BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   44 / 61

129K to 132K   out of 180.4K words

Musulunci kuma amana da yarda sosai ta kara shiga tsakanin mu da turab har nake jinsa kamar dan uwa na jini, shima yake jina haka.
Mahaifina ma yana matuƙar kaunar turab, shima iyayensa na matukar kauna ta, ta dalilin hakane muka sada mahaifanmu domin su san juna, kuma ba dan albarka cin turab ba ko kusa mahaifina bazai yarda na zo Nigeria ba. Wallahi lewah saboda ke na dawo kasarnan,

Saboda nasan abunda ya faru da ke tun kafin mu tafi Allah ne bai kaddara zan fara bincike ba tare da naje Mexico ba,

Wallahi kaso chasa'in na dawowa ta Nigeria saboda kene lewah kisani ina sonki, ina kaunarki, soyayyar ki ta zamo jini da numfashina, ba wanda zai fita batare da nabar duniya ba, tun Ranar da nadawo shekaru biyu kenan, wallahi ba rana ta Allah da zata fito ta fadi ba tare da nayi bincike akan maharan da suka kawo muku hari ba, Dan Allah ki saka wannan a ranki leeyana wallahi billahi bantaba son wani abu a duniya daya wuceki ba, idan har kika cire iyayena, leeyana bana ganin yuwar mallakarki, amma wallahi nasan da soyayyarki zan mutu a cikin raina, ina ji a jikina bazan sameki ba leeyana, narasa yanda zan misilta sonki a zuciyata, inda ace zaiyu zaki ga gaskiyar sonki a jinina ina kaunarki na fad'a na nanata." Zafaran ya faɗa hawaye na gangarowa a kumatunsa.

Ba leeya ba hatta turab da kuma su Papu sai da sukaji tausayinsa sosai.

Mikewa turab yayi a sanyaye yaje har gaban Zafaran ya tadashi tsaye, muryar sa na rawa ya kalleshi yace;

"Abokina hakika na cika babban azzalumi idan na rabaka da leeya wallahi nasan hakkinku bazai barni ba, amma inaso kasani kamar yanda kake jin sonta haka nima nakeji wata kila ma nawan zai zarce naka, nayi alkawari koda soyayyar ta zata zamo ajalina bazan rabaku ba, dan Allah ka yafemin abisa kuskuren rashin sani da kuma kamuwa da soyayyarta danayi"

Yana gama fadin haka ya juya ga leeyana itama har gabanta ya d'ingisa domin ji yake kamar zai fadi saboda nauyin da jikinsa yayi masa.

"Leeya na rokeki da kiyi haƙuri ki yafemin iya abubuwan da namiki a rayuwarki da wanda kika sani harma da wanda baki sani ba, wallahi ki sani duk abunda nake soyayyarki ce ta janyo ba wani abu ba. amma nan gaba zaki gane nufina akan duk wani abu da nayi miki"

Yana gama fadin haka ya juya zai fita sai dafe kansa yake saboda tsakanin ciwo da yake masa.

Da mugun sauri dad ƙarami da zafaran suka isa gareshi tare da rike shi suka zaunar dashi ganin kamar zai fadi.

Duk irin alkunya da kawaicin da mum fanaya take hankalin ta yayi mugun tashi ganin yanda kamannin sa suka sauya, ga kuma alamomin tashin ciwonsa sun fara bayyana.

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, justice muje asibiti don Allah kar ya rasa ransa"

Da sauri mummy-neesah da haji suka kamata itama suka zaunarda ita, "kwantar da hankalinki hajiya fanaya, a yanzu hankalinsa bai gushe ba kuma ciwon nasa bai tashi ba koh, muna da damar da zamuyi masa magana yanzu kuma abashi abunda yake bukata, hakan ne kawai zai dakatar da damuwa da tashin hankalin da ke tunkaroshi"

Tun kafin wani yayi magana a cikinsu da sauri zafaran ya riko hannun leeyana ya haɗa dana turab ya durkusa a gabanta idanunsa na zubarda kwallah yace;

"Leeyana don Allah kar muyi sanadin rai!, wallahi turab ma yana sonki, da alama yafini sonki Allah ne kawai ya sani, I'm so sorry to say leeyana kije ki zauna da turab na barmasa ke"

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me kake fada haka zafaran kana nufin ka sadaukarda da soyayya ta ga waninka, kenan kamin adalci kake gani, meyasa ka fiye son kai? Ka sadaukarwa abokin ka da soyayya ta ne saboda kanason farin cikin sa nikuma ina nawa farin cikin?"

