Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
alin"
Million goma fa kace? Na shiga ukuna ni Zubaina, Bulama an aura maka mace mai farar ƙafa daga shigowarta cikin rayuwarmu, harta salwantar mana da dukiyarmu da aikin naka ma. Yanzu me muke dashi da zamu biya wannan uban kuɗaɗen? Gashi shagon abayoyin naka, wannan karon ba'a zuba komai a ciki ba. Sai ƴan tsirarun kayan da baza su wuce million ɗaya da wani abun ba" Ina kaiwa ƙarshen maganar na fashe da wani irin kukan baƙin ciki da takaici. Hankalina ya tashi iyakar tashi. Bulama ya kasa rarrashina, dan shi zazzaɓine ma ya rufe shi. A daddafe mu kai sallah, abinci a wannan daren ya gagari bakunan mu. Anayin sallar isha. Bulama yai mun sallama zai je ya kwanta, dan a ɗakin Yahanasu yake yau.
"Zanje in kwanta, zazzaɓi ke damuna sosai, bakina ɗaci yake yi sosai kuma" A ranar nayi_nayi da Bulama yaci abinci yaƙi. Haka ya fice yana tangaɗi. Yana fita Mama ta kira ni a waya.
"Hello Zubaina Sagiru ne ba lafiya muna babban asibiti an bamu gado" Cikin damuwa nace.
Meke damunshi kuma? Mama tace.
"Faɗa su kayi, suka sossoki junansu, yanzu haka shi Sagirun cikinshi a farke yake. Tiyata ma za'a shigar dashi yanzu, muna cikin tashin hankali. Sai da muka ɗauko ƴan sanda sannan aka karɓeshi ma. A lokacin nayi ta kiran wayarki bata shiga." Jikina ya sake mutuwa murus a sanyaye nace.
Bari in taso Nafisa mu tawo, yanzu ke da waye a asibitin?. Tace.
"Ni da Rakiya ne, itama yanzu take son ta tafi, tara ta wuce"
To Mama gamu nan, ni kaina a cikin wani irin tashin hankali muke yau a gidan, wani babban al'amarine ya faru" Taso in sanar da'ita a waya amma ina abun yafi ƙarfin waya. Nan da nan na fito daga ɗaki na nufi ɗakin Nafisa. Chartting ɗinta na jaraba take yi. Yara kuma duk sunyi bacci.
Nafisa ki taso mu tafi asibiti. Sagiru ba lafiya, yaje ya jawo mana magana. Ki ɗauko Maryam, ni bari in ɗauki Bawa mu kaisu ɗakin waccan abar." Da sauri ta shirya muka fice. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Yahanasu nayi. Itace tazo ta buɗe mun ƙofar da halama daga bacci ta tashi. Tana buɗewa ta ganmu a tsaye.
Ki shiga ki kirawo mun Bulama inason in bashi yara ni zan fita" Juyawa kawai tayi.
Yahanasu:
Da sallama a bakina na tura ƙofar ɗakin Bulama Babba. Kakarin amanshi na dinga jiyowa daga cikin ban ɗakinshi. Tsaiwa nayi cak a bakin ƙofar ina jiran fitowarshi. A mugun galabaice ya fito da bi bango, a bakin gadonshi ya zauna. Ya kalleni da jajayen idanuwanshi yace.
"Yahanasu lafiya, akwai abunda kike buƙata ne?"
Dama Anty ce tace inyi kiranka, wai zata fita ne" Maimaitawa yayi.
"Zata fita kuma?" Ya girgiza kanshi, a hankali ya miƙe ya fita, na mara mishi baya. Ina fitowa na koma ɗakina, dan har bibbiyu nake gani, ga jiri da yake ɗibana, ko maganar da nayi da dabara nayi ta, dan harshena yayi mugun nauyi ainun, nasha maganin tari rabin kwalba. Ina faɗawa akan gado na sake lulawa duniyar bacci.
Bulama:
Ina buɗe ƙofa naci karo da Zubaina rungume da Bawa a hannunta. Na dubeta a tsanake nace.
