Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
yana ganin idan ya tafi yanzu abune mawuyaci ya ƙara saduwa dasu kuma gashi yanada magana dasu mai muhimmanci,
kuma a ransa yana ƙudurce bazai iya barin su a wannan halinba sabida baisan hannunda zasu faɗaba, juyawa yayi kawai da nufin ya tafiya saboda yasan sun jima rabonda su sami bacci irin wannan shikuma tausayawar dayake musu bazata bari ya iya tadasu daga baccin ba.
Har ya juya zai tafi yaji an riƙo hannun sa, cike da farin ciki ya waiwayo dan ganin waye a cikinsu:
"Budurwa dama ba bacci kike yiba?"
Murmushi tayi tare da faɗin:"ehh ba bacci nakeba broth O tun sa'adda kazo Nan ina ganin ka"
"Aikuwa kin taimakeni da kika tashi"
"Taimako kuma?"
Aleena ta tambaya cike da zallar mamaki.
"Ehh.. Amma dai har yanzu da saura tunda leeya bata tashi ba kuma ni gashi banaso a tada ita, gashi inada magana mai muhimmanci da ita"
Okene ya faɗi maganar yana sanya yatsunsa cikin gashin kansa.
Ƙafa aleena ta saka a fakaice ta ɗan tsakari leeya nan da nan itakuma leeya ta ɗan juya alamar taji tsakaran da akayimata,
Toshe bakin aleena okene yayi gudun karta ƙara wani motsi da zai tada leeya, da gayya ta gantsa ramasa cizo a ɗan yatsa.
Babu shiri ya saki ihu tare da janye hannunsa daga bakin aleena,
ita kuma ta kyalkyale da dariyarta, yayin da leeya ta zabura daga baccinta a ruɗe ta fara kallonsu su duka biyun fuskar ta da alamar tambaya.
Hannunsa biyu ya saka tare da dafe bakinsa " budurwa ke kika tada ita amma mena cemiki ne Allah yarinyar nan bakyajin magana"
Cak! Ta tsaya da dariyar da take jin ankirata da wani sunan daban wai yarinya, me yake nufi kenan Ni aleena nice yarinya. Ɗago da kanta tayi ta galla mai harara kafin tace "maimaita abunda kace broth O nice yarinya?"
Cike da jan faɗa ya buɗi baki da nufin bata amsa leeya ta kalleshi tare da girgiza masa kai alamar kar ya ƙarasa, nan take ya sauya maganar zuwa wani ɓangare domin ya fahimci nufin ta.
"Okene ina kaje haka kajima baka dawo ba muna ta jiranka har mukayi bacci "
Naje makoko ne domin tattauna wani batu kuma mungama maganar Yanzu da ku kawai ya rage nayi maganar"
"Makoko!?"
Leeya ta tambaye shi aɗan tsorace.
"Ehhmana makoko na fito yanzun nan, akwai matsala ne, naje ne nayi magana da wani kawuna dake can kuma na sameshi munyi maganar idan kin shirya, attention kawai nakeso magana zanyi dake koma nace daku gaba ɗaya"
miƙewa leeya tayi sosai kafin ta janyo ruwan da yabata, ta wanke fuskar ta sosai Sannan ta dawo ta zauna kusa dashi.
Aleena ma tazo ta zauna yanda taga leeya tayi.
"Leeyana!!"
"Na'am"
Okene ya kira sunan ta a raunane:"babban dalilin da yasa nakeson magana dake leeya idan baki manta ba a kwanakin dasuka gabata nataɓa gayamiki zamubar garin Lagos ɗin nan kho?"
"Ehh"
Leeya ta amsa masa muryarta na cracking.
"Tho wannan tafiyar ce ta tashi, kuma zamubar garin Lagos mu koma can inda nagayamiki amma.."
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un okene yanzu shikenan rabuwa zamuyi, shikenan tafiya zakayi ka barmu?"
kukan da take riƙewa ne ya suɓutomata itama aleena tana ganin haka ta fashe da kukan.
Cikin matsanan ciyar damuwa okene ya rungumesu gabaɗaya a jikinsa yayita rarrashin su, cikin rarrashin kuwa har ya sanarmusu ya samamusu inda zasuyi rayuwar kamar sauran yara a can makoko gidan kawunsa kuma "kuyi haƙuri, sannan kuma ku kwantar da hankalinku domin tafiyar da nayi a makoko yanzu saboda nagana da kawuna ne kan batun zamanku a gidan, sun yi na'am da haka kuma sun yarda zasu riƙeku tsakaninsu da Allah, kuma sunce bazasu hanaku kuyi addinin ku ba kunji kho" ya faɗa yana shafa kan Aleena da ta lafe a jikinsa sai ajiyar zuciya take na kukan da tasha.
