Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
fita na miƙe a zabure. Jakata na zara ko mayafi babu a jikina, haka ko takalmi ban saka ba na fice da sauri. Matan gidan sai tambayata inda zani suke yi.
Ina zuwa, mantuwa Abban Maryam yayi" Na fice da sauri ina waige. Ina fita na samu ɗan sahu na faɗa da sauri hannuna bibbiyu riƙe da kaina.
Malam kai ni sabon gari. Ko nawa ne zan baka"
"Durob kenan Hajiya?" Ya jefo mun tambaya.
Kaga nace ko nawa ne zan biya ka, kayi sauri zan mutu wallahi" Ɗan sahun yaja fiii muka zo muka wuce Bulamana a guje. Tafiyar bata zame mun mai sauƙi ba, domun kaina sake birkicewa yake yi, harma na soma fisge fisge kafin mu iso. Muna isowa sabon gari na sakko da hanzari. Dubu biyu na jefa mishi a cikin ɗan sahun na tsallake a guje, ban tsaya ko ina ba sai gidan magajiya. A tsakar ɗakinta na zube ina nishi.
Wayyo Magajiya mutuwa zanyi. Ki taimaka ki mun allura, ki bani benelin in sha, zan haukace in na sake muntuna" Ihu na saka a cikin ɗakin magajiya. Ba shiri magajiya ta riƙeni dam. Inajin shigar ruwan allurar cikin jikina. Benelin ta ɓalle ta bani. Zuƙa biyu nayi na shanye, na fasa kwalbar, nasha laka mis roba ɗaya. Sai da na kwashe sama da minti talatin na soma jin dama dama. Amman sai na tsinci kaina a halin jiri, ɗakin Magajiya ma tamkar zai rikito mun nake gani. Fita nayi a guje, Magajiya ta rikeni dam.
"Ke karamar karuwa, ƙaramar ƴar shaye_shaye baki bani kuɗina ba, kuɗinki nera dubu biyar" Cikin muryar maye nace.
Ki cire a jakaaataaaa" Da ƙyar na haɗa maganar, harshena wani irin kakkarwa yake yi. Sai da Magajiya ta cire kuɗinta sannan ta sake ni na fice. Bazan iya tuno abubbuwan da suka faru dukka ba. Na dai ganni a cikin layinmu, ina tafe ina layi, yaran anguwa suna ihu suna jefana.
"Ta yi marisa, tasha kabso, tayi marisa tasha ƙwaya" Haka su kai ta bina suna faɗe"
MRS BUKHARI
[09/08, 12:55 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
35
BULAMA BABBA:
Ina isowa ƙofar gidanmu na tarar da Hajara da Ahmad a waje suna dube_dube. Sai naji gabana ya yanke ya faɗi ras. Kafin in kashe ɗan sahun Ahmad da Hajara suka shiga gidan baya.
"Hanzarta mu bi sahun Yahanasu, yanzu Hajara take faɗa mun wai ta fita a firgice ba ko mayafi a jikinta"
Subuhanallah subuhanallahi, Yahanasun ce ta fita ba mayafi, a cikin kuma halin da take ciki?" Ban jira amsarsu ba, domun ba nayi maganar bane domun ina bukatar amsar daga garesu ba. Juya ɗan sahun muka yi, nan mu kai ta karaɗe layin, amman babu Yahanasu ba dalilinta. Nan muka shiga tamabayar matasa masu zaman banza na anguwa, amman babu wanda yace damu ya ga dai _dai da gilmawarta. Zama nayi a cikin ɗan sahun na dafe kaina wanda yake sarawa da zafi_zafi. Ahmad ne ya dafa ni, da sauri na ɗago kai muka haɗa ido.
"Ka kwantar da hankalinka zamu ganta in sha Allah. Ni bansan ma ka fita ba ina cikin ɗaki a kwance zazzaɓi ya rufe ni ne."
Babbar damuwata shine kar aljanun su kaɗata ta shige inda ba zama a ganta ba, ko kuma wani mummunan abun yaje ya sameta, ga ƙaramin yaron ciki a jikinta. Ahmad ya zanyi, me kuma zance ma manya?"
