BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   31 / 61

90K to 93K   out of 180.4K words

bari hakan ta faru Domin gujewa tasowar wani abu.
Wannan shine takaitaccen bayani kan su haji mainah da ƴaƴanta da jikokinta.

A ɓangaren su leeya kuwa..........✍🏽


















BAYAN WUYA.......









By RUMANA M DIGGI







EP.33



____________zaune suke gaba ɗayansu a ɗaki ɗaya daga part dinsu khulud, ba sosai aka cika zama a cikinsa ba sai idan anyi baki haka, a kafff part ɗin ɗakin yafi ko wanne girma da faɗi domin gado huɗu ne a Cikin Dakin royal bed.

Zaune suke gaba ɗayansu a kasan Centre carpet, kowa ya sami abokin da yake fira dashi kuma sunayi a tsakanin su gaba ɗaya.
Airah ce ta ɗaga murya tace "Mayah wai ina fannah da Rukhsha"

"Wallahi kamar kinsan abunda zan tambaya kenan wata sabgar ta ɗaukemin hankali"

"Tau badariyyah uwar ƙarya sai yanzun dana tambaya ne kuma sabgar ta dawomiki da hankalin ki kho"

"Wallahi Airah bakida mutunci muna nan dai matsayin mu ba'a chanjawa tuwo suna mune dai ƙannen iyayenki"

"Mtswww, ƙannensu kikace ai ba ƙanne na ba"

"Tau iyayen masifa kun tambayeni twiney da Rukhsha amma kuna nan kuna zabga ruwan bala'i ku baku zaman lafiya ne"

"To malama mayah mun zauna lafiya, meya hana fannah zuwa"

"Hmm kedai bari banji daɗi ba ai rashin zuwan su, Ni banmasan Allah ya shirya khulud ba nacewa mummy wallahi idan nazo ban tararda ku ba bazan tsaya ba domin nasan bazamu wanye ƙalau da khulud ba ashe ma ta shiryu"

"Ai ke bari wallahi dah can baya ina cikin duhu ashe mutane rahma ne baramma ƴan uwanka, nidai ku ƙara yafemin. Ke kuma ana tambayarki sai surutan banza kikeyiwa mutane"

"Tau na daina surutan, kinsan ba skul ɗaya mukayi apply dasuba, su suna zuwa har yanzu basu kammala exams ba, mu kuma munyi tun wancan sati, shiya hana suka zo"
"Okay tau Allah ya basu Sa'a"

"Ameen kudai ƴan uwana muna godiya sosai"

"Ke ƙarfe uku da Aunty beelkisu tace za'a fara meeting, kunga saura mintuna bakwai uku tayi fa"

Miƙewa wasunsu suka yi da sauri suna fara shirya wa domin family meeting ɗin nasu nada dokoki masu tsauri sosai, kuma a dokar meeting ɗin nasu abune da kowa ya sani idan baka cikin familyn baza'a je zaman da kai ba, idan ma kayo rakiya ne saida kajira wanda ka rako kafin a kammala taron.

Haka ne ta faru ga leeya domin itama tasan da dokar tun kafin yau.

"Leeyana ki tashi muje ai kema kinzama familyn mu yanzu"

"Kuje kawai sis-khulud sai kun dawo, kinga Ni bacci ma nakeji idan kuka dawo ku ta dani" leeya ta faɗa tana hayewa kan ɗaya daga cikin gadajen da ke ɗakin.

Ba yanda basuyi da ita ba kan ta tashi ta bisu amma taƙi, har meenal ma da tunda suka shigo ɗakin suke ta surutu da ita tayi tayi amma furrrr tace bazata je ba.

Suna cikin hakane kuma sukaji ƙarar wayar leeya daga can gefe inda ta tashi, da sauri khulud ta miƙa hannunta ta ɗauko wayar tare da dubawa.

"Oga ya turo saƙo" ta faɗa cikin sigar zolaya.

Ƴar harara leeya ta jefamata da idanuwanta masu tsoratarwa khulud na kaɗuwa tace "ahhh rufamin asiri karɓi wayarki, kidaina harara ta kar idanun nan su cinyeni, kunga kuzo mu tafi wannan ba zuwa zatayiba kunga ma masoyinta ya zo suyi fira"

"Yana ina" Aneesa ta faɗa a ɗan tsorace.

