MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   18 / 67

51K to 54K   out of 198.3K words

dafo abinci, bata jima da fita ba." Zubaina ta miƙe tana gaba ina bin bayanta muka fita.
Yau baki da aiki ne Zubaina? Kinsan bazaki yi wasa da aikinki ba, dan shi zai ɗan taimaka mana kafin in samu wani aikin."
"Inada night ne, sai da yamma zan tafi, ya kwanan damuwa? Jiya ko runtsawa banyi ba Bulama cikin tunani da taraddadi na kwana" Ɗan dariya nayi mata nace.
Ni kuwa nayi bacci, na miƙa lamarin ga Allah. Sai dai yanzu dana fito tsakar gida, na haɗu da waccen baƙa mummunar yarinyar, wallahi sai mikin ya zame mun sabo. Ina zaman zamana an auro mun mai farar ƙafa, daga zuwanta komai nawa ya rushe lokaci guda. Ita kanta zata ɗanɗana kuɗarta, in dan kuɗi ta amince aka aura mata ni, to tafaru ta ƙare, sai in gani ai tare duk za'a sha wuyar ai ko?" Murmushi Zubaina tayi sannan tace.
"Ai masu farar ƙafa babu irin masifar da basa haddasawa. Akwai wani maƙocinmu, attajirin gaske ne, irin masu kuɗinnan na da ne. Ɗan kasuwana, ya mallaki tireloli da dama. Yana zaman zamanshi yayo sabon aure. A takaice, duk kadararshi sai da ta narke. Tirelolinshi sukaita haɗari ana rasa rayuwa, da gidan da suke kawai ya tsira. Shima cikin dare kawai gobara ta kama gidan, babu abinda wutarnan bata lashe ba. Dole suka dawo anguwarmu da haya, hawayi yake siyarwa yanzu haka fa, kai bakace ya taɓa yin kuɗi ba ma. Jinjina kaina na dinga yi har muka shiga ofishin likita, muka fito ina cike da mamaki. Wayata ce ta shiga kuka, ina zarowa naga number Ahmad.
Ahmad ba dai har kun iso ba ko?" Daga cikin wayar Ahmad yace.
"A'a muna dai hanya yanzu muka shigo wani ƙauye, an tsaya cin abincine, shine nace bari in kiraka"
Ai gara kuwa daka kira, dan insa ai muku girki, ka ganni a asibiti ƙanin Zubaina ne bai da lafiya. Amman yanzu zan koma gidan, zan sa a gyara muku waje, ai muku girki. Ahmad yace.
"To shikenan sai mun iso, ka isar mun da saƙon gaisuwata wajan Madam, kuma inai mata ya mai jiki" Yana kaiwa nan ya datse wayarshi.
"Ahmad ɗin garin zai shigo ne?" Nan na labarta mata dukkannin halin da Ahmad yake ciki, maimakon inji tayi magana, ko ta tausaya sai kawai ta taɓe bakinta. Ko da muka koma ɗakin da Sagiru yake a kwance, ya farka, sai surutai marasa kan gado yake yi, yana zage_ zagen shi bazai yarda ba, sai sun ɗauki fansa ko mutuwa zaiyi. Mama kuwa tayi shiru tana kallonshi, daka kalli fuskarta zaka ga cike take da damuwa a matsayinta na uwa. Goggo Rakiya ce ta balbaleshi da faɗa.
"Haba Sagiru ka shiga taitayinka mana, kuma ku tausayama mahaifiyarku, tun jiya muke nan babu wanda yai baccin arziki, amman yanzu da farkawarka ka ishi mutane da zancan ɗaukar fansa_ ɗaukar fansa, abunda ya faru dakai bai zamema ishara ba ashe? Da yanzu kana lahira naga yanda za'ayi ka ɗauki fansar. Yara basu san komai ba sai tada ma iyayensu hankali wannan wanne irin zamanine haka?" Ni dai ina gefe ina kallonsu kawai, kuɗi na ciro a aljihu wanda bansan adadinshi ba na miƙa ma Mama, sannan nayi musu sallama na fito Zubaina na biye dani a baya.
