MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   59 / 67

174K to 177K   out of 198.3K words

na miƙa mishi ya dailing number Ba Modu. Ringing biyu ya ɗauki wayar, bayan sun gaisa da Ahmad sai Ahmad yai mishi bayanin halin duk da ake ciki. Murmushinshi yayi yace.
"Ka bani Bulama Babban in yi mishi magana" Ahmad ya miƙo mun wayar dukkan illahirin bakina rawa yake yi, ina ji Ba Modu yana kiran sunana amman na kasa amsawa.
"Bulama Babba iyaye girma ne dasu. Ni bazan so kaina in hana ka bin umarnin mahaifiyarka ba. Tunda har tayi wannan furucin to ya fa zama dole ka saki Yahanasu domun ɗorewar farin cikinta, da dorewar zumunci. Ni kaina matakin da nake faɗa ma Hajja zan ɗauka kenan a kan aurenku. Akwai abubbuwa masu tarin yawa da Hajja Gana ta riƙe ya zame mata hujjar raba ka da Yahanasu. Kabi umarnin mu ka saki Yahanasu nima na baka wannan umarnin kar ka kuskura ka kuskure a bisa umarninnan dana baka. Kar ka bari akan mata ka dinga saɓawa da iyayenka. Bawa da kake gani baya wuce ƙaddararshi, ƙila dama Allah ya haɗa aurenka da Yahanasu ne na tsawon wani lokaci ba mai yawa ba. In kuma akwai rabon ku sake gudanar da rayuwa a gaba sai kaga daga baya an sasanta. BaKura ya barmun wasiyya masu nauyi a kan zumunci. Kuma yace ko bayan ranshi kar a raba aurenka da na Yahanasu kamar yana duba yasan wannan rikicin zai afku bayan ƙasa ta rufe idanunshi. Amman mahaifiyarka a yanzu zata iya maka baki rayuwarka taƙi yin albarka. Bakura shi kuma baice bai yafe maka in ka rabu da Yahanasu ba. Ka rubuto takaddar saki a rubuce gobe ka kamo hanya ka kawo mata takaddar irin umarnin data baka. Mu muna hanyar Zuwa ɗakko Yahanasu ne zamu dawo da'ita gida mu ci gaba da bata dukkan kulawa." Ƙit ya datse wayarshi. Kaina yaci gaba da jujjuyawa ina jin kamar numfashina na fusga. Haki nake yi tamkar mace mai ɗauke da juna. Bansan hawaye na zuba daga guraben idanuna ba sam. Ciwon da kaina yake yi baya musaltuwa. Allah shine shaidata akan kuɗirin ba Yahanasu farin ciki da nayi a rayuwata. Allah nake roƙo ya kawo mun mafitar dukkan abunda zai zama shine mafi alkairi a gare mu baki ɗaya. Alwala na ɗauro na dawo na ɗauki Qur'ani na soma karantawa. Ahmad yana zaune jikinshi a matuƙar mace sosai. Ni kuwa a hankali na soma dawowa dai_ dai. Kiran sallar magriba ne yasa na dakatar da karatun na ɗaga hannu na dinga ragargazo adda'a kafin kuma na miƙe naje na ɗauro alwala na samu Ahmad a zaune.
Mu je masallaci Ahmad." Idanu ya zuba mun yana karantar yanayina. Murmushi nayi mishi nace
Kar ka damu Ahmad khairan in sha Allah" Fita mu ka yi tare, ina ganin kiran wayar ƴan ɗakinmu. Su Gunsum ne, amman ban samu zarafin ɗaga wayoyinsu ba."








Yahanasu:
Ina zaune a ɗakinmu muna taɓa hira, kewar gida da kewar mijina kwana biyunnan duk ta isheni. Malama Fahiƙa ce ta shigo da sallama. Muna ganinta muka shiga cuccurewa a waje guda, kowa na kakkare jikinshi, jikkunanmu duk a farfashe sabida tsabaragen duka. Wata tsawa ta daka mana duk muka nutsu.
