BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   18 / 61

51K to 54K   out of 180.4K words

ya haɗo sosai basu kai ga cin abincin ba aka fara ruwa,
Ɗaki suka shiga suka nemi mafaka anan sukaci abincin anata fira da ban dariya,
Haƙiƙa su Nnene ma sunji daɗin kasancewa dasu leeya domin koba komai sun rage musu raɗaɗinda sukeji na rashin haihuwa,
Sai gashi yanzu abun na wanke wa acikin ransu.

A ta bangaren su leeya da Aleena suma sunji daɗi sosai dan basuyi tunanin sake kasancewa kamar haka ba.

Sunsha fira sosai da labarai daga bakin aleena, har suka raba dare suna fira bako alamar bacci saida uchie yayi musu umarni da kowa ya kwanta har da safe saboda yaga alamar idan ba'a kwanta ba za'a iya kai safe a haka.

Dan ƙaramin gadon karan da ke jingine aka sauke musu a ƙasa, sai kuma wata ƙaramar katifa wacce zata ishesu kwanciya su biyu.
zanin atamfa Nnene ta ɗauko tare da shimfida musu sannan aka kunna mosquito suka kwanta, wani zanin ta ƙara ɗaukowa mai ɗan girma ta yafa musu sakamakon unguwar tanada sanyi sosai, ko ba lokacin damina bane balle yanzu da ake tsakiyar damina.

Baccinsu sukeyi hankali kwance kamar ba abinda ke damunsu,
dayake ko a gida leeya ta saba da tashi tun da sassafe miƙewa tayi daga kwancen da take tare da sakkowa daga kan katifar, kallonta takai wurinda taga su uchie sun kwanta amma sai mutum ɗaya kawai tagani kuma batasan ko waye a cikinsu ba.

Fita tayi waje da nufin tayi alwala tayi sallah,
sai ta tarar da Nnene a cikin barandar ɗakin, inda ruwa bai jiƙa ba tana faman hura wuta.

isowa tayi wurin tare da dafata bata cetamata komai ba ta dauki buta, ta shiga ban ɗaki ta ɗauro alwala Sannan ta fito.
Inda aka ajiye musu kayansu da sukazo dasu tun a jiya ta nufa tare da ciro hijab da kuma sallaya domin duk ta haɗo dasu kuma tasan zaiyi wuya a samesu gidan nan.

Shimfiɗawa tayi inda take tunani Nan ne gabas a gidan ta tayarda sallahr ta hankali kwance, sai da ta kammala kafin ta tashi ta maida komai inda ta ɗaukeshi
Sannan ta fito waje
"Nnene barka da safiya, antashi lafiya?"

"Lafiya ƙalau, ya gajiya"

"Ba gajiya" leeya ta faɗa tana nufar inda aka killacewa dabbobi, domin nan ne kawai take tunani bai jiƙe ba da ruwan da aka sheƙa jiya da dare.

ta shiga ciki ne domin ta samu abun wuta bushasshe da zasu saka cikin wutar da Nnene ke hurawa cikin Sa'a kuwa ta samu ƙananan karare da sauran hakin da ya ɗan fara bushewa, ta fito sannan taje gaban murhun tare da durƙusawa, gaban murhun.

"Nnene bara na tayaki"

"Ah ah leeya kije ki huta mana ko jiya fa haka muka sha aiki dake, baki huce gajiyar jiya ba Sannan yau kizo ki daɗa wata akai"

Ɗan murmushi leeya tayi wanda tasan Nnene bazata gani ba domin fuskar ta a cikin mayafi take,
"ba komai kibani na tayaki kawai, Ae na iya hura wuta kije ki kwanta kawai idan na hura sai nagayamiki idan ta kama"

Duk yanda Nnene taso suyi aikin tare leeya taƙi barin ta wurin saida ta tashi ita kuma taci gaba da yaki da wutar har dai ta samu wutar ta kama daidai,

Miƙewa tayi ta nufi ɗaki domin ta kirawo ta amma tana juyawa sai gata ta fito

"sannun ki da aiki leeya kinyi ƙoƙari sosai"

"Nagode"leeya ta faɗa tana murza yatsan hannunta.

Tukunya Nnene ta ɗauko ta ɗora suka fara aikin tare ba jimawa suka kammala gabaɗaya. abincin su na Igbo Mai Rai da lafiya suka haɗa ba abunda leeya bata ganeba a Cikin abunda sukayi, domin tana tambayar duk abunda bata sani ba ita kuma Nnene bata gajiya tana gayamata duk abun da ta tambaye ta da kuma amfaninsa.


