Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
wannan sana'a naga sana'ar tana buƙatar lokaci "
Zan ɗebi ma'aikata Ba Modu, sabida babban shago nake son buɗewa. Amman zan bari in shekara ta zago na karɓi kuɗaɗen hayata, sai in haɗe da kuɗin wajenka in yi duk abunda ya dace." Baki Ba Modu ya riƙe.
"Uwata shagon kuɗi zai lashe haka" Da zolaya a muryarshi sosai. Murmushi nayi mishi kawai.
"To ga shawara Dala zai taimaka miki da Mama Gana ku tsara komai, a duba nawa shagon yake buƙata na kuɗi. Sai in ara miki ai uwata ki soma yi, shekara ɗaya ai yayi yawa." Nayi murna sosai, shi kanshi Ba Modu yaji daɗin yanda yaga na kasa rufe bakina ma tsabar murna. Ya Innana na je na labartama da su Fanna. Kowa ya taya ni murna sosai. Fanda ce ta taya ni na kwashe ƴan ragowar suturuna da basu da wani yawa. Na ba Fanda key ɗin motata ta kai mun kayan mota. Muka bi ayarin tawagar Amarya. Har zuwa Yobe. Har dani aka je gidan Bulama Babba. Gida ya zuga kyau Tubarakalla. A ɓarayin Hajara na zauna, ƴan uwanta sun cika falon. Sai uwar ɗaki ta kaini jikinta sai rawa yake yi. Zance kuwa ta soko wannan a cikin wancan haka ta dinga sokiburutsun zancenta.
Hajara ya'isa kaina ciwo yake yi" Ala dole ta barni, anan nayi kwanciyata har zuwa magriba Mama Gana da Fanda suka shigo ɓarayin Hajara kirana. Fitowa nayi zazzaɓi ya gama rufeni.
"Yaha sai mu tafi gida ai tunda biki an gama. Bance musu komai ba na nada lafayar ankonmu na fita, suka biyoni a baya. A dai _dai in da na ajjiye motata muka haɗu da Bulama Babba da Ahmad, dasu Dala ne Wakil ne, Ba'a Kaka ne. Duk ƴan maza_mazan duka dai. Idanu Bulama Babba ya ƙura mun, ni kuwa nayi saurin shiga mota na zauna a mazaunin direba na runtse idanuna ina hawaye. Su Mama Gana kuma sai hirarsu suke yi.
"Yahanasuna kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayenki. Wannan damuwar da nake gani tattare dake yana azabtar dani. Ban taɓa tunanin zaamu rabu ba Yaha" Idanuna na buɗe tar a kan fuskar Bulama, idanuwanshi sun kuma yin ja sun ɗan ciccika da hawaye. Na rasa me zan ce mishi, shi kuma ya cike ni da kallon soyayyar daya saba yi mun. Tsigar jikina da tsigar kaina sai zullo suke yi mun. Kishi ya sake turniƙeni ina hango Bulama Babba yayi ruf da ciki akan Yalewa. Idanu na kuma runtsewa nace.
Kaje dan Allah bana son ina ganin ka. Ka dena fama mun mikin da dashi zan koma ga Allah Bulama Babba. Allah ya baku zaman lafiya a tsakaninka da Yalewa." Saurin goge idanuna nayi, da naji motsin su Mama Gana. A daren ranar bacci wannan ya gagari idanuna. Amman ya zanyi bani da tudun dafawa. Dole na sake naci gaba da gudanar da rayuwata zuchiyata maƙale da son Bulama Babba. Bayan sati guda da Auren Bulama Babba na soma aiki a gidan talabijin dake kan tsuraron ɗan Adam. Nike gabatar da labaran safe, da wani program sabo da ni na soma gudanar dashi. Domun tattaunawa da manyan ƴan kasuwa. Dala kuma bashi Damaturu bashi Yobe muna ta tsare tsaren maganar shago. Mama Gana kuma ta tafi maidugurin domun saron mun buhunhunan itatuwan turaren wuta iri daban_daban. Da kayayyakin gyaran jiki da duk abinda ya dace. Mun bada aikin stiker, da sainbot ɗin shagon nawa. An yi fenti an yi duk abinda ya dace ayi ma shago. An fitar da ɗakin gyaran jiki, ɗakin gyaran gashi da gasa shi, da ɗakin ƙunshi, harma da office ɗina. Amman ba'a zuba kayan aikin ba tukunna. Mama Gana na dawowa muka shiga aikin haɗa turarukan wuta, dana jiki, da na gashi. Da su humrarori nau'i daban_daban. Haka dai mu kai ta shirye_shirye tsawon wata biyu. A iya tsawon watannin nan ban sake sa Bulama Babba a idanuna ba. Kuma yana zuwa gidan. Amman duk sanda zai zo ina wajan aiki. Ko kuma yazo nayi bacci da daddare. Haka rayuwa tai ta garawa, da son Bulama Babba nake kwana kuma da son nashi nake tashi, har ƙarshen rayuwata bana jin zan iya dena son Bulama Babba"
MRS BUKHARI CE[21/08, 9:35 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 58
GHANA:
Bayan wasu watanni.
