BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   48 / 61

141K to 144K   out of 180.4K words

bace. Yanzu ya zasuyi kenan?"
Fahad ke maganar a ransa, hanjin cikinsa kuwa sai wani yamutsawa suke da qarfinsu.

Lokacin da mum ta haɗa fuska da leeya kuma wasu abubuwan suka shiga dawo mata.

Mum kamar mai shafar aljanu ta kalli leeya cikin tsawa da daga murya tace "leeyana, ki gayamin asalin mahaifiyarki. Wacece ke leeyana? Ki gayamin"

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Aleena kizo dan Allah. Wallahi nasan ko kowa zai gujeni ke bazaki gujeni ba, dan Allah menene a fuskata da ya saka kowa yayi nesa dani ki gayamin kinji kanwata" leeyana ta fad'a cikin kuka tana qarasowa inda Aleena take.

Ganin haka sauran mutanen da basuda taurin zuciya suka qara zurawa da gudu kamar wadan da sukaga dodo ko wata halitta mai ban tsoro.

Sake dakamata tsawa mum tayi kamar zata rikota tace "leeyana ba tambayarki nake ba! Wacece mahaifiyarki nace?"

Kallonta leeyana tayi ido cikin ido, a yanzu ta rasa mezatayi lissafin ta gaba ɗaya ya kufcemata har bata iya yin controlling kanta tace "me kike so ki sani?"

"Ina so nasan wacece mahaifiyarki, haqiqa kama ma qarya take ace mahaifiyarku daya da wannan yarinyar Aleena, zan iya yarda da mahaifiyartace a makoko wacce aka sacesu tare, amma wallahi Indai kece ban yarda da cewa wannan da kika bada labari itace mahaifiyar ki ba. Gayamin asalin gaskiyar da kike boyewa leeyana, ke mutum ce ko aljan?"

Kuka mai tsanani ta fashe dashi kafin ta iya furta"Ni mutum ce wallahi, banada da hadi da wasu aljannu, don girman Allah kuyimin bayanin abunda nakeso na sani menene a fuskata dan Allah?"

"Ba komai a fuskar ki yayata, kuma koda kowa ya yarda da cewa ke ba mutum bace Wallahi bazan ta'ba yarda ba.
ki kwantarda hankalinki, muje mirror ki kalli kanki"

"Kafin nan Aleena!, nace kafin naje mirror ki gayamin dan Allah"

"Yahya ta, wallahil Azeem kyawunki ya yi yawa, ya yi yawan da ba'a iya fahimtar mutum ce ke ko bil'adama, wallahi da ace bakya saka mayafi da yanzu sai wata bake ba, abune mawuyaci a sami mai irin halittar nan taki, kwata kwata ba halittar mutane bace dake, kinfi shiga da jinsin aljanu shiyasa mutane suke gudu, kowa da kika gani a wajen nan a rikece yake yana gani kamar cutardashi zakiyi idan kika karaso inda yake"

Zaman dirshem tayi a kasa ta dafe kanta dake neman tarwatse wa.

"Leeyana dan Allah ki gayamin asalin gaskiyar wacece mahaifiyarki, wallahi na fara wani tunani a kanki" taji Muryar mum a sanyeye kamar zata fashe da kuka.

"Bansan wacece mahaifiyata ba, bansan asalinta ba, ban san dangintaba, wallahi ita kadai na sani sai abbina da kuma qanwata Aleena"

"Menene cikakken sunan mahaifiyarki??"

"Faheema Rawaan Hahmeed".

"Whattt??????" Mum ta fad'a baki na rawa.

A lokacin da sunan nan yaje kunnen papu da turab basu san lokacin da suka qaraso gaban leeya ba su duka ukun mum, turab, da kuma Papu.

"Leeyanah zo gareni, kizo gareni leeyanah nice mahaifiyarki, kuzo 'ya'yana" mum ta fad'a cikin Muryar kuka tana ware musu hannayenta biyu alamar suzo.

Kamar kuwa jira suke suka fad'o jikinta sai kuka suke su duka ukun gwanin ban tausayi.
Turab da Papu ma suna tsaye suna kallon ikon Allah da dimbin mamaki, hatta mommy neesah da dad qarami da suka san asalin sunan hajiya fanaya sai da suka kwashi taslimah jin suna nan da leeya ta fada.

Basu san ko wacece ita ba, ba kuma susan ina ta fito ba, amma sun tabbatar da koma wacece tanada alaqa da mahaifiyarsu.