"Gaskiya Aneesa ke doll ce ana maganar ya turomata saƙo kina wani maganar yana ina"

Wawan duka Aneesa ta sakarwa Airah a bayanta "shegiya mara kunya badan Aunty Safiyyah yayarmu bace danace ita ce doll, mara mutunci kawai"

Da sauri Airah ta daga hannu zata rama dukanta Aneesa ta yima ita kuma Aneesar ta fita da gudu, Airah ta bita a baya tana kukan shagwaɓa sai ta rama dukanta.

"Leeya mudai mun tafi sai mun dawo, karkiyi bacci kinji idan na dawo sai muci gaba da fira"

"Tau meenal sai kun dawo, Allah ya tsare"

"Okay be safe, muna gaida mijinmu"

Cikin jin kunya ta rufe fuskarta da pillow tana dariya a hankali, su kuma suka juya suka fita.

Suna fita kuwa taci gaba da firarta da masoyinta, ta sake sosai dashi kuma harga Allah tana so da ƙaunar sa domin Allah.

Itama tanaji a ranta ko shi wanene yana sonta kwatankwacin yanda take sonsa wata ƙila ma ƙaunarda yake mata tafi wacce take yi masa.








A can ɓangaren su mum kuwa anyi taron ne a farfajiyar gidan kuma an tattauna kan abubuwa da dama da kuma amfanin sada zumunci, an kuma faɗakarda sauran waɗanda suke tasowa kan su riƙe ƴan uwansu da kuma zumunci sosai, domin zumunta ibadace, kuma al'umma rahmace. Bayan haka anyi musu nasihohi da dama kan komai, musamman fahad da nauyi ke shirin rataya akanshi. Sosai taron ya tafi yanda akeso, kuma aka watse lafiya ba wata rigima ko sa in sa ko kuma tashin hankali.

Iyayen yara kuwa sai faman haɗa kan iyalansu sukeyi domin komawa gida, inda meenal da badar sukacewa mahaifiyarsu su ba inda zasuje suna nan sai anyi biki, Aneesa kuwa tana ganin haka itama ta sanarda tata mahaifiyar, Airah ma haka, sannan mayah itama taje ta samu mummy da maganarnan. Ba abinda iyayensu suka iya cewa domin kuwa duk dangine kuma duk an riga anzama ɗaya.

Sosai khulud tayi farin ciki da haka sai tsalle tsallen murna suke suna gani tare zasu shirya komai na bikin.

Da murna suka koma cikin gidan inda suka tarar da leeya tayi aiki tuƙuru wajen ganin ta tsaftace gidan gaba ɗaya, kana shigowa kanshin turaren tsintsiya mai tsada ne zaya fara tarbarka, sai kuma daddaɗan kamshin girkin da suka ƙara banbance wane kalar abincine.

Da sauri suka isa part ɗin ta domin ba ƙaramar yunwa sukeji ba, kuma hakan ya saka wasu daga cikinsu suka ƙara jin leeya ta kwanta musu sosai a rai.

Haka ma su mum da suka shigo suka tararda wannan ƙoƙari da leeya tayi, sosai ta birge wasu daga iyayen saboda ko wace uwa tana buƙatar ganin hakan ga ƴarta.
Bama wanda yakai mum farin ciki domin tun sa'adda aka kammala family meeting ɗin take ta tunanin abunda zata samarwa haji da sauran ƴan uwa da suka rage basu tafi ba.
Sai kuma ta dawo gidan ta tarar leeya ta girka isasshen abinci.

"Fanaya, dama kunada ƴar aiki ne amma banganta a gidan ba tun jiya danazo"

"Ah ah haji wallahi bamuda ƴar aiki, wannan yarinyar da tayi aikin nan ƴa tace ƴar ƙawata data rasu"

"Allah sarki, wacece yarinyar nan amma bangantaba kho"


"Itace wannan mai saka niqab idan kin kula a tare suke dasu khulud da Aneesa"

"Ahhh, itace Wannan yariyar mara son hayaniya kho, ɗazu naganta sai fama muke da ita kan ta shiga cikin su meenal suyi fira amma taƙi, sai daga baya nagane hayaniyarce bataso"


"Eh wallahi haka take amma wani lokacin kam tana magana haka tayi farkon zuwan ta gidan nan mun jima da ita kafin ta sake da mutane"

"Allah sarki tanada hankali gaskiya tayi ƙoƙarin yin aikin nan haka, ita dai bata jin wuyar yin aiki ɗazu ma naga ita ta girka mana abincin rana, kuma yanzu gashi ta girka na yamma Allah yayi albarka"


"Ameen haji, muje sashenki na zuba miki ruwa kiyi wanka idan kin fito sai na zuba miki abinci"

"Kedai ki barshi kawai zan iya wallahi, je kiji da su sahiya wato (Safiyyah) ki zuba mata taci abincin kinga mahaifinsu samirah wato (Airah) yana waje yana jiransu.