Bayan sun kammala girkin safen ne leeya ta haɗo duk kwanukan da suka ɓata jiya ta wankesu tsaff.

Nnene da uchie sunji daɗin samuwar leeya a gidan koba komai zata rage musu wani aiki musamman yanzu da tsufa ya fara kamasu:
"leeya sannu da aiki kekam bakya gajiya" Nnene ta faɗa tana murmushi,

Leeya ma ta maida mata da martanin murmushin, abincin su sukaci saida suka ƙoshi kafin Nnene ta ɗoro musu ruwan zafin da zasuyi wanka baki ɗaya, bayan ruwan sunyi zafi ta kaiwa uchie nasa a banɗaki yayi wanka, ya shirya ya fita domin yana sana'ar sayarda ƙwai ne a nan makoko, sai itama ta ɗiba nata tayi, sannan bayan ta dawo ta ɗiba tayiwa aleena har ta wanke mata kanta ta kunce mata shi.

"Leeya kema kizo na wanke miki kan naki sannan kije kiyi wanka"

Da "tho" leeya ta amsa tana miƙewa tare da nufar ta, ƙara gyara mayafin ta tayi yanda ko za'a wanke kan mayafin bazai fitaba kafin ta cire abunda ta ɗaure gashin ta, sai gashinta ya baje gaba ɗaya dama chan anjima ba'a gyara shiba, cikin zallar mamaki Nnene tabi gashin leeya da kallo tana nuna mamakin ta ƙarara, saidai bata ce komai ba saboda ta ba abunda yashafeta bane.

Sai da ta wanke mata gashin tsafff kana ta baje mata shi yanda zaiyi saurin shan iska sannan takai mata ruwa banɗaki tayi wanka.

Tana fitowa saiga okene ya shigo gidan, sai dai ganinta ya tsorata shi sosai, yanda ta baje gashin nata kai kace fatalwace, domin kuwa da dare ne ya ganta haka ba abunda zai hana masa ihu wata ƙila ma harda gudu zai haɗa.

Yatsarta ta saka tare da janye gashin da ya rufe gaban mayafin ta sannan tace:

"Okene barka dai har ka shigo"

"Barkanki leeya ya gajiya,

"Ah ba gajiya" ta faɗa tana ajiye bucket ɗinda ke hannunta tare da nufar inda su Nnene suke zaune, sai yanzu okene ya lura da Nnene datake sakawa budurwa kaya domin harta gama yimata kwalliya ta shiryata tsaff, gaisawa sukayi sosai cikin jin daɗin yanda okene ya tarar da Nnene nayiwa su leeya kamar dai itace ammi, haƙiƙa yaji daɗi sosai bada wasa ba.

Gyarawa leeya gashinta Nnene tayi sosai ta shafamata man gashi mai kamshi ta ɗauremata gashin nata sosai ya kwanta yayi sumul gwanin ban sha'awa, tashi taga daga wajen ta shiga ɗaki ta sanya kayanta ta chanja wani mayafi,
fitowa tayi tare da zauna wa aka ci gaba da fira da ita har Nnene tana gayawa okene irin ƙoƙarin da leeya takeyi harma take gayamasa yau ita tayi musu abinci.

"Wane kalar abincin tayi muku?
Cewar okene fuskar sa ɗauke da murmushi,

"Fufu dough" leeya ta bashi amsa, tun kafin ya tambayeta.

Da mamaki ya kalleta:"yaushe kika iya fufu dough kinsan kho ba abunda nakeso kamar abincin nan. Cewar okene yana kallon leeya cikin mamakin ta.

Ita dai Nnene kallonsu kawai takeyi kuma da alama firar tasu tanayimata daɗi.

"Tau Ae da sauranshi idan zakaci sai a zubo maka kaci kho" Leeya ta faɗa tana kallon okene

"zanci kuwa ki zubomin naci da yawa dan inason kalar abincin nan wallahi"
ya faɗi maganar yana shafa cikinsa.