Ina durƙushe a bakin murhu ina hura wuta, ga zungureren cikina haihuwa ko yau ko gobe. Amaren Alh Liti suma suna tsakar gidan tare da Hajiya Kubra. Yarane ƙanana ya auro, suma yarannan sun yi bore a tsakar gidannan kamar ba zasu dena ba. Daga ƙarshe ne suka dangana tare da zuba ma sarautar Allah ido. Duk wanda ya ganni bazai gane ni ba, gashi Mabaruka Mama ta kira ni jiya take sanar dani bata da lafiya tana cikin ciwo mai tsanani mijinta ya dawo da'ita gida da takaddar saki. Naci kuka sosai, dan na jima ma banji ɗuriyarta ba, to nima ta kaina nake da ta ƴan uwana. Ga Nafeesa ta haihu itama sai da su ka yi wata uku a asibiti ɗan ba lafiya, kuma mijinta yaƙi biyan ko sisinshi. Sai Mama da Musa ne su kai ta jigila, sai Kawu Tanko daya ke sa musu hannu. Daga baya yaron ya koma. Abubbuwa dai da dama sun faffaru. Ɗazu nan mu ka yi waya da Mama take sanar dani zasu je dubo yaran Asiya a Kano daga nan kuma zasu biya ta Damaturu su dubo su Bawa. Na ji daɗi sosai, da a kwance nake ma jikin ba daɗi amman bayan mun gama wayar ne naji dama_dama shine har na samu damar fitowa iza wuta. Ƴan biyu suna tsakar gida sai ta_ta_ta suke ta faman yi. Dan watan su biyu a duniya na shiga laulayin sabon ciki.
"Ahuwanku dai masu gidan" Muka jiyo muryar wani bawan Allah a tsakar gidan, yana saye da ƙananun kaya da ƙatuwar jaka a bayanshi. Hajiya Kubra ce ta tashi tsaye tana nuna shi tace.
"Wa nake gani kamar Jaba dama kana duniya baka mutu ba? Shekarun baya aka aiko mana da takaddar mutuwarka a cikin kogin lokoja" Dariya ya sheƙa mata kawai ya ƙaraso kusa da in da muke. Kamarshi ɗaya da Alh Liti tamkar kara aka tsaga, kuma shima ya manyanta sosai. Hajiya Kubra ta nuna mishi tabarma ya zauna.
"Jaba ashe baka mutu ba, to mai ya dawo da kai cikin gidannan bayan kasan halin Alh sarai. Yana nan fa a yadda ka tafi ka barshi. Kaga waɗannan yaran du matanshi ne. Waɗannan yaran kuwa du ƙannenka ne, sama da guda talatin ma suna gidan mazajensu. Jiya aka gama bikin Rashida da ƙannenta su biyar. Ni da kaji shawarata da baka dawo ba, domun Alh zai iya makaka a kotu Jaba" Ni dai da mamaki na dubi Hajiya Kubra nace.
Hajiya shima wannan yaron Alh ne wai? Murmushi tayi tace.
"Shine ɗanshi na farko a duniya. Wata tataɓurza ce a tsakaninsu mai girma, dan abun yafi shekaru ashirin da faruwa. To Jaba dai ya tsallake ya gudu. Sai takadda aka turo mana cewar ruwan lokoja ya cinye shi, sai kuma gashi." Baki na taɓe kawai ina kallon ikon Allah, jaba kam kamarshi ɗaya da mahaifinshi ba maraba. Gaggaisawa mu ka yi dukka.