Tun kafin ta karasa fadar abunda zata fada Papu ya katse maganar ta cikin bacin rai yace;

"Ka gani ko turab, kaga abunda ka janyo wa kanka kho? Tun a farko da muka baka wannan yarinyar a matsayin matar da zaka aura da ace ka nuna mata so saɓanin tsana da bazata nuna rashin so a gareka kiri-kiri ba, wallahi Ni kaina nasha ganin kana azabtar da wannan yarinyar amma nayi shiru saboda gudun abunda zaije ya dawo, idan baka sonta an baka zabi a cikin yan uwanka na gidan nan kuma kannen ka, amma ka qie haka kake so ayita zuba maka idanu, wallahil Azeem yau ba gobe ba zan daura maka aure da duk wanda naga dama"

"Zafaran!"

"Na'am Papu"

"Kaima ka shirya yau zan daura maka aure"

"Ba damuwa Papu Allah yasa hakan yafi zama alƙairi, amma Papu don Allah...."

"Karka sake kace komai Zafaran na gama yanke hukunci kuma yanzu zan kira mahaifinka na gaya masa"

"Leeyana my daughter, kiyi hakuri kinji, don't confuse yourself, kuma kiyi haƙuri a yau ba sai gobe ba kema zan daura miki Aure"

Leeyana bata iya cewa komai ba, ta daga kai kawai alamar taji kuma tayi biyayya, hawaye na kwararowa a idanunta.

"Na sallami kowa" papu ya faɗa yana shirin barin part din rai a matukar 'bace.

Daga gefensa yaji muryar dad ƙarami yana cewa;

"Idan har na isa dake, kuma kina kallona Matsayin mahaifinki da kike yiwa biyayya da d'a'ah yau zan daura miki aure Rukhshanah, kuma yanzun nan zan biya sadaki"

Da sauri Rukhshanah dake rike da kafadar leeya ta dago kanta ta kalleshi tace"kafi da nan dad, wallahi bana fata Allah ya kawomin ranar da zaka yi hukunci akaina na nuna baiyi min ba koda a fuska ne balle a zuciyata, nasan bazakaymin zaben tumun dare ba, kuma nasan bazaka zabamin mijin da bai dace dani ba, koda kayi hakan wallahi dad nayi maka alkawarin zama dashi har mai rabawa ta raba, kuma nayi maka alkawarin baza'a sami matsala a ta bangarena ba in sha Allah"

"Kin cika 'yar halak Rukhshanah, Allah ya saka miki da alƙairi, ya biyaki ladar biyayya"

Daga haka suka fice gaba daya har turab dinda hankalinsa ya fita daga jikinsa, domin bai san ma wane matsayi zai daura kansa ba tsakanin mai hankali da marar hankali.

"Leeya kije kiyi wanka ki fito ki sameni a parlour" cewar mum.

"Nayi wanka da asuba mum, da dai wani abu zanyi miki sai muje"

"Ina meenal?" Mum ta kuma tambaya.

"Meenal ta fita waje tun lokacin da ciwon ya-Turab ya soma tashi"

"Okay zo muje"

Fita sukayi sashen gaba dayansu, sai bayan fitowar su ne suka lura ba kowa a cikin yan gidan.

Zama sukayi a parlourn ƙasa har mum ta buɗi baki tayi magana sai ga khulud ta shigo da waya kare a kunne ta.


Sai da ta kammala wayar ne ta gaishe da mum domin basu gaisa ba tun da safe.

"Mum ba'ki mukayi, kuma suna so su gana da ke da kuma papu. Amma naga fitar sa da su dad ƙarami nasan ba nisa zasuyi ba"

"Eh ba nisa zasuyi ba, sunje sanarda daurin aure ne babban masallacin juma'a"

"Wallahi mum abubuwan da suka faru sun saka duk na sha'afa da batun daurin auren nan na ya-fahad"

"Ai ba fahad kadai za'a daurawa aure ba a gidan nan"

"Ban...gane ba" khUlud ta faɗa tana 'yar i'kina

"Eh, har turab da kuma zafaran sannan da leeya da shi fahad din da kuma kanwar leeya Aleena"

"Wallahi mum bangane nufin kiba taya haka zata faru, wa ye zai auri Aleena kuma"

"Fahad ne kadai yakeda tabbacin wacce zai aura, amma duk sauran ba wanda yasan wanda zai aura"

"Gaskiya akwai gyara a cikin lamarin nan mum, duk meya janyo wannan?"