Lafiya kuwa Zubaina na ganki da yara da daddarennan?" A sanyaye tace
"Zanje asibiti ne, Sagiru ba lafiya an basu gado, tiyata ma za'ayi mishi shine nake son zanje Mama ita kaɗaice a can ɗin. Ga yaran su zauna a wajanka ko?" Dubanta nayi jikina a mace, ina ganin kamar nafi Sagiru buƙatar kulawar Zubaina a cikin irin wannan yanayin da nake ciki, amman saita ɓige da haɗani da raino. Hannu nasa na ƙarbi Bawa a hannunta naje ɗaki na shinfiɗeshi, na dawo na karɓi Maryam itama.
Sai kun dawo, ku gaishe da mai jikin" Wucewa su kayi, suka barni ni kaɗai a tsaye a bakin ƙofar. Ɗaki na nufa a hankali na zauna tare da tusa yarana a gaba ina kallonsu cike da tausayin yaya makomar rayuwarsu zata kasance? Gashi duk abinda na tara banyi tunanin in zasu iya biya mun wannan kuɗin da ake bina ba. Wayata na zaro na soma kiran layin Ahmad, duk da nasan ranshi a ɓace yake dani, amman bai fiye fishi mai tsayi dani ba.
"Bulama kaine a cikin darennan kake kirana, inji dai lafiya ko?" Kai na girgiza nace.
Kaiya Ahmad lafiyarnan babu ita a gaskiya, dan yanzu haka maganar nan da nake yi maka zazzaɓine kau a jikina. Ahmad na rasa aikina a gaɓar da nafi buƙatar aikin, a gaɓar da iyalina suke buƙatar kulawata. Ba rashin aikin bane yafi girgizani ba, face bashin banki da naci ba tare da bin ƙa'idojin daya dace ba. Kai ka riga da kasan komai Ahmad. Million goma suke bina. Sati biyu kacal suka yanke mun, ko in biya ko su yi gwanjon dukkan kadarorina su haɗa kuɗaɗensu. Ahmad ina cikin tashin hankali, ina cikin tsaka mai wuya" Salati Ahmad ya saka cikin muryar damuwa yace.
"Million goma sha fa kace Bulama? Million goma kuɗaɗene masu yawan gaske, nasan kuma gidanka bazai wuce million huɗu ba tunda kayi mai gyare gyare, motarka data Zubaina duk ba zasu haure million biyar ba, tunda sun ɗan jima tashin hankali kenan wanda ba'a sa mishi rana. Yanzu kai wanne hukuncin ka yanke Bulama, ka sanar da su Ba Bakura halin da ake ciki?"
Ban sanar ma kowa ba, bana son kowa yasan halin da ake ciki. Amman kai kam ina buƙatarka a tare dani Ahmad"
"To Bulama matsalar itace kuɗin motar da zan zo wallahi bani dashi. Yanzu haka abunda za'aci a gidana da safe wallahi Bulama babu. A taƙaice Shayi da Buredi muka ci muka kwanta da daddarennan ma. Ni rayuwar Lagos ɗin ta isheni ta fice mun a kai, babu komai sai wahala kawai." Da mamaki nace.
Ina kasuwancin da Hajara take yi kuma, da zaku zauna da yunwa cikin taraddadin me gobe zata haifar?" Ɗan murmushin takaici yayi yace.
"Kuɗi sun rushe banda tarin tulin bashin data barni da biya, wasu ma sai yafewa su kayi. Wata matace ta haɗe kuɗaɗen nasu ta damfaresu, irin masu ƙaryar odar ɗinnan. Amman hukuma sunci nasarar cabketa, sai dai kuɗi kam babu, kotu ma aka turasu suke ta faman sunturi. Ni kam inaga tattarowa zanyi mu dawo Arewa kawai. Ko Kano sai in faɗa inci gaba da buga bugata kawai." Ajjiyar zuchiya na sauke. Na lula duniyar tunani. Duk arziki da muƙaman da Ahmad ya riƙe, yanzu duk sun zama tarihi. Ahmad ne yau bashi da abunda zaici da iyalanshi ma. Allah abun tsoro, duniya kuma zancen banza.