"Ai Hajiya Kubra ni kwana ɗaya nazo yi gidannan ba zama zanyi ba. Wani aikine ya kawo ni, dana gama aikina cikin dare ba lallai mu yi sallama ba ma." Ƙasa_ƙasa yayi da murya yace.
"In tambayeki mana har yanzu Liti yana nan a Litin dana sani mai ajjiye maƙudan kuɗaɗe a ɗaki?" Dariya tayi mishi tace.
"Babu inda kai kam ka baro uban naka wajan son abun duniya. To mai za'a fasa. Ghana most go_ghana most go yake shiga da kuɗi turakarshi ai. Sai dai na cizo ba."
"To ni zan je masauki Hajiya Kubra dama zuwa nayi in gaisheki. Ina su Halifa kuwa duk sun girma"
"Halifa yana kasuwa yana sai da maganin basir, su Bala kuma cima zaune kenan." Murmushi yayi yana zare ido yace.
"Zan biya wajan Halifa ya zagaya dani in ga ƴan uwana, dan gobe duku_duku zan wuce." Ya zaro dubu biyar ya ajjiye a gaban Hajiya Kubra ya juya, yana tattale ƙafa kamar agwagwa." Ni dai naci gaba da aikina ina jan ƙafa. A haka na gama abincin rana, na kuma rabama kowa da kowa. Na zubo mana namu a ƙaton faranti. Duk muka sa sannu muna ci ana taɓa hira, zuchhiyar kowa babu daɗi sam. Ni yanzu bana ƙoshi sam duk abinda naci bana ƙoshi sai dai in haƙura. Ƴan biyu na kalla suna ta cin nasu abincin, rabi a ƙasa. Kamarsu ɗaya sak har bana iya banbancesu da kamanni sai dai ta gashi. Gashin Hassana yafi na Usaina baƙi, shine kawai banbancinsu. Rayuwa kenan, da tsohon cikinnan nayi tuwon dare na sake rabawa. Ina fitowa wanka ana kiraye_kirayen Sallah. Sai da nayi sallah mu ka zauna zaman cin abinci da hirar tsakar gida. Takwas saura na kinkimi tran Alh na wuce ɓarayinshi. Ƴan biyu suna hannun Mariya Amarya a ɗakinta ma suke kwana Allah ya mata son yara, duk da dai itama ta kusan juyewa, duk ciki ne dasu riƙi_riƙi. Ina shiga ɓarayin Alh, motarshi ta iso bakin get. Kafin yayi hon na wangale mishi get ɗin ya shiga. Ya futo a cikin mota, ya buɗe buth ya ciro wata ƙatuwar jaka ya shige ciki abunshi, baiko kalleni ba. Kai kawai na girgiza ko kuka yanxu na dena zuchiyata ta riga data dake. Tiran abincin na ɗauka na bi bayanshi. Da dabara nake hawa saman cikina ya tsufa sosai. Na shiga na same shi yana waya.
"E Alh ga kuɗaɗennan yanzu na shigo dashi. Nera million Arba'in ne. Cikoton kuma sai yaushe, kasan ni bana wasa da kuɗi. Shanu ko guda dubu kake so zaka samu fa, lafiyayyu ƙosassu ma kuwa" Ni dai ajjiye tiran nayi na zauna da ƙyar a bakin gado ina cije leɓena, anya ba naƙuda na ke yi a tsattsaye ba ma tukunna?" Ya dai gama wayarshi, bayan nayi mishi sannu da zuwa na gabatar mishi da abincinshi. Sai loma yake yi.
"Daɗina dake hannunki ya iya miya sosai, sai kiji kan kifin yayi wani mugun taushi gwanin daɗi." Ni dai bance komai ba, dan ba iya mishi akeyi ba. Yanzu zaka yi magana in baka ci sa'a ba ya ƙare da zagin maka iyaye.
Alh dan Allah inason daga yau in barma su Hajiya Kubra kwana, cikina ya tsufa gashi ƙafafuna du sun kumbura, ko awo ban taɓa zuwa ba. In na haihu na yi arba'in na ci gaba. Kayi haƙuri "
"E babu shakka Kofur kinzo da iskanci. To in ke ɗin nake sha'awa shikenan sabida a kan ki aka soma ciki sai bazan huta dake ba? Wai me yasa baki da hankali ne wai?"
Kayi haƙuri Alh......"
"Ya isa dallah bana son magiya" Shiru nayi ina zaune har yayo wanka ya fito.
