Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
amarya face ke, mai zanyi da wannan mummunar yarinyar. Bama wannan ba, kin ganni a shagon siyar da atampopi na mudassar and broda shine nace bari in kiraki, atampar wanne kamfani kike so? Far nayi da idanuna kamar yana ganina kana nace. Da yake duk atampopin da nake saye a hannun Hajiya Zulai nake siyansu, kuma nafi yarda da kayayyakinta, me zai hana ka bari in ka dawo ba sai mu je gida mu sameta ba?" Murmushi yayi mun yace.
"To shikenan bari in sai takalma da mayafai da jakunkuna tunda dai na shigo shagon, da girmana goɗai goɗai ai bana shiga in fito ban sai komai ba, sai munyi waya, kuma ina ƙara baki haƙuri a bisa ɗanyan hukuncin da su Ba Bakura suka yanke mana, kuma ina kan tunanin yanda zan ɓulloma da lamarin, Ahmad ma yana office ɗina yana jirana, ashe ya shigo gari bai ko kirani ba. Sallama mu kayi da juna, wayar nabi da harara, Mabaruka sai dariyar ƙeta take yi mun.
"Kai ƙawata a cikin wayar ma ba'a barshi ba harda uwar harara kuma? Ki dena ba kanki haushi, baki da wata matsala, wallahi in cewa zaki yi Bulama karya je aiki, zama zaiyi ya tusaki a gaba kuita soyayyarku. Ke dai ki daure zuchiyarki karki sake ki nuna mishi kishinki, itama haka kar ki bari tasan kina kishinta. In ma ya shiga wajan nata, bacci kawai zaita shantaka bashi da sauran kuzari, ballantana har yayi miki halin nasu na maza, dan ƙaramin aikin namijine yayi ruf da ciki akan yarinyar washe gari ki ganta da ciki. Kinga saiki tashi a tutar babu, kin aureshi tun bashi da wani abun hannu, kuna tare aka tara komai. Daga ƙarshe kina gani za'a raba gado ƙila ma kasonta yafi kasonki yawa, musamman in maza take haihuwa, tuminin takaba kuwa daidai za'a baku, kinga kuwa ai kwaɓarki tayi ruwa, shi asiri gaskiya ne, amman kissa da kisisina wani sa'in tafi asirin saurin aiki, duk macen da tayi watsi da kissa ai ta makaro wallahi" Wani ƙududun ƙwallon kishi na haɗiye, ya tafi tuƙuƙuƙuƙu har ya faɗa cikina.
Ki dena wannan lissafin, ai nice mace kaɗai da zan gaje dukiyar Bulama ko ƴan uwanshi sai dai suyi hange Mabaruka. Babu macen da Bulama har ya isa ya kwarara mata maniyyinshi a mararta ta samu cikin da zata samar mishi da ɗa. Wallahi babu ita, nifa gani nake yi gangancine wannan rabon kwanan, duk ranar da asiri ya karye, zasu sadu da juna fa kenan? In kuwa haka ta faru ina kike tunanin zan iya saka kaina Mabaruka, anya ba kuskure bane sallama miji ga kishiya dan gadarar an zargeshi da surkulle?"
"Babu ganganci a ciki. Ni dai shekara huɗu ina kan wannan tsarin kuma babu, saɓanin lamba da na taɓa cin karo dashi, ke nafa yadda da bokannan yana da muggan rauhanai baƙaƙe da yake aiki dasu, wallahi ko kashe yarinyar kikace yayi, ko shurawa bazata yi ba, sai dai mu koma gida mu samu gawarta anai mata wanka, ke munci dubu sai ceto fa. Ajjiyar zuchiya na sauke, har muka isa garin Jos Mabaruka tana bani labaran irin gumun da tayi a gidanta, ta kwaci ƴancin kanta. Munsha wuyar hanyar saminaka sosai, sabida har gobe hanyar a ratattake take sosai. Amman ko da muka shiga jos kafin mu isa Ƙauyan maza munyi tafiyar fin awa uku.