"Abban Maryam in an gama abincin sai ka dawo ka kawo mana namu ko? Ni na ɗauka zaka sa tayo abincin safe ka tawo mana dashi ai" kaina na dafe nace.
Kinsan da yake hankalina ba a jikina yake ba, na sha'afa shaf. Amman zansa tayo abincin, zuwa rana zan kawo muku" Murmushi tayi tace.
"Tayi kamar na mutane goma haka, dan nasan zuwa anjima asibitin zai cika da mutane, kuma inason ka bani kuɗi zan siyo kayan tea in ajjiye, kuma ba kuɗi ishasshe a hannuna" Nayi mamakin da Zubaina ta tambayeni wasu kuɗaɗe a cikin wannan halin da nake, duk da kuɗin dana dunƙula na ba Mama. Amman kasancewar bana ganin wallen dukkan abunda Zubaina ta aikata, a idanuna gani nake duk abinda tace ayi shine abunda ya dace. Kuɗaɗen jikina duka na bata, mu kai sallama na fice daga asibitin zuwa gida"




Zubaina:
Bulama na fita na shige motata, a guje na fice a asibitin. Kai tsaye gidan Mabaruka na nufa, da sallama na shiga ɗakin ba tare da na jira anyi mun izini ba. Adam yana rungume da Mabaruka ita kuma sai zabga shagwaɓa take yi. Suna ganina yai maza ya saketa, yana sosa kanshi. Kaina a ƙasa muka gaisa ya fita, Mabaruka ta mara mishi baya tare da ce mun.
"Ƙawata bari in rakashi zaure in dawo" Jigum na zauna a kan kujera, sai wasiƙar jaki nake karantawa, gabaki ɗaya hankalina baya jikina sam. Sallama naji anyi, tare da shigowar kai tsaye kamar dai yadda nima nayi. Hadiza ce ta shigo ɗakin da ganinta kasan a ruɗe take, waje ta samu ta zauna.
Hadiza kece a gari da safiyarnan haka? " Kallona tayi kamar tana tunani, daga bisani tace.
"Hmmmm Zubaina ke dai ki bari. Aurenane ya mutu, shine kika ganni a firgice haka, kishiya ta hanani saƙat ni da yaran duka, ke ya kika ga yanda na lalace?" Dubanta nayi da kyau, tabbas Hadiza ta lalace sosai, tayi duhu kuma. Hadiza ƙawarmu ce tun ta ƙuruciya, tare mu kai karatun islamiyya da'ita. Tana Aure a Zaria. Ta auri mijinta tun yana talaka, daga bisani Allah yai mishi arziki, arzikinshi ke da wuya yayo sabon aure. A lokacin mun ba Hadiza shawarar ta tashi tsaye danta ƙwaci ƴancinta a gidan mijinta. Amman sai ta nuna mana ita bata akan irin layinmu,harma tana binmu da nasihar muma da muke bin malamai mu Daina, wannan kenan.
Baki na taɓe nace.
