Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
yatsun ta tana rubuta wa.
Tun zaman ta a gidan bata taɓa zama a nan ba hasali ma bata ganin kowa yana zuwa nan.
Ita kanta bata taɓa kula da wurin nan ba sai ɗazu da suka dawo school taga wani ma'aikacin gidan ya fito daga wurin ya tsayar da papu, sukayi magana.
Sosai tayi mamaki domin bata taɓa sanin akwai wurin nan a gidan nan ba, ko kuma dai dan bata fita waje ne yasa bata sani ba.
Taji daɗin wurin sosai domin ba hayaniya ga sanyi da iska mai daɗi, ga kuma kamshin furanni daban daban, ga tsuntsaye kala daban-daban masu matukar kyau da ban sha'awa.
Hankali kwance tayi assignment ɗin ta tagama, bayan haka takai mintuna talatin tana hutawa a wurin domin bataƙi ace tazo nan ta dinga kwanciya ba. Sai da lokacin Sallar la'asar yayi sannan ta tashi ta koma cikin gidan.
Da litattafan ta a hannu sai wani nishadi takeji.
da sallama ɗauke a baƙinta ta shigo parlourn jin shiru ba'a amsa mata ba yasa ta ɗago kai domin ganin wanda ke zaune.
"Lahhh khulud assignment kikeyi, wallahi kuwa bansaniba dana zo munyi tare, gashi kuma mathematics kikeyi kho I'm good in mathematics I can help you, if you don't mind"
"I mind!!!, leeya I mind. Stay away from me, bana bukatar taimakon ki. Mtswww taja tsaƙi taci gaba da aikin ta.
"Ahhh khulud me yayi zafi dan Allah ki bari na taimaka miki kinji"
"Kehh, wai ke bakyada zuciya ne da bazaki iya fita harakata ba, ki tashi daga nan, bar nan nace bana buƙatar taimako ga talakar yarinya irinki ƴar talakawa". KhUlud ta faɗa a tsawace kamar zata daki ta.
"Khludddd" leeya ta faɗa Muryar ta na cracking kamar zatayi kuka.
"Get out!, get out of my presence. Leave! Bar nan ta faɗa cikin daka murya.
Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka leeya ta miƙa ta nufi sashin ta.
Huci irin na jin haushi khulud ta ajiye tana faɗin "Ni ban ma fahimci topic ɗin nan ba, kwata kwata banmasan menakeyi ba wallahi. Koda yake bara nayi kawai can ta matsewa malamin ko summit ma bazan yiba, ko dai na kira leeya ta zo ta dubamin mtsss who cares bama zankirataba bana buƙatar hannayen ta masu datti su taɓamin book"
Washe gari.
Yau ma Kamar jiya sai ƙarfe 2pm na rana suka dawo, mum ce tsaye a parlour tagama turaren wuta.
Da sallama dauke a bakin leeya ta shigo ɗakin. Khulud na biye bayan ta, saidai ita batayi sallama ba.
"Mum sannu da gida"
leeya ta faɗa tana ƙarasawa gaban mum. khulud kuma tayi kamar batasan da mum a wurin ba.
"Yar makaranta, an dawo"
"Ehh mum na dawo"
leeya ta faɗa tana ƙoƙarin sauke school bag ɗinta.
Khulud kam bata shige ciki ba tana nan laɓe tana jira taga me leeya zatayi.
"Mum, albishirin ki".
"Goro fari".
"Mum, ba dai goroba. Goro kam ɗaci gareshi".
Ɗaga kai mum tayi kamar me tunano wani abu sannan tace"to zuma".
Dariya mai sauti leeya tayi. Khulud kuwa ji tayi kamar zuciyar ta zata fashe.
"Mum, assignment ɗin da aka bamu jiya danayi shine nafi kowa maƙi a class ɗin mu. Kinga har kyauta aka bani"
cewar leeya tana fitowa da kyautar da aka bata......✍🏼
BAYAN WUYA.......
By RUMANA M DIGGI
Ep.14
____________dogon tsaki khulud taja tare da barin wajen, mum da leeya duk sunji tsakin da taja amma ba wanda yace mata uffan.
"Je kiyi wanka kiyi sallah kizo kici abinci kinji"
Mum ta faɗa tana shafa kan Leeya.
"Okay mum Nagode"
Cikin tafiyarta ta nutsuwa tabar wajen ta nufi sashen su.
Tana isa ta fara tuɓe uniform ɗinta sannan ta ɗaura towel ta shige toilet.