"Ku rufa ma mutane baki. Wani ne yasa ku shan abunda zai gusar muku da hankali har a kawo ku nan? Ƴan cin uwa. Ke Yahanasu ki shirya ki mayar da kayanki na gida suna durowa, iyayenki suna cikin gidan malam Rilwanu sun zo tafiya dake" bansan sanda nayi sujudur shukur ba, tsabar farin cikin dana tsinci kaina a ciki. Ina dingishi na miƙe zuwa bakin lokar ɗakin, na buɗe lokar na ciro rigata na nufi ban ɗakin ɗakin namu na mayar da rigar tawa, sururu nayi a cikin rigar tamkar rigar aro. A hanzarce na fito bakina yaƙi rufuwa. Muna kuka nayi sallama da su maman Amira, akan in Allah ya yarda zan kawo musu ziyara har garuwawansu tunda muna da adireshin juna. Kuma wa'adin zaman gidan nasu ya kusan zuwa ƙarshe. Cikin ɗakinmu babu wacce hankalinta bai dawo dai_dai ba. Malama Fahiƙa ta tusani a gaba zuwa gidan malam Rilwanu. Ina tafe ina ɗingisa ƙafata, ciwo ne babba a cinyata wanda malama Fahiƙa ta ji mun shi sati guda kenan. Muna shiga cikin gidan na tarad da Ya Innana a tsakar gidan tana gabatar da alwala. A guje na isa gabanta ina zubar da hawaye. Ƙirjinta ta dafe tana kallona.
"Hukunci sai mai tsaga ido. Yahanasu kece kika zama haka? Innalillahiwainnailaihilrajiun." Durƙushewa nayi a gabanta ina kuka. Tasa hannu ta ɗagoni. Tana share mun hawayena.
"Dena kuka Yahanasu ya isa haka" hannuna ta ja muka shiga ɗakin da aka saukesu. Matan gidan ƙila sun saba da ganin irin wannan lamarinne dan naga su ko a jikinsu. Zaunar dani Ya Innana tayi tace.
"Bari in yi Sallah kafin su Babanku su fito masallaci zasu wuce cikin Katsina ne a can zamu kwana washe gari kuma mu ɗau hanya." Ina zaune ina kuka har ta idar da sallar.
"Ki fita ki yo alwala ki zo kiyi sallar kema" Miƙewa nayi ba musu na fice ina dingishi. Ban jima ba na shigo ɗakin da sallama. Lafayarta ta warware ta keta ta gida biyu. Ta miƙo mun rabin tace.
"Yafa kiyi Sallah" Yafawa nayi ina sallah ina kuka a haka na idar. Ina sallamewa matar malam Rilwanu ta yo sallama a dokin ƙofa.
"Hajiya me gidan yana jiranku a waje, wai ku fito ku tafi. Nace ma ku dakata kuci tuwon gero, amman yace sauri kuke yi. Ya Innana tace.
"Wallahi mun gode Allah ya saka da Alkhairi." Miƙewa mu ka yi, muna tafe matan malam Rilwanu suna yi mana Allah ya tsare hanya, har muka fice. Mota muka shiga, Ba Modu dake gaban mota ya juyo muka haɗa idanu. Sai hawaye shar_shar ya gangaro a idanuna. Shima shiru yayi yana Kallona, hankalinshi a mugun tashe ainun.
"Uwata kece kika zama haka? Allahu Akbar" Shiru yayi ya ƙura mun idanunshi, ni kuma sai kuka nake yi. Wakil yace.
"Ki dena kukan kar ki jangwaloma kanki wani ciwon mana" Ba Modu yace.
"Wakil tuka muje gidan Alh Shitu can anguwar alƙali maza. Na kirashi ma suna tsumayar zuwan namu." Jingina nayi a kujerar motar, ina jin wani tsantsar farin ciki. Tafiya mai tsayi muka yi kafin na ganmu a wellcome to katsina anguwar Ɗanɗagoro. Tiryan_tiryan sai ga mu a anguwar alƙali mun iso gidan Alh Shitu abokin Ba Modu da su ka yi jami'a tare. A harabar gidan muka samu iyalan gidan suna jiran isowarmu. Wakil ya parka mota a wajan ajjiye motoci. Ya Innana tace.
"Ki sakko a hankali naga kina ɗingishi, ciwo kika ji ne?" Kai na girgiza mata halamar a'a ba ciwo bane.
"Hmmmm" kawai tace dani. Na fito a motar a hankali. Su Ba Modu har sun isa wajan su Alh Shitu. Can muka samesu
"Hajiya Innana zumunci ya yanke, saduwa tayi wuya" Wata farar mace ce ke magana da fara'arta har tana ɗan rungumar Ya Innana.
"Ke dai Hajiya Kati ki bari kawai. Hidindimu sunyi yawa, girma na ta hawa kanmu. Alh Shitu barka da dare" Cikin fara a ya amsa ma Ya Innana. Nima da ladabi na bisu na gaishesu, kafin daga bisani muka shiga zuwa babban falon gidan. Nan muka zazzauna su Ba Modu suka ɓalle da hirar yaushe gamo.