"A'a kar kace haka Bulama, in sha Allah zamu ganta, mu yanka can anguwar ko zamu ganta. Ke Hajara shiga mu je" Ahmad ne ya tuƙa ɗan sahun, ina gaba a gefenshi, Hajara tana gidan baya ita kaɗai. Muna zuwa bayan layinmu muka hango dafifin yara a bakin wata kwata suna ihu suna jefa duwatsu. Har mun karya kan ɗan sahun mu zamu juya, wani matashi yazo wucewa ta gefenmu yana faɗama abokinshi cewar.
"Wata ƴar ƙwaya ce ta faɗa kwata fa, shine yara suke ta jifanta" Inajin haka jikina ya bani anya ba Yahanasuna bace?
Ahmad tsaya bari in leƙa kwatar can in gani dai, ku jirani ina zuwa" Da sauri na fice, na tutture yara na samu damar kutsawa da ƙyar. Dam gabana ya yanke ya faɗi, zuchiyata ta karye, idanuna suka soma zubar ruwa, yayin da jikina ya shiga kakkarwa a sakamakon tozali da Yahanasuna da nayi a cikin wani mummunan yanayi. Kwance take tsamo_tsamo cikin ruwan kwatami, baccinta take yi rai ɗaya, goshinta da gefen bakinta sai jini suke zubarwa, yarannan su suka fasa mata da tsuwatsu. Ahmad ne ya ƙaraso da sauri, yaran ya soma kora tare da hanasu jifan Yahanasu. Ni kuwa idanu kawai na zuba mata ina tunanin garin yaya tayi gamo da Aljanu, yaushe, kuma a ina ko dai abun maye tasha kamar yadda matashin saurayinnan ya kirata da ƴar ƙwaya?. Kai Yahanasuna bata da halaƙa da shaye_shaye, sai dai shafar alhanun gaskiya"
"Daure mu cirota mu kaita asibiti Bulama, kayi haƙuri nasan kai musulmine cikakke mai yarda da dukkan ƙaddarar data sameshi." Ahmad ne ya dawo dani daga zancen zuchin da nake yi, tare da ƙarfafeni, dole ba dan naso ba Ahmad ya kama ƙafafuwan Yahanasu, ni kuma na kamata daga hammatarta. Sharaf _sharaf da ruwan kwata muka sata a cikin ɗan sahun, Hajara tayi mata matashi da cinyarta. Kallo guda za kai mun ka gane ina cikin ɗimuwa. Malam Aminu Kano muka wuce kai tsaye, a guje Ahmad ya shiga cikin asibitin, zuwa kamar minti goma sai gashi da gadon ɗaura marasa lafiya yana turowa. Akai muka ɗaura Yahanasu, Ahmad ya dubi Hajara yace.
"Ki koma gida ki ɗakko mata kayanta kala ɗaya, dole za'a buƙaci sake mata kaya tunda wannan ɗin ya jiƙe" Hajara jiki a mace tace.
"Babu ko ficika a hannuna Abban Anisa" Ahmad ya laluba aljihunshi bashi da sisi, haka nima babu kuɗi a jikina.
"Ki shiga ɗan sahu ki jirani, in aka bata gado in sha Allah sai in fito muje mu ɗakko kayan nata" Cikin ganzari na dinga tuƙa gadon da Yahanasu take ciki har zuwa bakin wani ɗaki da ma'aikaciyar jinya ta nuna mun akan in shigar da'ita. Shigar da'ita nayi ga majinyata nan a kwakkwance gado_gado. Ma'aikaciyar kiwon lafiyar dake tsaye a kan Yahansu wacce take sanye da farar lab kot ta dubeni tace.
"Malam kai wanta ne, ko kuwa mijinta?"
Mijinta ne likita"
"Amman meye ya sameta haka jikinta duk rauni, sannan jikinta duk warin kwatami garin yaya hakan ta faru"
Wallahi likita fita tayi daga gida muka nemeta muka rasa , kuma dama ko bacci bamu samu damar yi ba, shafar aljanu take fama dashi, a cikin kwata muka tsinceta kai tsaye muka nufo asibiti da'ita" Kai likitannan ta girgiza tace.