"Ni gaskiya kaka-haji kidaina kirana sahiya ni ba haka bane sunana idan baki iya faɗin sunan mutum ba kidaina mana ki bari a koyamiki"

"Ni bazan iya lankwashe harshe ba da wani game leɓe wajen faɗin sunankun nan na zamani"

"Haji Safiyyah ne sunan zamani kuma"

"Eh mana mu sahiya muka sani kuma shi zamu faɗa Ni kinga tafiyata ma"

Haji mainah ta faɗa tana wuce sashen ta cikin tafiyar ta ta tsofaffi.

duka gidajen ƴaƴan nata maza an ware mata sashenta inda zata riƙa zama duk sa'adda tazo gidan ɗaya daga cikin su, ko suleja ko kuma Kaduna, ko Abuja.

Washe gari su khulud suka haɗa karfi su duka shida sukayi aikin gidan tun kafin su mum da papu su tashi. Dayake gidan ma ba wani aiki sosai domin duk mafi yawan ayyukan leeya tayi tun jiya.

"Tau Mr. Chief, yanzu ke zaki shiga kitchen ki mana girki kho wallahi jiya girkin ki yamin daɗi sosai har sarauyina saida na bashi labarin abincin kuma yace idan kika tashi shiga kitchen na je nagani idan munyi aure nadinga yi masa" badar ta faɗa cike da rashin kunya.

"Bazata jeba dan bakida tausayi jiya tayi mana abinci har sau biyu kuma yau tayi kamar wata baiwa, leeya kije ki huta Bara na shiga kitchen na girka mana"

"Nop Aneesa ki bari naje kawai ai ni bana gajiya da yin girki, saboda haka kowa a cikin ku ta faɗi kalar abincin da takeso a girko mata"

Har badar ta buɗi baki da nufin faɗin abunda takeso meenal tace"muje na tayaki muyi tuwon doya da miyar cabbage da crayfish kawai, duk wanda zai ci yaci wanda bazai ciba kuma ba wanda ya tare masa hanyar kitchen" bata jira cewar kowa ba ta janye leeya daga wurin suka koma kitchen area.

Mintuna kaɗan suka gama haɗa komai da komai dai-dai lokacin da papu da mum suka sakko.

"Ahhh ɗiyan albarka sannunku da aiki, Allah dai yayi albarka"

"Ameen papu, barkanku da safiya"
Haka su meenal suka gaida su mum da papu cikin farin ciki da nishaɗi tare da gabatar musu da girkin da sukayi musu.

Daga nan kuma aka zubawa haji nata girkin leeya da meenal sukaje suka kaimata, koda suka tarar da ita ma tana shirin zuwa sashen nasu sai ta fasa zuwan sakamakon Abincin ta da aka kawo mata har nan.

A mutunce leeya da meenal suka gaida haji bayan ƴar guntuwar fira da sukayi sannan suka tafi suka barta Domin taci abinci.

Da suka fito basu tsaya ko ina ba sai hanyar da zata sadasu da sashen su khulud, abun mamaki koda meenal da leeya suka iso sashen Sai suka tarar da su Mayah gaba ɗayan su sun dawo sashen.

"Badar har kunci abincin ne" ta faɗa cikin sanyi ta.

"No sis-leeya mum da papu muke jira idan sun gama sai muje parlorn domin cashewa zamuyi, wai Aneesa ce take faɗin ta fini iya rawa, shine Airah ta aza mana competition mayah da khulud suka ce su zasu bayarda kyauta ga duk wanda yafi iyawa. To shine muka dawo domin musaka kayan yin rawa"

"Hummm, to Allah ya kyauta muje kho meenal"

"Badar wai yaushe zakuyi hankali dan Allah, ita rawar ce zaku fita har parlour bazaku tsaya a nan ba in ma rashin kunya kuke ji"

"Aunty meenal kidai ki yi shirunki ba abunda zai hana mana rawar nan saboda haka kiyi shirunki kawai, kuma ma ai speakers ɗin ɗakin nan basuda ƙara na parlour sunfi ƙara"


"Tau Allah ya taimaka" daga haka meenal bata ƙara cewa komai ba.

