MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   28 / 67

81K to 84K   out of 198.3K words

kaya ba?"
A'a bansan yaushe zai koma ba. Ni dai yace mun zai barni anan tukunna kafin ya nema mana wajan zama" A taƙaice na ba Ya Innana labarin gobarar da mu ka yi, da rabuwa da Zubaina da Bulama Babba yayi. Ajjiyar zuchiya ta sauke tare da cewa.
"Babbar magana, to Allah ya kyauta ya mayar muku da arziki. Ki je kiyi wanka ki yi sallah. Ga abincin mijinki yana ɗakin Bagulaji sai ki kai mishi, in sun dawo masallaci." Cikin farin ciki nayi wanka a bayan gidan Ya Innana mai ɗumbin tarihi a gareni, na ɗauro alwala na fito. Wadrope na buɗe na ɗakko wata doguwar rigar Ya Innana ta shadda blue na zura, na saka hijabin sallanta na ta da sallah. Ina kan sallaya a zaune na gama azkhar kenan na jiyo sallamar Ba Modu da Ya Innana. Zama yayi a bakin gado, muka gaggaisa cike da kulawa yake kallona.
"Yaya kuka yi da Ba Bakura ne Uwata. Naji dai batun gobara, da batun sakin waccan sheɗaniyar yarinyar da Bulama yayi. To amma Bakura ya wakiltani in sanar ma yaran gidan dai dai da allura bai yarda a ɗauka a ba Bulama da sunan taimako ko wani abun ba. To inason jin yadda ya ce miki ke" Jikina a mace na bashi labarin abinda Ba Bakura yace mun. Ya Innana tace.
"To amman ni malam ina ganin da anyi haƙuri an tausayama yaronnan, hannunka bafa ya ruɓewa ka yanke ka zubar." Ba Modu ya dubeta ƙur yace.
"Kina son a taimaka musu kenan ko sabida Uwata yake aure ko?"
"Bance a taimaka musu da kuɗi ba, amman ko da aikine a nema mishi wanda zai iya riƙe gidanshi dashi. A duba lamarin yaronnan fa, yaro mai tausayin kowa, mai hannun ungo. In hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi."
"Ya isa Innana, ki bar yaro ya nema da kanshi kamar yadda ya samu a baya ya kula da iyalinshi. Bazan iya ja da Ba Bakura ba. Kuma ki sani duk irin so da ƙaunar da nake ma Bulama ba kamar yadda Bakura yake son shi da ƙaunarshi bane, kuma bazai ga abinda zai cutar da shi ya zuba idanu ba. Kaza tana taka ɗanta ne ba dan bata sonshi ba, tsawatarwa ne. Sau nawa Bakura yayi kuka ya kasa bacci akan Bulama? Harfa asibiti ya kwanta, meye Bulama bai yi ba a gidannan ba? Kema na baki umarni ban yarda ki ɗauki kuɗi ki ba Uwata ko Bulama ba. Na yarje miki ki bata sutura inma naki, inma ki ɗinka mata sababbi, ɗan zanin gado labule duk zaki iya taimakonta dashi, baya ga wannan ban yarda ki bata komai ba. Aiki take yi, shima yana aikin shi. Tayi ma mijinta biyayya su taru su rufama juna asiri, ni shine kwanciyar hankalina, duniyar guda nawa take Innana. Ke Uwata tashi ki je ki kaima mijinki abinci, sai ku tafi asibiti ku dubo matar Wakil. Kuma ki kwana tare da mai gidanki." Yana kaiwa ƙarshen maganarshi ya fita. Binshi Ya Innana tayi da sauri. Ni kuwa ina ɗago kaina na hango maganin tari a saman mirror ɗin Ya Innana. Ajjiyar zuchiya na sauke harda Murmushi, dan ji nake gabaki ɗaya kamar zan zautu. Zuƙe maganin nayi tas na jefa kwalbar a ƙarƙashin gado. Ina jiyo su Ya Innana da Ba Modu suna tattaunawa a kanmu. Sai da ya fita Ya Innana ta dawo.