"Muje masallaci Modu, Wakil taso muje" Cewar Alh Shitu kenan. Masallaci suka nufa. Mu kuma Hajiya Kati ta shige damu haɗaɗɗen uwar ɗakinta.
"Hajiya Innana ga ɗaki ga ɓan ɗaki kuyi sallah kafin su dawo sai muci abinci. Har zata fita Ya Innana tace.
"Dan Allah Hajiya Kati Kaya nake so ki bani Yahanasu zata yi wanka sai ta sake na jikinta." Sai lokacin Hajiya Kati tace.
"Amman yarinyar nan jinya tayi ko? Ni naga duk ta zabge, ba ita bace wannan ƴar lukutar ba?"
"Itace fa. Jinya tayi na sama da wata biyar. Yanzu haka daga gidan magani muka ɗakkota, shi yasa nake son ta gasa jikinta ko zata ji daɗin jikin." Kai ta girgiza ma Ya Innana tace.
"Hmm Allah ya bata lafiya. Ta shiga tayo wankan bari in kawo mata kayan ummina zai yi mata, ummi na haka take ba auki" Tana faɗar haka ta wuce. Ya Innana tace.
"Bari in yo alwala sai ki shiga ki gargasa jikin naki ko?"
To" Shine abunda nace mata. Ina tsaye har Ya Innana ta fito. Ban ɗakin na shiga na soma taran ruwan zafi a bokiti. Wanka nayi da sabulun ruwa mai ƙamshi, jikina duk ciwuka wani wajan ma bana iya wankewa, dan ciwon yayi ɓawo ɓawo. Shampoo na zuba a kaina na wanke tas, kitson kaina bai wani sha jiki ba. Dan ana mana kitso duk bayan wata. Alwala na ɗauro na fito ɗaure da mayafin lafayar Ya Innana. Iska da ni'ima na shigata ta ko wanne gaɓa. Hamdala nayi a zuchiyata. Ina jina tamkar baiwar da iyayen gijinta suka ƴantata, baka sanin kana cikin ni'ima sai ni'imar da kake ciki ta kufce ma a hannunka. Ko maƙiyina bana mishi fatan ya faɗa ƙangin shaye_shaye. Hajja Fati da Binta ƙawata ne suka faɗo mun a zuchiya, harma da gidan magajiya mai kodin.




MRS BUKHARI CE
[19/08, 9:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 54
















Numfashi na ja, na koma bayan gida na saka kayan, rigar ta ɗanyi mun yawa kaɗan, zani ne da riga, zanin na ɗaura na fito ina ɗaurin ɗan kwalin nawa.
"Zo maza kiyi sallah Yahanasuna" murmushin jin daɗi ne ya subuce mun, na saka hijabin da Hajiya Kati ta ajjiye saman kayan, da ganin mahaɗin atamfar ne. Sallah na tayar. Har na idar Ya Innana sai adda'a take ragargazowa. Ni kuma ina gefe ina jan carbi. Da aka yi kiran sallar isha, muka tashi muka gabatar da sallar isha. Hajiya Kati ce taa leƙo.
"Hajiya Innana bismilla kuzo mu ci abinci, Alh Modu sun shigo. Ya Innana na gaba ina biye da'ita a baya har zuwa falon gidan. Akan daining muka tarar dasu. Nan aka shiga sake sabuwar gaisuwa. Cikin ladabi na gaishe da wasu maza wanda da gani babu tambaya ƴan biyu ne. Dan tsananin kamar da su kai da juna. Abinci muka shiga ɗiba, kowa na ɗibar wanda zai ishi tumbinshi. Dashishi ne da miyar ganye. Dashishi abincin katsinawa ne, wanda akeyi da ɓarjajjiyar alkama, anacinshi da miyar taushe, ko mai kabewa ko mai gyaɗa.
"Alh Modu Yahanasu ciwo tayi sosai ko? Ko ba ita bace wannan ƴar lukutar dana sani ba?" Cewar Alh Shitu. Ba Modu yace.
"Itace ka ganta. Jinya tayi ta tsawon sama da wata shida ma. Kaga duk ta zuge ko? Ciwo babu daɗi" Kafin Alh Shitu ya tambayeshi ciwon me nayi yayi saurin kawar da zancan ta hanyar tambayarshi.