Bayan wasu ƴan mituna kaɗan ta fito sannan ta saka Kayan ta tayi sallah.
tana idarwa ne ta tsahi ta shafa mai da sauran kayayyakin kwalliyarta.
Uniform ɗin da ta cire ta ɗauka ta nufi laundry room ɗin gidan kaana ta saka uniform ɗin a washing machine ya wankesu fess Sannan ta fita bayan gidan ta shanya su.
Tana cikin shanyawa ne ta hango wurin nan da ta tafi jiya.
Dariya mai sauti ta saki tare da faɗin
"Hi furanni da tsuntsaye yau ma zanzo na tayaku fira Kunji".
Ta faɗi maganar cikin barkwanci ne kawai duk da tasan ba jinta zasuyi ba.
Cikin gidan ta koma bayan ta ajiye washing basket ɗinda ta saka uniform ɗin ta. Kaana ta koma bedroom ɗin ta ta gyara ta saka turare sannan ta fito.
Daining area ta nufa kamar dai kullum fuskar ta sanye da niqab kalar green mai duhu.
Sai kuma riga da skirt ƙanana da kuma hular kayan.
"Assalamu alaikum" Leeya ta furta lokacin da take isowa a daining ɗin.
"Wa'alaikisalam"
Mum da papu duk suka amsamata saɓanin khulud da ko kallon wurin da take batayiba.
Durkusawa leeya tayi ta gaidasu baki ɗaya. Bayan ta tashi ta janyo daining sit a kusa da khulud ta zauna.
"Sis barka da rana"
"Mtswww" khulud ta yi tsaki tana cigaba da cin abincin ta.
Abincin ta da aka ajiyemata a wurin da take zama tun kafin tazo, aka ajiye mata. Shi ta janyo ta fara ci.
Suna cin abincin hankali kwance har suka kammala.
Wayar mum ce tayi ƙara alamar kira ya shigo, "hello, hajiya fanaya"
"Yes, Dr.eraa ya aiki"
mum ta faɗa tana ajiye spoon ɗinda ke hannun ta.
"Hajiya fanaya na kiraki ne kan maganar khulud k. Waasib yarinyar ku"
"Okay to Dr. Ina saurarar ki".
"A gaskiya hajiya khulud k. Waasib bata maida hankali kwata kwata a class, gwanda ma can baya tana maida hankali ƙadan kaɗan, amma yanzu kam gaba ɗaya bata karatu. Kunga na farko idan tazo bama ta zama aji balle tasan abunda ake, sannan kuma idan aka bada classwork batayi. Idan aka bada homework ko assignment duk batayi gaba ɗaya.
Gashi jiya ma anyi test tayi failed gaba ɗaya, gashi kuma promotional exams za'a yi idan bata mayarda hankali ba gaskiya bazata je gaba ba sai next year, kuna ba amafani ace ana biyan school fees over a million thousand of naira amma ba'a mayarda hankali"
Wacce aka kira da Dr.eraa ce tayi maganar daga cikin waya.
"Okay ba damuwa dan Allah ku ƙara hakuri in sha Allah zanyi magana da ita, Nagode sosai"
Cewar mum tana ajiye wayar.
Miƙewa khulud tayi zata bar wajen mum ta daka mata tsawa
"Khulud, koma ki zauna magana zanyi dake"
Ba wani musu khulud ta zauna domin kuwa tasan tanada babban laifi tunda taga haka daga mum.
"Wanene ya kiraki Hajiya fanaya?" cewar papu cikin alamun tambaya.
"Kiran daga makarantar su khulud ne, sun qara kirane suna complain kan rashin tsayi tayi karatu. Justice me zamu yiwa wannan yarinyar kuma don tayi karatu. Menene bamu yimata ba" mum ta faɗa tana mayarda kallon ta ga khulud.
Cikin tsananin ɓacin rai da takaici mum ta fara magana
"khulud menene kike buƙata a wannan rayuwar, gayamin? Nida mahaifinki mun samarmiki da komai da kike buƙata. Saboda kawai ki tsaya ki kwantar da hankalinki kiyi karatu, so me kike buƙata kuma. Mun sakaki a maɗaukakiyar makaranta Saboda ki sami ingantaccen ilimi. A kowane wata mahaifinki na biyan kuɗin makarantar ki over a million thousand of naira. Just to learn khulud. What exactly do you want in this life, an ɗaukar miki extra lesson teacher a kowane weekend domin ya koyar dake during the holidays you on vacation. So what are you liking, meyasa bazaki tsaya ki koyi abunda ake koyar da ke ba meyasa khulud?, me yasa koda yaushe kike zuwa poor grades, always zero meyasa"
Mum ta ƙare maganar idanun ta duk sunyi jajir saboda tsanani ɓacin rai.
