Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
siyo, ɗaya tamu ɗaya ta yara. Mayafina na zare, na shiga kaye kaye, dadduma na shinfiɗama su Bawa a gefe suka zauna. Ni kuma na fito tsakar gidan ina neman ɗan dogon abu da zan iya hawa in kafa labule. Maman Sabeer tace.
"Bari in ɗakko miki kujerar ɗinkina inaga zata kai miki, labule zaki buga?"
E kawai nace mata. Ta shiga ɗaki ta miƙo mun kujerar, nayi godiya na koma ɗakina. Amman ko da na hau kujerar tsayina bai kai ba, sai da na ɗaura jakar kayanmu sannan tsayina ya kai. Labulen ƙofa na saka, na saka labulen windo. Ragowar labule biyun da suka rage, nayi dabarar raba ɗakin biyu da labulayen, kuma yayi kyau. Dakatawa nayi dan naji an soma kiraye kirayen sallar magriba. Ruwa na ɗiba a butar da na gani a kusa da wata ƙaramar randa ta wajan bayan ƙofa. Na shiga ƙyanƙyami da tashin hankali sosai sanda na shiga bayan gida, da ƙyar na samu gefe guda na tsugunna, a tafin hannuna nayi fitsarin dan gudun Infection (sanyi) ya kamani in shiga ukuna. Kamar zanyi amai haka na fito, nayi alwala a tsakar gida na koma ɗakina. Bawa na zuba ma ruwa nace ya fita ƙofar ɗakinmu yayo alwala yazo mu yi sallah, dan naga kowa a gefen ɗakinshi yake komai, naga wasu ma a tsakar gida suke sallah. Ina idar da sallar magriba, na ci gaba da gyare _gyare, nice har bayan isha ina abu ɗaya. Cin cin da kilishin da Hajja ta bani na fito dashi na ba Bawa da Maryam su ka ci. Na ɗiba da yawa na miƙa ma Hajara. Shinfiɗe Bawa da Maryam nayi a katifarsu, ina zaune a cikin duhu. Sai tunane tunanen rayuwa nake yi. Sallamar Bulamana na jiyo a bakin ƙofa, da sauri na taso na nufi ƙofar. Kurfot da kwatan buhun gawayi ya ajjiye mun a gefen ɗakina kamar yanda na kowa yake, ledar hannunshi na karɓa na shigo ciki, ya biyo bayana.
"Subuhanallahi na mance a duhu na barki ke da yara ai." Yai maza ya kunna wayarshi, a lokacin ne yaga yanda na gyara ɗakin yayi tsab dashi, murmushi ya mun tare da cewa.
"Allah yai miki albarka matata
Ameen mijina. Nace ina dariya dan in ƙarfafa mishi guiwa, amman a zahirin gaskiya ina tausayin rayuwar da zamu yi a gaba, ina fatan Allah ya shiga cikin lamarin namu ya taɓa."
"Ga taliya na siyo leda biyu, akwai mai da maggi,da kayan miya duka, sannan akwai ƙosai da biredi a cikin ledar, ki tashi yaran sai kuci, in yaso da safe kya dafa taliyar ko?" Hannunshi na kamo, na ɗauki ledar, yana biye dani muka shige uwar ɗakin da na haɗa mana. A bakin katifa na zaunar dashi, na taimaka mishi ya cire rigar jikinshi wacce ta jiƙe da zufa sai warin rana yake fitarwa.
"Ka zauna ka huta, yara sunci abinci kafin suyi bacci. Amman ni banci ba ina jiranka. Amman ko zaka ɗan watsa ruwa kafin muci abincin?" Murmushi yayi tare da lumshe mun idanunshi.
"Nagode da kulawarki a gareni. Mu ci abincin tukunna bana son ki yi ta zama da yunwa." Bana son inyi jayayya dashi shi yasa na buɗe mana ledar ƙosai da biredin, muna ci muna korawa da pure water, muna hira harda dariya. Bayan mun gama, na zuba mai ruwa a bokiti ya ɗauka, na zuba wani a buta na bi bayanshi dashi. Matan gida ko wacce ta baje a tsakar gida da iyalanta, wasu na cin abinci da mazajensu da yaransu, wasu kuma firarsu suke yi, wasu a zaune, wasu a kwance. Duk inda muka wuce Bulama na yi ma mazan sallama kafin mu wuce. Ruwan butar hannuna na kora dan rage dattin bayan gidan kafin ya shiga, ni kuma na dawo na sake cika ruwa a buta na koma. Ina komawa yana fitowa, nima wankan na faɗa nayo yana gadina, dan babu ƙofar kirki a bayan gidan. Bayan mun gama muka tawo tare muna ɗan taɓa hira har muka shiga ɗaki.