"Niko Alh Shitu ina Ɗan Filato yake ne, yana katsinannan taku kuwa?" Dariya yayi yace.
"Ina yana Dubai shi da iyalan nashi dukka. Yana aiki a ƙarƙashin wani kamfanin sutura. In ga ganshi a katsina sai dai ziyara. Kwanakin baya dai da mu kai waya yake mun magana akan yana son su zo shi da iyalan. Kuma kafin su koma yana son yayi ƙarin aure, ya gaji da zaman Dubai ɗin. Kasan katsinawa da son mata hudu. Nima shashatau Hajiya Kati tayi mun fa" Dariya suka kwashe dashi. Mu kuwa kowa ya mayar da hankali ne akan cin abincinshi. Bayan mun kammala kuma, aka raka mu ɗakunan da zamu yi bacci. Ni ɗakin da aka kaini ba kowa a ciki, da halama ni kaɗai zan kwana. Ina kwance ina cikin murna da zabarin ganin gobe. Babu wanda idanuna ke son yin tozali dashi sama da Bulamana. Naso in tambayi Ya Innana dalilin rashin biyosu da bai yi ba. Amman ina jin kunya da tsoron kar suga nayi rashin kawaici. Murmushi nayi tare da lumshe idanuna ina tuno gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye shaye. Gidan ukuba da azaba. Bazance ire iren gidajen basu da amfani ba. Domun na samu lafiya ta dalilin gidan. Da dama an kawosu cikin hauka tuburan, kuma sun samu lafiya. Saƙona ga irin wannan gidajen shine. Su ji tsoron Allah, su sani mu ma ƴaƴane, kuma babu wanda yafi ƙarfin faɗawa irin halin da muka riske kawunanmu a baya. Kuma su sa tausayi cikin lamuransu. Daga ƙarshe ina godiya a garesu bisa kulawa da lafiyar ƙwaƙwalwata da su ka yi. Ta hanyar bani rubutu, da ƙwayoyin bature, da koyar damu sana'a domun dogaro da kai. Da tunanuka masu dama bacci yayi awon gaba dani.


WASHE GARI:
sassafe muka kamo hanyar Damaturu, dan ko karyawa bamu tsaya mun yi ba, sai dai Hajiya Kati tasa masu aiki su kai mana abincin karin mota, tace ko a hanya maci. A cikin motar ma bacci na dinga yi sosai, domun ba samu lafiyayyen bacci mu ke yi ba sam. Misalin ƙarfe biyun rana muka shiga Damaturu. Kai tsaye babban asibiti Ba Modu yasa muka wuce. Ni dai har muka shiga ɗakin ganin likita gabana bai bar faɗuwa ba. Wajan Likitan ƙwaƙwalwa Ba Modu ya kawo ni domun a duba lafiyar ƙwaƙwalwata. Alhamdulillah kyakykyawan labarin sa farin ciki. Shine lafiyar ƙwaƙwalwata ras, sai dai zazzaɓi cizon sauro, da tiyfot da nake fama dashi, sai kuma raunuka da suka samu a jikina. Ya rubuta magunguna, Ba Modu yai mishi godiya muka fito, nan muka nufi gida."




Bulama Babba:
Bamu muka shigo gidan ba, sai da mu ka yi sallar isha tukunna. Sukuku haka nake tafiya kamar zakaran daya taka wuƙa. Ahmad kuwa ya kasa tafiya ɓarayinshi. Abinci ya tusa ni a gaba, sai da ya tilasta ni, na ɗan tsakura na sha ruwa. Gunsum ne ya kira wayata, naga kirare_kirayen ƴan Damaturu da yawa, naƙi fur in ɗaga wayar kowa. Ahmad ne ya ɗaga wayar Gunsum.
"Gunsum yaya akayi, kana lafiya?"
"Yaya Ahmad lafiya lau, tun ɗazu inata kiran wayar Bulama Babba baya ɗauka, na gwada taka kuma a kashe take."
"E hakane wayata tana kashe tun safe ma. Yaya akayine?" Gunsum yace da Ahmad.
"Hajja ce ba lafiya, muna shirye_shiryen kaita asibiti ne ma yanzu haka. Muna ta kiran wayar Ba Modu bata shiga wayar, Wakil ma wayarshi tana gida bai tafi da'ita ba. Kuma Hajja sai ambaton sunan Bulama Babba take yi. Wai ya kawo mata takadda, mu bamu san wacce takadda bace, shine nace bari in kira in sanar mishi." Duk tattaunawarnan ina ji dan Ahmad ya ƙara ƙarfin jin magana. Numfashi naja kafin nace.