Murmushi tayi mai sauti sannan ta tashi ta shiga ɗaki ta zubo masa abincin mai yawa kamar yanda ya buƙata,
tazo gabansa tare da ajiyemasa abincin
Sai kuma ta juya ta koma ciki, kofi ta ɗauko tare da ɗebo masa ruwa ta dawo ta ajiyemasa, sannan ta koma gefe ɗaya ta ƙura masa ido har ya gama cin abincin tsafff,

"Nnene a gaskiya banyarda leeya tayi abincin nan ba akwana ɗaya kacal da zuwanta gidan zatayi wannan, ya kenan idan tayi shekaru"

Murmushi Nnene tayi kafin tace:"ehhh mana ita tayi komai, nuna mata kawai nakeyi, sai kuma inda tayi kure na gyaramata"

Baki okene ya washe sosai cikin jin daɗin yace:"kenan idan nazo ziyarar ku zanci girki mai daɗi kenan bama acewa komai, tabbb aikuwa idan kika girma restaurant zan buɗamiki irin wannan abinci haka"

Sai bayan yayi maganar ne ya tuna tun sadda suka fara maganar Abinci da Nnene bada hausa sukeyinta ba da yaren Igbo ne sukeyinta,

"Saura wannan kuma"
Okene ya faɗa yana kallon leeya.

"Me kenan"
Itama ta tambaye shi.
"Yare mana"
Ya bata amsa .

Ƴar Siririyar dariya tayi kafin tace:"shima na iya ta faɗi maganar tana ɓoye fuskar ta da tafin hannayen ta kamar shi okenen ganin fuskar tata yakeyi.

"Ae naga alamar kin iya dan gashi nan naga kinyi abincin mu,
Nnene kema kice ta koyamiki abincin su na hausawa kar tayi miki wayo ta iya namu bamu iya nasu ba"
Ya faɗi maganar cikin yaren Igbo ne shiyasa leeya bata fahimci abunda yake nufi ba.

"Ae kuwa hakane kaga ma ɗazun da muke girkin tace gobe zata yi mana tuwon shinkafa" Cewar Nnene.

"Iyyeee kice gobe uchie zai chanja abinci kenan ina ma ina nan da nima naci tuwo". Faɗar okene yana ɗaga kansa sama kamar mai tunano wani Abu.

"Ae kuwa hakane yau ne tafiyar taku kho"
Nnene ke tambayar okene

"Ehh shine ma nazo na muku bankwana dan kinsan idan mun tafi shikenan munbar ƙasar Lagos ba abunda zai maidamu saidai ko ziyara" cewar okene yana kallon leeya dayake ita batasan maganar da suke ba shiyasa hankalin ta baya kansu,

Firarsu sukayi sosai harda Aleena da ta tashi daga baccin rana da takeyi da kuma uchie daya dawo daga kasuwa yanzu, okene ya jima sosai a makoko kafin yayi musu sallama zai wuce.
"Budurwa kinsan yau ne tafiyar tamu kho? Yau zan barmuku garin Lagos"
"Lahhhh broth yaune tafiyar taku kho, wane gari ne ma zaku koma? Aleena ke tambayar okene idanun ta na kanshi.

Yana shirin bata amsa leeya ta tari numfashinsa:"broth shikenan idan ka tafi bazaka dawo ba, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un muko yazamuyi broth kai kaɗai garemu kaikaɗai muka sani,
Gashi zakayi nisa damu.

"Haba leeya ga Nnene nan da uchie nasan zasuyi muku fiye da abunda zan yi muku.

duk yanda kikeso na zauna Lagos ɗin nan wallahi na fiki son na zauna,
haka kawai nakeji kamar na rasa wani ɓangare na jikina kuma nakejin Zuciya ta na karyewa idan na tuna babu ku a inda zanje

amma wannan alƙawari na ɗauka miki zan dinga kawo muku ziyara akai-akai abunda kawai nakeso dake shine, dan Allah ki saki jikinki ki ɗauki Nnene da uchie kamar ammi da Abbi nasan basukai Matsayin suba amma za'a iya kwatanta su da irin wannan matsayi saboda suma iyayene daga ƙarshe leeya dan Allah ki dage da karatun islamiyyarki da kuma boko.

nayi magana da uchie har ma yagayamin sai sakaku wata makaranta Anan makoko sai kuci gaba da zuwa islamiyyar ku a ife kinji leeya, okene ya faɗa idanunsa na cikowa da kwalla.

Tuni ruwan hawaye sun wanke wa leeya fuska ganin da gaske yau okene zai barsu shikenan Okenen ta.

ɗagowa tayi ganin ya miƙe take ta isa gareshi da gudu tare da rungume shi tare da fashewa da kuka.

rarrashin ta yayi sosai kafin ya samu ta sassauta da kukan da take.


"me zaki bani na riƙa tunawa dake wanda idan ina tare dashi zanji kamar kina tare dani?"


Dakata wa tayi da kukan da take kafin da ɗanyi tunani,

"broth Banada abunda zan baka har na tuna lokacin da ammin mu take faɗin duk ranar da zakuyi tafiyar nan dani za'a je saina ga garin da zaku zauna sannan na dawo" leeya ta faɗa Muryar ta a sanyaye.

