MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   51 / 67

150K to 153K   out of 198.3K words

Kubra kike rabka salati haka sassafe?"
"Zubaina wannan yarinyar Rabi naƙuda take yi fa, domun duk halamun naƙuda sun baiyana a tattare da'ita, har faya ta fashe." A razane na dubeta inason yin magana Rashida ta fito tana rabka salati.
"Shikenan Rabi ta mutu ta huta da rayuwar cikin gidannan. A guje muka shige ɗakin da Rabi take kwance male_male a cikin jini. Duk wani mai tausayi in ya ga Rabi a cikin wannan halin sai ya zubar mata da hawaye. Muna cikin alhinin mutuwar Rabi Alh Liti ya buɗe labulen ɗakin da muke yace.
"Ohh sabida gidajen iyayenku babu arziki baku gajeshi ba, shine zaku yi mun almubazzaranci da dukiyata ko? To acikinku wacce ƴar iskarce ta bar kokko akan wuta yake ta amai?" Jin ya ambaci kokko na zuba jikina ya hau rawa, muryata ta shiga karkatsewa.
"Ba magana nake yi ba dan ubanku kunyi mun kunnen uwar shegu, ko sai na kawo hannu?" Jikina na rawa nace.
Nice Alh dama, Rabi ce Allah yayi mata rasuw....." Tas ya zabga mun mari lafiyayye ya tokareni da ƙafa na faɗi a gefen gadon ɗakin bakina ya daki katakon gadon. Take jini ya hau zuba daga bakina. Wani kuka gigitacce na saka domun zafin kau ya karaɗe jijiyoyin kaina ya dinga tartsatsi ta ciki.
"Zaki tashi kije ki sauke mun kokko a wuta ne ko saina illataki?" A guje na fice a ɗakin ina waiwaye. Ina ji yana tambayar garin yaya Rabi ta mutu, kuma ya ya ganta a cikin jini male_male. Bansan amsar da Hajiya Kubra ta bashi ba, hankalina na wajan sauke tukunyar kokkonnan. Ina saukewa na zubar da jinin daya cika mun bakina tab. Haƙorin ƙasan bakina na gefen dama ya biyo jinin. Ina ganin haƙorin a ƙasa kukana ya sake tsananta, bakina ya suntuma him, harshena na soka a wajan dan in tabbatar shin da gaske ne ko gizo ne. Sai naji wajan wawalo. Yau ni duniya ta juya ma baya, yau ni da nake juyawa ni ake juyawa, yau ni da nake wulaƙanta dangin mijina, yau ni miji yake wulaƙantawa harda arzikin duka da fasa baki, da cire haƙori? Duniya mai ido a tsakar ka. Duniya budurwar wawa, duniya zancan banza. Bani na samu kaina ba sai dare, kafin daren fuskata ta kumbura tayi suntum, dan ko shagalin bikin Amaryar Alh ban samu damar fita zuwa ƙofar gida inda akeyin bikin ba. Zazzaɓi da ciwon baki ya far mun. Inda haƙorinnan ya fice har numfashi yake yi mun tsabaragen azaba. Washe gari muka rankaya zuwa ɓarayin Alh Liti. Yaranmu da manyanmu, mata da ƴaƴa. Harda magidantan yaranshi dake zaune da iyalansu a waje duk sun zo. Na lura suna mutunta wannan ranar ta ganawa, domun a ranar kowa ke da damar shigar da kokensu. Ni a ganina wannan ranar ta ganawa bata da wani amfani a wajena. Domun babu wani koke da Alh Liti ya taɓa saurara ya biya ma mai koken buƙatarshi. Da zage_zage yake korar kowa, wasu ma tashi yake ya mugun rufesu da mugun duka, ko ya bisu a guje, dan na fahimci baya jin nauyin jikinshi sam." Amaryar Alh Liti tana cikin ruɗun da tashin hankali ganin mun mamaye wawakeken falon Alh Liti, kuma yana gabatar damu a matsayin matanshi, bataliyar jama'ar data gani kuma ya gabatar mata a matsayin yaranshi. Amaryar Alh Liti mai suna Zarah tayi kuka harda birgima a falon Alh Liti. Sai daya daddaka mata tsawa ya miƙe kamar zai daketa. Ba shiri ta maƙale a bayana har tana riƙe mun hijabina. Sai da hankalin kowa ya nutsa, sannan aka soma gudanar da abunda ya taramu. Amman jiya dai i yau. Korar kare Alh Liti yai mana. Ba shiri Zarah ta miƙe da zummar binmu.
