Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
Murmushi kawae Ammi tayi, ganin yanda leeya ta shigo gidan tana ji a ranta kamar ba ta yimata adalci ba, amma ya zatayi? Duk da itama kanta ba dadin hakan take jiba, batajin daɗin ganin ta a yanda take, domin nema mata kariya ne daga macuta yasa take sakata ta ɓoye fuskar ta ga kowa.
Miƙewa tayi ta nufi kofar shiga ɗakin saboda tasan dalilin Wannan kukan.
Kuma tasan yanda leeya takeyi idan an taɓota, shiyasa bata wani damuba.
shiga ɗakin tayi tare da nufar bakin gadon da leeya ke duƙunƙune tana ta sharɓar kuka,
"leeyana!!"
ta kira sunanta cikin murya mai nuna alamar ba wasa.
"na'am"
"tashi ki zauna"
miƙewa tayi tare da gyara zaman mayafin da ta rufe fuskarta sannan tace
"Ammi na zauna"
"Yawwa, Leeya ina so ki fahimci wani abu, nasan kina nan da tambaya a cikin ranki kuma kina tsoron furtamin tambayar. Dan numfashi tajaa taga nan ta ɗora da faɗin "Nikaina banaso kina yawan tambayata akan duk abinda kikaga nasakaki domin duk abunda zanyi inada dalili, leeyana a gani na kinyi ƙanƙanta da sanin komai daya shafi rayuwarmu, amma kisani mu mutanene kamar kowa kuma.
Wallahi inada dalilin da yasa nake hanaki yin wasu abubuwa, kinga kamar yanda nasani kema kanki bakisan dalilina na sakaki ɓoye fuskarkiba, kuma bakisan dalilin dayasa na hanaki kallon madubiba.
A yanda nasani kema kanki bakisan yanda fuskarki takeba balle wani na waje, to idan har zaki iya ɓoyewa kanki fuskarki mezai hanaki ɓoyewa sauran mutane, har ga Allah banayi haka bane dan na tauyemiki rayuwa ko kuma na hanaki sakewa kamar ƴar uwarki, kisani keda Aleena ba ɗayabane ko kusa baza'a haɗakuba,
Allah ne kawai yayi zaku fito ciki ɗaya da ita amma kunada bambanci ba ɗan ƙarami ba.
Leeyana kidaina saka ranki zaki cigaba da zama kamar sauran mutane ko yanda suke rayuwar su, kema kanki ban yarjemiki ganin fuskar ki ba harsai ranar auren ki, ko kuma idan kika tabbatar da ba makawa sai anyi aurenki kin tabbatar da ba wata matsala a ranar ne zaki san babban dalilina nayin haka. leeyana ko mijinda zaki aura banyarda da ki bayyana nasa kanki ba har sai lokacin ya cika!! Indai a sonane bana buƙatar yaga fuskar ki harsai an shafe fatihar daurin aurenki dashi, ko kuma a na gaf da yin haka.
Hannu ta saka ta tallafo habarta tare da faɗin "dan Allah ƴata kiyimin alkawarin komai tsanani komai wuya, komai zafi da rintsi, komai wahalar da zaki shiga bazaki taɓa bayyanar da fuska ki ga kowaba hatta ke kuwa! ba tare da an ɗauramiki aure ba.
"In sha Allah ammi na ɗaukar miki wannan alƙawari kisaka hakan a ranki. Leeya ta dauki alkawarin ne badan ta gane me hakan yake nufi ba. Sae ta kalli ammin Tata da mamaki tace "amma Ammi ku kuna ina ne harda kike tunanin zan shiga wahala, da rintsi, da tsanani"
Murmushin Ammi tayi kaana tace"idan Bama kusa dake leeya, ko kuma ke bakya kusa da mu, kinsan ba wanda yasan ranar zuwan ƙaddara, haka kuma ba wanda yasan abunda zai faru gaba. Yau kawai mukasani leeya bamusan me gobe zata haifar ba. Sai da Ammi ta ɗan nisa, sannan ta kai dubanta ga leeya a karo na ba adadi tace, "Toooh ki daina hawayen mana tunda komai ya wuce yanzu duk da bana ganin fuskar ki nasan har yanzu hawaye kikeyi kiyi hakuri wata rana zaki gane dalilina nayin haka kinji"
Jijjiga mata kai kawai leeya ta iya yi har zuwa wannan lokacin hawaye basu daina fita a idanun ta ba.