"To Allah ya bata lafiya, muna buƙatar kayan sawarta, sannan in tana da kati ka ba nurses su duba, in kuma bata da kati sai ku yankar mata kati ko? Ka jira mu a waje, mu kammala gwaje_gwajen daya dace" Jikina a mace mus na fita a ɗakin ina waigen Yahanasu wacce wannan likitan ta soma duba lafiyarta. Ahmad na samu a tsaye a bakin ɗakin, yana ganina ya nufoni.
"Yaya ake ciki Bulama?" Cikin ƙarfin hali nace.
Zan je in yanko mata kati ne sabida bata dashi. Suna buƙatar kayanta domun a sake mata na jikinta, Ahmad ku tafi ku ɗakko mata kayan." Numfasawa Ahmad yayi yace dani.
"To shikenan bari muje ba zamu daɗe ba zamu dawo, ka kula da kanka, ka kuma yi haƙuri sai mun dawo" A tsaye a bakin ƙofar ɗakin Ahmad ya tafi ya barni, da ƙyar naja jikina zuwa bakin teburin yankan kati na yankar mata kati na kaima nurses ɗin da likita tace in basu, sannan na nemi waje na zauna nayi tagumi ina tunanin halin rayuwa, jarabawa daga wannan sai wancan, Allah dai ya bamu ikon cinye dukkannin jarabawar da zai jarrabemu da'ita domun gwajin ƙarfin imani a garemu. Ina zaune ina zancen zuchi har Ahmad da Hajara suka dawo. Sun kwaso kaya harda tabarma da flask ɗin ruwan zafi da kofi.
"Ga kayan Bulama ka shiga ka basu sabida a cire mata masu jiƙan kar sanyi ya shigeta kuma. Karɓar ledar da kayan Yahanasu yake ciki nayi na shiga ɗakin, wanna likitan tana zaune a gefen gadon, wani likita namiji yana gaban Yahanasu yana dubata. Wannan likitar na miƙa ma ledar kayan Yahanasun.
"An yanka mata katin ne?" Ta tambayeni.
E an yanka mata, na ba nursses ɗin da kika ce in ba katin"
"To shikenan ka jira mu daga waje, zamu nemeka da zaran mun kammala dukkannin bincikenmu" A sanyaye na fice ina duban fuskar Yahanasu, sai naga tayi wata muguwar rama ta sake yin duhu sosai. A kusa da Ahmad na zauna jigum ina tunani.
"Bulama ya kamata ka kira su Ba Bakura ka sanar dasu rashin lafiyar Yahanasu, domun kaga ciwon dake damunta babbane ba ciwo bane da za'a ce zamu ɓoye ba. Ni a ganina kayi gaggawar sanar. Musu ko babu komai za'a turo wanda zai zauna da'ita Yahanasun domun ba zasu bari kai kayi jinyarta ba, Hajara kuma zata dinga komawa gida da daddare sabida yara." Wayata na zaro a aljihuna na danna number Ba Bakura. Kuka uku wayar tayi ya ɗaga.
"Bulama lafiyar Yahanasu kuwa inata kiran layinta bata ɗauka, kwana biyu bata kira kowa a waya ba?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Ba Bakura bata da lafiya ne, yanzu haka ma muna asibitin Aminu Kano a kwance bata ma san inda kan nata yake ba" Ba Bakura nan ya shiga sallallami daga bisani yace.
"Subuhanallah meke damunta Bulama?"
To Ba Bakura ciwonta ina tunanin makarai ne suka shafeta, dan yafi kama da hakan, da safennan a waje muka tsintoto wallahi babu ko mayafi balle takalmi, a kwata muka zarota"
"Innalillahi wa'inna ilaihil rajiun, Yahanasun ce makarai suka rabketa? To to yanzu bari in sanar ma Modu sai mu ga wa ya dace a taso yanzu_yanxu su tawo, in dai makarai ne, ai ba asibiti ya kamata a kaita ba, Damaturu ya kamata ku wuto da'ita ayi mata tsakani dasu kuma a bata jiƙe_jiƙen magungunan sheɗanu, amman da mamaki ace iska ya ka da Kanuri fa. Bari zan sa Modu ya kirawoka yanzu.
Ba Bakura
DAMATURU:
wayar ya sauke a kunnenshi yana salati Hajja Gana ta dubeshi tace.
"Malam iska naji ana batun ya bige Yahanasu iskokai a cikin zuriyarmu anya kuwa?" Ba Bakura yace.