Khulud kuwa jikinta duk yayi sanyi likiss a hankali ta furta"mum I'm sorry" tana ƙokarin ta riƙa hannun mum domin bata hakuri.
"Khulud idan kika ƙara dawowa da wannan grade a gidan na rantse miki da Allah sai an fitarda ke a Private School an sakaki public school".
Cikin tsananin tashin hankalin jin abunda mum ta faɗa khulud ta matsa gabanta "mum don Allah kiyi hakuri wallahi nidai dana zauna public school gwanda na zauna gidan nan. Mum don Allah kiyi hakuri".
"Sakar min hannu bana wasa dake, kuma bazan soma ba a yanzu. Kinji dai na rantse miki kho wallahi idan kika ƙara zakiga cikawa da iyawa".
"Sorry my kid zo nan Kinji" papu ya faɗa yana miƙa mata hannunsa.
Da gudu ta faɗo jikin papu tana ta sharɓar kuka" pa, bana son public school don Allah pa kace mata kar a cireni a BUSY BRAIN INTERNATIONAL please pa"
"Kagani kho justice, wallahi kai kake ɓata wannan yarinyar"
"It's okay HAJIYATA zamuyi maganar daga baya ki barta hankalin ta ya kwanta yanzu Kinji"
"My kid, zanyi magana da mamanki later, amma kiyi min alƙawari ɗaya".
"Nayi maka pa, nidai banason public school wallahi"
"Kin min alƙawari zaki dinga zama class"
"Ehh nayi maka alƙawarin zan dinga zama class, amma banason public school"
"Shikenan baza'a saka kiba tunda baƙyaso"
"Thanks you pa I really love you so much my wonderful pa".
kwanciya tashi, ba wuya a wurin Ubangiji har gashi leeya na ajin ƙarshe a secondary ita kuma khulud tana ss2 kenan zata shiga ss3.
Mum da papu sunci gaba da rikon leeya tsakanin su da Allah kuma da zuciya ɗaya ba abunda suka rageta dashi.
A bangaren khulud kam game da kiyayyarda take nunawa leeya ba abunda ya ragu sai dai ma abunda ya ƙaru.
Yaune ranar da ko wanne mahaifi da yakeda dansa ko diyarsa a BUSY BRAIN INTERNATIONAL ACADEMY SULEJA zaije domin gudanarda gagarumin taron yaye ɗaliban wannan shekarar.
Papu da mum kam suna gaba wajen zuwa domin kuwa idan har ba sani kayi ba bazaka taɓa cewa ba subane iyayen leeya na asali ba.
Sosai akayi decorations na alfarma a makarantar abun gwanin ban sha'awa. Sahu-sahu dalibai suka fara fitowa, an raba ɗaliban kashi uku kowa da tawagar su.
Yayinda ko wace tawaga ta tafi wurin da aka tanadar mata.
kowace tawaga a cikin waɗan da suka fito sunada mai jagoranci ta.
LEEYANA HAMRAZ AWAIS itace mai jagoranci tawaga ɗaya a cikin sauran sai kuma. Wata students ɗaya a set ɗin nasu mai suna HALAN NURAIN itama tana jagorar wata tawaga aciki yayinda tawagar ta Uku ta kasance namijine mai suna TAWQIR YUNUS.
Bayan an gabatar da addu'ar ga musulmai. Sannan aka dawo akayiwa Christian addu'ar su suma.
Sai kuma aka fara kiran malumma suzo domin yin jawabi, bayan malamai sai kuma aka kira dalibai.
Mutum huɗu aka kira ta biyar ɗin ita ta kasance kasance LEEYANA HAMRAZ AWAIS.
Bayan dogon bayani da tayi akan kanta, wanda dayawa daga cikin mutanen wurin sun tausayamata matuƙa.
Sai kuma kalaman ta na ƙarshe da suka ƙara sanyaya jikin mutanen wurin. cikin wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tace
"Daga ƙarshe ina godiya ga waɗan nan bayin Allah JUSTICE KHATTAB WAASIB da kuma matarsa HAJIA FANAYA. Sune suka zamo jigona, su sukaymin gatar da na rasa ta iyaye, su suka fitardani daga cikin rana suka mayardani a inuwa, su suka soni lokacin da ba wani da zai iya zuwa kusa dani, sune suka zamo gatan maraicina, su suka bani ruwan sanyi yayinda ko wace korama ta rayuwata ta ƙafe, su suka cetoni daga faɗawa wani hali, sune suka fara rufemin ƙofofin kaddarata da suka bayyana a filli.