Ƙauye Maza wani ƙauyene daga cikin ƙauyukan jos, yawancin mazauna ƙauyen Maza ba musulmai bane, musulman ƙalilanne. Ada duk musulman ƙauyan sun watse, sakamakon yaƙin ƙabilanci da aka lashe shekaru masu dama ana zabgawa, amman yanzu birnin na Jos Alhamdulillah kowa na zaune lafiya babu taraddadi. A bakin wani shirgegen tsutse mai abun tsoro muka tsaya, jikin dutsen ciyayine sosai, harda manyan bishiyoyi, duk da bana gani sosai, sakamakon hazon daya rufe gari, ga kuma hadari yayi baƙi sosai. Kallon Mabaruka nayi nace.
Munzo inda bokan yake kenan ko?" Dariya tayi tace.
"Za dai muzo, kinga wannan dutsen sai mun haureshi mun gangareshi, sannan zamu yanki hanyar gidan bokan, an faɗa miki abun na wasane wai? Zagewa zaki yi dan sai mun yi tafiyar data share awa biyu gaba jeji baya jeji." Naji tsoron dutsen sosai, dan dutsene gari guda, amman haka muka soma hawa dutsennan, muna hawa gansa kuka na zamar damu, ni dai jikina in banda rawa babu abunda yake yi. Ita kanta Mabarukan jikin nata rawa yake yi ita ma kenan da ta saba kawo ziyara, sai Allah kawai nake ambata, amman zuchiyata tayi taurin da babu abunda zai sata laushi, face inga na raba Bulama da dukkan masu raɓarshi, ita kuwa Amaryarshi kashinta ya riga ya gama bushewa, dan har hasaso irin azabtar da'ita da zan yi, dan wallahi Mabaruka bata komai, dan ni ba sauƙi a cikin lamarina. Da ƙyar muka gama hayewa tsaunin nan, dan dutsen yafi kama da tsauni, bayana na dafe.
Wash Allah Mabaruka wallahi na gaji, bayana kamar zai rabe gida biyu, wai Allah, yanzu ya zamu yi mu gangare dutsennan?
"Ki zauna ta zaune miki, garin kallon ruwa kwaɗo yai miki ƙafa, ke duk macen da kika ga ta kafa kanta a gidan mijinta, to sai fa data dage, kuma ko da Asiri sai an haɗa da kissa irin tamu na mata, farkon zuwana wajannan, wallahi dana koma gida saida Adam ya gargasamun jikina, ke dai daure mu gangara cikin likkafa, tafiyace miƙaƙƙiya a gabanmu." Haka mukaita faman gangarawa, tun ina salati a zuchi, har na soma yi da mugun ƙarfi, ban ankaraba, naji tuntuɓe da wani ƙaramin dutse, ai kuwa na gungura.
Wayyyyo Allah na mutu na lalace, Mabaruka zan mutu" Cikin ihu gami da kururuwa nake magana, sai wata ƙatuwar bishiyace taimun burki na saki wawuyar tusa ji kuke buuuut, guiwata da hannayena duk sun kukkuje. Mabaruka sai ƙarfafani take yi, a taƙaice mun sha ɗan banzan wahala kafin mu gangare wannan dutsen. Muka yanki jeji, shima yi muke, yi muke kamar ma bama yi, duk tsoro ya gama kamani, sai karo muke da wasu irin tiƙa_tiƙam tuɓaɓɓun arna marasa riga, masu jan idanu, sai ƙanƙame Mabaruka nake yi, su kuma sai sannu suke yi mana da gurɓatacciyar hausarsu, a haka muka iso wata bukka, inda muka tarar da mata su biyar a kan layi, sai wasu manyan maza su uku, da ganinsu masu muƙamine sosai, dan suturarsu da yanayin murjewar fatarsu ta nuna hakan. Matan kuma guda biyun hajiyoyine da ganin yanda suke, sai kuma su biyun irinmu ne, masu fafutukar neman na rufin asiri.
"Sannunku bayin Allah, waye ƙarshe dan Allah?" Cewar Mabaruka, dan ni tuni na samu gefe na zauna ina faman haki, wata mata tace.
"Nice ƙarshe kinga yanzu na iso, tsoron da nake ji ma, kamar kwana zai iya kamani a cikin jejinnan, to ko yanzu ma ƙarfe biyar na yamma har tayi, yaushe ka gama har ka tafi, duk da daga nan Bauchi nake bani da nisa" Ɗayar hajiyan tace
"Aini ban taɓa zuwa nan na tafi a ranar ba ni nafison kwanan ma, sabida amun aiki da kyau ba cikin sauri ba, daga Abuja nake zuwa. Yana da ɗakunan da yasa aka gyara na sauƙar bakin kwana." Ni dai ina zaune sai ajjiyar zuchiya kawai nake, faman saukewa. Mabaruka ta dube ni tace.