Janye jikinta tayi daga nasu tana shafa fuskar leeya, a hankali ta furta "Masha Allahu fi ahsanil kaliqiin" kinada kama sosai da mahaifiyarki, sai dai ke kinfita kyau nesa ba kusa ba, amma kuma duk wanda yasan ta farin sani daga zarar ya ganki zai fahimci kinada alaqa sosai da ita. Ba banza ba danaji ina qaunarki tun ranarda na fara ganinki a bakin hanya, Allah ya sakamin qaunarki da tausayinki, a she soyayyar jini ce leeyanah ke ƴa tace"

"Mum, Nagode sosai da duk wata qauna da kuka nunamin. Kuma ina roqon Allah yasa ku jera kafad'a da annabi wajen shiga aljanna akan wannan, Amma mum har wannan da kike gani qanwatace, mahaifi da mahaiyarmu d'aya da ita" leeya ta fad'a tana kallon Aleena dake tsaye.
Ita bata gane komai ba, wannan matar tana fadin mahaifiyarsu ce, amma kuma bata san alaqarsu da ita ba, a yanda take nunawa ma kamar itace ta haifi leeyanah, taya haka zata faru?

Riko hannun Aleena mum tayi tana shafa kanta cikin tsanin so da qaunar su tace " Allah yayi muku albarka, nasan labarin da zaku bani akan faheema bai wuce kuce ta rasu ba. Tunda naga kunyi fama da rayuwa har haka nasan bata raye, Allah ya jikanta yayi mata rahama, Allah yasa ta huta, Allah ya yafemata kurakuranta dan darajar fiyayyen halitta"

Tun kafin su leeyana suce wani abu Dayammah ta tari numfashin mum cikin tsananin mamaki da rashin gane makamar zancen ta tace "hajiya kema kinsan wani abu game da yaran nan ko kuma mahaifiyar su?"

Sai da mum ta isa kan sofa ta zauna tare da d'aga kanta sama kadan kamar mai wani tunanin hawaye na zubowa a hankali daga cikin idanunta tace "nasan mahaifiyarsu, mahaifi da mahaiyarmu d'aya da ita, mu biyu ne kacal Allah ya bawa iyayenmu, mahaifiyarsu faheema itace yahyah a wurina nikuma ina matsayin qanwarta.

Mahaifinmu ya kasance mutum ne mai tsanani akan abunda ya saka gaba, kuma babu abunda ya tsana kamar cin amana da kuma karya alqawari, mahaifinmu Rawaan Hahmeed mutum ne mai saurin fahimta da sauqin kai, sai dai kuma baya so ya nuna ya isa dakai kai kuma ka nuna masa bai isaba, mu ba masu kudi bane amma muna da rufin asirin Allah sosai. Domin za'a iya sakamu tsaka tsakiya.
Sana'ar mahaifinmu itace ya sauke masuyin cirani ya basu masauki, a kwai wurare da dama da aka ke'be a wajen gidan mu inda ake sauke mutane komai yawansu.
Mahaifinmu nada wani yardajen amininsa dake daura jahar katsina, wata rana aminin mahaifinmu yazo kawo mana ziyara da babban d'an sa su biyu, sun jima a gidan mu kafin su tafi bayan mahaifinmu ya gabatar da mu wajen Aminin nasa har kuma babban d'ansa da yazo dashi ya nuna yana son faheema mahaifiyar ku.

Abu kamar wasa soyayya mai karfi ta kullu tsakanin su harda maganar aure. Ana cikin hakane kuma wata qaddara ta afku akan faheema, ba kowace qaddara bace face ta soyayya.
faheema ta kamu da matsananciyar soyayyar wani bako da ya sauka gidanmu cikin yan ciranin da ke zaune tare damu, mutane da yawa sun tabbatar da cewa babu wanda ya sanshi, kuma babu wanda ya taba ganinshi ko a wani wurin, hasali ma mu'amalarsa ta bambanta da ta sauran mutanen da ke wurin, kuma sannan baiyi kamada ya'yan hausawa ba ko kadan, duba da yanayin maganarsa.
Abu kamar wasa magana tayi karfi tsakanin mahaifin mu da faheema, ita ta tubure akan bazata auri wanchan ba wannan takeso, kuma mahaifinmu ya riga ya karbi sadaki har ansaka rana sati biyu masu zuwa.
Wani Abun bakin cikin ma da aka kira shi wannan da takeso aka tambaye shi wani abu game dashi ba wata gamsasshiyar amsa da ya bayar, amma kuma shima ya nuna mana irin tsananin qaunarta da yakeyi, a lokacin kuma nima inada manemi domin kusan ma lokaci daya aka shirya dauramana aure da ita.