"Akwai brosh da man goge baki, daure ki ɗakko mana mu goge bakinmu." Buɗe ledar da ya shigo dashi nayi na ciro sabon brosh ɗin dana gani, na haɗa da nashi brosh ɗin da man goge bakin. Shi kuma ya ɗebo mana ruwa a buta muka fito mu ka yi brosh a bakin kwatar data raba gidan biyu, hatta wanke wanke a bakin kwatar naga sunayi, yara kuma a wajan suke tsula fitsarinsu. Mun raya wannan dare da soyayya mai wahalar goguwa, rungume da juna mu kai baccinmu cikin farin ciki sosai. Da asussuba ina bacci Bulamana ya tashi ya buɗe ƙofa ya fice. Zare sakatar da yayi shi ya tasheni daga bacci, a hankali na miƙe na mayar da doguwar rigar baccina, na yafa mayafi na leƙo. A gaban kurfot na samu Bulamana yana ta kiciniyar hura wuta da leda ya kasa. Murmusawa nayi, bai ankaraba yaji na karɓi ashanar a hannunshi. Bansha wuya ba wutar ta kama, a hankali ta ruru na ɗaura ruwan zafi. Shi kuwa da ruwan sanyi yayo wankan sallah, dana soso da sabulu. Ƙarfe huɗun dare ne, amman mata har sun soma fitowa domun hura wuta. Allah sarki dama haka marasa ƙarfi suke gudanar da rayuwarsu abun tausayi? Allah sarki, ni ban taɓa ganin irin hakan ba, kasancewar gidanmu akwai rufin asiri babu laifi. Juye ruwan zafin nayi a bokiti nayi wanka na fito, a tsaye na samu Bulamana ya soma sallah. Kayan jikina na sake, na fita da kayan jajjage gashi banda turmi ko gireta. Leda na ƙulla a hannuna, na yayyanka kayan miyan da wuƙa. Bani na gama haɗa sanwa ba sai bayan sallar asuba, lokacin gidan ya ɗauki haramin kacaniyar yara da iyayensu, anata gaishe _gaishe. A ƙofar ɗakina nayi ma su Bawa wanka kamar yadda naga matan gidan nayi. Ƙarfe bakwai na gama girkina tsab, na zuba gaushi a kaskon turaren wuta na shiga dashi. Turaren wuta mai daɗin ƙamshi na zuba a wutan.
"Su Bawa zasu ci gaba da zuwa makaranta, amman wata makaranta ce mai suna Zainab Acadamy na sanya su. A cikin layinnan take, in zamu fita zan nuna miki. Sai ki kaisu, ƙarfe uku suke tashi a makarantar, tunda 2 ki ke dawowa gidan sai ki dinga ɗakkosu."
To in sha Allah, Allah ya basu nasarar karatu. Bawa to maza a gamakaryawa ko za'a koma makaranta. Bawa ya dubi Abbanshi yace.
"Dady ina momy take?" Bulama Babba ya dubeshi da kyau, yayi ɗan jim kafin daga bisani da bashi amsa da cewa.
"Momynku tayi tafiya kaji Bawa, ba yanzu zata dawo ba, ka kwantar da hankalinka kaji?" Abunka da yaro kai kawai ya gyaɗa. Yana gama cin abincin ya miƙe yana kallon agogon hannunshi.
"Madam bakwai da rabi harta wuce, ya kamata ki taso mu fita, kar Ahmad ya soma ƙorafi" Dama a shirye nake tsab cikin farar lafaya mai taushi, takalmi kawai na saka na rataya jakata, na kama hannun Maryam, shi kuma ya riƙe hannun Bawa, a jere muka fito, dai dai fitowar Ahmad da yara shima.