"Ki kwantar da hankalinki a gindin magalin duk matsalolinki kike, ai ada ba juya Bulama kike yi ba, lallaɓashi kike yi, shi yasa ƴan uwanshi suka yi azarɓaɓin cusa masa ƴar uwarshi.
Note
( Mata muji tsoron Allah. Ki sani bin bokaye halakace, bin bokaye babu abinda zai haifar miki face dana sani wanda hausawa suka kirayeta da keya ce. Akwai mallakar ta fisabilillah da mace zata yi ma mijinta, ta hanyar yi mishi biyayya, jawo ƴan uwanshi a jika, yima iyayenshi biyayya da hidima, girmama kanki. Da abubbuwa ire irensu masu yawa, wannan itace mallakar dana sani ta tsakani da Allah. Ki sani bin bokaye shirka. Kuma ki sani in kika mutu kina shirka, a wutar jahannama zaki dauwama ba faɗata bace. Ya ke ƴar uwata an faɗa miki wutar ubangiji wasa ne, ko kuma meye ya shiga kanki da har kika mance da mutuwa, kwanciyar kabari, hisabi? Wallahi wallahi in baki tuba kin dena bin bokaye ba kina ruwa, kuma kin shiga uku, ƙarshenki tun a duniya ba mai kyau bane. Ina kira ga duk macen data ci karo da wannan littafin tayi ƙoƙarin siyen nata kafin in kammala free page dan jin yanda ƙarshen wannan labarin zai kasance, na tabbatar zaki ilimantu, zaki kuma wa'azantu. Ki neme ni ta pc kawai mu sasanta, koma nawa ne da ke. Sannan karfa ku mance labarinnan ya faru a gaske ba ƙirƙirarshi nayi ba.....)
MRS BUKHARI CE
[26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
GAWURTATTU UKU
8
YAHANASU:
Mun samu kyakkyawan tarba sosai a gidan Aminin Ba Bakura Alhaji Munka'ilu, tare da matarshi Hajiya Ramlatu.
"Allah sarki Mama Gana naji daɗin wannan ziyarar taku sosai, jiya ya kirani muka yi magana shi Bakura ɗin, yake sanar dani abun arzikin da aka haɗa, mun jima ba muyi wayar ba ma. Bulama Babba kuwa, wallahi bai zuwa, na tura yara gidan ma, amman dai basu samu tarba mai kyau ba a hannun ita matar tashi, ita kanta iyalina Hajiya Ramlatu tana dai zuwa amman bata samun sakin fuska. Duk yaran Bulama Babban da'ita akayi sunansu duka. Ni kaina ina zuwa wajan Bulama Babba a Bankinsu ina kai mishi ziyara, Allah ya sanya alkairi, Allah yasa hukuncin da aka yanke ya zama shine mafi alkhairi" Cewar Alhaji Munka'ilu kenan, Mama Gana tace.
"Ai wallahi Yaya Munka'ilu in dai Bulama Babba ne bazai zo ba. Yaje gida ma can Damaturu, wallahi matarshi ta shiga ta fita ta hana, sabida Bulama ba haka yake ba, yarone mai ƙawazucin iyaye da ƴan uwanshi, muna fatan wannan haɗin da akayi ya zama shine silar dawo da hankalin shi ga iyayenshi da ƴan uwanshi" Hajiya Ramlatu tace.