Gaskiya kin lalace sosai. To amman ke kika so ganin kanki a haka, dubeni da kyau ki gani, ga Mabaruka itama ai kina gani, Safara'u ita kuma tana can Abuja. A cikin ƙawayenmu kece kaɗai koma baya. Hadiza wa ya faɗa miki borno gabas take. Kowa fa da kika ganshi ba'a zaune yake ba. Zaka ɗan dinga neman taimako ko babu komai. Amman ko da muka baki shawara ai wa'azi ma kika jefemu dashi. Ai namiji da kike gani bashi da wani burin daya wuce, ya samu dama yai arziki ya ƙaro Aure. ke kuma da kika sha wahalarshi ya saki a kwandon shara ke da bola babu maraba. Duk da tashi tsayen da nayi akan Bulama, sai da munafukan iyayenshi su kai mai Aure, yanzu haka akwai kishiya a gidana Hadiza" Kai na girgiza ina mai cike da takaicin wai ni Zubaina ina da kishiyar da ake mana rabon kwanaki da'ita. Duk da ma ba kwanciyar aure akeyi da'ita ba. Amman zuchiyata a cikin zafi da raɗaɗin ganinta ta ke a ko da yaushe. Mabaruka ce tayo sallama ta shigo
"Me zan gani Hadiza kece a gidan Ƴan bin bokaye yau kuma?" Hannu Hadiza ta kamo ma Mabaruka, bata ce komai ba, sai ta saki wani irin kuka mai tsuma zuchiya. Shiru mu kayi dukkanmu muna kallon ikon Allah, daga baya Mabaruka tace.
"Kece ai da abin haushi Hadiza, yanzu me kike buƙata? Ki share hawayenki ki mun bayani dan Allah" Hadiza nan ta buɗe baki tana labarta mana irin ƙunci da takaicin ɗa namiji da tai ta ƙunsa, da takaicin kishiya iri iri, ga sakamakon haƙurin da ta dinga yi nan Muktar ya ƙare yai mata saki biyu tare da yi mata korar kare."
"Danƙari sunan kare a lahira. Lallai Hadiza kinga duniya, duniya ta ganki. Amman in kina da kuɗi wallahi kafin ki kammala iddarki Muktar zai zo bikonki, kuma daga shi har kishiyar taki sai kin jasu a ƙasa, kin riƙo kuɗi ko?" Da sauri Hadiza ta ce ma Mabaruka.
"Na riƙo kuɗi Mabaruka Gonata na siyar na riƙo kuɗin, bani da wani buri daya wuce in koma gidana, badan komai ba, sai dan sabida yarana. Wallahi baku ganni ba, a cikin ƙannena mata nake kwana, banda ikon ince su yi mun wani abun, sai sui mun rashin kunya. Mama ko gaisuwata bata amsawa, duk aikin gidanmu ni ke yinshi, sati na ɗaya a gidan, inna jima ya zaman zai kaya kenan?" Mabaruka ta saka dariya tace.
"Uhm ki kwantar da hankalinki, ƙila gobennan kiga Muktar yazo har ƙofar gidanku zai tafi dake. Ƙawata Ƴar sanda ya labari ne. Ni na ganki wani kwasha_ kwasha ne?"
Hmmm Mabaruka ba doke ki ganni a haka ba. Ai a cikin garari nake, Bulama ya rasa aikinshi, ga bashin million goma da banki ke binshi. Sati biyu kacal suka bashi ko ya dawo musu da ƙuɗaɗe su, ko su zo suima kadarorinshi gwanjo su cire kuɗaɗensu. Wallahi jiya ban rintsa ba, ina zan shiga a garinnan, ina zan saka kaina? Gashi zinaran dana mallaka duk na kaɗar dasu a neman biyan buƙata. Danma dai buƙatar ta biya shine. Nace Mabaruka ko wannan halin da muka shiga shine abunda boka yake nufin zai biyo baya ne?" MABARUKA ta shiga salati tana tattafa hannayenta tace.
"Kinsan ni kaina irin hakan sai da ta faru dani. Amman gashi yanzu komai yana warwarewa, dan yanzu haka Adam abubbuwa sun warware mishi, sabon gida ma zamu koma sati mai zuwa. Amman bayan naje wajan boka da wata guda, duk wani tattalin arzikinmu sai da ya rushe, har sai da ta kai, nike ciyar da Adam. Na sayar da ƴar motar tawa, kayan ɗakina kansu sai da na siyar, hatta zanen ɗaurawa sai da yaso gagarata fa. Rufin asirin da muka samu, shine gidanmu da muke ciki. Zubaina haka aikin bokannan yake, amman komai zai dawo daidai" Kaina na kama wanda yake yi mun ciwo kamar zai tarwatse nace.
