MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   24 / 67

69K to 72K   out of 198.3K words

Allah ya kuɓutar da kai daga hannun Zubaina. Ai mu tuni mun daɗe da sanin sihiri na yawo a jinin jikinka. Sabida hidima da kariyar da kake ba Zunaina da danginta yayi yawa. Ba Bakura kuma zasu yafe maka da ikon Allah. Suma suna kewarka kuma suna son ji daga gareka, fishi kawai suke yi da kai. Hakan bazai hana suima adda'a ba. Ba'a cikin fishin Hajja Gana tasa ɗan uwanta ya nema mana wannan aikin ba? Ai su iyaye duk yanda ɗansu ya kai ga lalacewa, wallahi burinsu a kullum rayuwarshi tayi kyau da albarka. Ita kanta Yahanasun wacce iriyar wahalarku ce bata ɗauka ba. Ka kuma duba yanda tai ta hidima da kai da iyalinka, a lokacin da kake buƙatar majingina. Amman ita Zubaina data gama tatikeka daka taɓata ba cewa take yi gini take yi ba? Da kuɗin wa aka sai filin? Da kuɗinka, ga gida ka siya ma uwarta, kai ko bulo yanzu baka dashi. Kayi haƙuri kar ka takurama zuchiyarka gudun gaiyato hawan jini, dame zamu ji, da talauci ko da ciwo? Gara mu ji da ɗaya dan Allah" haka Ahmad yai ta bani baki, bai barni ba har sai da ya ragemun kaso mai tsoka na damuwata."