MRS BUKHARI CE
[06/08, 4:26 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
25
*INA MIƘA SAƘON GODIYA GA ƊUMBIN MASOYANA. NAGA SAƘONNIN KU NA YA JIKI, NAGODE SOSAI, NA SAMU SAUƘI ALHAMDULILLAH AMMAN HAR YANZU INA KAN MAGANI, ZAMU LALLAƁA IN SHA ALLAH. ƳAN BATI ASHE SUNA DA YAWA, WASU SUNYI ƘARFIN HALI SUN KIRANI SUJI JIKINA, KUMA FA BASU SAI LITTAFIN BA BANSAN MA DAGA INA SUKE BA. AMMAN WALLAHI NAJI DAƊI TUNDA NASAN SO NE, AI AKWAI LITTATTAFAN KYAUTA MA DA KO SAURARENSU BA'AYI. NI BANYI ALLAH YA'ISA BA, ƘOFA A BUƊE TAKE KOWA YA KARANTA, ABUNDA ZAN SAMU IYA SHI ZAN SAMU. INA ALFAHARI DA RUBUTU, INA SONKU MASOYANA*
Mabaruka ta dube ni tace.
"Zanyi miki baya ni ƙawata daga baya, kafinnan bari in kwafe number motarshi" Wuce mu yayi a hankali baya wani gudu. Nan da nan Mabaruka ta ɗauki number motarshi a hoto. Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
"Ni nafison ɗan bana bakwai, so nake in gwangwaji romon soyayya da yaro matashi mai jini a jika. Wani sa'in sunfi daɗin sarrafawa ki mallakesu hankalinki kwance. Ƙila baifi ace matarshi ɗaya da ƴan ƙananan yaranshi da basu wuce biyu ba. Kinga basu girma ba, balle suma suita cin kuɗinki ta hanyar kai sunayensu wajan boka dan ai musu farraƙu su da uban, tanan kuɗina ya huta, sai inji da ubansu da uwarsu kuma. Wannan shine dabarata ƙawata, gobe sai Jos in Allah ya yarda " Baki kawai na taɓe bance da'ita komai ba, ra'ayinta ta faɗamun, nima da nawa. Washe gari da duku _duku muka kuma ficewa, ba mu muka dawo Kaduna ba sai bayan isha. Amman aikin gama ya gama, boka ya bata kwallin da zata sa a idonta, da misalin ƙarfe biyar na yamma, taje kan titin isa kaita ta tsaya. Wannan matashin zai ganta, zai tsaya ya ɗauketa"
Ai kuwa yanda boka yace hakanne ya faru, komai ya tafi dai_ dai irin yanda Mabaruka take so. Abunka da sihiri Salisu ba ƙaramin rikicewa yayi akan Mabaruka ba. Bayan ya kaita gida, su kai musayar number, tare da alƙawarin zai dinga kiranta, kuma zai yi ƙoƙarin fahimtar da iyayenshi kafin ta gama idda. Sabida wai bai jima da auren ba, ɗan shi ɗaya ne, matar tashi tana gidan iyayenta tana wankan gida. Wannan kenan, haka rayuwa tai ta tafiya, komai na tafiya yanda ake son shi. An kawo sadakin Nafisa da kayan na gani ina so na garari, biki ƙarshen watan da muke ciki za'ayi shi, Amarya zata tare a Abuja. Kwana biyu da bikin zasu wuce ingila. Shirye shiryen biki ya kankama sosai, Alhn Nafisa sai ɓarin kuɗi yake yi mana tamkar mara hankali, ko da yake duk wannan abunda yake yi bai san yana yinsu ba, dan an juyar mishi da tunaninshi ne, kuɗin da yake jibga mana bama amfana da komai, malamai ke morarsu dan kullun a cikin kawo kaza, za'ayi miki kaza, sai an kace bakin wane, haka dai karatun yake kullum. Ana cikin haka Sagiru ya dawo, ya sake zama abun tsoro, ya kuma riƙa a iskanci, har karya ya ajjiye mana a gidan mai ciki ma, kuma a dole Mama take zuba ma karyannan abinci da ruwa. Ni kuwa dashi ko ga maciji bama yi."
YAHANASU:
Cikin raɗa Bulamana yake mun magana.
"Kukan ya isa nace ko? Taya raina bazai ɓaci ba uhm Yahanasuna, kinsan irin sonki da kishinki da nake yi kuwa?" Cikin shessheƙar kuka na ɗago kaina muka haɗa idanunmu waje guda.