"Adda'ar daya dace ayi kenan. Ita kuma yarinya ta kula da ibadarta, kar tayi sanya da kai kukanta ga Allah. In sha Allah zamu dinga zuwa dubata, akwai Zainab Auta zan haɗata da'ita zasu yi sa'a da juna. Sannan Alhaji Bakura ya faɗa mana a sama miki aiki, kuma fannin jarida kika karanta. Ta kwana miki gidan sauƙi, dan ina ɗaya daga cikin shuwagabannin gidan talabijin dake kan faifayin tauraron ɗan Adam, ki ba da takaddunki, in sha Allah kin samu aiki, nan da sati biyu in kin gama amarcinki sai ki kirani a waya, saiki soma zuwa aiki in sha Allah " Godiya muka shiga yi sosai da sosai, dama tafi da gidanka mu kayi, takaddun nawa Mama Gana ta ɗebosu dama, karɓa Hajiya Ramlatu tayi, Alh munka'ilu ya dudduba takaddun ya mayar mun da abuna. Sunyi ciye ciye sosai a gidannan, ni dai ina azumi nera dubu goma Alhaji Munka'ilu ya bani, ya ba su Mama Gana dubu sha biyar, Hajiya Ramlatu kuma ta basu dubu biyar, nima ta bani dubu biyar, sannan ta bani lalle na gargajiya, da baƙin salateb me yawan gaske. Sai da muka sallaci Azahar muka yi musu sallama, muka doshi gida. Nan kuma suka shiga gyare gyaren BQ, jere har da su Wakil, sun dage sai kafa gado suke yi. Ni dai ina zaune a falo nayi jigum, ni zazzaɓi ne mai ƙarfi ma a jikin nawa, ga zuchiyar ba daɗi sam. Tunda wannan ƙaddarar ta riskeni, na tsinci kaina a cikin wannan sabon yanayin, wanda bashi da daɗi sam, haka kurum sai inji zuchiyata tana rayamin in raunata kaina, ko in hallaka kaina ma baki ɗaya, gabana yaita dokawa kuma, bana samun nutsuwa har sai nayi karatun Qur'ani, ko kuma in kunna a wayata in saurara, bacci wannan bana samun yi, abubbuwa a lokaci guda duk suka kwaɓemun. Muna zaune da Hajja Fati muna tattaunawa, su Wakil suka fito daga uwar ɗakin da suka kafa mun gado, suka fice a gidan baki ɗaya. Mai gadi ne yayo sallama bakin ƙofa, Hajja Fati tace.
"Kamar sallama nake jiyowa, bari in duba"
Tashi tayi ta fita, ta bar mun ɗiyarta, a wajena bata jima da fita ba, sai gata da manyan ledoji cike da take away da lemukan sha. Fanda ta shiga ta miƙama, ta barni a zaune ni kaɗai, ina wajan su Wakil suka shigo kici kici da kitchen kabinet wanda ake ajjiyewa a ƙasa kawai, doguwa sosai. Cike da mamaki nake ta kallonsu, mai aikin fanfo dama tun kafin su fita yake ta aikinshi ta bayan windon wajan daining ɗin a wajan daining suka fitarmun da Kitchen mai kyau, an saka mun abun wanke_wanke a wajan an jawo ruwa ta wajan. suka yi jeren kayan kitchen, wajan ya bada tsari mai kyau, aka saka labule mai raga raga wanda bai tare komai ba, an dai sa shine dan ado. Falonma aka gyareshi tsab, sai ƙamshin turaren wuta ɗan asali yake fitarwa. sai magriba suka gama komai, duk muka yi wanka, mu kai Sallah sannan mu ka ci abinci,na kai azumina lafiya. Bamu jira komai ba, muka shige ɗakina, Su Wakil suka shige ɗakin da muka kwana jiya. Ni dai ina kwance hawaye na suntiri a gefen kumatuna, damuwoyin da suka aureni a darennan da yawa suke, yanzu inaji ina gani gobe duk Kowa zai watse ya barni, ni da ko bacci bana iyayi, ya rayuwata zata kasance shine ni kaina ban sani ba, gashi ina gudun yin abunda zai ɓata zumuncin iyayenmu, da kashe kaina zanyi, koma in gudu a nemeni a rasa. Amman in sha Allah duk rintsi duk wuya zan juri zama da Bulama Babba da matarshi, kuma zanyi musu biyayyar da suke nema daga gareni, fatana shine Allah ya dafamun. Bacci daya gagareni saina tashi na ɗauro alwala.
Bulama Babba:
Bayan gama wayata da Zubaina a cikin kantin sai da sutura na mudassar. Ina sayen takalma da jakunna, sai nayi maza na koma office, dan ma'aikacin banki bashi da lokacin ɓatawa, a ofishina na taradda Ahmad a zaune yayi jigum.