"Ni kaina tunanin da nake yi kenan. Amman bari in kira Modu a duba mutum biyu zuwa uku daya dace su je ayi komai a gaban idanunsu, inta kama su tawo da'ita Damaturun ne sai su tawo da'ita, tunda makarai ke damunta sai muji me suke so." Hajja Gana tace.
"Ƙila ma sabida zalunci su suka hanata haihuwa suke ta faman ɓarar mata da juna da zaran ta same shi. Baice komai ba yasa kai ya fita har zuwa ɓarayin Ba Modu. A dokin ƙofa suka ci karo da Ba Modu shi da Ya Innana da halama fita zasu yi zuwa wata ƴar anguwa.
"Bakura kaine da kanka baka sa anyi kirana ba?" Ba Bakura yace.
"Babu komai dole ce tasa na taso ai Modu, wannan yaro BULAMA BABBA ya kira ka a waya kuwa?" Cikin fargaba Modu yace.
"A'a ni rabona dasu tun shekaran jiya, har kaima kace kwana biyu su basu kira ba, muma bamu kira ba. Bakura lafiya dai ko?"
"To lafiya ba lafiya ba zamu ce" Ya Innana da jin haka ta dafe ƙirjinta, tayi zuru tana sauraren me Ba Bakura zai ce.
"Yahanasu ba lafiya, suna asibiti yanzu haka ma. Bulama yana neman ƴar uwa wacce zata zauna da Yahanasu kafin jikin ya warware, ni kaina inason zuwa in ganta ɗin ba dan jikina ba kuma gobe zan koma asibiti, amman suwa za'a tura musu kana ganin, mace biyu da namiji da zai tuƙasu?" Ba Modu jikinshi duk yayi mugun sanyi, yasan in ba gagarumin ciwo ba, mai zai sa har sai an ɗebi majinyata daga nan Damaturu har zuwa Kano? Ya Innana tuni ta shiga tashin hankali, sai Allah take ambato a fili tana sauke haki.
"To Bakura Bagulaji da da Aissa ta wajenka sun isa, sai Gunsum ya tuƙasu ya kaisu ko shi ko Bukar" Ba Bakura yace.
"To shikenan ka kira mijin Aissa ka sanar dashi, in yaso in sun fita sai su ɗauketa in ya amince, Bagulaji ta shirya, Gunsum sai ya kaisu, ka basu dubu ɗari su riƙe a hannunsu, Bagulaji zaka ba, Gunsum kuma duk wani abu daya taso zai biya a aljihunshi tunda Bulama bashi da ƙarfi. Allah ya bata Lafiya Innana a taya mu da Adda'a, kya sanar ma sauran matan gidan.
Cikin ƙanƙanin lokaci labarin rashin lafiyar Yahanasu ya karaɗe babban gidan. Bagulaji kuma tuni ta fito, Gunsum take jira ya fito, fitowa yayi cikin sauri. Gareji ya shiga ya fito da mota suka shiga. Ba Modu ya matso jikin tagar direba yace da Gunsum.
"Duk halin da take ciki kayi ƙoƙarin sanar damu da wuri Gunsum, sannan kul aka kira Bakura a waya aka sanar dashi wani abun, kaga a haka ma jikinshi na son tashi. Bagulaji ku kula sosai, Allah ya tsare hanya ko?" Sallama su ka yi, anata musu adda'ar isa lafiya tare da adda'ar Allah ya ba Yahanasu lafiya. Kowa yana son ace dashi akaje. Wakil ya kalli Ya Innana wacce take sharar hawaye yace.
"Ya Innana ki dena kuka in sha Allah zata warke. Kuma in aka kwana biyu ni da kaina zan ɗaukeki muje ki dubota mu kwana ɗaya mu juyo." Sai da yace haka ta ɗan ji dama_dama."
MRS BUKHARI CE[11/08, 7:03 p.m.] +234 708 194 6843: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
36
..
Ghana:
Kofur Zubaina:
Da kyar na lallaɓa jikina na faɗa bayan gida nayo wanka, na gabatar da sallar asuba. Jigum nayi a kan sallayar inata tunane_ tunane barkatai. A wajan Alh Liti ya shigo ya same ni. Yana saye cikin doguwar farar jallabiya, tumbinshi ya fito titsitsi a gaba kamar mai cikin wata tara, sai wani munafukin murmushi yake yi mun.