Gunsum ka kwantar mata da hankali, zan kawo mata takaddar, in jikin ba mugun tsanani yayi ba ku jira zuwan Ba Modu tukunna. Ya je Katsina ne. Da sassafe zan tawo, duk abinda ake ciki ka tabbatar kana sanar mun." Wayar Ahmad ya katse. Ni dashi an rasa me cewa komai, muna zaune har sha ɗayan dare. Da ƙyar na roƙi Ahmad ya tafi wajan iyalinshi. Kan sallaya na hau na dinga karatun Qur'ani babu ƙaƙƙautawa shine kaɗai ke saukar da sanyi da salama a ƙirjina. Misalin biyun dare kuma na shiga raya daren da nafilfili, ina roƙon Allah ya kawo mun ɗauki. Sai wajan huɗun asuba na samu na runtsa. Ana assalatu na miƙe. Wanka nayi na goge bakina, na ɗauro alwala. Na nufi masallaci. Ban fito a masallaci ba sai da rana ta fito, nayi nafila ra'aka biyu, nayi azkhar. Sannan muka fito ni da Ahmad.
"Yaya jikin Hajja?"
Jikin da sauƙi dama ciwon na ƙiyaryar Yahanasu ne, kuma na ba Gunsum saƙon zan kawo takaddar yau in sha Allah. To tunda ya faɗa mata jikin nata yayi sauƙi,munyi waya da Gunsum cikin dare sau biyu. Babu wata matsala. Yanzu inason in kama hanyar Damaturu, kafin nan zan je wajan Mama Gana mu tattauna tukunna." Ahmad jikinshi ya mace mus.
"Hmmm Allah yasa mu dace, Allah yasa rabuwar itace mafi alheri a gareku baki ɗaya. Allah ya hadaku da madadin alkhairi. Nima wanka zanyi in zan wuce office sai in kai yaran makaranta. Su basu san a gidan ka kwana ba ma" Da haka mu kai sallama da Ahmad kan cewar sai na dawo, kowa ya nufi ɓarayinshi. Takadda da biro na ɗauka, gabana sai dokawa yake yi da ƙarfi, rubutu nayi da bai wuce layi uku ba, na nannaɗe takaddar nasa a ajjihun rigata. Na kulle ko ina, na shiga mota na fice a gidan. Gidan Mama Gana dana so zuwa ma, fasawa nayi, hanyar Damaturu kawai na nufa abuna. Tafiya kawai nake sukuku kamar bazan kai ba. Tunani da tausayin halin da Yahanasu zata tsinci kanta a gaba yafi koma azalzalar zuchiyata. Ina gudun kar in jefa kaina a rijiya gaba dubu, da badan haka ba babu wanda ya isa ya sa in saki matata, na sani komai zai iya faruwa dani in har na rasa Yahanasu, domun ta gina zuchiyata ta ƙarfafa jijiyoyin jinina da soyayya zalla mara algus..... Ƙiiiiiii naji wani abu ya tokare ni, a dai_ dai wani ɗan gauye dake gefen titi, da dukkan halama kasuwar ƙauyen yau take ci. A guje na fito na kukkutsa tsakiyar mutanen da suka rufe abunda na bige.
Wani dattijone a kwance ƙafarshi na fitar da jini. Kaina na dafe inaji tamkar zuchiyata zata faɗo.
Subhanallaah sannu Baba. Dan Allah kayi haƙuri Baba tsautsayine" Nan fa jama'ar da suka zo kasuwar ƙauyaa nan suka nemi su dake ni, sabida tsabaragen rashin hakuri, gidadanci, da rashin ilmi. Sai wannan tsohonne yace.
"Ku dakata kar wanda ya doke shi." Shine fa Allah ya kwace ni.
"Naci sa'a ma daya bige ni ya tsaya. Da wani marar imanin aka samu, sai dai ya ari na kare ai. Yaro kaini kemis a wanke mun, su ɗan bani magani, domun bani da ko sisi da cewa zanyi kayi tafiyarka." Jikina a mace nace.
To Baba zaka iya tashi ko in ɗaukeka? Ku kuma wani yai mun jagora zuwa kemis ɗin da za'a duba shi" Baba tsoho yace bazai iya tashi ba, dan yaji rauni sosai. Wasu samari biyu ne suka taimaka mun muka sa Baba a mota. Suma suka

59 / 67