Mahaifinmu ya gargademu akan bayason wannan Magana ta fita domin bayaso a dinga yimasa kallon mutumin banza, in takaice muku ma hatta su iyayen angon basu san da wannan matsalar ba, shidai kawai yaga sauyine a tattare da ita ba kadan ba, amma dayake mai hakuri da yawan uzuri bai taba kawo kararta wurin iyayenmu ba.

Anyimata iyaka sosai da wannan bakon mutumin, kuma mahaifinmu mutum ne mai gaskiya cikin al'amurran sa, shiyasa bai kori bakon mutumin a gidanmu domin yawan kudin da ya bada ko rabin su bai ci ba.

Ana washe gari za'a dauramana aure ne cikin dare faheema ta kasa bacci sai kuka take da tunani, mikewa nayi zaune na rarrasheta hadi da ban baki domin tayi shiru ta daina kuka ta yarda komai nufin Allah ne.

"Dan Allah karki manta dani fanaya, inaji kamar bazamu sake haduwa ba. Ko ba komai zanyi nisa dake sosai"

"Haba dai, ki daina wannan maganar kinji. aure zakiyi fa, in Sha Allah babu abunda zai faru dake yar uwata"

"Inaso ki bani wannan zoben na hannunki ko zan dinga kallonsa naji kamar muna tare dake"

Murmushi na mata lokaci daya kuma hawaye na zuba daga cikin idanuna, hakika ba wanda ya siyamin zoben da ke hannunta, amma wallahi ina matukar kaunar zoben da ta nemi na bata. Idan za'a ce in lissafa abubuwanda nafi qauna a rayuwata Wallahi nasan zoben nan zai shigo a cikin abunda zan fada.
Ganin da gaske ne nisan zatayi dani ya sa na cire zoben na saka mata "yar uwata dan Allah kiyimin alqawarin zaki riqe zoben nan da amana, sannan kuma ki dinga tunawa dani a duk lokacin da kike tare da zoben nan, idan kinyi aure kinzo gida ganin mu bazan fara tambayar komai ba sai shi idan kuma kika gayamin wani abu sabanin abunda nakeson ji, shikenan ba ruwana dake tunda nasan kin manta dani ne kawai"

"In Sha Allah komai nisan da nayi zan kula da zoben nan fiye da komai fanaya, ki saka wannan a ranki"

Mahaifiyarku faheema ta fadi haka tana qara daidaita zoben a yatsanta.

Da haka dai har bacci ya daukemu gaba daya. Koda safiya ta waye ban ganta a dakin ba domin kuwa ban tashi da wuri ba yau ko sallahr asuba banyi cikin lokaci ba, dubana na kai kan shinfidar ta nayi murmushi kawai ina tuna yanda mukayi da ita jiya tana wasu maganganu kamar mai shirin barin duniya.

Ban nemeta ba domin nasan tana dakin mahaifiyarmu ko kuma tsakar gidan duk da yawan jama'a yan bikin daura aure da suke faman tururuwa.

Munsha kitso da lalle ga kuma gyara irin wanda akeyiwa amare kana gani ba sai an cemaka komai ba.

Nasha mamaki sosai danaga har rana ta hudo ban ganta ba, kuma bata tsakar gidan, dakin iyayenmu ne kawai banshiga ba saboda ina jin kunyar wasu mutanen da ke zaune a dakin.

Sai dai wani abun tsoro da mamaki ina zaune a dakinmu nida qawayena da sukazo tayani zama sai ga wata mata ta shigo da sallamar ta tace wai ummanmu na neman faheema.

Da mamakina na kalleta na kuma tambayar ta faheema ko kuma ni, domin ita faheema bata nan tunda na tashi daga bacci bansakata a idanuna ba. Wannan dalilin ne ya saka nayi tunanin ko tana wurin umantamu.

Abu kamar wasa har magana ta fito fili akayi neman duniya a gidan babu ita babu labarin ta.
Dawowa nayi cikin dakin mu domin ni ban gasgata abunda yake faruwa ba cewar wai an nemi ta a ko'ina ba'a ganta ba.