Mum na shirin yin magana a karo na biyu wayar khulud tayi kara alamar kira.

Da sauri ta dago wayar tana dubawa "mum ba'kin suna waje pah"

"Su waye wai??"

"Zaki gansu idan sun shigo mum, Bara na je na shigo da su yanzu"

Mum bata furta komai ba haka ma leeya da kuma mummy-neesah domin su kadaina a parlourn Yanzu.

Fitar khUlud ba jimawa ta dawo tare da baki biyu mace da namiji, macen ta ɗan manyanta shi kuma namijin saurayi ne matashi fuskar sa Fal da annuri.

Da sallama suka shigo parlon gaba ɗaya har khUlud din dake biye dasu, saurayin na bayanta sannan sai matar ta shigo da karshe.

Fuskar mum cike da mabayyanin mamaki take bin matar da kallo kafin ta iya karfin halin hade kalmomin da ta samu damar yimata Magana dasu.

"Dayammah!, kece ko mafarki nake?"

"Ni ce hajiya barka da yau, ya gidan, ya dawainiya"

"Alhmdullillah dayammah, yaushe gari dan nasan bakya nan tsawon wannan shekaru duk baki waiwayo muba"

"Ina nan ba inda naje hajiya, kawai na dan ja baya daku ne na wani lokaci yanzu kuma gashi na kara dawowa rayuwarku"

Cikin rashin fahimtar inda zance dayammah ya dosa mum tayi mata tayin wurin zama ta kuwa zauna.

Gaisheda mum da kuma sauran mutanen da ke parloun id yayi, khulud kuma hakan yayi mata dadi sosai ganin bai yi girman kai ba, zama sukayi anata firar yaushe gamo tsakanin dayammah da mum, har mum ke tambayar dayammah a inda ta kuma haduwa da khulud a karo na biyu.

Labarin duk abunda ya faru tsakanin su da khulud ta gayawa mum, inda suke firarsu su biyu kadai, sannan ba kowa yakejin abunda suke fadi ba.

Girgiza kai kawai mum tayi tana kallon khUlud tana dan murmushi, "yaran zamani sai a hankali, kalleta kamar bazata iya haka ba"

"Mena yi kuma mum" khUlud ta faɗa a dan shagwaɓe.

"Ungo nan" mum ta fada tana ware mata hannu.

Kara zum'buro baki tayi, cikin rashin Sa'a idanun su suka sarke dana idrak, hararar wasa ya sakarmata da sauri ta washe baki tare da kashe masa ido ɗaya.

Mum da ta lura da su murmushi mai sauti kawai ta sake ba tare da ta kalli inda suke ba.

Fannah da Rukhsha ne suka shigo parlon bakinsu dauke da sallama, wucewa rukhsha tayi inda leeya ke zaune tayi mata Rad'a a kunne.

"Yahyah wallahi yau ina cikin madaukakin farin ciki"

"Farin ciki kuma budurwa tho farin cikin me? Ko don saboda za'a daura miki aure"

"Ohh, wallahi fa kinga Ni har mantawa nake da batun auren nan ina ganin komai kamar wasa"

"Hmmmm, wallahi nafi ganin sa kamar wasa budurwa, to amma gamu nan mun zubawa sarautar Allah idanu"

"Tau Allah ya yi mana jagora yayata, Bara na gaida bakuwar mum"

"Dan tsaya!" Leeya ta faɗa lokacin rukhsha ta tashi zataje ta gaishe da su mum.

Dakatawa tayi daga tafiyar da take, dayake kuma ba wata tazara a tsakanin su tace "ya akayi"

"Baki bani amsar tambayar da na miki ba"

"Wace tambaya kuma?"

"Farin cikin da kikeji a yau, menene dalilin haka?"

"Yayatah, kin manta yau aka shaidar mana da za'a daura miki aure kho"

"Ban manta ba Aleena, amma ko ya ne inason ganin ki cikin farin ciki"

"To zaki ganni cikinsa a yau kinji"

" menene silla" cewar leeya.

"Yahyah-leeyana, alqawarin ku da mum ya cika yayata, yau ne ranar da zata fito miki da darajar ki, ta kuma bayyanar dake a idanun mutanen da ke kallonki ba komai ba"

"Bangane nufin ki ba qanwata"

"Ina nufin yau, a yau din nan zaki buɗe fuskar ki, ki kuma bayyanar da asalin halittarki ga ko waye da aka aura miki"

Da dan karfi Rukhshanah ke maganar saboda haka ne yasa sauran mutanen suka mayarda hankalin su kansu.