"Khulud muje muci Abincin Please wallahi yunwa nake ji"
"Muje nasan ai su mum sun isa kammala wa"

Tare suka fita parlourn gaba ɗaya kowa na faɗin albarkacin bakinsa game da competition ɗinda zasuyi tsakanin Aneesa da Badar. Koda suka sauka parlourn sai suka ga ashe su mum bama parlorn suka ci abinci ba, ta yu sun koma bedroom ne ko kuma suna main parlour.

Hakan kuwa yayi musu daɗi sosai, nan kowa ya ɗiba Abincin da zai iya ci har ya ƙoshi.

Bayan sun gama cin abincin ne sai suka kunna tv kuma suka ƙure volume a speaker, sabuwar waƙar joeboy mai suna just for you aka saka musu tare da ƙure volume ɗin kowace speaker dake parlourn bakajin ƙarar komai sai sautin waƙar dake tashi. sukuma sai ihu suke da shewa tare da yin tafi, badar da Aneesa kuwa sai tiƙar rawa suke suna bin waƙar da salon rawar su.

Meenal kam Abincin ta takeci hankalinta akanta, domin ita daɗin abincin ma ya hanata ko ɗaga kai ta kalli shirmen da suke.

Leeya kuwa tana ɗan gefe dasu kaɗan, wayarta a hannunta daga yanayin zaman da tayi ta ƙurawa wayar idanu zaka fahimci abu mai muhimmanci take dubawa a wayar.

Shigowa yayi parlourn fuskar sa a haɗe kamar ko yaushe, sanye yake da uniform ɗin sojoji fuskar sa kuma tasha baƙin glasses wanda ya ƙarawa fuskar tasa kwarjini sosai.

Kafin ya shigo parlourn yayi sallama kusan sau biyu, ta ukun ce ta maƙale masa a baki sakamakon arba da yayi da ƙannensa suna kwasar rawa haka ba sauƙi, ga babban abun haushin ma sun ƙure volume sosai ta yanda ko anyi magana baza'a ji me ake faɗa ba kamar wani sabon club ɗin chasewa da ake tallatawa.

Da sauri ta ɗaga kanta tana kai dubanta a kofar parlourn sakamakon jin ƙamshin turarensa data yi ya ziyarci hancinta, karaff idanunsa suka sauka a kanta itama lokacin da ta sauke nata akansa, wata mummunar faɗuwar gaba ta dira a zuciyar ta sakamakon wani mugun kallo haɗe da muguwar harara daya jefa mata.

Da sauri ta mayarda kanta ƙasa zuciyarta na tsalle saboda tsananin tsoro, tanaso tayiwa su badar magana amma ba dama kuma kaf a cikin su ita kaɗai da ke zaune a gefe ta lura dashi.

"Ai ya kamata koda khulud ce taji kamshinsa kho? tunda tasan ƙamshin turarensa itama, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un allah ka takaita mana" leeya ta faɗi maganar a zuciyarta yayinda tsoro da fargabar ya-Turab suka cika taff a lungu da saƙo na zuciyarta.

Shikuma tunda suka haɗa ido ya ɗauke kansa daga gareta domin bayason kallonta kwata kwata, shi a ganinsa ma idanun ta canja kala suke bai taɓa kallonta yaga idanun ta da kala ɗaya ba.

Kittt sukaji an danna remote ɗin tv dana speakers ɗin gaba ɗaya. Da sauri Airah ta juyo cikin matsifa domin ganin waye, ai kuwa tana juyowa taga turab ne ta zube gwuiwoyin ta gaba daya a ƙasa, "itadai ta Banu ta shiga uku, ba ranarda zatazo gidan nan ta fita lafiya batare da ya-Turab ya mata dukan jakai ba, ita tana gani ma ko bata yimasa laifi ba sai ya ci ubanta balle da laifin, ya lafiyar kura bale taga nama" Airah tayi maganar a ranta tana matsar ƙwallah samm taki bari su haɗa ido.

Sosai gaba ɗayansu suka shiga tashin hankali ganin ya kafesu da idanunsa masu matukar ƙaɗa ƴaƴan cikin waɗanda sukayi masa laifi ba mazan, ba matan ba.

Baramma Yanzu da yake sanye cikin uniform ɗin soja, ita kuwa Aneesa ba abunda take tsoro ta kuma tsani gani kamar bindiga, sai kuma gata a fili a gefen ƙafar wandonsa na hagu.

Duk sun sanshi, kuma sunsan halinsa idan aka yimasa laifi aka cika bashi haƙuri to bazai haƙura ba koda yayi niyyar yin haƙurin saboda hakane yasa sukayi tsitt ko wacce a cikinsu kanta a ƙasa tana saƙawa da kuncewa har leeya da meenal ma da suke gefe yanzu sun dawo gabansa.