"Tashi Yahanasu ki je ki ɗauki abincin mijinki ki kai mishi. Kiyi haƙuri da jarabawar da kuka riski kanku a ciki. Ki riƙe adda'a, karatun Qur'ani, sallar dare, azumin litinin da alhamis. Ki dinga cire lokaci sosai kina ma mijinki adda'a Allah ya kare miki shi. Kar ki kuskura ki mishi iyaka da kuɗin albashinki, ki shiga cikin cefanen gida dumu dumu. Yaranki kuma karki bari suyi maraicin uwarsu, ki riƙesu fiye da yanda zaki kula da naki. Ki kasance mai sauƙi da sanyi a ko da yaushe. Kuma ki zama mace mai dabara gami da hikima. Zaki samu ɗaukaka a wajan mijinki, ki samu matsayi mai girman da ko da nan gaba zai ƙaro aure, to fa babu macen zata ture matsayinki a zuchiyar mai gidanki. Amman fa ki sani duk zaman lafiyan dake gidan aure, ba'a rasa jarabawa da saɓani a tsakani. Ki dai kasance mai mallakar kanki yayin da kike cikin fishi. Ki kasance mai tsawatar ma zuchiyarki, ba ita zata tsawatar miki ba. Tashi maza ki je ki same shi, ki kwantar mishi da hankali, yanzu ne dai dai lokacin da yafi buƙatar kulawarki fiye da ko yaushe. Karayar arziki fa bata da daɗi, shi yasa zaki ga waɗanda basu da tawakkali sai kiga sun haukace ma." Jikina a mace tulus na miƙe har zan fita Ya Innana ta dawo dani. Wani turare ta bani a cikin wata ƴar kwalba.
"Ungo ki shafe duk jikinki da wannan turaren, kina Kanuri amman kin watsar da ƙamshi. Yahanasu ki kula fa. Ita zuchiyar ɗa namiji da kike gani, babu abinda take buƙata, sai sanyi, daɗi, laushi, sauƙi. Ai da ƙamshi zaki iya mallakar zuchiyar Bulama wannan ai babban sirrin matan ksnuri ne" Kunya duk ta rufeni ni kam. Shafe turarennan mai mugun sanyin ƙamshi nayi a jikina. Wasu garukan magungunane kwance a ƙasan kwalbar. Mayafi ta bani, na cire hijabin na yafa gyalen na fice." Ɗaki ɗaki na dinga bi ina gaishe da kowa. Har izuwa ɗakunan matan su Dala. A ɗakin matar Dala nayi sallar isha, sai da na tabbatar su Bulama Babba sun dawo sallah nayi mata sallama na fita. Ɗakin Ya Bagulaji na koma na ɗauki abincinmu wanda aka jera a babban tran silver na fito. Sai kunyarsu nake ji, kamar ba gidan da nayi rarrafe a cikinshi ba. A tsakar gida na tarad da Wakil da su Dala sun kewaye Bulama, sai hira suke yi a tsaye. Fuskokinsu cike da annuri. Idanu Bulama Babba ya zuba mun mu kayi kallon ƙuda na wasu sakanni, saini na zare idanuna a cikin nashi na sauke kaina.
"Wakil karɓi trannan ka shigar mun dashi ɗakina. Sai kazo muje asibiti mu dubo madam ɗinka" Wakil ya karɓa ya shigar da abincin ciki, mu uku muka shiga mota zuwa asibiti. Ina baya shiru, Bulama Babba da wakil sai zuba hirarsu suke yi, har muka isa asibitin. A kwance muka samu me jegon amman ba bacci take yi ba. Yarinyar kuma tana hannun Yanunu. Yanunu tana ganinmu ta washe bakinta.
"Kadunawa kune a tafe, lallai wannan yarinyar da halama zata yi goshi" Dariya nayi nace.
Takwarata tayi kira ai dole inzo ayi shidimar suna dani. Yanunu ina wuni?"
"Lafiya lau ƴar albarka, kun zo lafiya?" Bulama Babba ne ya gaisheta, faram_faram ta amsa mishi. Me jegon muka yi ma ya jiki, na ɗauki baby.
"Kin ganta ko Yahanasu, takwararki ce" Yanunu tace.
"Takwarar takwararta dai. Karma ka rufeta" Dariya mu ka yi dukkan mu. Bamu jima a asibitin ba, mu kai musu sallama. Idanuna a rufe suke zaune nake a bayan mota, babu abinda nake son sha sai ƙwaya, ita kaɗaice zata sauke mun wannan hayaniyar da taima kaina yawa, kwakwalwata har wani tsalle take yi mini. Muna shigowa gida, nayi tafiyata ɗakin Ba Bagulaji, inason in kwanta. Amman har ɗakin Ba Modu ya biyoni yace in fice in je in samu mijina. Yunwa kamar zata kasheni, amman bana sha'awar komai face in afa ƙwaya. Sum sum na fito, Ya Innana ce ta kirawoni, rigar bacci sabuwa ta yage ta bani.
