BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   19 / 61

54K to 57K   out of 180.4K words

shiga Rahmarsa da shiriyarsa, mungode kwarai Allah ya biyaku ta ƙarasa"
maganar tana sakin kuka mai qarfi.

Rarrashi sosai Nnene tayi mata tare da gayamata wannan ba komai bane, kawai dai su zama ɗiya nagari masu tarbiyya, kuma su dage da karatu ko don su zama wani abu nan gaba.


Bayan haka fira sosai sukayi amma duk a sanyaya leeya take amsa firar domin jikin ta duk ya mutu, ita kanta Nnene saida ta fahimci sauyin leeya a ɗan ƙanƙanin lokaci.

Sosai Nnene tayi ta tambayarta domin ta gayamata abunda ke damunta amma ta

"wai kekam leeya mayeke damunki ne ko kuma dai kintuna da ammi da abbi ne shiyasa naga kin shiga damuwa"


"Nima kaina wallahi bansan abunda yasa ni cikin damuwar nan ba koda tambaya ta za'a yi, Nima inaso naga nadawo Kamar yanda nake amma nakasa, kawai dai nasan yanayi kuma zanfita cikinshi in sha Allah"
daga haka leeya bata ƙara cewa komai ba itama Nnene haka.

Shiru suka yi baki ɗaya ba wacce ta ƙara cewa komai acikin su, sunɗauki lokaci mai tsawo a haka.


Shigowar uchie da budurwa ne suka katse musu shirun da suke:
"Nnene lapiya naganku haka kowa shiru"
Aleena ta faɗa tana ajiye ledojin ke hannunta

"Lafiya ƙalau budurwa andawo ina uchien yake?"

"Yana shigowa, tare muke dashi yeryer ko ba lafiya naganki shiru sosai"
faɗar Aleena tana zaunawa kusa da Nnene.

murmushi mai ma'anoni da dama leeya tayi sannan tace "lafiya ƙalau fa kawai kasala nakeji yau, me aka siyo haka?"

Ledar da kayan yake ciki aleena ta janyo tana kawota gaban leeya:"duba kigani yarhyarh, uchie yasiyamana kayakin nan harda kayan kwalliya aka siya miki, gaskiya yarhyarh uchie da Nnene na ƙaunar mu, bamuda abunda zamu saka musu dashi, wallahi nasan ko ammi da abbi ne bazasu wuce mana haka ba"

Aleena ta faɗa tana fitowa da kayakin da uchie ya siyamusu. kuma duk wannan abun da akeyi tuni Nnene tabar wajen.

shigowar uchie yasa ta tashi daga wajen su taje domin ta bashi abincinsa, kayane na sakawa masu dama Uchie ya siyamusu.

kuma kayan masu kyau daidai dasu, harda kayayyakin kwalliya da sauran abunda zasu buƙata.

Haƙiƙa sunji daɗi sosai, kuma sunyi farin ciki da ganin kayan, duk da ba wannan ne na karo na farko ba daya taɓa yimusu siyayya amma sunfi jin daɗin wannan musamman ma mai gayya mai aiki Aleena domin ta dalilin ta ne ake wannan hadada da girke-girke da komai:"yarhyarh nidai kinga kayanda zansaka gobe" Aleena ta faɗa tana ɗazo wata gown golden dake hannunta.

"Tau Allah ya kaimu goben nima sai in saka irinta kho"

"Ah ah wallahi idan kika saka irinta tawan nan Ae baza'a gane Ni nakeda bikina ba, za'a iya cewa mu biyune ai, kedai ki zaɓi wata ki saka kawai kingama ga wasu riga da skirt kho zasuyimiki kyau sosai tun can wajen da aka siyo su, kece na zaɓarwa su" faɗin Aleena tana ɗago da wasu kaga dasuke ninke cikin roll lader.

"Naji toh, biki ki saka duk waɗan da kikeso nikuma sai waɗanda kika zaɓarmin zan saka tunda kinsan kece Aunty dama"
leeya ta faɗa tana ƙara kallon aleena domin ganin yanda fuskar ta zatayi idan ta kirata da suna Aunty.

Ɗan fari da ido tayi sannan tace:"yawwa yarhyarh leeya haka akeyi a dinga bawa babba girmansa bawai yanda kike yi can baya ba, kamar dai banice budurwa"

Ta karashe maganar tana ɗan jujjuya bakin ta.


Murmushi leeya tayi saboda tanajin daɗin Ganinta tare da ƙanwarta, ƴar uwarta, rabin jikinta sannan kuma cikon farin cikin ta.