"Ku!" Ya faɗa da kakkausar murya "dan uwayenku wannan tarbiyyar aka baku a gida kuzo kuna shan kiɗa kuna rawa kamar wasu arna, kuma abin haushin ma kun kure Volume kamar wani club, idan rawa kuke so kuyi ga hanyar gate nan, duk wace take so kuma taga takai ta isa to ta tafi gidan rawa mana, wallahi summah tallahi, na rantse da Allah wannan shine First and last nazo na sameku a haka, billahil azeem kunji rantsuwar da nake ko wallahi idan na kara ganin ɗaya daga cikin a haka saina kakkarya ƙasusuwan jikinsa" ya faɗa yana nuna alamar karyawa da hannayen sa cikin matuƙar ɓacin rai.

"Kunci albarkacin gajia da kuma ɓacin rai danake ji wallahi da badan haka ba ku da kanku zakuyi bayani shashashu kawai, ku tafi kubani wuri" ya faɗa cikin Tsawa.

Da sauri suka tashi wasu harda haɗawa da gudu ita kuwa leeya har harɗewa take tambakar zata faɗi saboda tsananin tsoro su ka koma sashen su.

Hanyar da zata sadashi da part ɗin haji ya nufa domin koba komai zaifi samun nutsuwa a can, wata ƙila ma fushin da yake ciki ya wanke idan yaje wurinta, domin kuwa tasan abunda yakeso tsaff idan ranshi na ɓace yafiso ayita bashi labarin dariya, to da zarar labarin yanada dariya shikuma idan yaji yayi dariya shikenan ba wani sauran fushi ko ɓacin rai za'a buɗe sabon fejin fira.

"Assalamu alaikum haji, haji!"

"Na'am Abu manyan ƙasa, yaushe gari irin saukar ba zata haka"
Haji ta faɗa tana fitowa daga bedroom ɗin ta.

"Haji dan Allah ba sunana Abu ba sunana abu-turab idan zaki iya faɗar haka, idan bazaki iyaba ki dinga kirana da turab kawai ko kuma tk (turab Khattab) kenan.

"Ungo wannan, nace karɓi wannan ɗan damtsen uwa ba abu aka saka maka ba, kune dai ƴaƴan zamani kuke yiwa suna wani kwaskwarima, nifa bazan iyaba wallahi, tun da aka haifeka nake ina kiran Abu har yanzu, sai yanzu dakaga ka tara ƙasumba ne da gashin baki kake so na kiraka da sunan da ba naka ba"

"Mtwsss", yaja guntun tsaki can ƙasan zuciyar sa.

"nidai haji ba wannan ba so nake naji dalilin da yasa aka yimin kiran gaugawa bayan kuma ansan aikinda nake kuma bana ƙasarnan"

"Awww, baka masan dalilin kiran naka ba kenan"

"Haji wallahi kinada abun mamaki danasani dazan tambaye ki ne" turab ya faɗa kamar a ƙule.

"Kajimin Abu da iya shege, kai ba'a yimaka Maganar lalama ne, to je ka tambayi ubanka"

"Haba hajiyarmu babba, Allah dai ya ƙara Lafiya da wadata da nisan kwana, kiyi haƙuri mana"

"To kaje kawai, ai ko bakazo nan ba za'a kiraka tunda har ka dawo ka bari mahaifin ka yazo kawai, za'a gaya maka ko menene. Yanzu kaje ka huta kafin ya dawo"

"Haji lafiya dai?"

"Lafiya lau kaje ka huta karka saka komai a ranka ba komai ba ne kawai magana za'a faɗa maka. Kaje kayi wanka ka ci abinci ni kwanciya zanyi bacci nakeji sai mahaifin ku yadawo zakuzo har nan kusanar dani"

"Okay ba damuwa amma me aka dafa a gidan haji?"

"Tuwon doya da miyar ganyen cabbage da bushasshen kifi"
Dan yatsune fuska yayi kafin yace;

"haji anya kuwa abincin nan bazai ɓata wa mutane ciki ba, kinga ni ko a Mexico danayi rayuwa ba kowane irin abinci nake ci ba balle a nan"

Wani kallo haji ta wurga masa tare da yin ƙofa tace;
"sannu jikan Elizabeth turawan duniya, to ni kaga tafiya ta baccin nan naso yafi ƙarfina"

"Haji da gaske ne kenan da'akace idan

31 / 61