Babu komai Ahmad yanzu yaushe kake son ka tattaro ka dawo Arewan?" Yace.
"Kuɗin motar da zamu tawo kawai nake ta ƙwadagon haɗawa, kasan mu uku ne. Kuɗin motar mutum ɗaya ma, dubu goma ce a macapolo. Kaga dubu talatin ai ba nan kusa take ba."
Haba Ahmad yanzu kana cikin irin halinnan shine ba zaka mun magana ba?"
"Haba Bulama nauyin ai sai yayi ma yawa. Duka albashin naka nawa yake, ga iyalai? Ai babu komai wallahi" Ajjiyar zuchiya na sake saukewa nace.
Zan tura maka nera dubu hamsin, sai ku shirya tafiyar taku, tsakanin gobe zuwa jibi, duk sanda kuka tsayar shikenan. In yaso sai ku sauka anan gidana, mu tattauna yanda al'amura zasu kaya" Nan mukai ta tattaunawa, muna jajantama juna. Falo na dawo na zauna. Sai tunane tunane barkatai da sukaita zuwan mun kaina. Daga ƙarshe nayi alwala nayi sallah, tare da roƙon Allah akan Allah yasa hakan shine mafi alkairi a garemu. Tun daga wannan lokacin na dangana, wata nutsuwa, da dawowa cikin hayyacina ya sameni. Ɗaki na koma na yi kwanciyata"
Zubaina:
Da isarmu muka tarar Sagiru an shiga dashi ɗakin tiyata, jini malala a ɗakin da aka fita dashi. Mama sai hawaye take yi.
Mama ki dena yin kuka. Ai shi ya jama kanshi, kuma shine zai wahala. Irinsu ke tada rikici a cikin al'umma, wallahi ba da ban ke ba, babu abunda zai kawo ni asibitin, ɗan iskan banza da wofi, ɗan shaye_ shayen banza" Zage _zage na dinga yi ko zan ɗan samu sassauci a zuchiyata, dan gabaki ɗaya a cikin tashin hankali nake, ga ƙaramin ciki a jikina, wanda naita ɗokin dawowar Bulama domin in sanar dashi, dan na sanshi da son yara, Allah Allah nake yi gari ya waye in je wajan Mabaruka. A daren akaima Sagiru ɗinki, aka fito dashi ɗakin jinya. Kowa yayi shiru da abinda yake saƙawa, Goggo Rakiya ma ta kasa tafiya, haka muka kwana a zaune a kan tabarma, tare da masu jinyar ƴan uwansu. Ni damuwata ɗaya shine, a halin yanzu bani da komai ƴan gwala gwalan da nake dasu, su na haɗa na ƙunduma na kai kuɗin wajan boka. Sai ɗan fili guda ɗaya da nake dashi ina kan gini, yanzu shikenan abunda zan tsira dashi daga dukiyar Bulama? Kai ina ai sai ƙawayena suimun dariya, da gwalo duk ranar da suka ci karo dani ina daɓawa a ƙasa, zaman garinnan gagarata wallahi zaiyi. A cikin wannan tunane tunanen na kwana a zaune, banko iya runtsawa ba, ashe yin bacci ma samun wajene ke sa ayishi, ni inyi mana a daren yau, daren da yafi ko wanne dare muni da tsayi a wajena"
LAGOS:
Obhalande
Tunda Ahmad ya kashe wayarshi bayan sun kammala magana da Bulama. Sai ya miƙe zumbul ya goya hannayenshi biyu a baya, ya shiga aikin kai kawo a falonshi, yana jinjina lamarin ubangiji, haƙiƙa sunga ishara, kuma sun ɗauki darasin da nan gaba in sun samu aiki, zasu tsaya tsaiwar daka dan ganin sun riƙe wannan aikin da kyau sosai. Hajara ce ta farka, tayi juyi a katifarsu taji Ahmad baya kai. Tana buɗe idanu ta ganshi a tsaye yana ta faman sunturi"
"Abban Anisa lafiya da wannan tsohon daren amman kake tsaye?" Dubanta yayi tare da cewa.
"Ki shirya ke da Zulai gobe zamu bar garin Lagos in sha Allah. Zamu bi motar yamma" Da hanzari ta miƙe tace.