Yahanasu:
Ina zaune a gaban teburin aikina,na duƙufa sai faman aiki nake yi. Dan zuwa sha biyun rana akwai program da zan gabatar, na gayyaci wata uwar marayu da mijinta ya mutu ya barta da yara tara. Ina aikin ina duba lokaci, Binta abokiyar zamana kuma ƙawata sai tsaki take zabgawa. Duk da dai ta girmemun sosai, dan babbar ƴarta shekararta goma sha ɗaya. Amman jinina da nata ya haɗu sosai da sosai, na kan ranci kuɗi a hannunta, itama takan ranta a hannuna. Har adashe ta kafa mana a ma'aikatar tamu, maza da mata. Hannu biyu na shiga, duk wata ina zuba dubu shida daga cikin albashina, saura mutum biyu ɗauka yazo kaina, nice ɗaukar ƙarshe.
Lafiya Binta kike ta faman tsaki tun zamanki? Kinsan fa kina da labarai zuwa ƙarfe ɗaya, ya kamata ki mayar da hankalinki ki samu ki haddace, kar a samu matsala irin na jiya. Hawayene ya cika tab a gurbin idanuwanta, ta sauke wata nannauyan ajjiyar zuchiya tace.
"Damuwar dake cin ƙasan raina ba zai barni in samu nutsuwa ba. Dole a cikin aikina aita samun kusa kurai iri daban daban Yahanasu. Wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki, sai maƙociyata da matsalarmu tazo ɗaya. Dubi nan" Ta yaye mun hannun doguwar rigarta, naga wajan a ɗaye yayi jaja zur da halamar shatin bulala.
Me zan gani haka Binta? Wannan ai duka ne. Murmushi tai mun tace
"Da zan buɗa miki bayana ashe zaki daskare a nan wajan. Hmm duk wata mace da kika ganta da irin matsalolin da take fuskanta a wajan mijinta. Ke dai kiyi aikin ki kawai" Jikina ya mace mus, a fahimtata kamar mijinta ne ya doketa. Lallai gidan aure cike yake tab da ƙalubale iri daban daban. Ina nan ina tunani naga Binta na dube dube, kafin ta zaro wata allura a cikin jakarta. Ban ankara ba naga ta tsira allurarnan a saitin jijiyar hannunta. Tana gama janye ruwan allurar ta mayar jakarta, tare da kifa kanta a kan benci ta rushe da kuka."
Binta allurar me kikai ma kanki, dama kin karanci fannin kiwon lafiya ne?" Ɗagowa tayi idanuwanta caɓe_ caɓe da ruwan hawaye, tai mun wani murmushi mai kama da kuka.
"Yahanasu, kullum sai nayi ma kaina wannan allurar nake samun nutsuwa, kuma ita ke mantar dani abinda na baro a gida. Ada babu irin nau'in kayan mayen da bana sha. Daga baya ko na sha basa gusar mun da ƙishin ruwana. Maƙociyata ce ta ɗaurani a kan wannan hanyar, itama shi take yima kanta duk kwanan duniya." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Kema kina ta'amali da kayan maye ashe?"
"Sosai ma, ai a wannan zamanin in baki yi ta'amali da kayan maye ba. Zaki yi ta'amali da likitan zuchiya, kona hawan jini kuwa. A gaskiya a garin Kano mata da yawa sun faɗa harkar shaye_shaye fiye da yanda kike tunani. Ba matan auren ba, ba ƴan matan ba. Matan aure da dama suna ta'amali da miyakun ƙwayoyinnan ne, dan su samu wata ƴar nutsuwa, sakamakon rashin dace da namijin arziki. Ƴan matan kuma sunfi sha sabida samarinsu, ko dan burgewa, naga ƙawata nayi nima sai nayi." Murmushi nayi mata, nima saina tuno da halin da nake ciki a gidan Bulama Babba. Yanzu haka ma bansan me zanje in tarar a gidan ba, dan na baro baya da ƙura.
To Bintain akwai wata allurar a jakarki, ki siyarmun mana, nima sai in gwada ai. Dariya na bata, tace.
"Allurarnan zata iya fin ƙarfin ƙwaƙwalwarki, ki ci gaba da afa ƙwayoyi ko maganin tari kawai."
Binta kenan, kaina yana ɗaukar kaya fa sosai, ke dai bani in jarraba" Zaro wata allurar tayi a jakarta ta nuna mun, amman tace in bari inna gama program ɗina, sai ta mun allurar. Ai kuwa hakan akayi, ina gama program ɗina, Binta ta jani hanyar bayi tai mun wannan allurar a hannuna. Wallahi in ɗaga ƙafata a wajan na kasa, sai tsugunnawa nayi na soma rarrafawa, ko ina sai ya zame mun rafi, har kifaye na gani suna iyo. Binta kuma ba dan taso ba, ta wuce ta gabatar da labaranta, ni kuma ta sanar cewar banda lafiya, zata kaini gida. Muna tafe ina ganin garin na jujjuyawa, ita kanta Bintan ganinta nake yi kanta a ƙasa, ƙafafuwanta a sama. A haka ta shiga dani cikin gida, har zuwa ɗakina. A kwance ta barni bacci ya kwasheni.