Kayi haƙuri bazan sake ba, nayi hakanne dan in samar maka sauƙi"
"A'a wannan sauƙin bana buƙatarshi sam Yahanasuna. Wannan ai aikin maza ne ni zanyi abuna. Na barki da girki da kulawa da yara." Banyi aune ba naji ɗumin leɓenshi akan nawa yayi musu riƙon alewar yara. Nuna rashin gajiyawa nayi, na ba mijina kulawar da duk ta dace. Cikin minti goma na faranta ranshi. Kanshi na saman pillow yayi baccinshi, ni kuma na shiga sosa mishi kai. Cikin baccin yasa hannunshi ya cire mun hannuna daga sosa kanshi da nake yi.
"Allah yayi miki albarka, ya faranta miki kamar yadda kika faranta mun kiyi baccinki. Idanuna na lumshe wasu zafafam hawaye suka gangaro kan kuncina. Tausayinshi ya kama ni sosai, naso ace na kawo ma Bulamana budurcina, amman kash ƙaddara ta riga fata. Yanzu ne na gane hikimar Ba Bakura daya haɗa aurenmu. Tun a baya da Bulamana ya ci mun mutunci akan ƙarya ma nake yi ba fyaɗen da akaimu. Bayan wannan bai sake yi mun maganar ba, ko a fuska bai nuna mun ya ji zafin jina ba cikakkiyar mace ba. Da wannan tunanin nayi baccina, bani na farka ba sai huɗun asuba. Akan sallaya na tarar da Bulamana yana tulawar Qur'ani. Muna haɗa idanu yayi murmushinshi yace.
"Kaddai karatunane ya tayar dake a baccin? Nima murmushin na mayar mishi.
A'a baccinne ya ƙare mun, da yake na saba tashi Sallah.
"Hakane, ruwan wankanki yana wuta, ki yo wanka ki dawo, ko raka'a biyu sai kiyi nafila ko ƴar albarka?" Kallon tuhuma nayi mishi, inason tambayarshi waya hura wutar? Amman sai ya girgiza mun kai halamar A'a. Bakina na rufe bance komai ba. Zani na ɗaura a ƙirjina na zura hijabina na fita tsakar gidan. Maman Hassan ce kawai take ta faman wankin wake, tana yin alalar siyarwa da safe, dan jiya da zan fita naga an yi layi sai saye akeyi. Gaisawa mu ka yi, na wuce ta zuwa bayan gida. Duk sammakona wasu sun riga ni. Sai da na jira aka fito sannan na shiga, nayi wanka biyu, dana sallah, dana soso da sabulu. Nafila nayi, tare da shafa'i da wuturi. Qur'ani nima na ɗauka, nayi karatu kamar na minti goma haka, kafin na soma ragargazo roƙon Allah, buƙatun duniya dana lahira, arziki mai amfani ta hanyar halali babu wanda ban roƙama mijina ba. Kafin na tashi kuma na shiga ɗan kaye kayen ɗaki. Ƙarfe biyar na tashi yara nayi musu wanka, a lokacin matan gidan kusan rabi duk sun fito, ko wacce na hidimar dake gabanta. Biyar da kwata su Bulamana suka wuce masallaci, harda Bawa. Kafin su dawo na gyare ɗakina tsab sai ƙamshin turaren wutan dorot yake yi, ina ɗaura ɗumame na gabatar da sallar asuba. Na dama kokko na gama ɗumamen shinkafa da miyar da muka ci da daddare. Sai ƙarfe shiddan safe suka shigo. A tsanake kowa ya shirya, cikin annashuwa muka gama karyawa Tsab. Na ɓararraka ma su Bawa taliya da miyar jiya wanda zasu yi break dashi a makaranta. Tare muka fice yauma. Sai da na shiga ɗan sahu Bulamana yace.
"Aff madam na mance yau ba sai kin biya ɗakko yara ba, Hajara zata dinga ɗakkosu tunda tana gida.