Taya zan soma rayuwa a gidan haya a garinnan namu Mabaruka? Mutane da dama idanu suka baza suna jiran faɗuwarka, nifa wallahi a cikin ɗimuwa nake, gaskiya talauci fa masifa ne"
"Zubaina ashe baki shirya neman duniya ba? Ke meye naki dan Bulama ya rasa aikinshi, ke da kike jan albashi sama da dubu ɗari, duk abinda kikeson yi, ko son ci ai zaki ci ma ranki. Shine a wahale shi da waccen jakar da masu dattin baki suka aura mishi." Ajjiyar zuchiya na sauke nace mata.
Kuma hakane Mabaruka, ni da in zauna takaicin ɗa namiji da kishiya ya haifarmun da hawan jini da hau, gara Bulama ya mutu ma baki ɗaya Wallahi. Kinga yanzu ne zanyi mulkina ma sosai. Ni damuwata bakin mutanene dama." Mabaruka tai ta ƙarfafani, har sai da ta samamun nutsuwa. Tare muka fito dasu, a tashar kawo na sauke su, zata raka Hadiza Jos wajan boka. Tuƙi nake yi, amman sai tunani nake ta fama dashi, zuchiyata sai aukin saƙe saƙe take yi mun iri daban daban, duk da na kasa samun matsayar tunanina, abu ɗaya na sani shine, ina yima BULAMA so mara musaltuwa, Amman zan iya bin ko wacce hanya ce dan ganin ni kaɗai na mallakeshi.
Kayi haƙuri Bulama, sonka da ƙaunarka ne ya ja mun tsananin kishinka. Da in rayu da takaicin kishiya da iyayen miji na gwammaci ka mutu kowa ya rasa.
Note: mata muji tsoron Allah akan kishin da zai rabamu da Ubangijinmu, kishin da zai kaimu ga halaka. Wannan rayuwa da mai tayi kama. Wai mai muka ɗauki kalmar kishi, da kishiya ne? Muji tsorom Allah mu dinga tunawa za'a mutu kuma akwai hisabi a tsakankanin junanmu"




Yahanasu:
Wayata na jawo na kira Hajja Fati, bayan mun gama gaggaisawa nace.
Hajja Fati a ina zan samu wannan maganin da kika bani ne? Ya ƙare har na siyo maganin tari na yara, amman banji daɗinshi kamar yadda naji daɗin naki ƙwayoyinba. Su kaɗai nake sha in samu lafiyayyen bacci, ni gani nake yi ko a haka aka auna jikina ya haura sosai, Hajja Fati ina cikin wata iriyar rayuwa mai wuyar fassarawa gaskiya."
"Haba Yahanasu kar kiyi sake ciwo ya kamaki a banza da wofi. Maganin dana baki yana da wuyar samu zancan gaskiya kenan, dan ba'a samunshi a kemis, nima wani yaron unguwarmu ne yake siyomun ya kawo mun a ɓoye. Da zaki fita haka kiga wani ɗan shaye shaye sai ki tareshi ki faɗa mishi sunan maganin, sai ya faɗa miki inda ake siyarwa. Wai babu wani abu daya shiga tsakaninku ne da Bulama, kamar hoto haka yake kallonki?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Kallo ma ai ban isheshi ba. Ga fishin da su Ba Bakura suke yi dashi, abun ni duk yabi ya dameni Hajja Fati. Amman zaman gidannan ya isheni, wallahi da badan furucin da Ba Modu yayi akaina ba, da sun wayi gari sun nemeni sun rasa na shiga duniya. Jina nake yi kamar a cikin kurkuku nake wallahi Hajja Fati, kullum zuchiyata a cikin damuwa take." Hajja Fati tace.