"Okene haƙiƙa bamuda kamar ka, bamusan abunda zamu saka maka ba.
Allah ne kaɗai zai yi muna sakayya ta alƙairi tsakanin mu dakai okene Allah ya biyaka, Allah ya kawomaka tsaftatacciyar shiriya dan alfarmar nabiyullah"
leeya ta ƙarasa maganar tana zubda hawaye.
Gashinta daya sakko a saman mayafin fuskar ta yasaka yatsansa ya gyara mata, wanda sauda yawa shine mutane suke gani su ƙara tsorata da ita saboda idan ta saki gashin nata gabaɗaya zai iya rufe ko'ina a fuskarta har ma ya sakko kamar yafashi tayi.
"Saboda Ammi bata nan shine kika daina gyara gashin nan ko?"
Okene ya faɗa yana ɗan murmushi domin kwantar mata da hankali.
"Nidai bazan iya gyara shi ba kasani ae, Ni ban ma taɓa gyarawa ba saidai ammi ta gyaramin"
"Tau meyasa bakya gyarawa?"
Okene ya tambaya yana kallon ta
"saboda ban iya ba"
leeya ta bashi amsa.
"Tau idan baki iya ba aini na iya, sai ki kawo na gyara miki kho, sai anyi magana ki wani kin girme mutum" Aleena ta faɗa tana janye mata sauran gashin da ya fito waje.
"Lahhhh leeya aina manta ga budurwa nan ta dinga gyara miki mana" Okene ya faɗa yana kallon aleena dake faman mayarda gashin da ya fito inda yake.
"Yanzu dai ki tashi ki haɗa kayanda kukeso anan, waɗanda bazakuyi amfani dasuba kuma ki fitardasu gefe a je a siyarwa da ƴan gwangwan, sannan ku tashi muje makoko saboda yanzu haka muma ana can ana shirye shiryen tafiyar tamu"
Miƙewa tayi da azama ta fara aikin cire kayan, suma suka tayata aikin su uku, ba jimawa suka ƙare fitarda kayan.
Okene da kansa yakira masu saye aka siyarda su Sannan aka basu kuɗin, suka tattara sauran kayayyakin nasu suka shiga napep sai makoko.
Basu ɗauki dogon lokaci ba suka iso arear yayinda mai napep yayi parking bakin teku.
bayan yayi parking suka fito tare da fitarda kayansu, suka kira mai jirgin kwale-kwale sakamakon unguwar ta makoko tana saman teku ne, gidajen su kuma na saman tekun, kuma sun kasance na katako ne gaba ɗayan unguwar.
Bayan mai jirgin ruwan ya iso aka loda kayan nasu sannan suma suka shiga, ba jimawa suka ƙaraso gidan, koda isowarsu kuwa suka tararda kawun na okene tare da matarsa suna jiran ƙarasowar su.
Haƙiƙa an karrama su saboda basuyi tunanin samun tarba kamar haka ba, duk da kasancewar suma mutanen ba musulmai bane igbo ne kamar dai okene.
Sanin halayen okene da karamcin sa yasa suka daina mamakin ganin haka daga kawun Okene da Matarsa.
Abinci irin na igbo mai rai da numfashi aka kawo musu.
Bayan sunci abinci sunsha sun ƙoshi sannan aka fara firarraki da labarai. ba sosai mutanen kejin hausa ba, sunayin tane gwanin ban dariya, ganin haka ya nishaɗantar dasu baki ɗaya.
Abunda yabawa leeya mamaki shine ganin babu wata ƙyama ko tsorata da sukayi da ita kamar yanda sauran mutane suke yimata, hakan ya bata damar ƙara sakin jikinta da wadannan mutane.
"Uchi!" Okene ya kira sunan kawunsa da nutsatstsiyar murya "Ga amana nan na baku nasan zaku iya saboda Nima kaina na zauna daku kuma nasan yanda halayen ku suke, bansanku da ƙyara ko nuna rashin soba, bankuma sanku da wulakanta dan adam ba. Ga leeya da kuma ƙanwarta aleena idan kunzauna dasu lafiya zakuji daɗin zama dasu koba komai, zasu ciremuku kewar rashin yara da bakuda su, Please Nnene ya faɗa yana mayarda dubansa ga matar kawunsa "kece uwa, kece kikasan tarbiyya dakuma sanin zafin yara, bawai dan baki taɓa haihuwa bane zaizamo baki san wannan ba ah ah a ko'ina mace uwace, uchi kaima haka dan Allah kuriƙe amana.