"Allah sarki tau Allah yayi muku rahma"

"Amen"

Okene ya faɗa sannan ya kuma cewa:"leeya bakida abunda zaki bani fa kikace"

"Broth O wallahi da inada abunda zan baka saboda karka manta dani dana baka. Nima kaina bana so kamanta dani kayimana komai a rayuwar nagode sosai Allah ya sada mu Da alƙairi"
leeya ta faɗa Muryar ta na cracking.

"Wannan fa?" Okene ya faɗa yana nuna abun hannun da ke daure a hannunta na dama.

"Wannan??" ta ƙara tambayarsa itama tana kallon abun hannun da ya nuna mata da ke daure a hannunta.

"Shi!" Ya faɗa yana ci gaba da kallo da kuma nuna mata abunda yake so a hannunta.

Wannan kakeso na baka?"

"Shi nake so ko bazan samu ba na hakura"

Da sauri ta cireshi a hannunta ta ɗaura masa da kanta,"ko abunda yafi wannan ka nema indai a wurina ne zaka samu, balle wannan".

godiya yayi mata sosai kana yayiwa su uchie sallama suka rakashi har ecoco gaba ɗayan su Sannan suka dawo gida makoko.

Bayan sun dawo, suka ci gaba da safgar gabansu, saidai tunanin okene ya kasa fita zuciyarta.




****


Shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Nnene, leeya, uchie da kuma Aleena a cikin ƴan kwanaki, ba abunda zasu nema su rasa a gidan.

ba wani hantara ko nuna ƙyama, ba kuma wani banbanci da suke nuna musu ata bangaren addinin su, dan har islamiyya suke zuwa ife, kuma suna sallah, har makaranta uchie ya sakasu a makoko, kuma suna riƙonsu da tarbiyya kamar iyayenda suka haifesu.

A bangaren leeya kuma tana ƙara kwarewa a iya girkin kala-kala Nnene na koyamata gashi tanada saurin riƙe abu bata da mantuwa sosai.







★★★
BAYAN SHEKARU BIYU, Abubuwa da dama sun faru a rayuwa, ciki kuwa harda rasa wani ɓangare da leeya tayi na rayuwar ta, wanda shine silla ta biyu da ya jefata a wata rayuwar mai tsananin wahala da ƙaƙanikayi, da halin ƙunci da tsananin wuya da azaba.

Wata rana da safe a cikin ranakunda leeya bazata taɓa mantawa da suba a rayuwarta.

zaune suke a tsakiyar gida ita da Nnene da kuma budurwa anata magana yanda za'a shirya ɗan ƙaramin shagali da uchie yakeso ya haɗawa Aleena da zata kammala examinations ɗinta na JLCE Anan makoko yayinda leeya take ss two a wannan lokaci.

"Nnene kinga daidai chan zamuyi decorations zaifi haske domin nan rana take facing" Aleena ta faɗa tana nuna wani ɓangaren a gidan nasu.

"Nnene nidai can nace kinga zaima fi kyau da ɗaura balloons, sabida rana bata isowa can, sannan bamusan lokacin da zamu ɗauka anan ba, amma can datakeso idan rana zata faɗi nan take fuskanta, ɗazu ma naga uchie ya shigo da balloons a hannunsa" Cewar leeya.

Cikin ƙaguwa da son jin tabbacin abunda leeya ta faɗa aleena ta ƙara tambayar ta:"yarhyarh da gaske uchie ya siyo min balloons ɗinda za'a yi decorations dasu?"

"Eh da gaske mana Ae ba balloons kaɗai ya siyo ba harda sababbin kayan da zamu saka gobe ya siyo mana" leeya ta faɗa tana janyo wata leda dake ajiye gabanta.

Farin cikin Aleena ya kasa ɓoyuwa har saida ta matso sosai tare da rungume Nnene.

"Nnene Yakamata mufara aikin fanken nan kada dare yayi mana a aikin"

"Ehh yanzu nake shirin yimiki zancen ai"

"Nnene Nima dani za'a yi aikin yau tunda domin ni za'a yi komai ninakeda komai n
Kuma laɓaku kawai nayi saboda muna gida ɗaya daku kar a ce nayi rashin kirki" cewar aleena tana miƙewa daga jikin Nnene.