Sai yanzu suke jiyo muryar budurwa datake faman balbala bala'i a awaje. da sauri suka fito dakin, inda sukaci karo da abunda ya basu mamaki.
momyn Kingsley suka gani a tsaye tana faman ɗura ashar da ƙazamar hausarta da sai ka kula kake gane abunda take faɗa.
ita kuma Aleena gata ƴar mitsitsiya a gaban ta amma tana maida mata da martanin zagi kamar yanda take musu, dama hausawa sukace "kowa a gidansu sarki ne"
"Na rantse da Allah ƴar ku bata ciji bazan ba, jinin ɗana bazai fita a banza ba kuma ta zauna lafiya, mayya, kawai muguwa, ai dan Wannan muguntarne kika rufe fuskarki tauraruwa mai wutsiya. Me kingsley yayi miji da zaki cije shi harda fitar masa da jini" momyn ya faɗa tana nuna ɗan ta dake tsaye kusa da ita sai faman matso hannun tashi yake saboda jina ya kara yawa.
"Wallahi sai munje police station Dan bazan ɗauki dangana ba, haka yanda kika yi ƙoƙarin tsinka masa yarda"
maman Kingsley keta ɓaɓatu a tsakar gida ammi kam sai hakuri take bata amma inda take shiga ba ta nan take fita ba.
"Ammi kiyi wa Allah kidaina bata hakuri, inace police station kikace zakije kho, hmmm wallahi kin rago tunda a duniya take, bansan ke cikakkiyar mara mara mutunci bace sai kin wuce police station, ki kaimu inda yafi police station kinji, ko kuma idan kin kaimu kice a yanka mu a gasamu da rayuwar mu, kuma da kikace me ɗanki yayi aka cijeshi ai gashi nan a gabanki ki tambayeshi tunda ba wanda ya rufe masa baki munafukai kawai"
Aleena ta faɗa cike da matsifa da rashin tsoro.
Abbie daga shago yaji hayaniyar tayi yawa ya shigo gidan, tambayar abinda ke faruwa Abbi yayi, amma ta kalleshi cikin sanyi tace,
"ɗazune leeya ta fita shine Kingsley da madu suka tareta zasu cire mata mayafin da da rufe fuskar ta"
Abbie yadan zaro ido kaɗan sannan ya kalli Kingsley yace "haka akayi?"
Ɗaga masa kai yayi kawai domin har yanzu hannun na masa zugi gashi jinin ba tsaya sosai ba,
kuma har yanzu kuka yakeyi irindai yarannan da suka ƙware a makirci.
Abbie yajawo hannun yaron yacewa mum dinsa tazo suje Chemist a sakamasa magani.
dakyar da suɗin gishi ta fita gidan tana balbala ruwan bala'i.
budurwa kuwa harda binta da kasa tana watsa mata dan neman rigima.
zama sukayi gaba dayansu anata juya maganar, budurwa ce tace ''Wallahi ammi a kyale yayata ta daina saka mayafin nan, Ni abani in saka sai naga ɗan iskanda zaizo yace saiyaga fuskata, da ya tarowa kansa aradu da ka"
Ta faɗi maganar cike da matsifa a fuskar ta.
murmushi kawai ammi tayi domin itama abun yafara isarta duk da itama ba wannan ne farko ba kuma bashi bane na biyu,
kai idan da sabo itama ammi ya kyautu ace ta saba.
" Ammi waima na tambayeki dan Allah meyasa tana saka mayafin nan a fuskar ta? wallahi Ammi nima inaso yayata ta dinga buɗe fuskar ta, yanzu fa Ni ko a waje na ganta ba mayafi bazan ganeta ba.
saboda nima bansan fuskar taba, koda nasani na manta.
"uhmmm zaki sani kinji budurwa amma akwai lokaci har yanzu" cewar Ammi.