Hajara:
"Baiwar Allah lafiya kuwa naga kin kawo Yahanasu a rurriƙe bata da lafiya ne?" Hajara ce ke tambayar Bilkisu wacce duk ta ruɗe.
"E bata da lafiya ne, kanta ne yake ciwo mai tsanani da jiri. Bazai wuce wahalar aiki bace. Amman yanzu naga harma ta samu bacci" Hajara tace.
"Ba dole ciwon kai na wahala ya rabketa ba, am mayar da'ita tamkar baiwa. Duk da dai ita Zubaina taga ƙarshenta yau" Duk wannan surutan Hajara uwar gulma ta zaci a zuchiya take magana. Sai da Binta tace
"Ban gane me kike nufi ba fa" Hajara ta riƙe bakinta da hannayenta tace.
"Au ance baki shi ke yanka wuya. Zancan zuchi ne ya fito fili."
"To Allah ya bata lafiya, gobe zan dawo in duba jikin nata." Tana kaiwa nan ta fice a gidan. Maryam da Bawa kuwa, sai koke koke suke yi na yunwa.
"Dalla ku rufama mutane baki, so kuke in kashe kaina ko me? Abincinnan yana wuta, ai sai kuyi haƙuri ko?" Zulai tace da Hajara.
"Anty ni ina ga kamar kukan mamansu suke yi, bana yunwa ba. Kinga cincin ɗin da kika sai musu ma basu gama cinyewa ba, sun dawo dashi harda jus ɗin." Hajara dai bata ce komai ba, taci gaba da aikin abincinta. Shinkafa ce fara da manja, da yaji sai salak da tumaturi da albasa a yayyanke. Ƙarfe shida ta sauke tukunyar abincin. Sai da ta sallami yaran sannan tace.
"Zulai ɗakko kular da Yahanasu take zuba ma Bulama abinci, in zuba mishi. Ita ba lafiya, abincin ma sai dai da safe mu dama kokko" Ɗakko mata kular Bulama tayi, ta zuba mishi a kularshi, bayan ta zuba na Ahmad.
"In yarannan sun gama cin abincin, ki ɗan share gidan. Dama Yahanasu ce ke sharewa, gashi bata da lafiya, sai bacci take ta yi. Ki zuba wanda zai isheki kici." Ruwa taja a rijiya tayo wankanta tsab, data fito ta ɗauro alwala. Ta shiga ɗaki ta sanya kaya ta fito fes da'ita. Dadduma babba ta fito da'ita ta jera abincin Ahmad a kai, da ruwa da komai. Ta hau kan taburma ta soma sallar magriba. Zulai ma a gurguje ta ɗauro alwala ita da yara suka ta da tasu sallar a gefen Hajara.




Bulama:
Assalamu alaikum. Na yi sallama da ƙarfi a zaure, tunda ba matana bane kaɗai a cikin gidan ba. Ahmad ya kutsa ta bayana ya shiga, dan ya sanar ma Hajara ta suturta jikinta. Daga baya yace in shiga. Yara na ganina suka taso da gudu, duk suka rungumeni harda yaran Ahmad. Sai Baba oyoyo suke yi mun. Biskit ɗinsu dana saba siyo tsaraba na miƙa ma Zulai tare da ledar biredi da kayan shayi dana siyo ma Hajara.
"Zulai raba musu biskit ɗinnan ko zasu barni in huta. Wallahi na gaji, kaina kamar zai fita. Wannan ledar kuma ki ajjiyeta da safe kwa haɗa tea ku da yaran. Hajara tace.
"Angode sosai Bulama, sannu da ɗawainiya. Am Yahanasu tana ciki babu lafiya, ba yanda take. Dan ko ɗazu dana leƙata, saina samu tana ta firgita, harda surutai. Na dai tuttufa mata adda'a saita samu baccin ya kuma kwasheta." Ya Allah na furta a raina. A zahiri kuma tambayar Hajara na shiga yi meke damun nata.
"Ban sani ba. Abokiyar aikinta ce ta dawo da'ita gidan a rirriƙe, ta dai ce ciwon kai mai tsanani da jiri ne ke damunta. A sakamakon yawan aiyuka da su kai mata yawa. Kuma fa hakanne, aiki yayi mata yawa, gana gida, gana wajan aiki, Zubaina fa ko tsinke bata taɓawa a gidannan komai Yahanasun ce ke aiwatarwa. To zubaina ɗazu kuna fita taja akwatinta da ɗanta ta fice a gidan, bayan ta ƙare mun tana di ni da Abban Anisa, wallahi sai da ta daka ni kamar wacce ta kama ɓarauniya kafin ta bar gidan." Da sauri nace.
Ta fita da akwatifa kika ce?" Ahmad yayi carab yace.
"Shiga kaga jikin Yahanasu fita batun Hajara. Banda gulma ba abunda yake damunta, daga dawowarmu ta tare mu da wannan maganganu haka. Kallon Hajara yayi yace.
"Ke kam kinji daɗin halinki Hajara, wato ba zaki dena gulma ba ko?" Ban bi ta kansu ba, na faɗa ɗakin Yahanasu. Tana kwance a kan katifa tayi shame shame tamkar wata matacciya. Idanu na ɗauko na zuba mata, tare da ƙarema fuskarta da jikinta kallo. Ban taɓa tunanin akwai wani abu da zai iya ramar da Yahanasu ta zama haka ba. Sai gashi sanadiyyar aurena, da ƙuntata mata da mu kai ta yi ni da Zubaina, ya zugar da Yahanasu tashi guda, gashi har cutar da'ita da muka dinga yi yai sanadiyyar kwantar da'ita. Ni da wanne ma idanu zan ɗaga in kalli Ba Modu dashi? A lokacin da nine kaɗai ɗa a gabansu, na samu gata da kulawa a wajan Ba Modu fiye da kima. Har Ba Bakura ne yake mishi faɗa kan irin yadda yake ji dani ɗin yayi yawa. Shi ya dinga koya mun karatu tun kafin in soma zaman aji, hakan yasa na goge, ko da na shiga makarantar nafi duk ƴan ajinmu ƙoƙari. Shi yake riƙe hannayena ya kaini makaranta, ya ɗakko nera biyar ya bani a saman nera ukun da Ba Bakura ya bani. Banda carbin malam da gudi_gudi da yake sai mun a bakin makaranta. Kaina na dafe wanda yake shirin tarwatsewa. Zubaina ta cutar dani cutarwa mafi girma, gashi ta tsallake tayi yaji bayan cin mutuncina da tayi a bainar nasi. Ta faru ta ƙare wai anyi ma mai zani ɗaya sata. Wayata na zaro a ajjihuna, hannuna yana kakkarwa na rubuta ma Zubaina shika kamar haka.
_Ni Bulama na sake ki matata Zubaina saki biyu_ Babu daɗi babu ragi na tura mata, na kashe wayata ɗib.
MRS BUKHARI CE
[31/07, 8:22 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
18