Labarine kala-kala ya shigo tsakani harda labarin okene aka ɗauko saida rana ta take kafin suka bar wajen leeya ta tashi da nufin taya Nnene aikin da sukeyi na abincin dare.

Aleena kuma ta fita zuwa wajen uchie domin can suke wuni tare dashi.

Sai da yamma liƙis kafin suka kammala aikin abincin, leeya ta ɗauko kwanukan da ake zubawa ta zubawa kowa nasa.

Nnene kuma ta tafi domin tayi wanka dan haka suke a duk lokacin da suka ƙare aikin abinci, sun gama komai tsafff, daga bisani leeya ta fara sharan tsakar gida da takeyi koda yaushe idan yamma tayi.

sai da ta share ko ina na gidan fesss kafin taje tayi wanka.
Tana cikin sharar ne su uchie da budurwa suka shigo
gidan:

"sannu da zuwa uchie ya kasuwa?" Cewar leeya.

"Lafiya lau leeya ana nan ana ta aiki."

"Ehh uchie ae na ƙare sharan wanka kawai ya rage".



Zakuyi mamaki sosai idan nace muku ba da hausa leeya tayi magana da uchie ba, ita kanta mamaki take yanda ta iya yaren Igbo a shekaru biyu kacal, hatta tsakanin ta da Aleena batayin hausa a wani lokaci, hakan kuma yasamo Asali ne daga uchie da Nnene domin sau tari idan zasuyiwa ɗayan su magana to basa yimasa Hausa, tun suna ɗaukar abun dariya hardai suka maida hankali sosai, yanzu sai can ba'a rasaba suke magana da hausa kafff gidan nasu.

Bayan ta ƙare sharan ne ta ɗibi ruwa sannan ta shiga ban ɗaki tayi wanka ta shirya ta fito tayi musu shimfida.

lokacin har anyi sallar magrib, tana gama yimusu shimfida taje tayi sallah sannan ta fito ta dawo ta gaidasu da wuni aka cigaba da yanda aka saba wato fira kafin lokacin cin abinci yayi, idan kuma kana buƙata kaci abinci zaka iya ci ba saika jira sai wani ya tashi cin nasa ba.

"Nnene gobe tun da safe ki tadani kinsan sai munje school mun dawo Sannan zamu fara celebrating ɗin namu a gida koh".


"Ehhh budurwa ina sane ban mantaba, zan tadake tun da safe kuma ai kinsan anan gida bamuda wata Matsala tunda mun gama shirya komai decorations kawai suka rage ayi, kuma ko decorations ɗin nasan da leeya batajin kasala da angama shi tunda balloons kawai za'a ɗaura"

Nnene ke maganar tana shafa fuskar leeya.

"Nnene nifa zan iya yin komai dakin gayamin decorations za'a yi tun dazun da na gama ai, amma ae koda haka ba laifi a bari goben kawai"

Saida lokacin da sukecin abinci yayi, sannan kowa yaci Abin cinsa daga Nan basu tsaya wata fira ba duk suka shige tilon ɗakin nasu suka kwanta, kowa yayi bacci sai leeya ce kaɗai bata yi bacci ba, sau biyu uchie yana tashi yana tambayar ta abunda ya hanata bacci amma ta rasa dalilin sai ba komai kawai take cemasa. hardai shima nannauyan bacci yayi awon gaba dashi.

ita kaɗai zaune ba bacci kuma ta rasa dalilin sabida ko kwanciya ta kasa yie, tashi tayi daga inda take zaune da nufin ta fita waje tayi fitsari, amma tayi lalubar touch light inda take tunanin an ajiyeta amma bata ganta ba.
haka ta tashi ita kaɗai ta buɗe ɗakin ta fita kuma ba wanda yaji fitarta da buɗe ɗakin da tayi duk a cikinsu hatta Aleena kuwa da suke gado ɗaya da ita bata ji fitarta ba, domin kuwa baccinsu sukeyi hankali kwance......✍️




BAYAN WUYA....







By RUMANA M DIGGI







EP.20


_________bada jimawa ba Leeyana ta fito toilet ɗin itama, koda ta fito ma zohal ta fara shiryawa.

Gaban mirror tazo ta ɗauki soft body Cream ɗinda take shafawa.

Amma ko ɗaga kanta batayiba balle taga kanta a mirror sanin cewa bata kallon mirror, kuma bata taɓa kallawa ba ma kwata-kwata.