"Zamu koma Damaturu kenan kake nufi Ahmad, sai da komai namu ya galgance sannan zamu kwashi jiki mu koma ƙauye dan wulaƙanci?"
MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE
AKWAI FA TURARUKAN WUTA IRI IRI, DA HUMRORI MASU SIRRI SOSAI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN TURARA KAYA, TURAREN GASHI, TURAREN MOPPING, TURAREN TURARA JIKI DOMUN SAMUN DAUWAMAMMEN ƘAMSHI, ROOMFREESHNER. DUK WANI KAYAN ƘAMSHI MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI TA TANA DAR MUKU, KU TUNTUƁENI
08179523215 NAGODE DA KASANCEWA TARE DANI.
MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
13
*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*
Tsab Ahmad ya ƙarema Hajara kallo da kyau. Ya tuno a lungun daya haɗu da'ita tana tallen mangwaro, ya wanketa ya aureta, gidansu gidan talakawa futuk ko karatun boko ba'ayi, amman yau shi take faɗama wai Damaturu ƙauye ne."
"Ji Hajara yana da kyau ki iya bakinki, kinganni nan? Wallahi bazan taɓa zuba miki idanu kici gaba da rainani a cikin gidannan ba. Ohh sabida yanzu bani dashi ko, ashe ladabi da sinsin ɗin da kike mun da kai, duk ba dan Allah bane? Ni da ya dace ace a yanzu ne zan samu cikakkiyar kulawarki a gareni, amman a yanzune kike ɓullo mun da salo_ salon wulaƙanci, dama ance mata haka suke da yawansu, ku ci ku goge baki. Duk da akwai matan arziki marasa manta halacci. Nine shugaba a gidannan, umarni nake baki ku tattare duk abinda zaku tattare zamu tafi gobe" jikinta ya ɗanyi sanyi amman ba wani sosai ba, tace.
"Maganar zuwa kotu da muke yi akan ƴar damfarannan kuma fa yaya kake son nayi kuɗaɗena fa da yawa?" Harara ya zabga mata yace.
"Ke in ma zaki cire ranki akan yiwuwar fitowar kuɗaɗenku gara ki cire rai, kibi abinda nace miki kaina ciwo yake yi mun. Tsaki taja dogo ta koma kan yagalgalalliyar katifarta ta kwanta, sai mis_ mis take da baki irinna mata marasa kunya.
Washe gari kuwa tun safe Hajara ta soma fito da kayayyakin ɗakinta zuwa cikin tsakar gidansu. Gidane mai cike da ɗakuna falle falle ɗakuna sunfi ashirin. Da matan aure da zawarawa da karuwai, maza da mata, ƙabilu iri_ iri babu wanda gidan bai tara ba. Rayuwar kudu in ba ƙwaƙƙwaran sana'a gareka ba, ko wani muƙamin gwamnati, ko aikin kamfani ba. Ai wahalace kawai mai mugun girman gaske, ga tsadar rayuwa, uwa uba tsadar kuɗin haya. Duk kwaraɓewar gidan da su Hajara suke ciki nera dubu biyu da hamsin suke biya a duk shekara, ɗakine ƙarami ba babba ba, bayan gida a tsakar gida yake, girki kuwa sai dai ko wacce tayi a bakin ƙofarta. Zulai a ɗakin Maman Isa take kwana, kasancewar maman Isan bata da miji zaman kanta take yi. Amman sana'arta take yi, bama yarinya babbar macece. Hatsi tsada, kayan miya tsada, rayuwar kudu akwai tsanani sosai. Matan dake zaune a gidan duk suna sana'ar sai da abinci, kasancewar Obhalande anguwace data tara ƴan cirani na jihohin arewa da dama, anguwace da marasa ƙarfi su suka fi yawa, duk da masu kuɗin ma akwaisu, unguwar tana kallon barikin sojoji. hakan yasa sana'ar abinci take garawa. Hajara ma tana sai da kunun zaƙi ƙaramar gora nera ɗari, kuma ba ƙaramin ciniki take zubawa ba. Firjin nata sacewa akayi, shi yasa ma ta dena, wannan kenan "
Matan gidan ko wacce tana tsakar gida, masu kayan sana'a na safe suna ta ragargaza ciniki. Masu masa, da ƙosai, da kulele ( Alala) da kunu sai faman ciniki suke yi. Masu abincin rana kuma sunata haramar soma gyare gyaren kayan miyansu, yayin da wasu ke iza wuta. Haliman Lokoja ta tashi tsaye ƙugunta a riƙe a hannayenta tace.