"Zancan ki shiga duniya ma bai taso ba Yahanasu, nasara tana cikin biyayyar iyaye, kiyi haƙuri wata rana kece da riba babba. Ni dai shawarata shine ki dinga shan magungunanki, kina ɗebema kanki kewa, kar ki sake damuwa ta haifar miki da matsala. Ki nemama kanki mafita, karki bari iyayenki suga gazawarki" Jikina a saɓule mu kai sallama da Hajja Fati bayan ta faɗamun sunayen kayayyakin maye kala kusan uku, da kuma yadda zanyi amfani dasu. A zahirin gaskiya banso na jefa kaina a wannan rayuwar ta shaye _shaye ba, amman wani gefen na zuchiyata yana kuma ingizani kan cewar in sha kawai, in samu sassauci. Daga lokacin da na soma ta'amali da magungunan maye, daga lokacin na samu nutsuwar zuchiya, kuma a lokacin zuchiyata ta dena raya mun in kashe kaina, wannan firgicin da takurewa waje ɗaya ne ban dena ba , tun daga sanda wannan al'amari ya faru dani kawo iyanzu. Ga wahalhalu da wulaƙanci da nake fuskanta a wajan Bulama da matarshi. Hijabina na zara na fice a gidan, dan burina shine in samo wannan ƙwayoyin in haɗiya ko zan ji sanyi, jikina har wani rawa_rawa yake yi, yayinda zuchiyata take sake ingizani. Sai gani ina neman lunguna, domun nasan sune matattarar ɓata gari. Cikin sa'a na ɓulla wani lungu, duk da zuchiyata sai da ta tsinke, abunda ya faru dani ya shiga dawo mun, amman ganin wata mace mai hijabi harda niƙab a cikin kangon, hakan sai ya ƙarfafa mun guiwata, a can gefe na tsaya, wani ɗan matashi da bai wuce shekara sha takwas ba ya leƙo yace.
"Yane Hajiya dame _dame za'a haɗo miki, akwai turaren wuta, akwai maggi, muna da macline, sannan kuma muna da fanta, akwai laka." Nan ya dinga jero mun kayayyakin maye, da irin adon maganar da bazan iya fassarawa ba, kasancewata ba Bahaushiya ba. A ɗarare na jero mishi wanda Hajja Fati ta faɗa mun sunayensu. Ni dai ina daga gefe ya koma kangonnan, wannan matar mai niƙab kuma sai ƙirga mata wasu magungunan kwalba akeyi a cikin wata ƙatuwar kula, da wasu magunguna a cikin takaddu, da gani dila ce ita kam. Wannan saurayinne ya dawo ya miƙo mun kayana a leda yace
"Nera dubu uku kuɗinki Hajiya. Mu na nan, nan itace majalisarmu, duk sanda kike buƙatar ƙiri kawai ki antayo zaki taddamu CE
masarautarmu cau cau Hajiya, a lafiya dai mata yanzu fa kuna wuta wallahi. Ni dai da sauri na karɓi ledar na cunkusa a cikin jakata, na bashi kuɗinshi, na fice da sauri a lungun ina waige. Zuchiyata sai harbawa take yi, inajin babu daɗi a jikina, nasan ba irin tarbiyyar da iyayenmu suka ɗauramu akai ba kenan. Nayi imani da Ba Modu zai san halin da nake ciki, babu abunda zai hana shi ya tsine mun albarka. Haka Ya Innana nasan saɓule hannayenta zata yi a kaina, ta sallamama duniya ni. Da wannan tunanin na koma gida, jigum nayi akan kujera ina tunanin, anya wannan hanyar zata ɓulle dani kuwa? Yayin da sheɗan shi kuma ya dinga buga mun ganga. Magungunan na harhaɗa na watsa a bakina na bisu da ruwa, hawayen daya zubo a kumatuna na share, ina cike da ɗunbun nadamar abunda na aikata."
MRS BUKHARI CE
MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI ( B4B)
14




*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.






















Wayata

18 / 67