"Ke Kubra! Ki nuna mata akurkinta ta shiga na lura ta tsorata dani. Dokikin daya kamata ta sani na cikin gidan a sanar da'ita, ragowar aikin nawa ne." Cewar Alh Liti, yayi maganar ne cikin zolaya. Hajiya Kubra ta girgiza kai tace mishi.
"To shikenan. Amarya muje ko?" Amarya Zarah ta riga Hajiya Kubra ma fita. Ni kuwa ina tafe ina tsaki abun duniya duk yabi ya isheni. Gashi wannan laulayin cikin ya haifarmun da wani irin mugun kwaɗayi mara misaltuwa ji nake kamar in gutsiri hannuna dan masifa. Ina shiga ɗaki na soma laluben abunda zan iya ɗagawa in siyar, hatta ƴan zinarai na duk na kaɗar. Hatta ɗan karamin dana sako a kunnena nazo gidannan dashi, na kaɗar dashi kuɗin duk sun ƙare a asibiti lokacin da aka sake ɗora mun hannuna. Tagumi nayi ina zaune a ƙasa jigum. Ihu da bige_bigen Zarah na dinga jiyowa sama_sama. Baki na taɓe ina ƙara tsinema Alh Liti a zuchiyata. Wayata ce tayi kuka, ina ɗagawa naga baƙuwar lamba. Jikina har yana rawa na ɗaga wayar.
Mabaruka mutanen turai" Ta cikin wayar tace.
"Ƙawata yaya naji muryarki a haka kamar ba ke ba? Ko da yake ba wannan ba, gani a Airport na Accra, ki turomun da Adireshin gidanki dan ba ganewa zanyi ba." Nan da nan na ruɗe ma mabaruka da ihu. A guje na shiga ɗakin ƴan matan gidan. Rashida na zaune yaranta sun kawo mata ziyara suna hirarsu. Sauran yaran gidan kuma wasu na zaune, wasu na kan cinyayyun katifunsu. Rashida na sama wayar a kunne ina murmushi nace.
Ga ƙawata dan Allah kwatanta mata gidannan namu, suna Airport ɗin Accra." Riƙe wayar Rashida tayi, turyan_turyan ta kwatanta ma Mabaruka gidannan ta miƙa mun wayata.
Hello ƙawata sai na ganku, tare da oga zaku shigo ne?" Mabaruka tace.
"Ban isa ba, zamu soma kama hotel in nayi wanka ni zan tawo inzo mu wuni, da daddare zai zo saimu koma hotel. Naso in kwana miki ƙawata amman bazan iya barinshi shi kaɗai a hotel haka nan aimun sakiyar da ba ruwa ba. Sai dai nazo kawai." Ƙit ta kashe wayarta.
Rashida na gode fa?"
"Lahh babu komai Anti Zubaina" Fita nayi ko kallon ragowar yaran ɗakin banyi ba, dan riƙaƙƙun marasa mutunci ne, dan su zageka ba komai bane, a gabanka, a dakesu yayyensu maza riƙakƙun ƴan tauri suzo har tsakar gida suna karta adda, suna maka barazana da rayuwarka. Ɗaki na koma na kasa zaune in kai mari in kai gwauro, ina tunanin kalar kunyar da zanji in Mabaruka ta shigo taga ɗakina. Duk da tasan halin da nake ciki, amman ko kusa bata san abun ya kai haka ba. Hankalina yabi ya tashi, abincin da zan bata ma tunani nake yi akanshi, amman nasan bani da wata mafita. Awa ɗaya awa biyu sai ga wayar Mabaruka.
"Ƙawata get ɗin farko kikace zan shigo ko?"
E Mabaruka, bari in fito in tarbeki ma." Da sauri na saka mayafi na fita tsakar gidan. Sannu naima Nabila dake gaban murhu kace_kace.
"Ina zuwa da sauri haka Zubaina ke da baki da ishashshiyar lafiya?" Murmushi nayi mata nace.