"Me zan gani, yaji ko mutuwar aure Hajara da kike fito da kaya. In yaji ne sai ince miki kin gane hanya, in sakine ince miki zoki ɗau jar fulawa" Duk wannan maganar Haliman Lokoja tana yi tana yamutse mummunar fuskarta, wacce tasha kwalliya ta fito ɗoɗar take yi. Cikakkiyar karuwace mazauniya Lagos wacce ta fito yawon bariki, ta ƙare a karuwanci na ƙazanta, dan duk karuwan cikin Obhalande karuwaine, wanda mafiya akasarinsu ƴan cirani Arewa ke hutawa dasu da daddare, su ɗan basu wasu kuɗaɗen da basu taka kara sun karya ba. Hajara tace.
"Allah ya tsari gatarina da saran shuka, bana ga saki ba. Dan duk lalacewar masa tafi ƙarfin kashin shanu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta. Matan gida, ina mai shaida muku yau zamu bar garin Lagos da zama, zamu koma Arewa a yafemu." Daga nan bata sake cewa komai ba. Gidan ya kaure da hargowa, kowa na faɗar albarkacin bakinshi, da masu cewa karsu koma, gwamma suyi zamansu su kama sana'a sai masu cewa gara su koma Arewar ya fiye musu. Hajara dai bata da wani zaɓi face bin Ahmad a yanda yake so. Ala dole sukaima kowa sallama, suka nufi tasha da tilin tarin ƴan komatsansu, na amfanin yau da kullum. Misalin ƙarfe takwas motarsu ta ɗauki titi sai arewa. Da motar dare yaso su hau, amman da yaje siyan tikiti anan ya sake ra'ayi"
Kaduna:
Bulama:
Yau na wayi gari a cikin godiyar Allah, da dangana wanda hakan har yaso bani mamaki ainun. Ina dawowa daga sallar Asuba, nayi wanka na shirya tsab. Su Maryam kuwa sai sharara baccinsu suke yi, kasancewar yau asabar ne babu makaranta. Ɗakin Yahanasu na leƙa, bata ciki, sai da na fito tsakar gidan na ganta a gaban motata tana ta faman durzarta. Shiru nayi ina kallonta ina jin raina yana tafasa dana ganta. Ganinta ma bana ƙaunar yi. Ina cikin zaman zamana cikin farin ciki, iyayena da basa son ganin farin cikina sun auro mun mai farar ƙafa, daga zuwanta ta ruguza mun rayuwata. Da hanzari na isa wajan motar. Tana ganina ta soma kiciniyar gaisheni. Ni kuwa kallo wannan bata isheni ba, motata na shige naja na barta da moɗar ruwan da take kwarama motar. Ban zame ko inaba sai asibiti wajan su Zubaina. Da sallama na shiga ward ɗin da aka kwantar da Sagirun, bayan na kira wayar Zubaina tayi mun kwatance. Mama na ganina ta shiga washe baki tana mun gaisuwar ban girma. Hakan yana faranta raina ainun. Yanda Mama ta ɗaukeni tamkar ɗan cikinta, kuma take bani kulawa ta musamman. Zubaina kuma tana gefe ta zabga uban tagumi.
Mama ya mai jikin dai?" Mama tace.
"Toh gashi nan dai. Har yanzu bai farfaɗoba tukunna dai, amman muna sa rai zuwa anjima zai farka."
To Allah ya ƙara bashi lafiya, Zubaina a rakani ofishin likita, inji daga bakinshi, ko akwai wani abun da ake buƙata. Ina Nafisa fa?" Goggo Rakiya tace.
"Tatafi gida