Mum, papu, Allah Ubangiji ya saka muku da alƙairi, Allah ya kyautata muku fiye da yanda kuka kyautatamin Allah ya shayarda ku ruwan alƙausara, Allah ya hanaku jin kunya duniya da lahira, Allah yayi muku kyakkyawan karshe".
Leeya ta faɗa yayinda kukan da take ya soma cin ƙarfin ta. Duk da ta saka niqab bai hanawa mutane ƙiyasta yanda take kukan ba domin wasunsu tausayin ta ya hanasu ɗauke idanu akanta.
Papu da mum kuwa sai video ake yimusu, sai kuma masu yi musu addu'o'in samun nasara da gamawa da duniya lafiya.
Mum kam harda hawaye yayin da papu ya dake saboda shi namijine yanada ƙarfin zuciya.
Bayan wurin ya gama kankantuwa aka kira yaran da zasuyi program. Debate competition, aka farayi bayan shikuma sai akayi quiz competition. Daga nan kuma akayi impromptu speech. shine wanda aka rarrabashi a tawaga uku.
Bayan ɗaliban sun tafi gaban jama'a kowa yayi choosing topic ɗin da yakeso TAWQIR YUNUS ne ya fara, bayan ya kammala sai LEEYANA HAMRAZ AWAIS ta fara nata itama bayan ta kammala ne sai HALAN NURAIN tayi nata.
sosai yaran suka birge domin duk wanda yaje wajen to zuciyar sa fari sol take a wannan lokaci musamman wadanda ƴaƴansu suke ciki.
Bayan an gama wannan kuma sai akazo raba kyaututtuka ga ɗalibai.
Leeyana kam tasamu kyauta dayawa domin kuwa kowa kaji ita yake faɗi.
Kyautar farko da aka bata shine over roll Mark's, kyauta tabiyu kuma most brilliant and intelligent, kyauta ta uku da aka bata kuma tafi kowa nutsuwa da tsafta, sai kuma kyau ta ta gaba shine kyautar ta sami high grades a mathematics quiz ɗinda akayi. Sai kuma kyautar debate competition ɗinda akayi kuma itace tazo second position, sai kuma kyautar impromptu speech da sukayi da tawagar ta. Sannan sai kyauta ta karshe da class master ɗinsu ya bata datazo first class a ajinsa.
Tun su mum na ƙarɓar kyautar har suka rasa inda zasu ajiyeta domin kuwa motar su na can parking space sai anyi tafiya mai ɗan nisa.
Bayan wannan kuma aka kira iyayen yaran da akayi program dasu domin suyi jawabi, papu ne ya fito ya Tsayawa leeya. Sosai ya ƙara mutunci da daraja a idon mutane don gani suke ba wanda zai iya yin abunda yayi, koda an samu ma da wuya a samu kamarsa.
Mutane da yawa sunyi pictures da mum da leeyana da kuma papu, wasu papu kaɗai, wasu mum da leeya wasu kuma papu da leeya, wasu leeya kaɗai.
Khulud kuwa kamar da ɗora hannu aka tayi ta ihu domin ta rasa abunda ke yi mata ɗaɗi kamar ba ƴar gidansu bace akayiwa graduation.
Sosai ɗalibai da iyayen yara suka yi farinci da wannan taron.
Anyi taro lafiya an kare lafiya. Kowa ya ɗauki yaransa aka koma gida.
Daga Nan wani makeken mall papu ya nufa dasu sosai ya kashe musu kuɗi baramma leeya data darje ta zaɓi Kayan sakawa, dana kwalliya, turarruka, da sauran kayayyakin amfani. Domin yanzu ta sauya ba kamar lokacin da tazo gidan ba.
Daga nan kho restaurant suka nufa, bayan isowarsu ne khulud tace suje ita tana nan bazata fita, papu yayi rarrashi har ya gaji amma furrrr taƙi zuwa ko'ina. Dole papu ya tafi amma saida aka yimata take away.
Tuqi papu yake suna fira jefi-jefi a cikin motar papu ya danna wayarsa kaɗan sanna yace "hajiyata wai kinsan ashirin ga wata Turab zai dawo gida NIGERIA? gobe zai dawo daga WASHINGTON zai sauka a MEXICO kwana biyu zaiyi kenan a na uku zai dawo Nigeria in sha Allah"
"Justice rayuwa fa gudu take cikin ikon Allah wai yanzu Turab yayi shekaru biyu a WASHINGTON kenan".