Dan jimmm budurwa tayi kamar wacce keson tunano wani abu kafin tace:
"toh ammi Allah ya kawo muna lokacin lafiya" ta faɗi magana cike da natsuwa bayan ta gama masifa.
" Tooooo sabon salo Aleena ce ke magana haka, ammi Allah ya kaiki ga budurwa kuwa wallahi" leeya ta faɗi maganar tana dariya. Taɓe baki Aleena tayi zatayi kuka sai.......✍️
EPISODE 003.
*************
Aleena kamar zatayi kuka tace "Ammi kinjita kho dama can ni ba budurwa bace Ammi?"
"Ke budurwa mana ki shareta kawai tanajin haushine saboda ita ba budurwa bace"
MAFARIN ƘADDARA.......
janyota Ammi tayi jikinta sannan tayimata rada a kunne, gwalo tafara yiwa leeya, yayinda leeya ta cika tabbb kamar zata fashe ta ƙulu sosai ta tashi da niyar barin wajen, ammi ta riƙo hannunta tare da maida ita ta zauna, sannan itama ta janyota jikinta tana faɗin "me yayi zafi ƴan matan Ammi, kiyi hakuri da kanwarki kinji ki dinga binta a hankali wata rana sai labari Allah yayi muku albarka"
"Ameen" suka faɗa gaba ɗaya yayinda budurwa ke murza wani zobe dake maƙale a ƙaramar yasar ammi.
"Ammi kullum idan muka tambaya ina kakan nin mu muna sai live mana sunana, kuma idan na tambayeki ina yayarki kamar nida yayah leeya sai kice mana bakida yayah saidai ƙanwa, idan na ce to ina ƙanwar taki take sai ki nunamin zoben nan, ammi yaudai ki faɗamin labarin zoben nan dan Allah"
𝔸𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕜𝕠𝕞𝕒𝕚 𝕪𝕒 𝕗𝕒𝕣𝕦, 𝕒𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕞𝕒𝕚 𝕒𝕗𝕜𝕦𝕨𝕒 t𝕒 𝕒𝕗𝕜𝕦, 𝕕𝕒𝕘𝕒 𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕞𝕒𝕜𝕦𝕝𝕝𝕒𝕟 𝕜𝕠𝕗𝕠𝕗𝕚𝕟 𝕜𝕒𝕕𝕕𝕒𝕣𝕤𝕦 𝕤𝕦𝕜𝕒 𝕗𝕒𝕣𝕒 𝕓𝕒𝕪𝕪𝕒𝕟𝕒, 𝕒𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕜𝕒𝕕𝕕𝕒𝕣 𝕥𝕒 𝕤𝕠𝕞𝕒, 𝕒𝕟𝕒𝕟 𝕟𝕖 𝕜𝕠𝕗𝕠𝕗𝕚𝕟 𝕜𝕒𝕕𝕕𝕒𝕣𝕒𝕣 𝕤𝕦 𝕤𝕦𝕜𝕒 𝕗𝕒𝕣𝕒 𝕓𝕦𝕕𝕖𝕨𝕒, 𝕕𝕒 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒 𝕥𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕜𝕒𝕚 𝕙𝕒𝕟𝕟𝕦n𝕥𝕒 𝕘𝕒 𝕫𝕠𝕓𝕖𝕟 𝕓𝕒, 𝕕𝕒 𝕒𝕔𝕖 𝕝𝕖𝕖𝕪𝕒𝕟𝕒 𝕥𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕥𝕤𝕠𝕜𝕒𝕟𝕚 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒 𝕓𝕒, 𝕕𝕒 A𝕝𝕝𝕒𝕙 𝕪𝕒𝕟𝕒 𝕓𝕒i𝕨𝕒 𝕓𝕒𝕨𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒𝕪𝕚 𝕗𝕦𝕤𝕙𝕚 𝕓𝕒 𝕤𝕒𝕓𝕠𝕕𝕒 𝕒𝕞𝕞𝕚 𝕥𝕒 𝕣𝕒𝕣𝕣𝕒𝕤𝕙𝕚 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒, 𝕕𝕒 𝕒𝕞𝕞𝕚 𝕥𝕒 𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕣𝕦𝕟𝕘𝕦𝕞𝕖 𝕒𝕝𝕖𝕖𝕟𝕒 𝕓𝕒 𝕓𝕒𝕝𝕝𝕖 𝕥𝕒𝕜𝕒𝕚 𝕙𝕒𝕟𝕟𝕦 𝕥𝕒 𝕥𝕒𝕓𝕒 𝕫𝕠𝕓𝕖𝕟. 𝕀𝕟𝕗𝕒𝕔𝕥 𝕕𝕒 𝕒𝕞𝕞𝕚 𝕥𝕒𝕤𝕒𝕟𝕚 𝕕𝕒 𝕓𝕒𝕥𝕒𝕪𝕚 𝕞𝕒𝕘𝕒𝕟𝕒𝕣 𝕠𝕜𝕖𝕟𝕖 𝕓𝕒 𝕓𝕒𝕝𝕝𝕖 𝕙𝕒𝕣 𝕒𝕜𝕒𝕚 𝕘𝕒 𝕨𝕒𝕟𝕟𝕒𝕟.