To shikenan ranka shi daɗe sai kun dawo" Mu kai sallama na kama hanya. Rayuwa haka tai da yin tamaule da da mu, muna rayuwa cikin farin ciki da soyayya, harma mu kan mance a ɗaki ɗaya muke rayuwa, amman rayuwar ta maneji sosai muke yi, cikin sati guda shaƙuwata da Bulamana ta ƙara yin ƙarfi sosai. Kuɗin adashen dana ɗauka da kuɗin tallafin dana samu, na tarkata da ɗan kuɗaɗen da Ya Innana ta bani a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba, duk na haɗa na tarkata na siya mana ƙaramin fili a gandu, wanda baifi a gina ɗaki biyu da bayan gida da kitchen ba. Da sunan Bulamana aka cike takaddun, Binta ce ta shige mun gaba, da ƙaninta har aka gama komai, aka damƙa mun takaddun filin nazo na adanasu, ba tare da sanin Bulamana ba. Ɗan kuɗaɗen da suka saura a hannuna su nake son in soma juyawa amman inata tunanin me zan dinga siyarwa. Kamar wasa muna maganar da Bulamana yace me zai hana in dinga yin meat pie ina kaiwa wajan aiki. Ai kuwa munyi wannan hira da kwana biyu na soma yin meat pie. Na dubu ɗaya na yi, babu laifi duk ya ƙare har ana nema, sabida na yi shi da arha, ban bi babbar riga ba. Rayuwa sai daɗi take yi mana, kusan kullum sai mun yi waya da gida, iyaye da ƴan uwa. Bani da damuwar komai, sai shaye_ shayen miyagun ƙwayoyi da kullum a cikin sake dulmiya nake. Har cikin zuchiyata inason in dena shan komai. Amman abun ya ci tura, in nayi kwana ɗaya bansha ba, ko rintsawa bana yi, sai inji kaina kamar zai rabe gida biyu. Ko da na kira Hajja Fati a waya nake yi mata ƙorafi akan hakan, cemun tayi bazan taɓa komawa kamar da ba, kuma bazan taɓa samun sukuni ba in dai ban sha ba. Gaba ki ɗaya abun duniya duk yabi ya dame ni. Kamar ko da yaushe ina zaune nayi rashe_ rashe a tsakar ɗakina, labulen ɗakin yana rataye a saman ƙofa, kuɗi nake ta faman shiryawa, ina yi ina kora laka mis ɗina. Bawa ne ya biyo Maryam a guje zai doketa, ta faɗo kaina da hanzari. Nayi carab na riƙeta ina jin son yaran sosai, gani nake tamkar ni na tsugunna na haifesu.
"Umma kinga Maryam na tsokanata ko?" Cewar Bawa. Hannunshi na riƙe nace.
Ka yi haƙuri kaji Bawa? Maryam ƙanwarka ce banda duka. Ke kuma ja'ira banda tsokana, riƙe hannunta ku je ɗakinsu Anisa ku yi wasan ku. Hannunta kuwa ya riƙe suka fita, da kallo na bisu ina ganin cikakkiyar wautar uwarsu data kasa fauwala ma Allah lamuranta, ta tsugunna akan yaranta. Ina cikin tunanin nan sai na jiyo muryar Bulamana yana gaisawa da Hajara dake tsakar gida, sai kwankwatsa hira akeyi a ƙofar ɗakinta, gulme_ gulme kuwa kullum a cikinshi suke, suce mijin wannan kyakkyawa, suce mijin wance mummuna, ko ita matar ace mata mummuna. Kamar ni kam da Bulamana ina jin yaran da suke zaman kansu a gidan suna gulmarmu. Gamu baƙaƙe munana, wai in muka haihu yaranmu ba zasu ganu ba dan muni. Ni kuwa hamdala nayi da yasa iyakar munina a iya fatar fuskata da ƙirar jikina yake, amman zuchiyata mai kyauce, tunda zaman aure nake yi, ba dandi ba. Kuma na gode Allah da Allah ya bani miji mummuna mai kyakkyawar zuchiya ma'abocin addini da sanin darajar mace. Da sallama ya shigo yana washe mun baki
"Kaga Hajiyan kuɗaɗene kike lissafawa haka, iye" Dariya mu ka yi dukkanmu. Waje ya samu nesa dani ya zauna, kasancewar labulena a ɗage yake.
Me ka siyo mana ne naga leda har bibbiyu?"
"Kaji me bakin kwaɗayi ko? Sabulu da omon wanki na