*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*














"Bulama ya yanayin jikin nata, ko sai mun kaita asibiti ne?" Na jiyo Ahmad daga ƙofar ɗaki yana magana. Fitowa nayi jiki a mace na same shi.
To bata farka ba ma tukunna, ballantana inga yanayin jikin nata. Ahmad kai kaga yadda Yahanasu tayi wata uwar rama kuwa, anya yarinyarnan tana ma cin abinci kuwa?" Ahmad ya nisa yace.
"Yanzu zo muje muyi sallah tukunna. Hajara zata kula da'ita kafin mu dawo. Ka samu kaima kaci abinci ka haɗiyi magani, kaima ba ishasshiyar lafiya ba" Sukuku haka nabi bayan Ahmad muka je muka yo sallah. Amman yayi yayi dani inci abinci ko in sha magani naƙi fur. Haka dole ya rabu dani, nayi musu sallama shi da Hajara na koma ɗakin Yahanasu. Nayi mata tashin duniya akan ta tashi taci abinci tayi sallah, amman sai wasu surutai take yi na zafin zazzaɓi. A daren ranar kusan raba dare nayi ina sallah, tare da roƙon mahaccina ya yafe mun a bisa wulaƙanta mahaifana da nayi ba'a cikin hayyacina ba. Yahanasu, sai baccinta take yi, ni kuwa banko rintsaba sam har garin Allah ya waye, da ƙyar na samu Yahanasu ta farka, Na taimaka mata zuwa bayan gida, ina tsaye a kanta alwala ma wannan ta kasa, ta ɗauki buta ta riƙe da hannayenta ya gagara. Dole haka na riƙeta na mayar da'ita ɗaki, mu kuma muka wuce masallaci. Badan naso ba haka dole na shirya dan fita aiki. Yaran kuma suna wajan Zulai tana shiryasu zasu tafi makaranta. Sallahu na ba Hajara.
Hajara in Yahanasu ta tashi, ki kirani a waya ko Ahmad ki sanar damu, in ma zan dawo gidane muje asibiti sai in dawo. Kuɗi na zaro nera dubu ɗaya na miƙama Hajara, ta miƙo hannu zata amsa, Ahmad ya karɓe kuɗin a hannuna, yana hararar Hajara.
"Haba Bulama kar ka kuma yi mun haka. Aika zarce komai a wajena wallahi. Su Maryam ai ƴaƴanane, Hajara zata kula dasu kafin Yahanasu ta samu lafiya, kila ma zuwa lokacin mahaifiyarsu ta dawo. Jana yayi muka fice.
Ahmad ni fa tun a daren jiya nai ma Zubaina saki biyu. Ko kusa bazan iya ci gaba da rayuwa da'ita ba. Ina mai nadamar saninta ma da nayi a rayuwa. Na barta da Allah, yaro kuma tana yayewa zanje in karɓo abuna dan bazan bari yarona yai zaman agolanci ba. Kuma zanci gaba da adda'a Allah yai mun tsari da Zubaina da ire iren masu irin halayyarta ma. Iya cuta Zubaina ta cutar dani gaskiya, ka duba duk soyayyata da mahaifana da ƴan uwana, sai da Zubaina ta raba ni da kowa, kaine kaɗai ka jure aka tafi a haka Ahmad. Ni bansan da wanne ido zan kalli Yahanasu da Ba Modu ba ma wallahi. Shi kanshi Ba Bakura kasanshi da tauri fa. Tun jiya nake kiran wayarsu ba wanda ya ɗaga." Ahmad ya yi Murmushi yace.
"Na gode Allah da yasa kayi tunanin shikan Zubaina, ni kaina naso in baka shawarar sakin nata. To amman bansan ra'ayinka a kai ba, nasan kana yima Zubaina wani irin so. Kuma tsakanin miji da mata nasan sai Allah. Alhamdulillah da ka saketa, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareku baki ɗaya. A cikin zamantakewar da kuka gudanar a baya duk wanda ya cuci wani shi da Allah."
Hakane Ahmad gaskiya ka faɗa. Ahmad yace .
"Zancan su Ba Bakura kuma, ka bari zamu samu lokacine muje mu roƙi gafararsu, sai ka haɗa da yin ta'aziyyar Ba Baana bai ɗaya, Allah ya ƙara rufa mana asiri."




