Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
da hali wlh da na dena bin bokaye. Ga Mama ba lafiya sai sunturin asibiti muke yi. Ni gabaki ɗaya na tsinke da wannan lamari." Haka dai mu kai sallama da Mabaruka ina hawaye. Maganin zazzaɓin da su ka siyo mun na ɓalla nasha. Komawa nayi wajan Nabila, sai faman kuka da sambatu take yi. Washe gari sassafe Alh Liti yasa ɗanshi ya kaita tashar mota aka sata a motar Lagos. Cikin alhinin taima kowa sallama ta tafi. Rayuwa haka tai ta garawa damu, kullum ba daɗi, bala'in yau daban na gobe daban. Zarah kuwa Alh Liti ya ladabtar da'ita ta dena yi mishi tsiwar da take yi mishi. Sai dai na lura Zarah kishi take yi dani sosai. Dan ko wucewa nazo yi sai ta ja tsaki. Ni kuwa sai dai inyi mata murmushi kawai, lallai kura tayi lafiya. Da dane Zarah bata isa mun haɗa mijibaa, balle harta samu ƙwarin guiwar yi mun tsaki a tsakar gida.
MRS BUKHARI CE
[15/08, 2:50 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: 45
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
.
BULAMA BABBA.
Sai karo muke ci da iyayen yara masu shige da fice. Ni dai Allah Allah nake yi inga Yahanasuna, da kuma yanayin lafiyar jikinta. Muna shiga cikin asalin inda ɗakunan nasu yake, muka hangota tana zaune a bakin baranda, tana kallon ƴan uwan zamanta masu ganawa da iyayensu. Idanunta carab ya shiga nawa, take naga ta shiga sharar hawayenta. Ji nake ni kuma tamkar in je in rungumeta tsam a jikina in rarrasheta, kuma in tusata gaba mu dawo gida. Rashin Yahanasu ba ƙaramin giɓi yai ma rayuwata ba. Malam Rilwanu ne ya taryemu da fara'arshi.
"Alh Modu barkanku da shigowa, maraba lale an sha hanya. Tsaiwa gaisawa suka yi. Ni kuma na wuce wajan Yahanasu da take ta kuka. Ina isa ta miƙe tana son rungumata, nima abinda nake so kenan. Amman ana barin halak dan kunya, baya nayi da sauri sai ta faɗa jikin Yanuna tana mai kuka kamar ranta zai fita.
"Me nayi muku kuka kawoni wannan gidan azabar, gidan da kullum sai an dakemu, kashemu suke son yi. Dan Allah Bulama Babba kace a tafi dani gida. Wallahi na tuba bazan sake shan ko ruwan shayi ba balle wani abun maye." Zuru nayi ina kallonta cikin tausayawa. Ba Modu ne suka iso dasu Gunsum. Ƙasa Yahanasu tayi da kanta, kunya take ji da ganin yanayinta. Lallai akwai nasara fiye da ta baya. Sai dai muguwar ramar da tayi ya bani tsoro, ta sake yin baƙi sosai, kamar ba Yahanasu ƴar lukuta dana sani ba. Ba Modu ya ƙura mata idanu ƙur, sai kuka take faman rerawa. Kai kawai ya girgiza, nasan dole yana tausayin Yahanasu amman girman abunda ta aikatane yasa yake danne tausayinta da yake ji.
"Yanunu kuje ke da Fanda wajan Malama Fahiƙa kuji yanayin jikin nata. Kai kuma Gunsum muje gefe inason magana da Malam Rilwanu. Watsewa suka yi suka barmu mu kaɗai. Kallona take ta yi. Hankali da halama ya soma dawowa jikinta, amman ba wani sosai ba, sai dai naji daɗin yanda ta gane mu dukkanmu. Amman yanayin ramarta ya ɗagamun hankalina.
Zo muje mu zauna ki samu kici abinci Yahanasuna" Hannunta na kamo, ɗayan hannun kuma na ɗauki basket ɗin abincin. A wata tabarma kusa da wasu suma kamar mijinne ya kawo ma matarshi ziyara da yaransu. Bawa da Maryam suna biye damu. Muna Zama Yahanasu ta ɗauki maryam a cinyarta, Maryam kuwa tayi lub a jikin Yahanasu.
"Ina Yusuf shi?" Da mamaki na dubeta da har ta iya tuno Yusuf. Bawa ne ya bata amsa.