"Ki cire kaya ina buƙatarki" Ba damar musu haka dole nayi yanda yake so. Nasha azaba a wannan daren bana wasa ba. Ina zaune nayi tagumi ina tunano rayuwa. Alh Liti kuwa sai munshari yake yi babu ƙaƙƙautawa, ƙarfe ɗayan dare ƙarfe biyu idanuna biyu. Tashi nayi na faɗa ban ɗaki dan yin wankan sallah, inason in yi sallar dare. Ina fitowa ɗaure da zani a ƙirjina naci karo da wani mutum a tsaye haka. Da baƙaƙen kaya a jikinshi, fuskarshi a rufe. Take jikina ya soma rawa na soma ja da baya. Alh Liti bai san abunda ake ciki ba sai bacci shi yake shatatawa.
"Kar ki sake kiyi ihu ba wajanki nazo ba. Nazo ne in raba kowa da wahala" Ni dai ina maƙure a ƙofar bayan gida jikina na kakkarwa. Wuƙa ya zaro ya yanki babban yatsan ƙafar Alh Liti. Da sauri ya tashi.
"Wani ɗan abu ta kazan ubane haka?" Ya furta, ganin mutum a gabanshi bai bashi tsoroba sam.
"Wane mai ƙarar kwanan ne ya shigo mun turaka, yaro ba dai sata kazo yi ba?" Cewar Alh Liti.
"Kashe ka nazo in yi kamar yadda na lashi takobi." Yana kaiwa nan ya cire hular kanshi, da ƙyallen daya rufe fuskarshi. Wannan jaba ɗin da yazo da rana ne yaron Alh. Ba Alh kaɗai ba har ni sai da na razana da ganin Jaba."
"Jaba baka mutu ba dama? To yau wallahi zaka mutu ko ni ko kai" Alh yana faɗar haka ya miƙe yana ƙoƙarin dafa bango Jaba ya saurin cukuikuyeshi nan dambe ya kaure a tsakaninsu.
"Baka kayi layar zana ba yau, kwananka ya ƙare a duniya". Ni dai ina tsaye ina kallon tashin hankalin wanda ba'a sa mishi rana. Bansan yanda akayi ba na gansu jina_jina dukkansu. Alh Liti ya faɗi ƙasa tim kayan cikinshi na motsi, Jaba ya farke mishi tumbi, Wannan abun dana gani shi yasa na soma naƙuda, bani da ko kuzarin da zanyi ihu, jinin Alh Liti harya gangaro inda nake. Jaba kuwa ya kinkimi jakunkunan kuɗi guda biyu ya arce, juyowa yayi ya kalleni
"In kika sanar ma wani ni na kashe Liti duk inda kika shiga saina bincikoki na farkeki, hatsabibine ni fiye da tunaninki" Yana kaiwa karshe ya fice. Sai lokacin na zunduma ihu gigitacce ina jiyo tashin motar Jaba. Daga wannan ihu da nayi ban sake sanin ina kaina yake ba. Ni dai na farka na ganni a ɗakina anata faman yi mun fifita, haske har ya fito. Hajiya Kubra na kalla nace.
Jaba ya kashe Alh Liti Hajiya shi ya kashe shi" Bakina ta rufe tace.