Murmushi Nnene tayi batare da tacewa aleena komai ba

"leeya ki dauko abun zubewa ki zube fulawar nan sannan ki shiga ɗaki ki ɗaukomin sauran kayan haɗawa sai na nunamiki yanda zakiyi wannan, idan kin gani sai kici gaba ni kuma na fara aikin okra soups wadda na baki labari jiya"

"Ohh natuna itace kikace anfi amfani da ita wajen biki ko party koh"

"Itace kuwa ashe ma baki manta ba, to kije ki dauko abun da nace miki idan kin ɗauko sai innunamiki yanda zakiyi Wannan idan kin gama sai kizo kitayani muyita, ke kuma budurwa kizo in ki baki aikin da zakiyi tunda kince kema sai kinyi"

Miƙewa leeya tayi tare da nufar tilon ɗakin gidan nasu domin ta ɗauko abunda aka aiketa ta ɗauko, bayan ta ɗauko ne ta dawo ta zauna suka fara aikin nasu, sun ɗan ɗauki lokaci kafin su kammala haɗawa daga nan Nnene ta barmata aikin ta karasa ita kuma ta fara aikin okra soups.

Haka kawai leeya takejin jikinta a sanyaye yau kuma kome take a kasalance takeyinsa,
ji take gabanta yana duka kamar wacce wani babban abu yafaru da ita, haka kawai takejin faduwar gaba.

tunawa tayi da addu'ar da ake koyamusu a islamiyya idan kana jin wani abu makamancin wannan ka dinga karantawa, addu'ar ta fara jawowa a hankali tana Binta dalla-dalla hardai ta samu hankalinta yaɗan dawo jikinta.

Hatta ita kanta Nnene ta fahimci akwai damuwa a tattare da leeya domin ba haka suka saba aikinsu da ita ba:

"leeya me yake damunki?"

"Babu komai Nnene ba wata matsala bace, haka kawai nakeji gabana yana faɗuwa inaji kamar wani abu zai faru"

Guntun murmushi Nnene tayi sannan tace "kwantar da hankalinki leeya ba abunda zai faru damu, kinga yanayine kawai kuma da gajiya, ki tashi kije ki kwanta ki huta kafin anjima idan kin huta sai muci gaba aikin kinji, yanzu kije zamu idar da wannan nida budurwa"

"Ah ah Nnene zan iya muci gaba da aikin nan kawai kinga har yanzu akwai waɗansu ayukkan daban"

"Ah ah fa leeya jeki ki kwanta kawai kinji karki damu yanzu zamu kammala komai"

Kama hannunta Nnene tayi takaita har cikin ɗaki sannan ta dawo taci gaba da aikin ta.


Inda suke kwanciya leeya ta kwanta tare da lunshe idanu abubuwa da dama suna faɗo mata arai, kwanciyar ta wurin keda wuya bacci yayi awon gaba da ita.

ba ita farka ba saida yamma sosai, cikin mamakin kanta da baccin da tasha ta fita waje tare da kiran sunan Nnene:

"haka nasha bacci amma baki tasheni ba, yanzu ma nasan kun ƙare aikin gabaɗaya kho, gskiya nidai ba haka nasoba Nnene"

leeya ta kare Maganar tana buɗe wani babban faranti da aka zube fanken da akayi:

"kai amma gaskiya fanken nan yayi kyau Nnene aikuwa duk ranar da broth O zaizo a cikin kalaluwan abincin da zanyi masa harda wannan fanken sai na yi masa"

Murmushi Nnene tayi kafin tace:"aiko da kin yimasa ƙoƙari saboda ba wanda za'ayi wa irin wannan sai wanda akeji dashi sosai ko budurwa da kikaga nayiwa inaji da ita ne shiyasa"


murmushi itama leeya tayi:" ina Aleenan take naji gidan nan shiru, gidan nan yayi lafiya.
Leeya ta faɗa tana ƙara wulla idanun ta inda take tunanin zata ganta.


"Batanan tafita ita da uchien ta sun tafi ƙaro sayayya su siyo abunda ba'a siyaba"

Idanun leeya ne suka ciko da kwalla bata masan sanda ta rungume Nnene ba saboda ta tabbata koda su Abbi ne da ammi abunda zasuyiwa Aleena bai wuce wannan ba

"Nnene mungode, mungode kwarai kunyi mana gata a lokacin da bamuda wanda zai dubemu balle yayi muna, kun suturtamu a lokacin da muke neman wanda zai yimana sutura, kun mutuntamu a lokacin da wasu Mutanen suke nufin wulakanta tamu.
haƙiƙa bamuda Kamar ku, ina rokon Allah ya saka muku da alƙairi ya rabautaku da

18 / 61