Ina kwana Alh?" Na faɗa a taƙaice. Cike da fara'a ya dube ni yace.
"Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Kin tashi lafiya ko?" Kaina na sauke ƙasa ina jin wani iri a jikina.
"Motata tana jiranki ki wanke mun ita. Jeep ɗin zaki wanke mun zan fita taron ƴan kasuwa a tamil." Da mamaki na dubi Alh Liti da yayi kicin_ kicin da fuska kamar bashi yake dariya yanzu ba. Abun mamaki sai na tsinci kaina da kasa yin musu dashi, ba shiri na jini a tsaye cikin zabarin son cika umarninshi, jikina har rawa yake yi bana son in ɓata ranshi.
Soson wanke motar fa Alh yana wajan motar ne? Na tsinci bakina yana furta hakan. Cikin ɓata rai Alh yace.
"Yana daga jikin fulawowin da suke kusa da mota, zaki ga bokiti da brosh na gurje taya da car wash ɗin duk a wajan. Tsumman goge motar kuma yana cikin motar a buɗe take motar. Ki hanzarta ki gama maza"
To in sha Allah yanzu zan gama. Ina faɗar haka na juya na soma gangarawa gudu_gudu. Ina jiyo yanda Alh yake sheƙa dariya yana faɗin.
"Shegiya duniya mai ido a tsakar ka, wacce tafi bagaruwa jima. Tsakar gidan na isa ina jin wani ƙunci a zuchiyata mara musaltuwa zuchiyata sai tafarfasa take yi. Ina hawaye haka na soma wankin motar Alh, nice wai yau a durƙushe ina durje ma Alh tayar motarshi, kuma a cikin zuchiyata ina fatan ya yaba mun. Anya kuwa lafiyata ƙalau kuwa, to meke faruwa dani haka? Kuka na sake rugujewa dashi mai ƙarfi nafi minti biyar ina rera kuka. A durƙushe a bakin motar Nabila ta zo ta wuce ni da kwanukan abinci, sai kallona take yi cikin tausayi, ni kaina da idanu na bita. Gata a ido yarinyace mai ƙuruciya, amman tana saye cikin jemammun kaya, fatarta duk ta yamushe, harda kaushi a ƙafarta fara ce sol, abinda na nura Alh Liti yana mugun son farare da dukkan halamu. Harta fito daga ɗakin Alh ina durƙushe na shiga cikin zurfin tunani.
"Zubaina wankin mota kike yi ne?" Ta yi magana tana fara'a. Ɗaure fuskata tamau nayi nace mata.
E ina kwana?" Ban bi ta kan amsarta ba na zabura naci gaba da aikina. Na gaji iyakar gajiya mara misaltuwa, ina kan goge motar na jiyo ƙamshin turaren Alh. Shine ya fito yana saye cikin wata farar shadda mai kashe idanu. Yayi kyau sosai cikinnan nashi shirim a gaba sai tafiyar ƙasaita yake yi. Murmushi ne ɗauke a fuskarshi wayarshi na kare a kunnenshi, ya zagayo ya zauna a mazaunin direba.
"Ai kinfi haka gimbiyar mata, raina fansa ne gareki. Ina kammala mitin ɗin dana faɗa miki, zan dawo gida in kintsa sai jirgin Lagos, daga Lagos zan hau jirgin Sokoto da yardar Allah. Ki yi mun tsaleliyar kwalliyarnan taki mai jan hankalina." Shiru yayi yana jan numfashi. Hawayen dake kwarara a idanuwana na share ina kare ma Alh Liti kallo. Ya samo wata budurwar kenan yana yaudareta a waya sai ya kawota cikin gidan tasha azaba. Akwai yiwuwar mace ɗaya zata bar cikin gidannan kenan, dan mu huɗune a halin yanzu matan Alh. Wata zuchiyar tace mun.
"Ke ma ba sai da aka saki Rumaisa'u kafin aka auroki ba, sai da akai mata korar kare kika samu ɗakinta" Kai Alh Liti mugun mutum ne sosai. Dariya yayi shi da budurwarshi ta