Ammi takai idanun ta kan zoben nan take idan nun ta suka sauya kalla, jaaa ya maye gurbin fari.
Sai ga hawaye sun fara rige-rigen fita a idanun ta, janyesu tayi daga jikinta kafin suyi wata magana ta zabura da ƙarfi ta shiga ɗaki tare da rufo ƙofar ɗakin ta fara kuka mai sauti.
A duk lokacin da akayimata maganar zoben, ko aka ambata mata wani bayani akan zoben, to takan iya shiga damuwa da sai ankai Ruwa rana kafin ta iya dawo wa kamar yanda take.
Yauma kamar yanda ta sabane saboda ta shige daki tanata rizgar kuka
"Allah sarki ƴar uwata wallahi bazan taɓa mantawa dakeba dan Allah ku yafemin rayuwata batada Amfani idan har ban sadu dakuba ya Allah ka haɗa fuska ta da ta iyayena koda a mafarki ne"
Ammi ke maganar cikin matsanancin kuka mai taɓa zuciyar.
Jiki a sanyaya leeya ta miƙe ta nufi hanyar waje domin sanarwa da abbinsu abunda ke faruwa, hannunta Aleena ta rike cikin kuka take faɗin
"yayata kada kiyi fushi dani dan Allah wallahi mantawa nayi, kuma wallahi nayi tunanin ta daina yin kuka idan aka taɓa zoben wallahi dabazan taɓa ba, muje ki rakani na bata hakuri dan Allah"
sake fashe Aleena tayi da kuka yayinda leeya itama ta fara kukan nata, taso tayi dauriya amma ta kasa, a ƙidime Abbi ya shigo gidan inda ya fara tambayar su, dalilin kukan nasu,
leeya ce ta iya buɗe baki ta gayamasa abunda ya faru da sauri jiki na rawa ya isa bakin ƙofar ɗakin, ganin ta ƙofar garƙame yasa ya tattaro dukkan ƙarfinsa ya banke ƙofar take ƙofar ta faɗo ƙasa duk suka ruga cikin ɗakin,
turus sukayi a tsaye sakamakon ganin ammi cikin wani hali, kamar dai ciwon tane ya tashi.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un faheema!! faheema!!! faheema!!!"
Da ƙarfi yake kiran sunanta, kafin yayiwa leeyana magana da ta fita wajen gidan ta sama musu abin hawa suje da ita asibiti kafin ya fito da.
Leeya da jikinta keta kyarma sai ta kasa motsawa daga inda take, banda rawa ba abunda jikinta keyi. Sai faman kuka mara sauti take
Da mugun ƙarfi Abbi Daka mata tsawa.
Yayi abunda bai taɓa yi ba a rayuwarsa yiwa yaransa tsawa.
Ba leeyana kaɗai ba hatta aleena da ba gefensa takeba saida ta firgita da tsawarda Abbie yayi.