Baƙuwa nayi zan shigo da'ita. Aminiyata ce tazo" Ban jira me zata ce ba na wuce, mabaruka harta shigo cikin gidan da sallama a bakinta. Idanuwanta ta zuba mun cike da maɗauƙaƙin Mamaki"


MRS BUKHARI CE
[15/08, 11:55 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
44






















Kallon ƙuda mu kai ma juna ni da Mabaruka, bansan sanda hawaye ya soma gudana a fuskata ba. Mabaruka shar da'ita tana cikin kayan alfarma sai ƙamshi take yi, ga cikinta ya amsheta yayi ɗas a jikinta. Kai da ganinta kasan ana lalatata da gata.
"Kofurr Zubaina wanka, kece haka ko gizo idanuwana suke yi mun? Ina wanka, da kwalliya, ina hasken fata, da glowing. Ke kinga yanda kika koma kuwa?" Numfashi mai ƙarfi naja na ɗanyi Murmushin nadamar rayuwata, duk da nasan Mama itace ummul aba'isin dukkan halin dana tsinci kaina a yau. Dan uwa itace makwafin yaranta. Ya rage naki kiyi me kyau, ko akasin hakan. Amman a matsayinki na uwa ki dinga hangen goben ƴaƴanki.
Mabaruka maraba da zuwa ƙawata, nayi farin cikin ganinki kafin in mutu in huta. Hawayene suketa turereniya a kan kumatukana. Daga bayanmu muka jiyo tashin zage_zage da tashin muryoyi. Alh Liti ne da Amaryarshi Zarah suke cin uwar sabada. Akwatin kayanta take ja tana cewa ita sai ta tafi . Yayin da shi kuma ya caɓe akwatin yana faɗin.
"Ai wallahi Zarah in da uwarki kike yawo baki isa ki bar gidannan ba, ai tunda kwaɗayine ya kawoki cikin rayuwata, saina gurje kuɗina na mori gyaran jikin Amarci, da laushin fata. Ai duk wanda ya hau motar kwaɗayi, yasan sunan tashar da za'a saukeshi, sannan duk ƴan iskan da kika zo kika tarar da badan na kafesu a cikin gidan ba, baza ma kizo ki samu kowa ba, ba'ai macen da zata iya fita a cikin gidannan da zummar guduwa ba. Kinga can inda Zubaina take, baki isa kin wuce wajan ba, in kika ga kin wuce wajan to tabbas ba gudu zaki yi ba. Fita ce kawai ta jeki ki dawo." Zarah ta dubeshi tace.
"Ba dai uwata ba, sai dai uwarka ɗan kutumar...." Bata rufe baki ba, ya naushe bakin nata sai jini, ya zuzzuba mata wasu irin gigitattun maruka. Nan yayi baya yana neman madoki. Muciya ya ɗakko da gudu ya bi Zarah, ganin ya nufota gadan_gadan yasa ta ari na kare, rufa mata baya yayi nan suka shiga wasan tsere. Yaranshi ƙananu da manya duk suna gani, harda ƴan mazan ma. Haka su kaita zaga tsakar gidan a yunƙurinshi na ganin ya cin mata. Mabaruka tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihil rajiun Zubaina haka gidanki yake? Danƙari maƙari sunan kare a lahira. Hannunta naja kawai.
Zo mu tafi Mabaruka, sauran tattaunawar ta cikin ɗaki ce. Ko da muka shigewarmu ɗaki, muna shiga Mabaruka ta soma zabga salati, tana tattafa hannayenta gami da riƙe haɓarta.
"Na shiga uku Zubaina wannan akurkin mai kama da fursuna kuma inane?" Kuka na fashe mata dashi mai ƙarfin gaske, dama dannewa nake yi kawai gudun kar in kunyata kaina a gaban yaran Alh Liti. Na jima ina kuka kafin daga bisani na tsokatama Mabaruka kaɗan daga cikin halin da nake ciki, ragowar kuma na barma kaina, ciki ba dan tuwo kaɗai aka yishi ba, ko Mama da su Asiya bana sanar dasu halin da nake ciki. Dan Mama tace bani ba ita, in dai bazan bari ta turo mun wata laya data karɓo a wajan bokanta dubu dari uku ba, wannan layar tace dana matsa Alh Liti zai sauwaƙemun. Ni kuma a halin yanzu da'in kuma bin ruɗin bokaye na gwammaci wahalar gidan Alh Liti tai sanadina. Wanda nayi a baya ma ina ɗan daka ce banyi ba, kuma har gobe a cikin istigifari nake. Abunda na shuka ne nake girba, yanzu nasan zafi da raɗaɗin a mallake mutum, ana cutar dashi bashi da abunda zai iya aikatawa, sai dai zuchiyarshi tai ta mishi suya kawai.