Zohal kuwa ganin leeya ta fito batayi mata magana ba, yasakata tunanin ko itama tayi fushi ne

"bestie kinga fa hannun kin nan ya ƙara kumbura, ni wallahi
banmaso kiyi lallen nan ba. Duk da yayi miki kyau sosai wallahi ɗazun da muka fita waje kai abinci sai nuna lallen nan naki ake"

"Wallahi kuwa bestie zohal, Nima naga hannun ya ƙara kumbura, duk da yatsu ne kawai akayiwa"

"To Allah ya sauwaqe"

"Ameen, bara na kammala shafa lotion na fito miki da kayanki dana saka miki a wardrobe" cewar leeya.

"Ah ah, kibari kawai na fito mana dasu, keda kike mara hannu ina nie, ina sakaki aiki".

"Lallai ma bestie, nikam hannu biyu ne dani yanda kikeda hannu biyu kema"

"Tau shikenan naji, ina ne kayan naki suke na fito miki dasu"

"Ki duba inda na saka naki kayan, sannan ki duba a down box ɗin can ki zabamin niqab ɗinda zaiyi match da kayan".

"Okay, kawai zohal ta faɗa tana mikewa,

"Masha Allah, gaskiya bestie zohal kinyi sosai wallahi, kin ganki" cewar leeya tana kallon zohal da taga kamar ma an chanjatane domin kuwa tayi kyau ɗin da gaske.

"Humm, bastie abun har yakai sai anyi zolaya"

"Wallahi, bestie badai zolaya ba gskiya nake gayamiki, amma ko ban gayamiki ba ni nasan za'a gayamiki"

"Tau shikenan bestie naji, yanzu ki saka kayanki mu fita na ma daina jin motsin mutane sosai wata ƙila ma har an fita"

Wani bakin less mai ƙanan filawas red and black ta ɗakko, wanda aka yi mata ɗinkin doguwar riga, wacce tayi mata chif-chif ta saka. Kana ganin less ɗin basai ance komai ba kasan tsadadde ne, kayan sun ƙarɓi jikinta sosai ga kuma kwanci da sukayi a farar fatarta mai sheƙi, gyalenta ta d'akko ta yafa shima red ne wanda aka yimasa aikin bead mai kyau da tsari.

Niqab ɗin ta kuwa baƙi ne siɗik wanda ya ƙara fito da hasken idanunta. saidai ba kowa yake iya kallon idanun nata ba, saboda idan mutum yakallah yakan rasa dame zai siffantasu, sosai Leeyana tayi kyau, ga kuma jan lallen da aka yimata sharrr dashi.
Plat shoes ta ɗauko kalar gyalen ta ta saka kaana ta ɗauki wayarta suka fita.

Cikin tafiyarsu ta nutsuwa, suka fara tafiya har suka iso compound ɗin gidan inda akayi decorations. Sosai mutane ke kallonsu, domin kuwa ba wacce batayi wanka na gani, na faɗa ba acikin su biyun zohal da Leeyanah.

Itakam khulud mutuwar tsaye tayi ganin, kayan jikinta iri ɗaya dana leeya "yanzu haka papu zai min" khulud ta faɗa a cikin ranta tana barin wajen da sauri ta koma bedroom ɗin ta domin ta canja wasu kayan.

Leeya kuwa da zohal kutsawa suka dinga yi cikin taron mutanen da ke wurin suna neman mum amma basu ganta ba, duk inda sukaje saidai a ce musu yanzun nan ta ɗaga. Hardai suka gaji suka haƙura.

Leeya ce a gaba sai kuma zohal da ke bayanta sunada ƴar tazara sosai domin kuwa zohal komai tagani sai tayi video.

Tana shirin ƙwalawa leeya kira sai ta hango indiyawan nan wato FANNAH da MAYAH da RUKHSHANAH, saita kanta tayi sosai taje irin ta sansu ɗin nan domin kada su saka taji kunya.

"Sannunku" ta faɗa lokacin da take ƙarasowa gaban kujerun da suke zaune".

"Yauwa kema sannunki, FANNAH da MAYAH suka amsa kawai saɓanin RUKHSHANAH da ta ɗora NU'AIM kan ƙafarta suna kallon cartoons a wayar ta.

"Ki zauna mana sister kinyi tsaye kawai kuma ga wurin zama" FANNAH ta faɗa tana nunawa zohal kujera.

"Uhhm, Nagode sosai"

"Ahh ba komai" FANNAH ta faɗa da fara'ah a fuskar ta, "ke ƴar garin nan ce" FANNAH ta kuma yin Magana.

"Ehh, Ni ƴar garin nan ce kuwa, kefa?"

"Nikam a kaduna nake, menene sunan ki?" Cewar FANNAH.

"Kaduna kuma!!!?" Zohal ta faɗa cikin tsananin mamaki.

"Eh, a kaduna nake mahaifina kuwa cikakken ɗan garin Maiduguri ne, mahaifiyata kuma haifaffiyar BHOPAL ce a India".