Ahmad wannan jigum jigum ɗin da kayi na menene wai? Gashi ni kaina a cikin tsananin damuwa nake, Allah Allah nake yi in zo in same ka dan kaji halin da su Ba Bakura suka jefa ni a ciki. Ni na rasa wanne irin tsana sukaima Zubaina, ni kuma banga abunda Zubaina ta taɓa yi musu ba. Amman wallahi ko Damaturu na kaita, babu mai sake mata fuska, a takure muke cinye hutunmu mu dawo gida.
Ajjiyar zuchiya Ahmad ya sauke ya dubeni yace.
"Tun dana taso daga Lagos nake cikin tunani da ɗimuwa, Bulama mata masifane, kuma lallai zasu iya saka a cikin ukun da baka isa ka fitar da kan ka ba. In kaga rikicin da mu kai ni da Hajara za kai mamaki, Hajara sabida na bata damar kasuwanci shine take ganin a yanzu data kama ƙasa tafi ƙarfina, dan kawai Allah ya jarabceni da rashin aiki. Kuma fa kar ka mance duk a sanadiyyarta da iyayenta na faɗa cikin bala'in da Allah yasa ka fiddani da ƙyar, wai yau ni Hajara take ɗagama murya." Duban Ahmad nayi, ina jinjina abunda Hajara tayi mishi, mata kenan, yarinyar daya tsinceta a titi da farantin tallan mangoro har itace tayi kilin haka take gasa wanda yai mata komai a rayuwa? Take naji jikina ya mutu mus, dan ni kaina ina cikin kwatankwacin halin da Ahmad ya tsinci kanshi, naci bashin banki nera million biyar ba tare da saninsu ba, gashi har yau ko ragewa ban soma yi ba, ga bashin million biyu ma na kuma karɓa a yau ɗinnan, inason inyi ma Zubaina hidima dashi, dan ta samu raugwamen raɗaɗin da na yi imani da Allah zai dameta. Dukkan wata wahalata akan Zubaina da danginta nake yi, dan iyayena da ƴan uwana basu mori komai daga dukiyata ba,iska na fesar a bakina.
Ahmad kayi haƙuri a bisa abunda Hajara tayi maka. Da ba dan kaine ka sanar dani da bakinka canjawar da Hajaran tayi ba, da wallahi bazan yarda ba. Wato sabida taga a yanzu ta fika arziki shine wulaƙanci zai biyo baya, waye ya ɗaurata akan tsanin har ta samu arzikin ba kai ba? Ta bani mamaki amman ka daɗa haƙuri ka kuma bata lokaci, zan kirata in sha Allah, ina to ka baro yaran?
"Suna gida yaran tare da ƙanwata, na ɗauki Zulaihat na tafi da'ita Lagos ai tana karatu a hannuna, kusan ita ke kula da yaran ma, Hajara kasuwanci tasa a gaba, da nayi magana sai tace ai ita ke ciyar da gidan, kuma kuɗin makarantar Yara ita ke biyan rabi in biya rabi, wallahi ni gabaki ɗaya auren Hajara ya gama fice mun a raina" Da sauri na tare shi nace"
Kai haba ka dena cewa haka Ahmad, ko babu komai Hajara tana taimakonka, tunda ta ɗauke ɗawainiyoyinka da yawa, sannan ko babu komai su Aneesa suna tsakaninku, ka daɗa haƙuri kasan mata hukunane su sai da lallashi. Ni fa aure su Ba Bakura su kai mun, ba da sanina ba sabida tsabar mulkin mallaka. Kuma kasan su rasa wacce zasu aura mun sai Yahanasu ƴar lukuta wannan mummunar yarinyar ƙanwar su Dala fa, ai ka ganeta ko wannan mai ƙibar? Ita fa aka aura mun, babba dani Ahmad, dan ma sauƙin dana samu Zubaina ba tai mun rikici ba, tayi ba zata sosai Gaskiya " Tsuru Ahmad yayi yana kallona, sannan yace.
"Bulama bari in faɗa maka wannan gaskiyar dai wacce baka so, wacce take sawa mu rabu tsiya tsiya. Iyaye sun wuci gaban wasa fa, ya kamata ka dawo hayyacinka ka sani matarka bata isa ta kama ƙafar ƴan uwanka ba ma, balle iyayenka. Sannan