Da kuma abunda nakeso na roƙeku dan Allah kar ku damu da wannan mayafin da waccan take sakawa wallahi tun tanada shekaru biyu haka take kuma tun kafin mahaifiyarta ta mutu tayi mata alkawarin bazata cire shi ba har sai lokacin da ta ɗiba ya cika.
Uchi, Nnene ina yimuku magana ne matsayina na ɗanku ba kowa ba, ku taimaka ku riƙe amana koda munbar Lagos bayana nufin munbar ku bane ni nayi alƙawarin zan dinga zuwa ina Ganin ku, akai-akai"
Da murmushi a fuskar Nnene ta shafa sumar kan okene tare da faɗin "zaka samemu da rike amana Okene"
Bata sauke hannunta akansa ba shima uchi ya ɗaura tasa hannun yace " zaka samemu da rike amana eselu.
shikuma ya sunkui da kansa ƙasa kamar dai yanda
Yake a al'adar tasu ta Igbo.
Duk wannan maganar da suke ba abunda su leeya sukaji, sakamakon da yarensu sukayi bada hausa ba.
Miƙewa aleena tayi daga inda take tazo ta zauna kusa da okene, tallafe haɓa tayi sannan tace:" broth O hala me kake gayamusu haka?" ta faɗa cikin sigar tambaya.
Faɗaɗa fuskar sa yayi da murmushi, tambayar Tata ta bashi dariya baramma yanda tayi da fuska kamar wata babban mutum "gayamusu nake daga yau kun zama ƴaƴansu, kuma zaku dinga tayasu aiki, kuma zaku cigaba da zuwa kuna karatun ku kinji".
Daga masa kai tayi sannan tace:" naji gaskiya sun taimaka mana to wanene uchi wanene Nnene?"
Dariya suka kwashe gaba ɗayan su jin yanda ta faɗi sunayen n
" Wancan shine uchi, cewar okena yana nuna kawunsa, waccan kuma Nnene matar kawuna kenan, Uchi ana nufin kawu ne a yaranmu, Nnene kuma ana nufin gwaggo, Ku ma zaku iya kiransu haka idan zaku iya"
Alama uchi yayiwa aleena da tazo wajen sa, da murmushin ta ta nufeshi ya bata wuri ta zauna kusa dashi:"kasan menene sunana? Aleena ta tambayi uchi.
"Nasani" ya bata amsa cikin Hausar shi da bai gama iyawa ba.
"To menene sunan nawa?
"Aleena"
Ya bata amsa a takaice sunan nata kuma yayi daidai da bakin shi, da tayi tunanin bazai faɗa yanda akeso ba, sai kuma taga saɓanin haka, shiyasa daya faɗa sai ta haɗe fuska dan bahaka tasoba, taso yana faɗa a kwashe da dariya.
"Tho ba aleena bane sunana sunana budurwa"
"Budurwa!"
yasake tambaya, sai kuma taji ya faɗi daidai har yanzu, nan itama ta sake fuska dan kar a fahimci dariya kawai takeso tayimasa.
Haka dai suka kaci gaba da fira kamar waɗan da suka san juna tun fari, anata raha da dariya, saɓanin leeya da taƙi sakin jikinta tayi fira, jefi jefi take sako bakinta ko kuma idan an faɗi wani abu daya bata dariya sai tayi.
idan kuma na murmushi ne saitayi murmushi, amma ban da Wannan ba abunda take cewa.
Saida rana ta take okene ya tashi da nufin ya koma gida, duk sukayi masa rakiya banda aleena dake zaune wuri ɗaya takasa ko motsin albarka.
"Aleena ke bazakimin rakiyar ba?"
"Ah ah broth O ka tafi kawai nida ka ganni nan ba inda zan tashi, gidan nan fa tsakiyar babban Teku yake, ina zan tashi daga nan ga nauyin ku, ga kuma nawa ae sai mu nutse gaba dayan mu,
ku tafi kawai gobe idan kadawo zanmaka rakiya su sai su zauna kar nauyin yayi yawa tunda kace gobe zaka dawo kho?"
Aleena ke wannan maganar tana tankwashe ƙafafuwan ta alamar gyara zama.
Murmushi kawai sukayi dan su uchi har sun fara sanin halin ta ita yarinyace mai yawan barkwanci yayinda suka fahimci leeyana daban take da ita.......✍️
BAYAN WUYA.