"Sai a lokacin zohal ta sauke ajiyar zuciya, kamar wacce taga wani abun tsoro".

Dariya zohal ta bama fannah harma saida tayi sannan tace" wallahi sister kin ban dariya, sai kace wacce taga wani abun tsoro"

"Ai naga abun tsoro, naga mutum ba-indiye harda kayan sakawa na India kuma acemin ɗan kaduna ne ai dole tsoro ya kamani".

"Aikuwa dai, Ni ƴar kaduna ce koma nace ƴar Maiduguri".

"Ah ah kidaina faɗa dan Allah karki saka ƴan matan Kaduna prouding".

"Tau shikenan na daina faɗi, amma baki gayamin sunan kiba har yanzu" fannah ta faɗa da murmushi a fuskar ta. Domin ita haka rayuwar ta take tanada son mutane da fara'a da sakewa kamar dai Fahad.

"Sunana ZOHAL KHALIL GIRAH "

"Wow nice name ZOHAL KHALIL GIRAH, Ni kuma Sunana FANNAH GAHEES WAASIB, ƴan uwana biyu kuma wannan MAYAH waccan Rukhshanah sai kuma ɗan ƙaramin ƙaninmu NU'AIM, amma fa kinyi kyau sosai Wallahi" FANNAH ta faɗa tana yimata murmushi tare da ɗaga mata kai alamar gaskiyar abunda ta faɗa har ranta.

"Nice name sister FANNAH, kuma Nagode sosai kema kinyi kyau wallahi gaba dayan ku ma kunyi kyau, amma dai dakeda wannan MAYAH ƴan biyune kho domin kuwa ni har yanzu na kasa banbantaku".

"Haka mutane suke cewa, amma a zahiri gaskiya mu ƴan ukune harda waccan" FANNAH ta faɗa tana nuna Rukhshanah da yatsarta.

"Hummm, ke kuma a yanda kikace kenan, amma a zahirin gaskiya bakida kama ko silik da ita kinfi kama da Wannan da kuma yaron nan" cewar zohal tana nuna NU'AIM".

"Ah, ah bakisan kama bane kawai"

"Nasani mana tunda gashi na gani"

"A ina?" cewar FANNAH

"Anan" zohal ta bata amsa tana miƙewa.

"Ina zakije?"

"Tafiya zanyi, bani kaɗai nakeba ina tare da kawata ne bansan lokacin da ta ɓacemin ba kawai naga wankanku ya birgeni shine na biyo ta wurin nan".

Murmushi mai sauti fannah tayi domin kuwa harga Allah taji daɗi tace" shikenan sister zohal mun gode, zan iya samin contacts ɗin ki".

"While not, kawo na saka miki" zohal ta karbi wayanta ta saka mata contacts ɗin ta.

" Bara muyi photo kho" zohal ta faɗa tana ciro wayanta.

"Okay, Mayah ki taso ki mana photo" cewar FANNAH tana kallon Mayah.

Sai a lokacin Rukhshanah ta ɗago da kanta ta kallesu, sannan taci gaba da kallonda sukeyi a waya.

MAYAH kuwa ta taso ta ɗaukar musu photo Kamar yanda FANNAH ta buƙata, ta ɗauka a wayar kowanne su. Tayi musu photon Kala daban-daban sannan ta bawa ko wacce wayanta sukayi sallama ta tafi.

Tana barin wajen ta fara duba leeya bata gantaba. Duk inda take tunanin ganinta a wurin ta duba bata gantaba.

Wayar ta ta fitar tayi dailing number ta, tayi ringing sau ɗaya ta ɗaga "Assalamu alaikum, bestie kina ina na dubeki ban ganki ba".

Daga cikin wayar kuwa leeya ta amsata da faɗin "gani nan inda ake ajiye motoci nan ne kaɗai ba mutane sosai, na neme ki ban ganki ba, haka ma mum duk bangankuba shiyasa na zo nan".

"Ke kaɗaice a wurin ko da wani" zohal ta tambaya.

"Bangane da wani ba" cewar leeya.

"Sorry bestie gani zuwa" zohal ta faɗa tana yanke wayar.

Hanyar da zata sadata da packing space ta nufa, harta kusa ƙarasawa leeya tayi mata hannu alamar ta dakata wajen, itama leeyana tana ƙarasowa wajen zohal ɗin ma'ana
(ta baro parking space ɗin zatazo filin walimar)
Sakamakon ganin wata farar mota ƙirar range Rover ta tunkaro wajen yasa ta ba tashi domin ta bawa motar damar yin packing.