"Baki gane nufina ba, so kike inyaye hijabin da nayiwa maganar lullubi dashi, yahyah-leeyana ina nufin a yau ce rana mafi daraja a gareni, domin a yau ne zaki yaye mayafin da ke fuskarki ki bayyanar da fuskar ki ga kowa dayake kokwanto a kanki"

Gaban leeya ya yanke ya fadi, haƙiƙa Aleena ta fadi gskiya. Sai dai taya gaskiyar ta zatayi amfani alhali ita kanta tafi jin dadin haka, duk da tana kwadayin ganin fuskar ta amma hakan bai sakata jin cewa zata iya cire mayafin da take amfani da shi shekara da shekaru ba.

"Kin manta ko, na tuna miki idan mantawa kika yi. Saboda haka ki shirya tarbar sabuwar rayuwa" cewar Rukhsha ta wuce kawai ba tare da ta saurari abunda zai fito Daga bakin leeya ba.


Tunda ta doso inda su mum ke zaune Annah dayammah ta kafeta da idanu kamar zasu fado kasa saboda tsanin mamaki, ba mum dake kusa da ita ba hatta ita kanta rukhsha da kuma meenal, da fannah, da mummy-neesah dake shigowa yanzu sun lura da irin kallon da dayammah ke yiwa Rukhshanah.

Idrak ma da ya lura a yanzu da sauri ya karaso gaban mahaifiyar tashi ya duka saitin kunnuwanta yace "Annah menene haka dan Allah ki nutsu mana, duk mutanen da ke parlourn nan idanunsu akanmu yake, munzo yin abu mai muhimmanci a gidan nan, dan Allah ki daina kallo irin haka wallahi wani bangaren irin wannan kallo haram ne"

Saurarensa kawai take, ko motsi batayi idanun ta kawai ke dan yawo a hankali kan rukhsha na, dan ta'bata yayi kad'an, da sauri ta zabura kamar wacce ta farka da nannauyan bacci.

"Annah Lafiya?" Id ya tambaya a tsorace saboda yaga kamar mood dinta ya changer.

Da mamaki itama mum ke binta da kallo kafin ta furta "lafiya dai?"

"Hajiya dan Allah wannan yarinyar su waye iyayen ta?"

"Ban gane me kike nufi ba" cewar mum.

"Eh ina nufin su waye suka haifeta?"

Jin wannan tambaya da annah tayi ya saka leeyana kureta da idanu sosai ita kuma Rukhsha ta dan ja baya tana kara shigewa jikin mum, harga Allah ta fara tsoron wannan matar, ita bata ma yarda da ita ba kwata kwata.

"Ga mahaifiyar ta can kina gani, mahaifinta kuma on ready nasan kin sanshi tunda a gidan nan kike can baya, gahees ne mahaifin da kanin justice"

"Allah sarki, ai kuwa basuda yanayi da wannan matar gaskiya, sai dai ko dadyn twins din ta biyo"

"Eh shi ta biyo, dashi take kama ai" mum ta fada a fili, a zuciyarta kuma tunani take, batasan iyayen waɗan nan yaran ba me zata dinga cewa a game da haka, "ina ga lokaci yayi da ya kamata nasan wani abu"

"Me zai hana ki tambayi dayammah dalilin yin tambayar da tayi"

Wani sashe na zuciyarta ta faɗi haka.

Kallonta ta mai da ga dayammah da har yanzu bata daina kallon Rukhshanah ba kamar zata cinyeta tace "to amma dayammah meyasa kika min wannan tambayer"

"Wallahil Azeem hajiya ban taba ganin asalin kama ba kamar yanda nagani ga wannan yarinyar"

"Kama kuma, to da wa"

"Da wani bawan Allah dan uwan mijina, mahaifin wannan yaro idrak"

"Ikon Allah, to ai kama ce kawai, menene sunan wanda take kama dashi din, zai iya yiwa sun haɗa jini shi"

"Sunansa HAMRAZ, 'yan biyu ne shida mijina MAHARAZ"

Wani mugun wuntsilowa Aleena tayi da sauri ta dira gaban dayammah bata san lokacin da ta riko hannun ta ba, kusan lokaci daya suka iso gaban ta tare da leeyana........................✍🏼









EP.43




_____________________"Rukhshanah kunsan wanda take magana?"
Mum ta faɗa da mamakin ganin yanda suka iso wurin.

Murya na cracking ta daga baki da kyar ta furta "mun sanshi mum"

Sai a lokacin mum ta tuna da sunan HAMRAZ idan ba mantawa zatayi ba ai kamar da sunan leeyana ke amfani har a makaranta, kenan mahaifinsu ne kanin mijin dayammah.