By RUMANA M DIGGI.
007
_____________Bayan fitarta ɗakin sai ta ɗauki buta da nufin ta shiga banɗaki, da yake cikin ɗakin ne kawai da duhu domin kuwa waje akwai hasken farin wata tarrrr.
bata wani sha wahalar neman buta ba, saidai bata sami ruwa a cikin butarba, shiga tayi banɗakin domin akwai duro da suke saka ruwa a ciki.
Sai da tayi addu'a sannan ta shiga banɗakin, shigarta banɗakin keda wuya taji wani irin sauti daya girgizata matuƙa domin a shekarunta ta isa ta gane sautin kona meye,
("innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un")
Ta furta a fili yayinda ta tuna da labarin da uchie yakawo musu jiya da dare.
JIYA DA DARE:
jiya da dare zaune muke a tsakar gidan mu kamar yanda muka saba dayi duk dare na Allah.
Ni, aleena da kuma Nnene. Saiga uchie ya shigo kamar wanda aka harbo daga cikin baka.
Zama yayi dirshem agaban mu baicewa kowa komai ba Kowa kuma bai cemasa komai ba.
Nnene ce ta ƙatse shirun ta hanyar faɗin "uchie lafiya ka shigo gida a rikice haka"
"Inafa lafiya, babu lafiya Nnene kinsan labarinda mukeji na ƴan bindiga a Radio?"
"Ehhh" Nnene ta amsa masa da zaƙuwa.
"Tho sune sukaje ALARO AREA Jiya, sunyi barna sosai kuma babban abin bakin ciki su Waɗan nan ƴan bindiga basa kashe mata, iya maza suke harbewa sannan su kwashe matan su tafi dasu ba wanda yasan idan suke zuwa dasu"
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un na furta a fili domin labarin ya girgiza ni matuƙa, kuma na tsorata dajin labarin domin ina tsoron harbi da bindiga ko ya yake, ko sautin bindigar bana so, nafi tsoron sautin bindiga bisa ga ko wane sauti dana sani.
Cikin matukar tsoro na tambayi uchie:
"uchie a ALARO AREA sukazo"
"Ehhh ALARO AREA dai da kika sani nan sukazo kuma sunyi ɓarna da yawa saidai wanda ya tsira"
uchie ya faɗa yana kafe idanunsa waje ɗaya alamar tunani yakeyi.
"Yanzu menene jami'an tsaron ALARO AREA sukayi"
Nnene ke tambayar uchie.
"Ba abunda suka yi domin sun riga sun shirya duk yanda zasuyi kuma tsakar dare sosai ne sukayi aika-aikan nan"
Uchie ya kuma faɗi.
Mun tsorata sosai dajin wannan labarin domin har Aleena idan aka ganta za'a gane a tsorace take, ba wani abu ya tsoratamu ba kuwa sai don sanin duk abunda yasami ALARO AREA kamar ya sami MAKOKO AREA ne domin kuwa sune makwotanmu, Teku ne kawai tsakanin mu dasu domin idan aka haura za'a iya hango mutanen ALARO AREA ɗin.
Wannan shine babban dalilin da yasa muka tsorata baki ɗayan mu, amma uchie yabamu magana sosai yayi ƙoƙarin kwantar mana da hankali har dai muka sake baki ɗaya.
shiyasa yau dana shiga damuwa uchie yayi tunanin kamar labarin da yakawo mana jiya ne.
★★★
Tunanin leeya ne ya katse jin ƙarar bindigar data cika makoko, kuma gashi sautin na ƙarasowa kusa sosai, sai ihun mutane kake ji da ƙarar bindiga ta ko'ina.
A ƙiɗime leeya ta zunduma cikin duro ɗin da ke gabanta, ta janyo marufinsa ta sama ta kulleshi gammmm, sakamakon jin takun mutanen da kedoso ban ɗakin.
Da sauri mutanen suka shigo banɗakin tare da dallara tauch light mai rikitaccen haske, sosai sukayi binciken da zasuyi amma basuga komai ba, sai ɗayan mutumin da ke tsaye kusa da duro ɗin ne yace:
"kai nifa banyarda da wannan mazubin ruwa ba zobani tauch light ɗin nan naga menene aciki"
Dayan na shirin bashi fitilar ne sai babban cikinsu ya shigo zafafe ya daka musu tsawa
"me kukeyi a cikin ban ɗaki kuma, karfa ku lalata mana shiri wallahi kuyi maza ku fito muyi abunda ke gaban mu kar yanzu na kaddamar wa mutum".
babban ya faɗi maganar cike da dabanci.