Ae kuwa ta ƙara rikicewa da kuka yayin da leeya ta ruga aguje tanata kuka itama.
cikin Sa'a kuwa tana fita sai ta haɗu da mai taxi alayin nasu ya ajiye passenger,
Da gudu ta isa gareshi fuskar ta lulluɓe da mayafi kamar yanda ta saba ta haɗe hannuta wuri ɗaya, ta kasa magana banda kuka ba abunda takeyi sai nuna gidan nasu da hannunta.
Driver na ganin haka ya fahimci akwai matsala nan take ya kama hannun ta suka nufi bakin gidan nasu, suna isa kuwa saiga Abbie ya fito tare da ammie kamar wacce ta dade da ciwo ko taka ƙafarta bata iyayi, da sassarfa take tafiyar gwanin ban tausayi, isowa sukayi gaban mai taxi din kafin ya taimaka musu aka sakata a motar, wani asibitin gwamnatin suka nufa dake nan ECOCO.
Dayake bawani nisa ne dashi ba, nan take aka iso, suka fitowa da ita aka shiga da ita cikin asibiti, kamar dai yanda kukasan wasu malamam asibiti da halayensu ƙalilan ne suke da tausayi ba'a karɓesu da wuriba, saidaiaka jira wani babban likita yazo kafin aka karɓesu, wani daki aka sakata a ciki wanda ko gado babu.
A ƙasa aka kwantarda ita aka dauramata drip kafin likitan yayi kiran abbi a office ɗinsa.
"Hamraz awais ko kaine?"
Likitan ya faɗa yana cigabada da buɗe wani files dake gabansa.
"Ehhh nine doctor"
"A gaskiya hamraz matarka tana cikin damuwar wani abu data kasa cirewa a ranta, tun a farko da kuka fara kawota a asibitin nan na gayamuku ku dinga taka tsantsan wajen kiyaye abunda zai sakata tunani, wannan ciwon nata yanason kulawa, kuma nasan kunayi duk da yanzun nan ma bansan abunda ya faruba amma nasan antuna mata da wani abune dayake damunta"
ɗan jimmm Abbie yayi kafin ya ɗago kai idanunsa duk sun chanja kala sunyi jajir kamar wanda yaci kuka Sannan yace:
"hakane doctor ba shakka antuna mata da wani abu ne dayake damunta,
kuma bazai rasa nasaba da wannan zoben na ƴar uwartaba,
wanda shine dalilin yin doguwar jinya da muka taɓayi a can baya a asibitin nan.
Ni bana nan ina shago naji kukan yara koda nashigo gida suka nunamin tana nan a ɗaki, koda nashiga ma a rufe na tarar da ƙofar, sai da na ɓallata, to ɓalla kofar danayi ne yasa naganta cikin wannan hali. Yanzu dan Allah doctor menene abunyi.
ɗan guntun tunani doctor tauƙir yayi kafin yace:" inada wata shawara wadda idan akayi amfani da ita ko matsalar bata kau gaba ɗaya ba tho zatayi dama, bisa ga abarta a haka wata rana wannan ciwon zai iya zama ajalinta, saboda masu irin ciwon nan nata basa shiri da damuwa ko tunanin.
Shiyasa kaga ciwon yaki cie, yaki cinyewa saboda taƙi ta fitarda damuwa a ranta. Kuma taƙi ta daina tunani, nasan wannan abun dake damunta ba ɗan karamin abu bane. Amma in sha Allah idan kabi wannan shawara dazan baka za'a samu mafita"
Sake gyara zama yayi kafin yace bawata shawara bace nakeso na bada ba, face a arabata da zoben nan! haƙiƙa idan tana tare da wannan zoben damuwa bazata taɓa barin zuciyarta ba, amma idan aka rabata da zoben in Allah yaso abun Zaiyi sauƙi ba kamar yanda takeji ba a yanzu duk da bansan alaƙarta da zoben ba amma rabata dashi shine mafi a'alah tunda shine sillar janyo komai.
Cikin alamun tsoro Abbie yake kallon doctor tauƙir fawizz kafin yace:" haba dae doctor, da dai an chanja wannan shawarar gaskiya. Wannan shawara batayi ba, kana gani fa doctor taɓa zoben Nan idan akayi matsala ce dazata iya jefata wani hali na daban, kaga fa ko yanzu taɓa zoben nan ne kawai akayi bawai an cireshi ba, to inaga idan cireshi ne akayi? gaskiya doctor a chanja Wannan shawarar kawai" Abbie ya faɗa idonsa tarrr akan doctor tauƙir fawizz.