"Dayammah kinsan wani abu game da shi?"

Ita kuma dayammah ta kure yaran da idanu kawai ƙwallah na zubowa a cikin kurmin idanunta.

"Hakika an ci amanarku, an zalunci ku, da mahaifin ku gaba ɗaya, wallahil Azeem hakkin ku dana sauran mutane ba zai taba barin fairozha ba"

"Fairozha!, dan Allah wacece fairozha?" Sukaji muryar haji ta fada tana karasowa wurin da sauri.

Murmushin fuska kawai dayammah tayi domin tasan wannan rana zatazo a cikin zanen rayuwarta.

"Nasan zaki so sanin wacece fairozha hajiya mainah, amma kisani sanin fairozha a bakina babban bala'i ne a wurina, amma nayi alqawarin duk ranarda Allah ya bayyana min wani daga dangin ta, zan sanar masa da komai in ya so nima ta tsafaceni kamar yanda take tsafi da sauran mutane"

Matsowa sosai haji mainah tayi, har wata zufar tashin hankali ke keto mata.

Idan bazata manta ba, ranar da waasibudden mijinta wato kakansu khulud namiji kenan, ranar da zai mutu da sunan wannan baiwar Allah ya mutu a bakinsa wacce basusan ko wacece ba.

Ba iya sunan ta yake fad'i ba, ya fad'i abubuwa da dama dayasani a game da ita Kamar kuma yana ganinta kusa dashi, haka ya koma kamar wani mai rauhanai, abun sai ya baka tausayi, sai ji kake yana fadin;

"Fairozha kiji tsoron Allah, dan Allah ki tuba ki koma ga Allah. Wallahi Allah ba azzalumin kowa bane kuma yana ganin duk irin zunuban da kike tafkawa saboda son duniya kawai, kin sadaukarka da rayuka da dama saboda rayuwarki kadai, Allah Allah ba zai barki ba"

wani wahalallen numfashi ya ajiye zufa sai karyo masa take yana hakiiii kamar wanda yayi mugun gudu.

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, wallahi fairozha hakkina bazai barki kici gaba da rayuwa a doron kasa ba, jinina fa kike zukewa, kuma kina katsar min 'ya'yan hanci"

"Fairozhaaaaaa!!!!!" Ya furta da karfi daga haka bai kara motsi ba, idanunsa suka kafe, ya sandare wuri komai nasa ya daina motsi.


Koda hajiya mainah tazo nan a tunanin ta sai ta dago kai idanunta duk sun cika da hawaye ta kalli dayammah tace "dan Allah menene tsakanin ta da marigayi waasibudden"

Daga inda Aleena ke zaune itama sukaji tace "muna muna son sanin wani abu daga ahalin mahaifin mu ko ya yake dan Allah"

Kallonsu tayi gaba ɗaya ba tare da ta furta komai, ganin haka ya saka ba wanda ya kuma cewa komai tsakanin su, duk suka tattara hankalin su wajenta suna sauraron abunda zatace.

Cikin juriya da yarda dakai ta furta a zuciyarta "fairozha yau zan bude asirin da na dade ina boyewa domin tsira da Rayuwa ta, amma a yau gashi zan bayyanarda shi ga wadansu domin suma su tseratarda rayukansu, nasan babu wani abu dazai sameni fa ce yana rubuce cikin kaddarata. Idan kika ga kin cutardani to da yardar Allah, bakida wani karfi ko iko batare da Allah ya baki ba"

Tana gama fadin haka a zuciyarta, sai taji kanta kamar a mafarki ta daina ji da ganin komai, ganin kanta take zaune a parlourn, amma kuma mutanen da ke cikin parlourn kafin ta kwatanta bada labari, ba su bane yanzu da ta gama tunanin ta.

Ji take kamar an daureta bata iya motsa ko dan yatsan ta, babban abunda ya bata mamaki ganin waɗannan mutane.

Bata san su ba, kuma bata tunanin ta taɓa saninsu duba da yanda yanayin suturar jikinsu take.

Wata doguwar bakar riga ce wacce takai har kasa sosai tana sharar kasa, baka iya hango komai na jikinsu face fuska, kuma ko fuskar

44 / 61