Yahanasu:
A hankali na soma buɗe idanuna ina jin kaina na juyawa dani, ina dai kwance bana ma gane kaina. Ina dai jiyo maganganu haka a kaina sama sama, can nesa nake jin maganar, kuma ji nake maganar tana amsawa. Na jima sannan na gane a inda nake, har na gane Hajara dake zaune tana karyawa, ta nai mun sannu. Dafe kaina nayi nace.
"Hajara waya kawo ni gida, ya akayi na zo gida?" A jere nayi mata wannan tambayoyin. Ta bani labarin abinda ya faru tun daga lokacin da Binta ta kawo ni, har zuwa yanzu. A zabure na miƙe zaune, sai dai jiri ya mayar dani yib na koma kwance. Hajara tace .
"Subuhanallahi yi a hankali mana, sabida in kula da ke ne yasa banje wajan aiki ba. Bari in taimaka miki, wanka ya dace ki soma yi sai ki rarrama sallolinki." Hawayene ya ziraro a gefen kumatuna. Da taimakon Hajara naje bayan gida. Sallah sai a zaune na yi ta. Abinci Hajara ta kawo mun, ta nemi waje ta zauna.
"Hmm ci abinci in baki labarin gagarumin rikicin daya faru tsakanin Bulama da kofur Zubaina, ke ta yi yaji ma fa, bata kwana a gidan ba." Har wani rage murya can ƙasa_ƙasa Hajara take yi. Mamakin abinda ta faɗa ya kamani, jikina na rawa na yunwa na gama da duk abincin da Hajara ta kawo mun, na shanye ruwan ma tas, dana lumshe idanuna sai naji sabon bacci na kwasata..
Hajara kuma ta soma mun zuba, ta bani labarin tas abinda ya faru bayan zuwana aiki. Naji daɗin labarin da Hajara ta bani. Hamdala nayi a zuchiyata, Allah ya karɓa mun adda'ata, bayan shekara guda Alhamdulillah. A fili

24 / 67