"Zubaina to me kike tsarama kanki da baki koma Najeriya ba, sannan naga halama ƙaramin cikine a jikinki, ya zaki bari kiyi ciki a gidannan, zaki tsallake kema ki bar abunda kika haifane tunda kince bai bari mace ta tafi da yaro? Ga hannunki a jone har yanzu karayar bata warke bane, ga bakinki a suntume, haƙorinki ma naga ya faɗi, kenan jibgarku Alh Liti yake yi kamar yadda naga yana bin matarshi da muciya suna zagaye gidan? Zubaina ya kamata kiyi wani abun domun samarwa da kanki mafita. Kin ganni nan? Ni yanzu haka a cikin tashin hankali da matsalolin dangin miji nake wallahi, kuma nabi malaman duniya dan in mallakesu abu yaci tura. Suma mugayen ƴan biye_biye ne. Yanzu haka rikicin da ake ciki, hajiyanshi taje can gidanmu ta ɗauki uwar gidan ta mayar da'ita gidanta, akan tana jiran dawowarmu ayi wacce za'ayi. Duk abinda na tara na dukiya a gidan Salisu na kaɗar dashi a wajan bokaye, da abun da na tsira bazai wuce gyara mana gidanmu da Salisu yayi ba." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
"Yaya batun yaranki na wajan Adam, ince dai kina jin ɗuriyarsu ko?" Mabaruka ta gyara zamanta tace.
"Bana jin ɗuriyarsu wallahi Zubaina. Amman a cikin kwanakinnan sai na yawanta mafarkinsu, inason dai in dubosu da kaina. Amman Mama na zuwa dubosu. Nabila ce ta katse mana hirarmu da yin sallama. Shigowa tayi hannunta riƙe da kwanon silver da kofin silver na ruwan sha.
"Ga abinci aba baƙuwa" Ta dubi Mabaruka tace.
"Sannu da zuwa, ina yini?"
"Lafiya lau, nagode sosai" murmushi Nabila tayi kawai ta fice. Mabaruka ta jawo abincin ta buɗe, ina ganin sanda tayi turus tana kallona, kai kawai na sauke inaji tamkar ƙasa ta tsage in faɗa tsabaragen kunya. Numfashi naji tana ta saukewa tana ɗauka. Ni dai ban ɗago kaina ba balle mu haɗa ido.
"Zubaina wai shin kin zaɓi zama a cikin wannan uƙubarne har kika amince da zaman harma da ƙaruwar juna biyu a tattare dake? Ko ko so kike in kika haihu lafiya ki cika ma rigarki iska ko ya abun yake? Dubi wata jagalgalalliyar shinkafa fara sol da wani mitsitsin yaji a gefe, ke kanki kin ganki kuwa, amman kina duba madubi kuwa?"