Duk wani lungu da saqo da ke cikin dakinmu dubawa nake ko Allah zai saka na ganta amma banganta ba, gadonda take bacci na nufa tare ta fatar Allah yasa in ganta idan na daga bargonda nake hangowa daga nan inda nake.
Duk da nasan abune mawuyaci a sameta akan gado yanzu.
Ina zuwa na d'aga bargon da karfi banga komai ba sai wata nadaddiyar takarda ta fado daga cikinsa.

Hannu na rawa kamar mazari na buɗe takarda na karanta, abunda na gani a ciki ne ya saka na zube wurin bansan wane hali nake ciki ba sai jina nayi a ɗakin ummanmu.

A hankali na fara buɗe idanuna ina kallon kowa dake zaune a dakin anyi cirko-cirko.
Sake murtsika idanuna nayi cikin Muryar kuka nace "dan Allah umma kada ku gasgata mafarkina, dan Allah kuce banga wasiqar da faheema ta ajiyeba duk mafarki nake kinji ummana"

Dan guntun hawaye ummanmu ta share sannan tace "kwantar da hankalinki fanaya, Allah ba azzalumin kowa bane idan faheema ta zaluncemu Allah bazai bartaba, babban tashin hankalina shine dangin mijinta duk suna nan suna jira. Baramma mahaifinku dake can waje yana jira lokacin daura aure yayi a daura.

Maganar nan da muke yanzu saura mintuna Takwas ne a daura aurenku, taya zan gayawa Rawaan faheema ta gudu da bakon mutumin nan, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un Allahummah ajirnee fiii musibatii, wa'akhlifnii khairan min ha" mahaifiyarmu ta karashe maganar da kuka mara sauti.

Tausayin ta ya kamani sosai ganin yanda muka tara jama'a dangi da wad'anda ba dangi ba.

"Ummah me zai hana ki kira yaya arman (babban d'an yayan mahaifinmu kenan) sannan kuma ki kira uncle Bahar da kuma uncle Dawud ki sanar musu da komai tun kafin a daura auren tunda kinga lokaci kurewa yakeyi" Nima na fada cikin karayar zuciya.

Da shawarar nan mahaifiyata da kuma babbar amintacciyar ta sannan kuma da qanwarta da suke uba d'aya mukayi amfani wajen sanarwa da kanin mahaifinmu da kuma yayansa sannan da babban d'a a cikin familyn mu.

Koda aka sanarmusu sunyi Allah wadai da halin faheema sosai, kuma sun jinjina rashin hankali da kuma rashin wayonta da har zata dauki kafa ta gudu da wani saurayi. Saurayin ma ba'ko wanda ba'a san asalin sa ba.
Koda suka sami mahaifinmu da wannan maganar zuciyar sa kusan bugawa tayi domin sai da aka tafi dashi asibiti aka bar komai hannun uncle Dawud.

Shikuma uncle Dawud da yazo ya sami mahaifin angon da faheema zata aura da kuma shi angon ya gayamasu gaskiyar komai bai boyemusu ba anan kuma ya shaidarwa da ango baza'a a fasa daura auren ba za'a Daura.
Saidai ba da faheema da 'yar wajensa idan ya yarda, ango kuwa bai watsa musu qasa a ido ba ya nuna amincewarsa ɗari bisa dari akan hadin da sukayi.
Lokaci na cika kuwa aka daura aurena da angona, shikuma angon da akayi niyyar daura aurensa da faheema aka fasa aka daura masa aure da 'yar wajen uncle Dawud Babba a cikin 'ya'yans.

Har muka sami wata d'aya da aure ana ta jinyar mahaifinmu da ciwon da ya shigeshi rana daya.

Mun kwashe tsawon watanni takwas babu wani sauqi kullum abu gaba yake zuwa.
Mu ba masu kudi bane, amma kuma akwai manyan masu kudi da 'yan kasuwa sosai a cikin danginmu, shiyasa sukayi shawarar fita dashi waje a duba lafiyarsa.

Ana washe gari za'a yi tafiyar ne kusan asuba ciwon mahaifinmu yayi tsanani, kafin akai ga kiran sallahr Asuba Allah ya karbi ransa.
Amma wallahi bai mutu ba sai da ya furta kalmar yafiya ga faheema, yace ya yafemata ta dawo ta ci gaba da rayuwa cikin danginta, sannan kuma ya yarda ya amince da aurensu Allah ya saka masa albarka.
Da wadannan maganganu a cikin bakinsa har ya bar duniya

Munsha kuka sosai, dangi dana kusa da na nesa sai Allah ya isa akeyiwa faheema musamman ma dangin da suka fito daga bangaren mahaifin mu suna ta munanan furuci akanta.

