Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
dalilin murmushin ta daga jin knocking.
"Saboda mijinki ya dawo mana" zuciyarta ta bata amsa da haka.
Guntun tsaki tayi tana ture amsar da zuciyarta ta bata domin tasan hakan ba zai yiwu ba ace zatayi murnar ganin ya-Turab yanzu.
Knocking taji an sake yi, cikin tafiyarta mai cike da nutsuwa ta isa qofar ta buɗe.
Wata baquwar fuska taci karo da ita da ga kofar bayan ta wangaleta.
"Barka da safiya" ta furta cikin muryarta tana kallon wani dattijo dake tsaye da kaya a cikin basket.
Dattijon kuwa ya amsata da fadin "yawwa barka da safiya Hajiya, sunana ilu nine mai gadin gidan nan. Wannan kuma saqo ne wata mata ta bayar tace a kawomiki, sannan ga shi ta bayarda katin ta tace ki kirata idan na baki saqon zatayimiki bayani"
"Okay Allah sarki, nikuwa bansan wace mata bace. Amma nasan bazai wuce Aunty Rafa'at ba tunda da ita mukayi zata dawo da safe, amma wallahi banida wayarda zan kirata da ita domin na manta wayana gida"
Washe baki ilu mai gadi yayi yace "hajiya ga 'yar kwakuleta ta ki kira da ita nasan akwai sauran credit jiya da rana na saka bata isa qarewa ba yanzu"
Leeyanah taji dadi har ranta domin kho badomin saqon kiran Aunty Rafa'at ba....tanaso tayi waya da mum Wallahi.
Karɓar wayar tayi tana yimasa godiya, hannu ta saka zata karɓi basket yace ta barsu ya shigardasu gida. 'Kin amincewa tayi domin tana ganinsa dattijo dashi ta ya zata yarda ya shigar mata da kaya.
Sai da kyar ya mika mata kayan ita kuma ta shige ciki harda wayar tasa.
A daining ta dire basket din ta bud'e, yunwa takeji bil-haqqi domin rabon ta da saka wani abu abakinta tun jiya da la'asar.
Babban flask din ruwan zafi ne sai kuma cooler mai biyu da kuma wani qaramin bowl mai murfi.
Bowl din ta fara budewa sai ta tarar da soyayyen dankalin turawa da kwai da kuma toasted cheese.
'Daga bowl din tayi ta ajiye shi kan daining sannan ta bud'e cooler d'aya, taga tuwon semovita ne kulli uku.
Murmushi tayi cikin jin dadi ta ajiye cooler din kan daining itama sannan ta bud'e qaramar. Miyar ganye ce sharrr da ita taji manshanu sai qamshi spices take. Tun kan leeya taci tuni yawunta ya tsinke.
Flask kuma tea ne a ciki, sai kuma gefe daya na flask din cool water ne.
Miƙewa tayi lokacin da ta gama duba abincin sannan ta nufi kitchen ɗin ta.
Tasha wuya sosai kafin ta gane kitchen inda kitchen yake domin zagaye ta farayi da ta bud'e wannan kofar sai ta ganta anan, idan ta bud'e waccan sai ta ganta a wannan, ko kuma ta ganta inda ta baro.
harta kusa sharewa sai kawai ta ga wata qaramar kofa, tana budewa kuwa taci karo da tsararren kitchen mai matukar fadi da daukar hankali.
Ga kaya nan birjit kamar kanti, abunda tazo dauka ta dauka bayan ta gama baiwa idanun ta abinci, sai da ta gama kallon komai tare da duba duk abunda bata sani ba sannan ta fice daga cikin kitchen ɗin zuciyar ta na mata wasai.
Haqiqa mum da papu sun gama mata komai a wannan rayuwa sun zama gatan ta a nan duniya, Allah ne kawai zai yi musu sakayyar alƙairi tsakaninsu.
Fita tayi sashen bayan ta gama hardace hanyar da zata mayar da ita daining tsafff tayi zuwa da dawowa yakai uku kafin ta zauna.
Tea ta zuba a cup d'aya, sannan ta zuba dankalin turawan da kuma toasted cheese ta fita ta miqawa ilu mai gadi, Godiya yayi mata sosai, ta dawo ciki ta zuba nata sannan ta ragewa ya-Turab nasa.
Sai da taci ta qoshi Sannan ta adana tuwon domin batada space din da zata sakashi.
"Maybe ya-Turab zai buqata idan ya dawo" tsaki ta jaaa a fili lokacin da tayi maganar a zuciyar ta, a fili kuma tace to meye damuwata yaci ko kar yaci.
Sake jan wani tsaki tayi tana kunna wayar ilu mai gadi da ya aramata.
Katin ta d'akko ta kwashe number din da ke jikin katin tayi calling.
Bugu ɗaya da dauka da sallama a bakinta tace "barka da safiya"
Daga cikin wayar kuma akace"Yawwa barka leeyanah kin tashi Lafiya" bata jira amsa ba taci gaba da fadin "sai kikaga saqo ga mai gadi kho, kiyi hakuri wallahi wani uzuri ne zai mayardani suleja yanzu. Baban Aamir ne ya kirani yake sanardani wai Arfah tana asibiti jiya dare wutar nepa ta jaa ta har sai da aka kaita asibiti, shine ya kirani ya sanardani. Amma kuyi hakuri kinji zamu dawo nida su mum fanaya soon"
Leeya dake sauraren aunty Rafa'at tace "Allah sarki Aunty Wallahi babu komai, mun amshi saqo mun gode kuma Allah ya sanya albarka, Allah kuma ba bawa Arfah Lafiya ya tsare gaba"
Tun kafin Aunty tayi magana katin wayar ya qare, kamar leeyanah ta rusa kuka taji lokacin da wayar ta datse da kanta.
Mum ta so ta kira wallahi tayi missing ɗin ta, rasa yanda zatayi tayi dole ta miqawa ilu mai gadi wayarsa ta dawo parloun cikin bakin ciki.
Bedroom ta wuce ta gyara tsafff kaana ta bude wata qaramar kit daga cikin sababbin akwatunan ta da papu ya siyo musu jiya.
Turarukan daki ne a ciki birjit dana garwashi da kuma na tsinsiya.
Fitowa tayi dana garwashin domin qamshinsa yafi tafiya da imaninta, sa'ar da taci itace ɗazu ta lura da kwalin sabuwar borner akan tv stand.
Da ita tayi amfani wajen turara ɗakin gaba daya, bayan ta gama ta shiga toilet tayi wanka Sannan ta yi shirinta cikin doguwar rigar less mara nauyi mai matuqar kyau wanda yaji qanan Arab stones kamar anyi bari sai sheqi take kamar tauraruwa.
Ta Rasa abunda zatayi kawai ta dawo parlour ta kunna kallo da remote a hannunta tana sarrafa shi har iskan A.C da fanker dake parlorn suka kad'ar da ita tayi bacci.
Ba ita ta farka ba sai da aka kusa kiran sallahr azahar, wasu masallatan ma har an idar, miqewa tayi ta shiga bedroom ɗin ta.
tayi mamaki Sosai ganin sa yanda ta barshi.
"Kenan ba wanda ya shigo gidan nan?" Tayi tambayar a fili.
"Wata qila kuma ya shigo ya tarar dake kina bacci ya sake fitarsa"
Da wannan zancen zucin nata ta aminta, ya-Turab ya shigo ya tarar da ita tana bacci bai tayarda ita ba ya sake fita.
Alwala tayi sannan ta tayarda sallah, bayan ta idar gaba ɗaya sai ta koma daining, Abincin da Aunty Rafa'at ta kawomata ta duba, tasha mamaki sosai ganin har breakfast din tea da kuma toasted cheese din da ta ajiye suna nan a yanda suke ba'a ta'basu ba.
Tattara su tayi wuri daya sannan ta zuba kulli daya na tuwo da miya ta haɗa da tea din ta fita waje.
Wurin da ilu ke kwance yana shan iska ta nufa fuskar ta wasai.
Sallama tayi masa bakinsa har rawa yake wajen amsa mata, shidai yana tsoron hada idanu da wannan hajiyar mai kamada aljanu saboda tsanin kyawu, ko a hakan ma dauriya kawai yake yana yimata magana da amsa mata.
Bakinsa a washe yace "Hajiya sannu faa, Nagode Allah ya qara budi"
Itama murmushin ne a fuskar ta tace "Ameen baba ilu, yawwa nace ka saka credit ne wallahi banida kudi hannuna gashi mai gidan ya fita balle in yi masa Magana"
Da mamaki ilu ya dan dago kad'an yace "hajiya wane mai gidan kuma, ai tun jiya da dare da ya shigo ba wanda ya qara fita, kinga ma motar da yazo da ita" ilu ya faɗa yana nunamata packing space.
Motar ya-Turab wacce yafi so ta gani a pack ba ko alamar an ta'bata yau din nan.
Cikin madaukakin mamaki ta jinjina kai sannan tace "toh shikenan baba ilu Nagode sosai ka saka credit din inaso na kira gida wallahi"
"Allah sarki hajiya wallahi bansaka ba, amma bara in ranto bashi nasan zasu bani da yawa tunda ban taba rance ba kinga sai kiyi wayarki isasshiya"
Leeya cikin farin ciki tace"Kai amma Nagode baba ilu...... in sha Allah idan nayi waya da gida zan saka a turamin kudin siyen waya da kuma kudin credit dinka dana saka ka ranta"
Ilu mai gadi yace"haba hajiya, ai kinfi karfin nan wallahi. Ki karba sun bada rancen"
Karɓar wayar tayi da hannu bibbiyu tana yimasa godiya ta wuce ciki, number mum ta fara trying on ready tanada number din da kanta.
Sunyi gaisuwa sosai cikin kewar juna da so da qauna na tsakanin 'ya da uwa. Leeya kuwa harda d'an guntun kukanta da zasu gama wayar bayan ta gayawa mum duk matsalar ta, sai dai bata gayamata har yanzu bata sanya ya-Turab a ido ba.
illah ma cewa da tayi yana lafiya, daga nan kuma mum ta gayamata zasuzo nan da kwanaki hudu masu zuwa. Daga karshe kuma tace mata "ki je ki kaiwa ilun waya kice yayi magana da mai p.o.s na tura masa kudin ki fadi kalar wayar da kikeso asiyamiki, sannan ayi miki sim nima na gaji da shirun nan tsakanin 'ya da uwa" leeyanah taji dadi sosai har farin cikinta ya kasa boyuwa har mum sai da ta gane hakan.
Murmushi kawai tayi tana qarajin tsagwaron soyayyar 'yar uwarta na dawomata filll.
Mum koda leeyanah takirata akan ta turamata kudin siyan waya bata kawo komai ba. "Leeya kenan maybe bataso mijinta ya siya mata Ni take buqatar na siyamata shiyasa ta gayamin"
Haka mum ta fad'a lokacin da suka kammala wayar.
Fita waje leeyanah tayi a karo na biyu taje ta sanarwa da ilu mai gadi abunda hajiyarta tace.
"Aikuwa akwai wani shago da ake cire kudi gaba da gidan nan kaɗan bara naje yanzu"
Leeyana dai tana yabawa da mutuncin baba ilu tace "Nagode baba ilu Allah ya yimaka yanda kaimin, kuma idan kaje shagon Dan Allah ka kira wannan lambar" ta faɗa tana nuna masa number din mum dake kan kira yanzu.
Baba ilu yace "nagane hajiya zan kira idan naje in sha Allah, ki shiga ciki kafin in dawo, kuma ki rufe ko da yake ai Alhaji yana nan ko? Amma dai duk da haka ku rufe ko'ina saboda tsaro idan na dawo zan kwankwasa"
Annurin fuskar ta ne ya ɗauke gaba daya lokacin da ilu ya ambaci sunansa, tasan bata kyauta masa ba. To Amma meyasa zai tafi tun jiya da dare ya kasa waiwayo ta har yau zuwa wannan lokaci, ai ko dabbobi ka ajiye ya kamata ka dinga waiwaye balle kuma mutum d'an adamu mai daraja.
"Ki tuna irin wulaqancin da kika yimasa jiya, kuma fa ke ce kika koreshi da kanki"
Wata zuciya ta fad'a mata haka lokacin da tunanin ya-Turab ya zagayo ta.
Komawa tayi ciki jikinta sanyi kalau, yanzu ya zatayi ta fara nemansa, gashi bata san wane wuri aka ajiye kanwarta Rukhsha ba, da kuma bestin ta zohal, da ma ache d'ayar su tana kusa da ta kawo mata mafita...
*
A daren jiya kuma bangaren su Aleena. Su mummy-neesah ne da kuma Aunty zainab suka rakata. Gidan da aka ajiyeta da kuma inda aka ajiye leeyanah da zohal duk iri dayane, hatta tales da kuma painting gidan babu abunda ya banbanta.
Furnitures din Aleena da leeyanah duk iri dayane, har kuma yanda aka yi tsarin ajiye kayan komai iri dayane.
Mummy-neesah da Aunty zainab basu jima gidan ba domin drivern da yazo dasu shi ya koma da su garin suleja cikin umurnin da dad qarami ya bayar.
Aleena ma tasha kuka sosai amma mummy-neesah tayi mata alqawarin kwanan nan zasu zo gaba daya, kuma za'a je da ita gidan leeyanah da kuma gidan matar yayansu wato fahad duk suga juna domin ba unguwar su daya ba, kowa da bangaren da aka bashi.
Mummy-neesah da Aunty zainab basu jima da tafiya ba ango ya shigo, a lokacin kuma Aleena na zaune parlour tana game da wayarta domin ita bata manta da wayar ta ba da abunta tazo.
Sallamar da taji ne ya sakata dagowa, da mamaki take binshi da kallo, shima haka.
Muryarta na rawa saboda tsanin tsoro ta furta "broth O kaine ko idanuna ne"
Matsowa yayi kusa da ita fuskar sa dauke da murmushi idanunsa kuma sunyi jajir har da kwanciyar ruwan hawaye a cikinsu.
Har gabanta ya taka ya saka hannunsa d'aya ya shafa gefen fuskar ta "kinyarda nine ba mafarki kike ba kho" ya fada da murmushin da bai gushe masa ba.
Miƙewa tayi tsaye itama tuni idanunta sun kawo ƙwallah tace "broth dan Allah kai aka auramin, ya kakeso yayata tayi da soyayyarka dake zuciyarta"
Murmushi mai sanyi yayi mata sannan yace "budurwa, kinsan kuwa bawa baya wuce qaddararsa? To tun a farko Allah bai rubuta leeyanah a matsayin qaddarata ba, ke da banyi zato ba kuma banyi tsammani ba dake Allah ya tsara qaddarata. Duk abunda kaga ka saka rai kuma Allah bai baka shi ba, to ba shi bane daidai da rayuwar ka ba, domin kuwa ko ya shigo zai fita wata qila ma ba alqairi bane"
Aleena kam tuni tasan zafaran da tawakkali tun kafin ya musulunta, balle ma yanzu Da ya musulunta, ai sai abun ya qaru "Hakane broth O, Allah ya zaba mana mafi alqairi, Allah ya sanya albarkarsa a cikin zaman mu"
"Aleena kina sona?" Taji saukar muryarsa a kunnuwanta babu zato babu tsammani.
Batare da tunanin komai ba tace"ina sonka broth O ina rokon Allah ya kawomana kwanciyar hankali da kyakkyawar fahimta a tsakanin mu, ina rokonsa ya azurtamu, ya rufamana asiri a zamantakewar mu" ta karasa maganar muryarta na rawa alamun kuka take qoqarin tayi.
Ganin haka ya saka zafaran ya ware mata hannayensa biyu, da gudu tayo kansa ta rungume shi. Shima ya rungume ta tsamm a faffaɗan qirjinsa.
Kamar mai rad'a yayi mata magana yace "karki bari hawayen nan su zuba dan Allah kinji budurwa d'iyan amminta. Allah sarki rayuwa........ naso ammi taga wannan rana, naso ammi ma ta saka mana albarka a aurenmu, amma ba haka Allah ya tsara ba Allah ya jikan Ammi da Abbi ya basu kyakkyawan masauki"
"Amin ya rabbil alameen mijina" Aleena ta fad'a tana boye fuskar ta cikin qirjinsa.
Ganin haka ya saka shi sakin lallausan murmushi yace"hummm sannu mai miji wai bakya jin kunyata kho"
"Lahhhhh, dama akwai wata kunya tsananin miji da mata bansaniva broth O?"
"Kinga idan baki daina kirana da wannan sunan ba sai na cire miki bakin nan" ya faɗa yana ɗan jan lips din ta na qasa.
Cikin shagwaɓɓiyar murya tace "da zafi fa"
Yace "dama ina so kiji zafin ai dan idan ban miki hakan ba bazaki daina kirana da sunan nan ba"
Taɓe baki tayi zatayi kuka da sauri ya saketa ya kama kunnuwansa yace "tuba nake rankishidade a gafarceni bazan sake ba kinji, dan Allah kiyi haƙuri banason kukan nan"
Kamar zatayi dariya sai ta kanne tace "Ni bacci nakeji"
"Ok Madam, muje kiyi alwala sai muyi sallah sannan kici abinci sai kiyi baccin kinji"
"Nidai sallah kawai zanyi bana jin yunwa"
"Aikuwa baki isa ba dole sai kinci abinci wallahi ko in yimiki d'ure da qarfi da yaji"
Yar dariyar farin ciki tayi sannan tace"To kafini qarfin ne hala?"
"Sai an gwada ake sanin na kwarai malama"
"to muje a gwada" Aleena ta fada tana wuce gaba shikuma yana binta a baya.
Haka suka gudanar da daren su cikin farin ciki da nishadi, sai wasa da dariya suke kamar da can sun saba bayan tsawon shekarun da suka dauka ba sa tare.
***
A bangaren leeyanah kuma baba ilu bai wani ɗauki lokaci ba ya dawo da uban kuɗaɗen da mum ta turawa leeyanah, bata tsaya lissafawa ta cire dubu ashirin ta bashi kyauta sannan ta gayamasa wayarda takeso ya siyo mata, baba ilu kamar ya kai kasa saboda godiya.
Ko chan da ya je bai jima ba ya dawo mata da waya harda sim da credit mai yawa da ya saka aka yimata v.t.u
Sosai take masa godiya shima godiyar yake mata da irin kyautatawar ta gareshi.
Komawa tayi ciki ta fara shirin daura girkin dare, tunanin ta shine yanda zata saukewa turab kwandon rashin mutunci idan ya dawo, wato shi ga isasshe an kawomasa mata tun jiya ya tafi ya barta har gashi ana batun kwana daya babu shi ba labari.
Ai ba sai ya nuna mata baya sonta ba domin shima yasan ba sonsa take ba biyayya ne kawai, balle har ya wani tafi ya barta ya manta da ita.
Kitchen ta shiga ta dora girkin ta na dare tana ta mita har ta kammala kusan sallahr magrib, baba ilu ta kaiwa nasa sannan ta shiga tayi wanka ta dauro alwala ta fito, sai da ta jira aka tayarda sallah sannan taci abincin ta.
Daidai lokacin kuma wayanta da aka siyomata tayi full, number ɗin mum ta kira har wajen kira hud'u amma ba respond.
"Maybe wayan bata kusa da ita" ta fada a fili lokacin da take qoqarin kawo numbern bestin ta zohal.
Ta kira number yafi a qirga amma abu daya ake gayamata not reachable.
Kusan karfe goma da rabi ta rarraba idanunta ko'ina a gidan ko zataga ya-Turab amma bata ganshi ba, abun har ya fara bata tsoro. domin baba ilu mai gadi ya tabbatar mata da Turab bai fita gidan ba.
"Hajiya ko akwai wata kofa daban da ake fita a gidan nan bayan wannan da nake tsaro?"
Muryar a sanyeye leeya tace "wallahi Nima bansaniba baba ilu, amma dan Allah ka dan zagayamin a gidan nan ko zaka gano wata hanya, nikuma bara naje ciki in duba ko zanga wani wuri"
"Shikenan hajiya, Bara naje na duba Allah yasa adace, to ko zaki kira number din sa kigani Hajiya?"
"Banada number dinsa a kai na baba ilu, kuma na kira mum bata daga wayar ba"
"To Allah yasa komai da sauki zaizo hajiya, amma ahce tun daren jiya babu mutum ba labarinsa"
"Duk inda yaje da saninsa baba ilu domin shi ya fita da qafafunsa ba wanda ya fitar dashi"
"Bara naje na dudduba mugani ko Allah zai saka adace"
Daga haka ba wanda ya kuma cewa komai duk suka tafi.
Baba ilu kam yayi zagayen da duk zai yi a faɗin gidan amma bai gano hanya ko ɗaya da ake fita cikin gidan ba bayan hanyar da gate yake.
Yayi zagaye yakai biyar zuwa shida bai gane komai ba dole ta saka ya hakura ya nemi wuri ya tsaya yana jiran fitowar leeyana ya sanar da ita.
Itama a bangaren ta haka ta kasance, domin tayi duk duban da zatayi a ɗakunan da ke gidan bata gane komai ba.
sau biyu tana ɓata sai tasha wuya kafin ta mayarda kanta master parlour.
Tayi duk iya qoqarin ta wajen fahimtar ɗakunan da ke gidan amma ta kasa, haka ta fito parloun jikinta duk ya mutu ta