Cikin wani irin murmushi irin na yarda dakai dr. Tauƙir fawizz ya sake duban Abbi, "haƙiƙa zakaga rashin dacewar wannan shawara dana baka, amma kasani Ni aikinane kuma nasan baka fini sanin aikina ba tunda bazanyi Abunda zai cutar da wani ɗan adam ba. Wannan rantsuwa ce tsakanina da Ubangiji na, bawai ban taɓa cin karo da irin Wannan matsalar bane, ah ah matar ka ba ita kaɗai bace takeda irin wannan ciwon ba, akwai waɗan da damuwarsu dukice, akwai waɗan da tasu ta ƴaƴa ce, akwai waɗan da tasu ta soyayya ce,
akwai waɗan da tasu ta iyaye ce ko wata kadara ko aure duk dai akwai waɗanda damuwar nan ke damunsu. Amma kuma ta hanyar rabasu da abubuwan gaba ɗaya a rayuwar su, kesa asamu sauƙi akan damuwo yinsu kuma su manta da komai.
Jikin Abbie ne yayi sanyi kafin ya kalli doctor tauƙir sannan yace ''doctor taya za'a rabata da zoben to? kuma ace bazata sani ba, kar kuma ya sake jefata a damuwa, haƙiƙa bazan taɓa yafewa kaina ba idan na bari wani abu yasami fahima, kuma ban cika ɗan halak ba idan har haka ta faru, na amince doctor amma meza'ayi wanda bazai cutar da ita ba".
Numfashi doctor tauƙir fawizz yaja a hankali sannan ya jinkina da kujerar shi ya lumshe idanu ya fara gayamasa yanda komai zai tafi "da Farko inaso ayimata allurar da zata sakata bacci na ƴan sa'anni kafin daga nan acire zoben,
sannan sai akuma yimata wata allura da zata gusammata da hankali.
Kuma idan allurar tasaketa bazata tuna da zoben nan ba, saboda bazatayi tunanin ko an cireshi a hannunta ba balle takawo baya nan a hannunta. Wannan shine shawara ta,
ko daga baya idan ta tuna da zoben bazata kawo a nan aka cireshi ba, a haka zata yita tunanin inda ta ajiye shi hardai ta manta dashi ta daina batunshi tunda batada taƙamammen wurinda ta ajiye shi"
"Baki abunda kace doctor, kuma wannan shawarar tayi amma Ni bata karbu gaba daya a raina ba. Sai sai muyi addu'a Allah yayi mana jogora"
Achan kuma ɗakin da aka kwantarda da Ammi leeya ce tare da Aleena suna zaune kusa da Ammi, Aleena sai kallon amminsu takeyi tanata kuka kamar wacce aka cemata mutuwa zatayi.
leeya kuma nata ƙoƙarin kwantar mata da hankali domin tayi shiru ta daina kuka,
ita kanta dauriya kawai take yi amma ita kaɗai tasan abun da takeji. ammi kuma tana kwance idanun ta a lumshe suna zubarda wasu siraran hawaye.
Sallamar Abbie sukaji ta ratsa ɗakin kafin ya iso garesu Aleena ta tashi aguje ta nufeshi tana kuka
"Abbie dan Allah kace Ammi ta tashi sannan kace ta dakeni idan haka zai sakata ta huce ta dawo yanda take,
kuma dan Allah kace tayi hakuri wallahi indai nice Abbi ban komawa, bazan sake taɓa zoben ba dan Allah Abbi ka faɗa mata kaga Ni ko kallona batayi idan ina yimata Magana"
Aleena ke maganar tana kuka abun tausayi, rungume ta abbi yayi tsam a jikin sa sannan ya shanye hawayenda ke kokarin zubo masa ya ƙaƙalo murmushi ya shimfiɗa a fuskar sa duk domin ya kwantar wa da yaransa hankali.
"Haba