"Shiga kiyi wanka,ki zo ki sa ki je ku kwanta. Kinci abinci kuwa?" Sai kai kawai na iya girgizawa kunya ta hanani magana. Wanka na shiga nayi, na goge bakina da sabon brosh da na gani a bayan gidan. Rigar baccin na zura, bayan na shafe jikina da turaren humra. Rigar doguwace har ƙasa, hannun rigar yana da ɗan tsayi ba laifi, rigar tana da santsi sosai. Mayafi na saka na fita ina zunɓura baki. Ko da na je ƙofar ɗakin sai naji gabana yanata bugawa, daurewa nayi na shiga. A zaune yake hannunshi riƙe da ƙaramin Qur'ani yana karatu amman a zuchiya yake yi. Amsa mun sallamata yayi yana mun Murmushi, gefe na samu na zauna a takure, na kasa cewa komai
"Kinci abinci?" Girgiza kai nayi halamar a'a. Baice komai ba ya matso kusa dani, tare da tran abinci.
"Babu abunda zance miki sai dai ince miki Allah yayi miki albarka. Haƙiƙa na yaba da ƙoƙarin da kika yi a kaina wajan shawo kan Ba Bakura, har ya yafe mun. Nasan duk abinda suka faru a baya ba masu kyau bane. Wai nine da kaina na wulaƙanta Ahalina, iyayena ƴan uwana. Ina gani ruwa na dukan iyayena, hawaye na gangarowa a kumatun mahaifiyata, wacce bata iya bacci mai kyau a sa'ilin da nake ɗauke a cikinta, tai ta rainona cike da farin cikin son ganin na wanzu a duniya a matsayin mallakinta. Tasha zafin naƙudar haihuwata, kashi fitsari, kukana, hanata bacci. Amman wata mace tazo ta shiga tsakanina da'ita. Zubaina ta cutar dani wallahi. Hawayene ya shiga sunturi a kumatunshi.
Ka dena kuka, ka yawaita istingifari, sannan ka dinga yawan kiransu, ka basu lokacinka domun kawanke musu zuchiyarsu, duk ɗan abun da ka samu ka tsakura musu duk da nasan cikin yalwa suke, amman naka na neman albarka ne. Ɗago jajayen idanunshi yayi ya zuba mun. Nima shi nake kallo, ƙare mishi kallo nayi, naji tausayinshi na ratsa ni. Hancinshi na kalla mai kamar gajeren wando dan faɗi da buɗewa, leɓenshi baƙi masu kauri ya buɗe na kalli baƙin dasashin shi.
"Yahanasu. Kiyi haƙuri da abinda nayi miki a baya. Bana cikin hayyacina ne. Ni mai ƙaunarku ne dukkan ku, kina gani har su Ba Bakura ban kyale ba. Sannan bana son ki karɓi komai a hannun su Ba Modu, kuɗi ko sutura, ko wani abun. Ni zan kula dake zan nemi koyarwa in haɗa da aikina in dinga yi, dan in kula daku sosai. Ga su Maryam a hannunki ki riƙesu na baki su halak malak." Jikina ya mace mus, na kasa ce mishi komai. A kwano ɗaya mu ka ci abinci. Babu mai cewa da kowa komai. Bayan mun gama na fitar da kayan na dawo. A kwance na same shi daga shi sai gajeren wando. Saurin sauke kaina ƙasa nayi, ƙirjinshi sumul bako ɗigon gashi. Ba irin ƙirazan mazajen novels ba, dan ni ma'abociyar karatun littafinnan hausa ce. Kuma ni kaina ina hasaso irin kyawawan mazajen novels, da irin soyayyar da suke gudanarwa me daɗi. Duk da ni ban kasance kyakkyawa irin matayen Novels masu kama da larabawa ba, ni nasan ba kyakkyawa bace, Bulama Babba ma ba kyakkyawa bane sam, dan ba ko wacce mace bace zata yarda ta auri Bulama Babba ba, jajayen idanunshi kaɗai zasu iya firgitata, gashi da ƙatuwar murya, ƙaton hanci, da ƙaton baki. Amman Alhamdulillah ya kasance ma'abocin kyan zuchiya, mai addini, mahaddacin Qur'ani mai girma, kuma wannan shine cikakken so, dani da Bulama Babba mun dace da juna sosai.
"Tunanin me kike yi Yahanasu, kizo ki kwanta kema ki huta mana." Motsi wannan na kasa yi balle in ɗaga ƙafata.
"Zo ki kwanta, in kuma ba zaki iya kwana katifa ɗaya dani ba, bari in sakko in kwanta a ƙasa." Bai jira ta cewata ba, sai ya sauko. Nace dashi.
Kayi haƙuri ka koma, zan iya" murmushi ya sakar mun. Nima na mayar mishi a kunyace. Mayafin jikina ya cire mun, kaina a ƙasa amman inajin kaifin idanuwanshi da suke yawo a jikina.