Da murmushi papu yace "ehh wllh kinga har gashi zai dawo a kwana kin nan, mun kammala bikin graduation ɗin leeya gashi zamuyi bikin samun nasarorin da yayi"
"Masha Allah, to Allah dawo dashi lafiya" cewar mum tana ƙoƙarin tada leeya data fara bacci domin ko har sun ƙaraso gidan.
A gajiye suka dawo gidan baki ɗaya dama can a ƙoshe suke shiyasa ba wanda ya nemi yaci abinci, sai khulud ce kawai kecin abincinda aka riƙomata daga restaurant.
A parlour bacci ya kwashe leeya har aka kira sallahr la'asar papu kuma office ya koma yayinda mum ta shiga aikin gida.
Ita kuma khulud sashen su ta koma baccin ta take hankali kwance domin ba damuwa tayi da sallah ba balle tayi, kuma babu abunda tayi balle taji gajiya.
Miqewa leeya tayi daga gajiyayyan baccinda ya share ta ko wanka bata yiba.
Sashensu ta shiga tayi wanka kaana ta d'auro alwala tafito ta gabatarda sallah.
Bayan ta kammala ne ta tsaftace bedroom ɗin ta duk da lafiya ƙalau yake ba abunda ya sameshi.
Da ta gama ta sakko parlour da nufin taya mum aikin gidan wanda hakan ɗabiarta ne tun a gidansu..............✍🏼
BAYAN WUYA.....
By RUMANA M DIGGI.
EP.15
__________kitchen ta tararda Mum. Da sallama ta ƙarasa wajen bayan sun gaisa taje ta fara wani aikin daban.
Sai fira suke abunsu har mum ke tambayar leeya.
"Leeya wace makaranta kika nemo da kikeso kije, kinsan tun a waccan ranar justice yace ki zaɓa makarantar da zakije gaba"
Wuƙar da ke hannunta ta ajiye tare da faɗi
"kinganni nan mum wallahi ni banada sha'awar yin karatu mai zurfi, yanda ake tunani"
Cikin mamaki mum ta kalleta tare da faɗin
"bakida sha'awar karatu mai zurfi kuma, sai me to. Kina nufin aure kikeso kenan, ashe kuwa akwai babban aiki domin papun ku bazai lamunci wannan ba. Yafiso ya aurarda ƴarsa da karatu mai zurfi domin ta sami abun dogaro dakai, kuma ta samarda ingantacciyar tarbiyya a gidan ta, lallai bazaku wanye lafiya ba kenan idan yaji Wannan batu"
"No, mum bawai ina nufin bazanyi karatu ne gaba ɗaya ba, inaso ne nayi tunani domin kuwa Ni ko zan shiga school gaskiya sai dai CATERING SCHOOL amma idan ba ita ba bana gani zanyi karatu yanda akeso domin banada sha'awa"
Murmushi kawai mum tayi kaana ta furta
"to shikenan ba damuwa Allah yayi mana jagora".
"Ameeen ya rabbi mum, mum wai nace zaki barni na kwana wancan wurin"
Leeya ta faɗa tana janye labulen wurin tare da nuna mata balcony ɗin nan amma ba sosai ake iya hangoshiba sai idan ka kula sosai saboda bata bangaren kitchen area ɗin yake ba.
Baki sake mum ke bin wajen ta kallo tace
"ke ƴarnan waya nunamiki wancan wajen?"
"Mum nina gano da kaina"
"Ikon Allah, to ki rufawa kanki asiri a Kwanan nan ki daina zuwa wajen can domin wajen ba bayyanannen waje bane, wanda yasa aka gina masa shi yasa am'boyemasa shi domin ba wanda ya lamuncewa shiga wajen sai shi kad'ai, idan kina bu'katar shiga zaki shiga amma sai dai idan baya 'kasar gaba d'aya, domin idan yana nan duk inda yake a faɗin Nigeria yana iya gani a wayarsa idan wani ya shiga wajen can"
Mum ta faɗa tana ƙara nunawa leeya ƙayataccen balcony garden ɗin.
Cikin tsananin son tabbatar da abunda mum ta faɗa tace
"ta wayarsa kuma mum, kodai yanada aljanu?"
"Ko ɗaya" mum ta faɗa tana girgiza mata kai alamar babu.
"To taya zai iya ganin wani ya shiga a cikin wayarsa kuma Alhali baya nan suleja".
"Eh akwai CC TV cameras a ciki kuma yayi connecting da wayarsa ta hannu ta yanda zai iya ganin komai da cameran ta ɗauka"
"Okay mum na fahimta, amma mum meyasa yayi haka yanada wasu sirrukan ne a cikin wajen da bayaso agani?"
"Bayada sirrukan