nayi da zaune" ta fada fuskar ta dauke da mamaki.
"Soyayya tayi dadi har baki san kinyi bacci ba kho, wai dama ku kadai kuka kwana asibitin nan duk ina su Dr". Dad ƙarami kenan.
"Wallahi mu kadai muka kwana su dad sun tafi gida ai, amma zasu zo da safiyar nan"
Juyawa tayi ta kalli turab ta ga yanda yake kwance, cikin matuqar tausayinsa ta cire blanket dinda ya yafa mata ta saka masa.
"Ki cire kawai nifa alwala zanyi inyi sallah nasan lokaci yayi"
Cikin damuwa ta ce "ya turab Meyasa ka hana kanka blanket tsawon dare, kasan mura zata iya kamaka idan sanyinan ya maka yawa"
"Kema idan na barki kika kwana murar ta kamaki fa, kinga Ni zaki daura wa aiki domin zan rama jinyarda kika min haka kk so koh?"
"Ah ah ya-Turab Ni dan Allah nake zaune anan, da kuma kwadayin ladar da zan samu"
"To Allah ya baki lada, ki tashi kiyi alwala. Nima zanyi sai nazo muyi sallah"
Sosai farin ciki ya kama Dr mahad domin da tunanin halin da turab yake ciki ya kwana, shiyasa yayi sammako tun asuba yazo ya duba shi.
Amma yayi mamaki kwarai da gaske ganin yanda jikinsa yayi kyau, kuma ba mamaki a cikin ikon Allah domin Mafi yawa masu irin ciwon nan komai neesan da yayi idan aka samarmusu da abunda suke buqata zasu iya warkewa sumul cikin mintuna qalilan.
Bayan sunyi alwala sukayi sallah, bacci suka koma har sai da rana ta take. Fahad da matarsa suka fara zuwa, sannan dad ƙarami yazo da iyalansa gaba ɗaya.
Sai da aka dan jima mum da Khulud suka qaraso, sannan papu yazo. Zuwan papu ba jimawa ga zafaran da Matarsa Aleena.
Wata irin kulawa turab yake samu daga ɓangarorin musamman ma matarsa da basa rabuwa tare koda yaushe, sosai shaquwa ta shiga tsakanin su kamar da can sun saba.
Kuma hakan yana birge kowa, kowa yana musu fatar zaman lafiya mai dorewa.
Kwanan su uku a asibitin aka sallamesu domin yaji sauqi sosai, idan ka ganshi zaka iya rantsuwa ba shi bane mara lafiyan da ake jinya.
Duk a zatonsa gidan su dashi da matarsa za'a fara kaisu a ajiye sai yaga an koma dasu suleja, bai musa ba domin baisan dalilin iyayen nasa nayin haka ba.
Koda suka koma gida kuma mutane sai tururuwa suke wajen dubinsa musamman ma families.
Kullum ba'a raba gidan da ƴan dubiya, babban abunda ya bawa turab mamaki shine tunda suka dawo yau kusan kwanaki hud'u kenann amma ko kusa bai saka leeyana a ido ba.
Tawaga d'aya ta sojaji daga ko wane bangare na sassan duniya suka had'o zuga suka zo dubin turab.
Duk da su mum basu san da zuwan su ba, ba qaramar tarba suka samu ba, wanda har ƴan gidan tv da jarida suka zo ganin waɗannan mutane.
Turab kam bakinsa kamar gonar auduga, farin cikinsa ya kasa boyuwa har sai da ya tambaya a ina sukaji bashi da lafiya. Sai suka gayamasa a social media suka ga ana yad'awa shine suka kira sauran qasashe akayi meeting kuma aka za'bi 'bangarori da dama a kowane sashe har aka had'a tawaga akazo dubinsa.
Sosai abun ya bawa mutane sha'awa had'e da mamaki, sun jima a gidan kafin sukayi sallama da mutane suka koma inda suka fito.
Kwana biyu da faruwar haka kuma turab ya kasa hakuri har sai da yaje ya sami mum da maganar.
"Mum, tambaya nazo nayi dan Allah"
Murmushi mum tayi tace "nasan zakazo don yin tambayar ai"
"Mum ina take Please?"
"Me kake so?"
"Matata nake so mum" ya fad'a in funny way.
"Wai yaushe ka zama haka turab?"
"Tun ranarda muka dawo hospital, Ni ina zargin likitan nan fah mum..... inaga shi yamin allura na zama haka yanda kika gani nan"
Pillow ta dauka da niyar jefamasa ya hade hannunsa wuri ɗaya "I'm so sorry mum Wallahi ba shi nazo inyi ba, dan Allah ina leeyana"
"Turab....!, ta kira sunansa babu wasa a fuskar ta.