Dana ji munanan kalaman da suke akan yar uwata sun isheni na tashi da kausa-sasshiyar murya nace "ya isa haka dan Allah, menene amfanin munanata da kukeyi, ita qaddara idan zata zo bata shawara da kowa take zuwa, haka zalika ba wanda yasan dame zatazo, kuna ta fadar faheema ta kasha Abba taya ta kasheshi wacce a halin yanzu bata ma san abinda ke faruwa ba, qaddara ce tazo. Kuma a kanta ta fad'a.
komai yanada sanadi a duniyarnan, Allah yayi sana'ar mahaifinmu ce zata yi sanadin komai na chanjawar rayuwarsa. Da a ce bayayin sana'ar sauke ba'kin mutanen cirani, bansan inda faheema zata ganshi ba har ta bishi su gudu ba.
A wannan maganar idan akayi tunani cikin aikin nutsuwa da hankali to faheema ba ita bace sanadin mutuwar Abba ba, shine da kansa sanadin mutuwar ke hannunsa. Saboda haka na rokeku dan girman Allah kudaina zaginta.
Kuma abbanmu bai rasu ba sai da ya furtamata kalmar yafiya, saboda haka ko kun tsinemata ba inda tsinuwar zataje tunda mahaifin ta ya riga da ya yafe mata"

Duk jikinsu yayi sanyi likiss da abunda na fad'a daga nan kuma kowa ya ja baki yayi shiru ba wanda ya qara magana akan haka.

Lokaci ya jaaa sosai abunda zai faru dai ya riga ya faru, mun rasa mutane biyu daga cikinmu, muka saka salama a cikin ranmu muka manta da komai kamar ba'a yi ba.

Bayan watanni kuma wani iftila'i ya afku akanmu, cikin tsakiyar hantsi Yan boko haram suka sauka a Maiduguri sukayi kan mai uwa da wabi.

Mun samu nasarar tserewa ba tare da wani ya cutu tsakanina da mahaiyarmu, muna fita Maiduguri kuma muka dauki hanyar Bauchi domin a can ma munada wasu dangi da dama, koda muka je Bauchi ma mun tarar da wasu danginmu dake Maiduguri anata sam barka, anan muka sake kafa wata sabuwar zumunta. Yanzu maganar nan da nake miki gaba dayan danginmu suna bauchi d'ai-d'ai ku daga cikinsu ne Bama tare dasu.
Nan mukaci gaba da rayuwa da dangina, saidai Ni tuni mijina ya daukeni muka koma abuja da zama bayan anyi masa qarin matsayi a wurin aiki.
Sai bayan an haifi khulud ne muka dawo suleja da zama.
Amma yanzu duk dangin namu sun koma gida, mafi akasarin su duk sun koma Maiduguri.

Babban albishir ɗin da nake yimuku leeyanah shine ummanmu tana raye, kuma itama ta yafewa faheema, sannan da yawa daga cikin danginmu duk sun yafemata domin suna ganin kamar duk inda taje zata dawo, wasu kuma suna ganin ta dawo amma ta tarar da an tarwatsa mutanen Maiduguri.

Alhmdullillah ya Allah ina qara jaddada godia ta agareka, kaine sarki ɗaya tak, kaine muke nufa da buqatun mu ya Allah na gode maka da ka qarfi addu'a ta. Allah kabani ikon yiwa marayun nan naka gata wacce iyaye suke yiwa 'yayansu"
Mum fanaya ta fad'a hawaye na sakkomata amma a fuskar ta murmushi ne kwance.

Rungume su tayi tsamm a jikinta tanajin qaunar su na qara ratsata.

Wata sabuwar qauna takeji game da yar uwarta faheema sai dai ba halin nuna qauna gareta tunda bata nan. Saboda hakane yasa takejin qaunar leeya da Aleena na Ratsa ko'ina na sassan jikin ta.

Ba wanda baya hawaye a Dakin bayan mazan da suke tsaye, musamman ma Khulud hawayenta yafi na kowa ita har ranta kunya takeji wai ashe ma yar uwarta ce ta jini ta dinga wulaqantawa da tozarci.

Zuwa tayi gabansu itama ta rungumesu tana hawaye, turab da papu kuma suka qaraso suka zauna. Fahad, da zafaran da kuma dad qarami suka zauna kan sofa's dinda ke farkon shigowa parlourn.

Turab kam inda mum take ya nufa shima ya zauna kusa da ita sosai, ya kwantar da

48 / 61