Mrs Bukhari ce



*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
21




*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*


























Ajjiyar zuchiya naji yana ta saukewa, hannuna ya riƙe a hankali ya haɗamun wani shocking, danma hannun nashi ba mai irin taushinnan bane irinna mazajen littafi. Amman naji shigar riƙe hannun sosai, babu shiri na lumshe idanuna. Ahankali na dinga ɗaga ƙafafuna ina binshi tamkar raƙumi da akala, har izuwa bakin katifar. Ga katifar ba mai girma bace, ta gado waya shida ce. Zaunar dani yayi ta hanyar riƙe kafaɗuna. Nayi saurin shigewa can cikin katifar na juya baya, idanuna sai lumshewa suke yi. Amman dana tuno da azabar fyaɗen da akaimun, tuni na saki wani rikitaccen kuka mai dagula zuchiya, har wani firgita nake yi gani nake yi kamar abinda ya faru dani a baya yanzu ya faru, da rarrashi Bulama Babba ya bini, a tunaninshi taɓa ni da yayi ne yasa ni wannan kukan. Da ƙyar bacci ɓarawo ya ɗaukeni zuchiyata fal da fargaba da tsantsar tsoron Bulama Babba. Bulama Babba kuwa, sai juye juye yake yi, cikin bacci naji ni a jikinshi ya rungumeni ƙam, gashi yana halin buƙata, amman bani da nutsuwar da zan iya bashi kaina, shima bai nema ba, sai shafo ƙirjina daya dinga yi dai. Sannan ko ina da nutsuwar bai dace ace a gaban iyayenmu zamu yi wannan aikin ba. Sai dai ban haramta mishi wasa da sassan jikina ba, kamar yadda naga yanayi, ni dai kunya da tsoro suka rufarmun, jikina har rawa yake yi babu nutsuwa tare dani sam. Sakeni yayi, ya ɗan matsa kaɗan. Bai kuwa jima ba bacci yai awon gaba dashi. Ni kuma ya barni da karanta wasiƙar jaki. Haka muka kwana tare, washe gari kuwa, na kasa haɗa idanu da kowa, sai sauke kai nake yi. Gashi a ɓarayin su Ba Bakura na wuni, tare da su Fanna, da Fanda, sai yaran ɗakin Marigayi Ba Baana, su biyu Sufaim, da Ya gaji. Kasancewar dasu nafi shaƙuwa sosai. Su Yabulu kuma tana gida tana fama da tsowon ciki. Hira me daɗi muke gudanarwa, Sufaim babba ce, dan itace Babba a ɗakin Ba Baana, amman mun shaƙu sosai, shi yasa kai tsaye daga wajan aikinta ta wuto gida, tunda labarin zuwan nawa ya bazu a dangi. Yau garau nake jina, sabida da safe na zari jiki na fita na siyo magungunan maye, duk da ban samu irin wanda nake sha ba, amman suma sun sani naji garau. A ƙarƙashin pillown Ya Innana na ɗauki kuɗin. Rabon da in ɗauki kuɗi ba tare da an bani ba, tun ina yarinya ƙarama irin na yarinta da ake yi. Amman sai gashi yau nice nayi sata, na siyo kayan maye. Bulama Babba yaso tafiya yau, amman kuma ya Ɗauki Amada, da Dala, da Ba'a kaka suka tafi gaishe da dangi, dan Ba Modu yace lallai yaje Yobe wajan Mama Gana itama ya bata haƙuri, tun safe suka fice a gidan. Nima cikin aminci na wuni tare da ƴan uwana, daga ɓarayin Ba Bakura muka wuce ɓarayin surukan gidan dan in gansu da kyau kuma in gane su. Abun sha'awa daga masu tsohon ciki, sai masu ƙaramin goyo, ga matar wakil itama an sallamota daga asibiti tun safe. Ina da tsananin son yara, ina son inga na haihu nima. Lumshe idanunta nayi, ƙwaƙwalwata ta shiga hasko mun abubbuwan da suka faru a daren jiya ni da Bulama Babba. Dana tuna sai inji jikina ya sauya, na rasa gane takamaiman abinda ke raina. Bani na samu hutu ba sai da daddare, bayan su Fandau sun koma gidajensu. Ina zaune akan sallaya Bulama Babba yayo sallama ya kutso kanshi cikin ɗakinmu.
"Ya Innana kina ciki ashe?" Ya tambayeta yana ɗan sosa kanshi. Kallona yayi a fakaice.
"Inanan Bulama Babba, shiga ka zauna, dama yanzu zanje wajan Baban naku ne." Tana faɗar haka ta fice abunta, ɗakin ya rage daga ni sai Bulama Babba.
Sannu da dawowa, ina wuni?" Na furta a sanyaye. Sai da yaima

28 / 67