Ganin haka ya saka shima turab din ya shiga taitayinsa.
"Na'am mum"
"Kasan yanda yanayin daurin auren nan naku ya kasance ko?, hasali ma ba kowa yasan da shi ba. Hatta justice bai san kai aka aurawa leeyana ba sai daga bayan nan ya san haka, kuma kaga auren nan anyishi babu wani shiri kho? To yanzu Alhmdullillah tunda mun fahimci kuna son junanku za'a qara daura auren nan bayan sati daya, amma gskiya Ni sati daya yamin kadan saboda ina so in gyara 'ya'yana kamar yanda akeyiwa sauran 'ya'ya, da kyar justice ya yarda ya mayarda shi wata daya, kafin nan kuma munaso gobe zamu wuceh Maiduguri da ita da kuma qanwarta mu nunawa families dinmu su"
Cikin tsananin bakin ciki yace"wata d'aya mum?"
"Eh ko yayi kadan?"
Wata irin zufa yaji tana karyomasa tun daga tsakiyar kansa har tafin kafafuwan sa "mum Dani za'a je?"
"Ai yanzu haka ma kana can"
"Haba mum meyakai ga wannan, dan Allah mum ku barni na ganta Please kafin ku wuce"
"Idan mun dawo dai ka ganta, kuma ko mun dawo ba ranar ba sai ranarda aka kaimaka ita gidanka"
"No mum....., Dan Allah karki yankewa d'an ki wannan hukunci haba dai mum"
Ganin turab naso ya wargaje musu plain ya saka tace masa "tana gidan maman twins kaduna, na baka damar kaje gobe misalin ƙarfe sha daya na rana, idan ka wuce haka bazaka samemu ba"
"Mum me zai hana naje yau"
"Sai gobe nace maka! Idan kuma kaje yau wallahi zan gayawa maman twins kar ta barka ka ganta"
"Na tuba mum, yanda kikace haka za'a yi"
Washe gari tun karfe tara na safe ya fara shirin tafiya, ya kira zafaran da Fahad ya sanar musu.
On ready su suna Abuja, saboda haka basu tsaya wani bata lokaci ba suka zo suleja gaba ɗaya harda matansu, fahad gidansu zohal ya kaita kafin su dawo. Shikuma zafaran ya ajiye Aleena gidan mum Saboda sanin da ita za'a yi tafiya zuwa Maiduguri yau.
Sai da mum ta fahimci su turab sunyi nisa da tafiyarsu sannan suka dauki hanyar zuwa Maiduguri suma.
*
Bayan awanni biyu. turab, fahad da zafaran ne zaune a parlourn mummy-neesah suna cin abinci.
Su fahad sai tsokanarsa suke. "Yanzu duk girman nan naka anyi maka wayo fa chief military health service"
Tsaki yayi, bai kula ba yaci gaba da cin abincinsa. "Turab ka kira kaji ko sun sauka lafiya"
"Bazan kira ba......!, ai kaima matarka tana cikin tafiyar me zai hana ka kira kaji kai da kake son ji"
Dariya suka qara shekewa da ita fahad yace"mum dai ba ganin leeyana ta turo mu ba ganin abincin mummy ta turo mu"
"Ehh wallahi ka fahimci karatun" Zafaran ya fad'a yana dariya.
Haka sukaci gaba da tsokanarsa shikuma yaqie biyemusu har suka gaji sukayi shiru.
Haqiqa mum bata sanarwa turab da gaskiyar inda leeyana take ba, domin da sukazo kaduna mummy-neesah ta tabbatar musu da ba wata leeyana da ke zaune a gidan. Mum ta fad'a musu haka ne kawai.
****
A bangaren su leeyana kuma sai bayan la'asar liss rana na qoqarin shigewa suka iso Maiduguri, basu zarce ko'ina ba sai gidan ummansu mum fanaya. Su biyar ne a motar, mum da kuma Aunty Rafa'at sai Aleena da kuma leeyana.
Sosai suka sami kyakkyawar tarba domin mum kam ƴar gidace ba wanda bai santa ba, sauran ne ba'a sani ba.
Mahaifiyarsu su mum wacce suke kira da umma tace "fanaya da baki kuke tafe haka"
"Eh wallahi umma baki ne kam, amma a gidan nan ba baqi bane gskiya"
"Toh......,,,,, Aikuwa kema kanki baquwarce"
"Ah Ni ba bakuwa bace umma, yawwa Umma inaso atara mutanen gidan nan namu gaba daya, akwai bayanin da nakeso nayi da kowannen su"
"Lafiya dai koh fanaya?" Ummah ta tambaya.
"Lafiya kalau wallahi ummah nidai na buqaci hakan ne kawai"
"To shikenan bara na saka a gayawa kowa zuwa