Ita kuwa leeya a can cikin duro da take maƙe waje ɗaya, sanyi ya kaimata ko ina sakamakon ruwanda ke tabb da duro ɗin, tunanin ta a yanzu kawai wane hali Aleena, uchie da kuma Nnene suke ciki.
Wata zuciyar na bata ta fita taje da dubo, yayinda wani ɓangare na zuciyar ta na bugamata uban kashedi kan karda ta fita, ta zauna a ciki kafin komai ya lafa.
Zuciyarta kuma tafi karkata da wannan shawarar da wani ɓangare na zuciyar ta ke bata domin tana gani idan har ita ta sami waje ta ɓuya to tanada yaƙini cewa suma zasu sami waje su laɓe su ɓuya.
da wannan zuciyarta ta yarda yayin da taci gaba da zalalo hawaye a hankali domin ita kaɗai tasan abunda takeji,
Ta ɗauki lokaci mai tsawo sosai cikin duro ɗin saboda harta jigata kafin taji komai ya ɗauke ɗibbbb.
sai ƴan guntayen koke koke da takeji, yanke shawarar jira tayi domin tasan idan har su Nnene basu ganta ba
ba abunda zai hanasu suzo su nemeta, idan taji shigowar su kuma sai tayi musu alamar da zasuji tana cikin duro ɗin.
Tana nan zaune tana jiransu domin ta galaɓaita sosai, nan take wani tunani ya faɗo mata arai
"banji ko motsin su Aleena ba, idan sun ɓoya ae yanzu yakamata su fito su nemeni tunda dai basu ganni ba"
nan wata zuciyar tace da ita,,,,
"Taya zakice sun ɓuya waɗanda kika bari suna bacci mai nauyi kuma shigar ki nan ba jimawa wannan abun yafaru"
tana kawowa dai-dai nan a tunanin nata
Ta zabura da ƙarfi tare da izo duro ɗin iya ƙarfinta.
Bayan ya faɗi ne ta samu ta fita daga cikinsa, sannan ta fita wajen ban ɗakin a guje.
turussss tayi taja ta tsaya Sakamakon arba da tayi da gawar uchie bakin ƙofar ɗakin nasu, shiruuuuu..... Komai ya tsayamata a channn nesa da ita dakejin maganganun mutane na tashi tamkar ma bata cikin duniyar ƴan adam.
Zaman ƴan bori tayi gaban gawar ta uchie yayinda ta rasa mezatayi, wani irin sakaran ihu ta kurma, daga chan sai kuma tayi shiru kaɗan domin batamasan abunda ya dace da ita ba, dafa gawarsa tayi muryata na cracking:
"uchi dan Allah karka mutu ya kakeso muyi da rayuwar mu idan ka tafi ka barmu, uchie katashi dan Allah ka tashi idan har da gaske ne da kake cewa bazaka taɓa bari aga kukan Aleena........"
maganar ta ce ta maƙale sakamakon tunawa da tayi da Nnene da kuma Aleena,
Wani irin wawan zabura tayi daga gaban gawar uchie ta nufi ɗakin da suke kwana amma wayamm ba Nnene ba Aleena.
da sauri ta fito ɗakin ta fara dube-dube kamar wacce ta samu taɓin hankali haka take bin lungu da saƙo na gidan tana neman su kamar mai neman allura ko wani ƙaramin abu daya ɓata.
domin kuwa komai karantar abu sai ta ɗagashi ta leƙa ƙarƙashin sa tare da kiran sunan Nnene da Aleena.
Haka leeya taci gaba da kai da komowa tsakanin gawar uchie da kuma lungu da saƙo na gidan, har sanyin asuba ya sakko bata daina wannan gararamba ba.
Haka dai taci gaba dayi har rana ta hudo mutane suka fara tururuwa a gidan tare da jami'an tsaro na MAKOKO AREA waɗan da awannan lukacin sukeda alhakin ɗaukar duk wata gawa da aka kashe a kaiwa ƴan uwanta.
Bayan sunzo kan gawar uchie ne zasu ɗauka leeya tayi kukan kura ta nufesu a guje, dayake sun saba da samun irin haka yasa basu ɗaukeshi komai ba sunsan duk zafin mutuwar ne ta sanyata haka.
Mutum biyu daga cikin mutanen ne akasamu suka riƙeta har aka fita da gawar uchie gidan, sannan suka saketa sukayi