"In kina son kan ki arziki ki ja bakin ki kiyi shiru, karki sake ki ambaci sunan Jaba. Jaba hatsabibine na ƙarshe zai iya dawowa ya kashe ki kema. Alh Liti dai ya mutu sutura ma akeyi mishi za'ayi jana'izarshi zuwa goman safe, lokacin shine yayi babu makawa" ciwon naƙudane ya murɗeni na cije bakina ina ruwan hawaye da ruwan jiri. Ba kowa a ɗakin daga ni sai Hajiya Kubra. Sai da aka kira mun wani malami ya dinga mun tofi, dan jini ya hau kaina. Gani nake yi tamkar mafarki nake yi wallahi, ni naga bala'i ganin idanuna." Hijabi na saka muka fito tsakar gida sai ta'aziyya ake mana tare da yi mana jajen ashe ɓarayine suka shigo sata suka kashe Alh Liti. Ni dai bana ko iya magana a cikin ɗimuwa nake sosai, jina nake kamar zautacciya, ashe haka Hajiya Kubra tace ma mutane ɓarayine suka shigo sata suka kashe Alh. Yaran Alh Liti mata_matan sai gasu gungu_gungu sunata shigowa, ko wacce in ka ganta kasan kukan munafurci take yi. Maza_mazan kuwa ba wanda yayi kuka ma sam, fuskokinsu cike da fara'a. Ni dai ciwon naƙuda sai ɗan mintsinina yake yi sama_sama. Kafin ƙarfe goma gidan ya cika dam da mata. Mu kuma aka kirani muje mu yi ma Alh adda'a. Duniya ba komai bace, duk wanda ya bari duniya ta ruɗeshi yayi wawa. A falonshi na ƙasa muka samu gawarshi shinfiɗe, daga sama aka sakko da gawar falon ƙasa, Hajiya Kubra tasa aka rufo saman. Dan a saman dukiyarshi take. Adda'a mu ka yi mishi, muna kuka. Ba kukan rabuwa dashi na tabbatar muke yi ba. Ni dai kukan farin ciki da annashuwa nake yi har ga Allah bazan ɓoye ba. Nayi imani sauran ma babu mai kukan mutuwar Alh Liti. Yaranshi ne suka riƙo makarar aka fito da'ita zuwa ƙofar gidan. Mu kuma Hajiya Kubra tace mu zauna karɓar gaisuwa a falon Alh tunda babbane. Nan muka zauna ƙwanmu da ƙwarƙwatarmu, ni dai sai ciwon mara sama_sama. Aisha kuwa ana fita da Alh ta soma naƙuda zanga_zanga sai su Rashida su ka yi da ita ɗakinta. Wayata aka miƙomun Mama ce take kirana. Ina ɗagawa na sanar mata da batun mutuwar Alh Liti, kuma nace ko bashi ne su ciyo ita da Asiya su zo su zauna dani, dan ni gani nake nima Jaba zai zo ya kasheni. A haka muka gama magana da mama cewar gobe zasu taso. Jama'a kuma aka barsu akan ɓarayine suka shigo har gida suka kashe Alh." Muna zaune maza ƴan raka gawa saka dawo. Nan akaita shigowa yi mana ta'aziyya. Hajiya Kubra ce take da kuzari ita take ta amsawa dama ita aka sani gaskiya, yaran Alh Liti kuwa basu kareba sai shigowa suke yi, wasu ma ban taɓa ganinsu ba ni dai. Auwal ne ya leƙo yace.
"Hajiya ji mana ke da matan Baba" mu uku muka miƙe muka fito, tsakar gidan cike da al'umma.
"Hajiya batun abun da za'a girka fa. Kinga mutane an cika kowa yana jiran me za'ayi, ni dai na tura su Halifa nace su ɗakko Saniya guɗa ɗaya azo a yanka ƙatuwa. Ku kuma ku ɓalle store a fito da shinkafa da mai Hajiya, ayi lafiyayyen girki kowa yaci ya goge wuya, wala Allah ya samu adda'a ko?" Hajiya Kubra tace.
"Kasan komai ya shiga gado fa Auwal kubi a hankali, kar a kuma ɗakko Saniya gaskiya, duk da nasan anan Ghana gidan mutuwa yafi wani gidan bikin ma, amman abi a hankali " Dariya yayi yace.
"Haba Hajiya, giwa fa ta faɗi ai sai cin nama. Gayennan ya fa tara dukiya wallahi bana wasa ba, kuma mun gasu. Ai ni da an yi rabon gadonnan ƙasar zan bari ma" Harara Hajiya Kubra ta zabga mishi ba shiri yayi shiru. Haka kuwa akayi, aka kada ƙatuwar Saniya aka yanka. Aka shiga gidan maƙota aka shiga girkin shinkafa da miya da nama sutu_sutu. Rayuwa kenan yau ina wanda ya tara? Babu shima bai ciba, gashi yanzu za'aci ba lalle bane ya samu masu yi mishi adda'a ma. Kafin yamma Mariya ta haifi yaronta namiji tubarkallah. Ni kuwa a tsaitsaye nake naƙudar tawa. Bamu muka samu kanmu ba sai da daddare. Ina ɗakina ina cin tuwon shinkafa miyar egusi, taji naman kan saniya, ta yi mugun daɗi sosai. Ni dai a daren ban yi bacci ba, ina zaune a kan sallaya ina addu'a. Ciwo yana ta tsikarata,