Ina dubawa Mabaruka, amman inaso ki sani, Allah kamar ya kawoni cikin gidannan ne domun ya ramama Bulama da mahaifansa abinda na aikata a kansu. Mahaifiyar Bulama ta jima tana yin adda'ar Allah ya saka mata. A gaban idona a Damaturu ta faɗa, a wata ziyarar bazata da mu kai musu, ziyarar da bazan taɓa mance ta ba. Ni wacece da Allah bazai azabtar dani akan hakkin bayinshi dana ɗauka ba. Babban abunda yafi mun raɗaɗi shine, nisa da nayi da yarana. Yanzune na gane girman abunda na aikata, mabaruka duniya makaranta ce, mai cike da ɗumbin ajujuwa, ko wanne aji da irin darasin da ake koyarwa. Ni kam ko Alh Liti kasheni zaiyi, na yarda na aminta inyi bautar Allah, wataƙil hakan kankarar zunubine a gareni." Ina kaiwa nan naci gaba da sharar hawaye. Mabaruka tayi tsuru_tsuru nan take ta soma tunanin makomarta da kuma gobenta, bata san ya zata kasance ba. Dan Mabaruka azzalumace, tayi ma Adam da Sagira zalunci mai girma. Ita kanta tasha jinin jikinta sakamako yananan fitowa a kanta. Abincinnan kuwa bata ci ba, rufewa nayi abuna, da daddare naci, in huta da cin dokunu yau. Tana sallah na fita na karɓo abincina, a tsakar gidan na tarar da Zarah a bakin ƙofarta, sai harare_harare take yi. Ni kuwa banbi ma ta kanta ba, damuwar da take nuƙurƙusan zuchiyata ma kaɗai in aka barni dashi, a kwana a tashi zai iya zama sanadin ajalina. Sai da daddare Salisu yazo ɗaukar Mabaruka, da kwatance ya kawo kanshi har ƙofar gida, a bisa jagorancin dan lori daya ɗauko. Zuwa wannan lokacin zazzaɓin dake kaina ya wuce gaban misali, bakina kuwa ya aune ya suntuma. Mabaruka babu yadda batai dani ba, kan muje asibiti, amman fur naƙi, sai maganin zazzaɓi taimun alƙawarin zasu kawo mini. Har ƙofar gida na rakata, mu ka gaisa da Salis, sannan na dawo gida akan zasu je su siyo mun magani su dawo. Ina shigowa cikin gidan na ji Hajiya Kubra na fama da Zarah akan taje ta buɗe ma Alh Liti get ɗin ɓarayinshi. Da ƙyar ta tashi ta tafi fuu. Da idanu kawai na rakata, haka kurum sai naji jinina sam bai haɗu da Zarah ba. Dan na fuskanci irin yarannanne masu buɗaɗɗen idanu, masu ido a tsakar ka, bakina na taɓe, na nemi waje a gefen Nabila na zauna, sai cin Dokunu take yi, Amman ranta a jagule yake ainun.
Lafiya kuwa Nabila?" Ajjiyar zuchiya ta sauke.
"Daga gida aka kirani, mahaifiyata rai a hannun Allah, to inason zuwa gidane dan in dubata, shekarata uku rabona da gida. Kinji duk abinda yabi ya damu raina kenan. Alh Liti nasan ba barina zaiyi ba ko da na faɗa mishi uzirina. Kuma dole saina jira lokacin ganawa ta zagayo, ko kuma in kwanana ya zagayo. Bazan iya ɗauke har kwana biyar ban gana da mahaifiyata ba." Hawayene ya sulalo mata a kumatunta, ni kaina sai naji kamar in zubar mata da hawaye. Hajiya Kubra dake jinmu tace.
"Ki daure lokacin kwanan naki ya zagayo sai ki sanar mishi, tunda baki da wani zaɓi. Ba zamu gushe muna adda'ar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan halin da muke ciki ba. Har gaban abada bazan dena dana sanin Abinda na aikata har yai silar shigowata gidannan ba. Allah yasa ya zama izina ga mata masu shegen son abun duniya. Domun Alh Liti cikakken mayaudarine, wanda duk wayonka baka isa ka ganeshi ba. Yayi amfani da dukiyarshi, da kwaɗayinmu, dana iyayenmu ya ɓarar damu." Muna cikin wannan maganar muka jiyoshi yana rangaɗama Nabila kira a ƙagauce. Kanmu yazo ya tsaya
"Munafukan Allah ta'ala an kafa taburmar zagina da tsine mun ba?. Ke kuma iyayenki sun kirani da yamma suke sanar dani rasuwar mahaifiyarki. Dan haka sai ki shirya gobe a saki a mota zuwa Lagos, daga can sai ki nemi motar garinku. Kwana bakwai dai_dai na baki. In kika wuce hakan zaki gane kuskurenki." Fuu ya koma, Nabila kuma ta sau kuka harda kururuwa, sai mune mu kaita tunasar da'ita adda'a ya dace ace tayi, ga ciki a jikinta tayi haƙuri. Muna cikin wannan halin Mabaruka ta dawo. Na ganta da ledoji niƙi_niƙi a hannunta. A tsakar ɗakina ta dure.
"Ga kayannan na tabbatar zasu yi miki amfani. Akwai suturu kala uku a ciki, nawane dana siya a Dubai, kya yi fitar suna dasu. Akwai kuma kayan ciye ciye, irin su yogot, chocolate, cincin, da dai sauransu. Ga kuma wannan kuɗin da maganin Salis yace in baki. Zubaina ni kaina da

51 / 67