"Yana wajan Ya Innana, yana shan kunu da ƙwai" Murmushi nayi musu. Na buɗe abincin na zuba mata a plate. Hannu baka hannu ƙwarya ta dinga cin abincin tana shaƙewa, dan biski baka isa ka mai cin gaggauwaba. Ruwa na ɓalle zan miƙa mata, ta warce da sauri sai da ta shanye tas. Cikin raɗa tace.
"Dan Allah zaka bani laka mis in ɗan kora, ko ƙwaya zaka bani in zuba in kora da kodin? Sai kuma ta sau kuka dai, tana ambaton kayayyakin mayen data saba sha a koda yaushe. Lallai akwai aiki ja a gabanmu, na ganin Yahanasu ta dawo hayyacinta. Gashi Hajja tace tana son ta tattauna dani in na dawo, bansan mai take son mu yi magana a kai ba. Alkakin da Hajja tace in bata na damƙa mata a hannunta, na soma share mata hawayenta.
Ki dinga ambaton Allah a duk lokacin da zuchiyarki ta bijiro miki da wani abun maye da kika sha a baya kinji ko? Muma ba'a kwance muke ba, adda'a muke miki Allah ya yaye miki wannan ciwo. Ki yi haquri kukanki na dagula mun zuchiyata kinji ko?" Kai ta gyaɗa mun, bata ce dai komai ba, sai daga baya ne inta ɗebo zancan arziki ringiɗi_ringiɗi sai kuma ta kasa ƙarashewa, a mugun sanyaye take magana tamkar mai raɗa. Yanunu da Fanda ne suka iso inda muke, Yanunu ta zauna kusa da Yahanasu tana sharar hawaye.
"Oh Yahanasu Allah ya baki lafiya ki rabu da zaman gidannan. Nifa Bulama Babba da ace Modu zai ji shawarata da mun koma da Yahanasu asibiti. Gabaki ɗaya wajan bai kwanta mun ba, amman naga Modu a wannan karon ya ɗauka da zafi. Innana tayi mishi zancan a dawo da Yahanasu Babban asibitin Yobe amman fur yaƙi. Baiwar Allahnnan ko rintsawa bata yi, duk tabi ta ƙare sabida fargaba da tunanin me kaje kazo." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
To Yanunu Ba Modu bazai yarda da wannan zancan ba, kwanaki dana matsa mishi da zancan, cemun yayi in batun dawo da Yahanasu ne zai dinga kawoni Damaturu to kar in kuma zuwa in yi zamana a Yobe. Yanzu dubi duk yanda ta lalace fa, ni bansan ma ya zanyi ba. Bani da sukuni da kwanciyar hankali kwata_kwata. Duk wani kula da kamfani da wani gyaran gida da muke yi. Ahmad ke yin komai, Hajara kuma ke kular mana da yaran duka." Muna cikin haka Gunsum da Ba Modu suka iso inda muke.
"To inaga ya isa haka, sai ku taso muje ko? Amman kafinnan Bulama likita yana buƙatar ganinka." Miƙewa nayi na nufi ofishin likitan, yana zaune yana rubuce_rubuce . Gaisawa mu ka yi, ya bani kujera na zauna ina fuskantar shi."
"Yahanasu tana samun sauƙi sosai, duk da tasha manya_manyan ƙwayoyin maye kuma ta jima a cikin rayuwar. Duk sanda nazo dubata ina ganin sauƙi tattare da'ita. Kuci gaba da yi mata adda'a. Amman har yanzu bata dena kiran abata ababen mayen ba, har ihu take yi duk ta birkita kanta, in abun ya motsa mata. Shi yasa ake ɗan dukansu domun a dawo dasu haiyacinsu. Duk da hakan ya saɓa ma doka, amman ana samun ci gaba ta ɓangaren yi musu barazanar duka, ko a dake sun. Sannan kullum ana basu rubutu suna sha. Ga sana'ar ɗinki da jiya ta soma shiga koyo, duk da hankalinta baya kai. Babu walwala a tare da'ita sam, amman in aka dage da adda'a ba zata wuce wata shida ba ƙila a sallameta. Dan ko yau mun sallami mata bakwai sun koma cikin iyalansu." Ajjiyar zuchiya na sauke, ina jin ɗacin dukan da likita ya faɗa mun ana ma Yahanasu. Amman nasan Ba Modu ba saurarena zaiyi ba. Gunsum ne ya leƙo.
"Bulama Babba Ba Modu yace ka fito mu tafi, suna mota kai ake jira." Jikina a mugun mace na miƙe, musabaha mu kayi da likita na fita zuchiyata a raunace. Ko da na fito na samu duk an mayar da su ɗakunan su. Cikin gidan ya kaure da iface_ifacensu. Malam Rilwanu kuma sai sallamar iyaye, da ƴan uwa yake yi, kan cewar lokacin su ya ƙare dan Allah suje. Ficewa nayi ba tare da nayi sallama dashi ba. Baya na shiga kusa da Fanda, na jingina bayana a jikin kujera, idanuna a lumshe kaina mugun saramun yake yi. Ko a mafarki ban taɓa tunanin zanyi mafarkin Yahanasu a irin wannan mawuyacin yanayin ba. Ina zan tsoma raina ne, wajan wa zan kai kokena dan ai ma Ba Modu magana ya yarda a dawo da Yahanasu gida? Tunowa nayi da umman Ahmad nasan Ba Modu yana matuƙar ganin girmanta, shawara na yanke zanje in sameta in faɗa mata buƙatata. Da tunane_ tunane barkatai naita hira a zuchiyata. Ina jin su Yanunu suna zancan basu ji daɗin ganin Yahanasu a halin da suka zo suka isketa ba. Kowa na tofa albarkacin bakinshi. Ni kuwa sun ɗauka ma bacci nake yi, dan idanuwana a lumshe suke. Haka mu kaita sharara gudu a hanya. Bamu muka isa Damaturu ba sai taran dare. Ɗakin Ya Innana na zarce dasu Maryam na ajjiyesu, anan naci abinci kamar yadda na saba. A ɗakin Ba Modu ya shigo ya tadda ni, ina kallon labarai. Sannu da zuwa Ya Innana tayi mishi bayan ya zauna ne take tambayarshi yanayin jikin na Yahanasu.
"Jiki kam da sauƙi sosai, danni naga sauƙin jikin nata fiye da asibitin. Ki yi ta mata adda'a bazai faɗi ƙasa banza ba." Ya Innana tace.
"Amman ni da za'a daka ta tawa da an mayar da yarinyarnan asibiti. Ire_iren gidajennan fa ba ƙaramin mugunta da azabtar da mutane suke yi ba. Ga yawan mafarkai da suka addabeni duk akanta." Take Ba Modu ya gintse fuskarshi yayi kicin_kicin yace.
"Ko kasheta zasu yi sai dai su kasheta. Da ace Yahanasu ta riƙi adda'a batai watsi da tarbiyyar gidannan ba, da bata cikin halin da take ciki yanzu. Tsuntsun da yaja ruwa ai shi ruwa ka duka, kar ku kaini bango akan batun Yahanasu" A tausashe nace.
Ba Modu ko wanne bawa baya wuce ƙaddararshi. Ciwon damuwa ciwone da babu abunda baya sa mutum ya aikata. Tunda waɗanda suka tsinci kansu a irin wannan halin, har kashe kansu da kansu suke yi"
"Ita adda'a ai ta game komai. Da ace tabi koyarwar ma'aiki arrasul S A W da bata tsinci rayuwarta a cikin gidan mahaukata ba. Uwarta gata nan kullum a cikin damuwa take, cikin da take samu yaƙi zama, kullum a cikin yi mata adda'a take. Ashe ita ke zubar da cikin da gangan dan samun wani farin ciki na rayuwarta. Ku barni haka da batun yarinyarnan haka ya isheni. Na san da ƙaddara, sannan nasan adda'a na iya sauya ƙaddara daga mummuna izuwa kyakykyawa. Sanadiyyar yarinyarnan na rasa Bakura amini, kuma uba, wa a gareni. Baƙin cikin Yahanasune ya buga mishi zuchiyarshi. Ya bazan damu ba." Hawaye ya soma zubarwa, a wajan ya fita ya barmu, jikkunanmu a sanyaye. Ni kam abun duniya ya haɗu yai mun yawa. Yanzu ne na gane dalilin Ba Modu na nuna halin ko in kula akan lalurar Yahanasu, da kuma irin gidan da yasa aka kaita dan neman lafiya. Shi gani yake sabida ita Ba Bakura ya mutu. Alhalin ko Yahanasu bata aikata komai ba, Ba Bakura zai mutu da zaran wa'adin zaman duniyarshi ya ƙare. Nunfashi na fesar mai zafi. Ya Innana tace.
"Ka samu ka shiga cikin gida ka huta Bulama Babba. Babanku ya ɗauka da zafi sosai. A tunaninshi Yahanasu ce tasa yayi rashin ɗan uwanshi. Bashi da laifi dan ya ɗauki fishin da yafi wannan a kanta. Kaje, nasan Modu ya fini,ya fika son Yahanasu, kuma in Yahanasu ta cutu, sai ya fini ya fika cutuwa, ai shine mahaifinta, ba dan rashin so yake yin hakan ba. Sai dan tsoratar da ƴan gaba, su shiga taitayinsu. Tunda wannan shaye_shayen ya tashi daga hula ya dawo ɗan kwali. Babban abunda ya sani a damuwa yau ɗin nan, shine labarin rasuwar ƙawarta hajja Fati, sakamakon haɗarin mota data samu. Wanda ya bigetan yace wai a bige ta shige mai gaba a titi. Kuma ko da aka bincike jakarta wallahi Bulama Babba cike da kayan maye aka tarar da jakar. Ɗazu da na shiga yima mahaifiyarta ta'aziyya ne take labartamun wannan zancan, dan labarin haukacewar Yahanasu ya karaɗe anguwarnan dama kewayenta." Shiru nayi ina nazarin maganganun Ya Innana, ina tunanin ko dai Yahanasu ta koya ma Hajja Fati shan muyagun ƙwayoyi, ko kuma ita Hajja Fatin ta koya ma Yahanasu, domun amintarsu tayi kama da amintata da Ahmad, Ahmad kuwa babu abunda muke iya ɓoyema junanmu.
Allah ya kyauta, ita kuma Allah yai mata rahama. Zuwa gobe kafin in wuce zanje in musu ta'aziyya." Miƙewa nayi na fita. Sai da na zaga iyayenmu mata duk na gaishesu, na ba kowacce ɗan kuɗin kashewa, ɗakin Hajja ne ƙarshen shiga. Tana zaune akan dadduma hannunta da carbi tana ja, da sallama na shiga na zauna a gefenta nesa da'ita ba sosai ba.
"Yaya mai jikin kuka sameta?" Ɗagowa nayi muka haɗa idanu da'ita. Naji muryarta babu daɗi sam, na kasa karantar yanayinta.
Jikin Alhamdulillah, da muka je ta gane mu, harma tace sai dai mu tawo da'ita. Kuma acan ma ance mana jikin nata da sauƙi."
"To Allah ya ƙara sauƙi. Kaci abinci a wajan Innana ko?" Kai na ɗan sosa nace mata.
E nan na soma shiga ma, na kai mata yaranne."
"Maganar da dama nake son yi da kai shine. Me zai hana tunda kana da lafiyarka, kuma yanzu kafi ƙarfin ciyar da mutum ɗari ma, me zai hana kayi aure? Ai ba zaka zauna haka ba, tunda ita matar taka bamu san yaushe zata warke ba ko." Dum gabana ya buga, kuma na sha ruwan mamaki da naji irin wannan kalamin a bakin Hajja. Domun nayi tunanin ko ni nazo mata da irin wannan zancan ba zata yarda ba. Sai gashi daga rasuwar Ba Bakura komai yana son sauyawa, duk wasiyyar daya dinga jaddadawa akan muyi riƙo da zumunci, kar muyi sake zumuncinmu ya tarwatse. Ya Ba Modu zai fassara wannan maganar in ya jita, Ya Innana me zata yi tunani?"
"Kayi shiru nayi magana baka iya cewa komai ba."
Ba haka bane kiyi haƙuri Hajja. Bani da ra'ayin haɗa matsayin Yahanasu da ko wacce mace a zuchiyata"
"Har dani dana ɗauki cikinka nayi naƙudarka? Ko da yake ai barewa ba zata yi gudu ɗanta yayi rarrafeba. Innana ma ai ta riga data shanye Modu. Da badan tasan wanshi yafi ƙarfinta ba, ƙila da harshi zata mallake. Yanzune Bagulaji ta dena zuwa falonnan kawo ƙarar Modu bisa fifita Innana da yayi akanta. Zubaina ma ta mallakeka balle Yahanasu jinin Kanuri gabanta da bayanta" Kaina ne naji ya buga. Ni bansan mahaifiyata da haka ba, ban taɓa ganinta a cikin irin yanayinnan ba, to wa yake zugata, ko dai ƴan uwanta da suka zo ta'aziyya ne suka zugata. Bani da mai bani wannan amsar, baki na kada nace
Ko kusa, aike matsayinki da banne, baki a cikin jerin abinda nake nufi. Amman Hajja Yahanasu ƴarki ce, ko bani take aure ba nayi imani ba zaki so ta ƙuntata ba. Kuma tayi mun dukkan alkhairi. Bata da wani laifi a wajena, face wannan jarabawar data sameta. Ni bani da sha'awar mata biyu. Kiyi haƙuri, sannan bani da wacce na gani naji inaso" Na ƙarashe maganar har ina haki, tsabar yanda ƙirjina ke bugawa.
"Yayi tabbatacce. To naji, kai in baka da wacce kake so, ni akwai wacce na gani kuma nake so. Bazan sa aima ƴar mutane Auren dole ba. Amman kaje ku daidaita. In ma ka nuna mata baƙin rai dan ku kasa daidaitawa, to fa ka rubuta ka ajjiye zan yi ma Auren dole, kamar yadda aka yi maka akan Yahanasu, bayan ta saryar da mutuncinta, dan ba wani fyaɗe da akayi mata biri boko kawai akayi mana, ƴan uwanta ƴan maye ta bama jikinta suka yagalgala. Tashi ka bani waje, kuma gobe kafin ka wuce ka tabbatar ka je ka ga Yalewa ɗiyar ƙanina Bature." Da sauri na kalleta da naji sunan wacce ta ambata, amman ganin a hasale take, ga takaba tana yi sai nace mata.
To Allah ya nuna mana, mu kwana lafiya" Na miƙe jikina har yana rawa_rawa na fice. Ko da na shiga ɗakin masaukina. Kasa nutsuwa nayi. In kai mari in kai gwauro. Hajja ta jefa ni a cikin tsaka mai wuyar fita. Ina jin tsoron ƙiris abunda zai sa in zama silar ɓacin ran iyayena, ina tsoron kuma lalacewar zumunci. Amman taya zan yi aure, alhalin zaman lafiya muke yi da Yahanasu. Ita kaɗai ya cancanta tayi rayuwa a ƙarƙashina, taji daɗin dukiyata. Dole tun wuri Ba Modu yaji wannan labarin, duk da nasan ba labari bane me daɗi. Amman shigarshi cikin lamarin yana da kyau. Ahmad ne yake kirana a waya. Numfashi na fesar me zafi, na ɗauki wayarshi.
Hello Ahmad ba kai bacci ba?" Ahmad ya amsa daga ɓangarenshi da cewa.
"Wane bacci zanyi banji daga gareka ba. Na kira wayarka yafi sau a ƙirga, amman network bai bani damar samun naka ba. Kana Damaturunne, yaya kuma jikin ita Yahanasun?"
Ahmad jikinta ba laifi da sauƙi. Harma ta gane mu. Amman Yahanasu ta zube ta lalace sosai ba ma kace ita bace. Na sake shiga damuwa sosai dana ganta Ahmad" Ahmad cikin sigar rarrashi yace.
"Dama ai dole ta lalace Bulama, ciwo take yi fa na rashin hankali. Amman tunda sauƙi yana samuwa ai abunda muke nema kenan. Cikin kwana bakwai kake yin sauka, kuma kayi sadaka tare da tawassali cewar Allah zai bata lafiya. Kayi haƙuri kar kaima ka jefa kanka a cikin deepretion, ayi ƴa kwance uwa kwance, kaga an ɓata goma ɗaya bata gyaru ba."
Ahmad Hajja tazo mun da wata magana mai tayar da hankali ainun, a wannan halin da nake ciki in ba'a rarrasheni ba, ai ba'a ɗaga mun hankali ba. Aure fa Hajja take so inyi. Kuma ta rasa da wacce zata haɗani sai Yalewa ɗiyar Kawu Bature, yarinyar da tsabar boko take ganin maza ma ba a bakin komai suke ba. In ƙi aurenta Ba Bature yace naƙi jininshi, in aureta Yahanasu taga kamar nayi mata butulci." Ahmad ya fi minti talatin yana rarrashina tare da tunatar dani girman iyaye, da fa'idojin adda'a, dana istikara. Madallah da abokin