Gefe kaɗan da wurin suka samu suka tsaya, leeya ta kalli, Zohal tace "wai ina kika shiga ne haka kawai muna tafiya tare koda na waiwaya ban ganki ba"

"Wajen indiyawa na tafi" zohal ta faɗa tana murmushi.

A wannan lokacin hankali leeya baya kan zohal kwata kwata domin jin wani ƙamshi daya ziyarci hancinta, wanda bako shakka tagane kamshin turaren waye, a ranta ta furta "baqon balarabe!!"
"Kinga zohal dan Allah kizo mubar wajen nan"

Zohal ma ta kula da kyawawan samarinda ke fitowa daga cikin motar duk hankalin ta ya koma kansu, domin kuwa ba wanda zai gansu a wannan lokacin basu birgeshi ba.

Samarin gaba ɗaga ɗayansu uku kayan jikinsu iri ɗayane saidai kalar kayan ne ta banbanta.
Domin biyu daga cikin su American suits kalar pitch and white ne. Yayinda ɗaya daga cikin su yafita daban domin shi nashi kayan kalar pitch ne kawai babu fari ko kaɗan.

"Lahhh, bestie kinga ikon Allah, dubi samarin can uku ɗaya ba-indiye, ɗaya bature ɗaya kam Balarabe ne, amma kukam kunada family kala-kala wallahi" cewar zohal tana ƙara bawa idanunta abinci.

Gaban leeya ne ya faɗi rassss, jin kalmar balarabe a bakin zohal. Haka kawai takejin wani irin tsoron sa ba shiga ranta.

"Zohal na roƙeki da Allah kizo mu tafi, tunda kinga ga wanda akeyi walimar nan ya ƙaraso"

"Wallahi bestie kinada matsala bantaɓa ganin balarabe ba sai a TV ko waya, haka ma Bature, haka ba-indiye ma. Shine zan gansu yau gani gasu kice kar in kallah" Zohal ta faɗa tana gyara tsayuwar ta.






A bangaren samarin kuma, suna fitowa daga cikin motar ZAFARAN ya dafe saitin zuciyar sa, domin kuwa tunda ya shigo garin suleja yakejin zuciyarsa na bugawa a hankali, sai bayan ya shigo gidan nan kuma ya ƙara jin bugawarda take ya tsananta har saida ya dafeta sosai a gabansa.

Fahad daya lura da kallon da zohal ke yimusu yasa ya sakarmata murmushi ya kuma ɗaga mata hannu, yayinda suka fara tafiya. Shiƙaɗai ya lura da ita a wajen ZAFARAN da Turab kam duk basusan ma da itaba.

A tsakiyar su suka saka TURAB yayinda ZAFARAN keta hannun hagunsa, sai kuma FAHAD dake damansa kuma saiti da zohal.

Sunata tafiya ba wata tazara mai nisa a tsakanin su, har suka kawo daf da ida zasu wuce, sai duk ta daburce domin har yanzu Fahad murmushi yake yimata.

"Bestie mu tafi" cewar zohal tana miƙa hannun ta zata haɗa dana leeya. Sai taji wayammm, da sauri ta waiwaya tagni koda kuskuren miƙa hannun tayi, amma data waiwaiya taga ba leeya na alamar ta. kunyace ta kamata duk saita jita wani iri.

Daidai lokacin da su fahad suka kawo daff da ita saita ratse ta basu hanya.
Dawowa fahad yayi daga baya fuskar sa ɗauke da wani shu'umin murmushi yace,

"Yadai ƴammata, kinyi kyau sosai" ya faɗa yana kallon idanunta har yanzu dai da murmushi a fuskar sa.

"Nagode" zohal ta faɗa amma kuma ba wani murmushi ko fara'a a fuskar ta.

"Amma fa ban fahimci kinada kyau sosai ba, saida kika daina murmushi kamar haka gaskiya kin haɗu"

Cewar FAHAD yana kallon kwayar idanunta

Murmushi mai sauti tayi kaana tace "kaima u're so cute man, haka indiyawa suke ne da zolayar mutane".

"Ba zolaya gaskiya ce ai, kina da kyau sosai baiwar Allah. Kuma Allah yasa zuciyar ma kyakkyawa ce kamar dai ke ɗin nan".

"Ameeen ya rabbil ibaddd, Nagode sosai"

"Sunana FAHAD GAHEES WAASIB and you?"

"ZOHAL KHALIL GIRAH, amma kai yayan FANNAH ne?" Zohal ta fada cikin sigar tambaya.

"Nice to meet you zohal, ina kikasan FANNAH, ƙanwatace".

"Aiko baka faɗaba nasan

19 / 61