MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   11 / 67

30K to 33K   out of 198.3K words

ka sani suna da damar da zasu aura maka mata uku ba tare da saninka ba. Sabida sanda suka haifeka ai ba sanar da kai su kai ba. Ni a gaskiya lamarin yanda kayi watsi da dangi da iyaye abun ya ɗaure mun kai, domun ban sanka da hakan ba sam, nasan kai mai bala'in son danginka ne. Yarinyar da suka aura maka ƙanwarka ce, gashi ta zama matarka ni dai ina roƙonka ka riƙeta da amana, kar ka ruguza muku zumuncinku mai daɗi da ban sha'awa, ka riƙe ƴar mutane da gaskiya, kaine dai shugaba, ni wallahi sai in ga kamar tsoron Kofur Zubaina kake yi mijin police ko dai kashi take baka ne a ɗaki?" Ya ƙarashe zancen nashi da barƙwanci, Ahmad Abokinane tare muka taso mu kai wasan ƙasa dashi, a bayan layinmu a Damaturu yake, ada shima yana aikine a kamfanin rodi dake garin Kaduna, daga baya kuma sai ya bar wajan, ya koma Lagos da zama, a ƙarƙashin kamfanin shinkafa, daga baya kuma aka kamashi da yi ma kammani ɓarnar dukiya, Kamfani tace bazata yarda ba, shine har firzin. Da taimakon Allah dai na shiga na fita, aka siyar da motarshi da gidanshi na nan Kaduna, aka biya kamfani kuɗinta, shine har ya samu ya fito,amman aiki yaƙi samuwa, sai ƴar buga buga da yake yi a can Lagos ɗin. Matarshi Hajara kuma itama ƴar Damaturunce. Munyi aure da Zubaina da shekara biyu ya Auri Hajara, soyayyar da su kayi bata wuce ta wata shida ba, Ahmad ya aureta, ya kawota garin Kaduna suna zaune a hayin malam Bello, wajan makarantar silver bright. Yaransu Uku Biyu mata, sai Namiji da take goyonshi a yanzu. Harara na zabga mishi nace dashi.
Ahmad kenan, ni sai in dinga tantama anya kuwa ka damu da farin cikin rayuwata kuwa? Allah shi ya halicceni ya kuma halicci so, wallahi so ɗaya ne tak kuma Zubaina nake yi ma shi, bazan iya kasa shi kashi biyu ba. Amman bazan iya cutar da Yahanasu ba kaima ka sani, sai dai fa ni bazan iya zaman aure da'ita ba." Nan mu kaita muhawara a tsakanina da Ahmad ko wannne cikinmu ranshi ya ɓaci, yana nuna mun hanya, amman ƙaunar Zubaina da son danginta ya makantar da rayuwata, irin makantar da bana iya tantance fari balle baƙi. A zuchiye Ahmad ya fita ya barni, hankalina sai ya tashi kuma, dan Ahmad masoyine kuma Amini ɗan ƙwarai, na dinga kiran wayarshi ban samu ba sam, Zubaina ma na yi yunƙurin in kirata amman wayarta ban samu ba. Jinjina nayi a jikin kujera ina tuno rayuwar da nayi da iyayena, da ƙannena masu ƙaunata, sai inji babu daɗi inna tuno da cewar na kan share tsawon watanni ba tare da na kira wayarsu na ji lafiyarsu ba. Kuɗina bazan iya tuna yaushe rabon da ya shiga hannunsu ba, in je in gansu abun ya zamemun nauyi. Wunin yau ban yi aikin kirki ba, lokacin tashi nayi na fice a office ɗin na nufi gida, kai tsaye na shige ɗakina, sabida tsabaragen damuwar data fitineni, ko masallaci na kasa zuwa a ɗaki nayi magriba nayi isha, bana fatan abunda zai sa in haɗu da ƴan uwan nawa ma, dan haushin kowa nake ji, kuma gobe ma da sassafe zan bar gidan, sai dai in ba Zubaina saƙo ta basu. Asiya da Nafisa ne suka bani abinci, na karɓi Bakura da Maryam a hannunsu na shinfiɗesu a gadona, nasan tunda naga Zubaina ta kai yanzu bata shigoba, tana da aikin dare kenan, dan case ɗin ɗan luwaɗinnan ya tsaya mata a wuya ainun, shi yasa ma ban kirawo wayarta ba, dan kar in dameta tana bakin aikinta, kuma dama haka muka saba gudanar da rayuwarmu."








Zubaina:
Har wajajen Magriba ma bamu samu ganin boka ba, ga mata biyu a gabanmu, mazan kuma duk bokan ya gansu tun ɗazu harma sun tafi. Wani saurayine ya fito, yake mana bayani da gurɓatacciyar hausarshi
"Baba yace ya tashi aiki. Ku shigo muje in Kai ku wajan Ungo, ta baku masauki zuwa gobe sai ya soma duba ku" Ni dai wallahi duk na gama sarewa, ga tsoron wajan daya cika mun rai na, ko sallar azahar gashi bamu yi ba, ga magriba tayi. Mabaruka tana riƙe dani muka shiga cikin gidan bokan. Gidane ƙaton gaske, anyi ma gidan ginin dutse, suna kiwon aladu, da karnuka da akuyoyi a gidan, ga mata da yara masu yawa a gidan. Saurayinnan ya kaimu wajan Ungo uwar gidan boka.
"Ungo baƙin Baba ne na kwana, a basu masauki." Matar Bokannan ta dube mu tace.
"Ku biyoni muje" Muna biye da'ita ina ƙara ƙarema gidan kallo, mutanen cikin gidan ma ganinsu nake yi kamar ba mutane ba. Matan da suke gabanmu kuwa naga su babu fargaba sam a tare dasu. Mabaruka kuwa ita kanta tsurewa tayi. Cikin wani ɗaki ta shiga damu, ɗakine mai ɗauke da gadon ƴan boarding mai hawa hawa, guda biyu, ga kafet shinfiɗe malala a ƙasan ɗakin. Matar bokan tana fita na cabki hannun Mabaruka.
Mabaruka ni wallahi tsoro nake ji, yanzu kina nufin a gidan bokannan zamu kwana?" Mabaruka tace.
"Haba Zubaina to yaya zamu yi? Kinsan dai ba zamu iya shiga cikin surƙuƙin jejinnan ace zamu tafi ba ko? Kiyi haