Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
ayi kasafin dukiyarsu da aka bashi amana amana tsawon shekara da shekaru.
Bayan anyi bincike an kuma warware komai sai Papu ya miqawa kowa takardasa domin yayi signing.
Sai da suka kammala leeyana ta tsayarda shaidun ta miqawa mum fanaya takardar tana hawaye tace "wallahi mum banada wata uwa a duniyarnan data wuce ki saboda haka na mallaka miki dukiyarnan halak malak idan dai inada haqqi da ita, kuma ina roqon kowa dake wurin nan yayi shaidata ko lahira"
Kamar yanda tayi haka itama Aleena tayi saidai ita dad qarami ta baiwa domin ita shine matsayin mahaifin ta saboda yayi mata abunda ko mahaifinta ne iyakarsa haka.
Haka shima Idrak ya mallakawa mahaifiyarsa dukiyar baki daya.
Sosai hakan ya qara qauna da zumunci mai qarfi a tsakanin su.
Su 'yan uku da twins da kuma ifrah tuni sukayi wayo wasunsu harsun fara tattakawa suna koyon tafiya, yaran sun shaqu da juna sosai, domin kuwa bayan iyayensu mata sun gama biqi sabon gida mai dauke da part uku da kuma d'akuna barkatai suka saye suka koma gaba ɗayansu.
Wani lokacin yaran kaɗai ake barinsu su kwana a daki daya sai qalilan na ma'aikatan gidan da ake sakawa suje su kula dasu.
amma gado daya ake shimfid'e su suduka shidan, wannan yasa sabo da shaquwa mai qarfi ta shiga tsakanin yaran da iyayensu daga abota suka zamo 'yan uwa na jini da hanta da babu rabuwa.
ALHMDULLILLAH!
ALHMDULLILLAH!!
ALHMDULLILLAH!!!!!
_GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAMALLAKIN MULKI DA DAUKAKA MAI KOWA MAI KOMAI MAI BAYARWA DA HANAWA MAI IKO AKAN KOMAI, TSIRA DA AMINCI SU 'KARA TABBATA A WURIN SHUGABA, JAGABA KUMA ƊAN GATA MANZON RAHMA ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM TARE DA AHALIN GIDANSA MASU ALBARKA. DA SAHABBAI DA ALAYENSA MASU TSANTSAR DARAJA.
_ALHAMDULILLAH ALLAH INA KARA GODIYA A GAREKA DAKA BANI DAMAR KAMMALA WANNAN LITTAFIN DA RAINA DA KUMA LAFIYATA, KUSKURE NA A CIKI ALLAH INA MAI TUBA, ABUNDA NA FAD'A DAI-DAI ALLAH KA BADA IKO AYI AMFANI DASHI.
_INA GODIYA GA DUK MASOYANA DA SUKAYI KOKARI DA HAKURI WAJEN BIBIYATA TUN DAGA FARKON LITTAFINA HAR IZUWA KARSHE ALLAH YA BAR ZUMUNCI DA KAUNA MASOYANA.
BISSALAM, SAI KUMA IDAN ALLAH YA QARA HADAMU A WANI LITTAFIN NA GODE.
*RUMANAH M. DIGGI.......✍🏼*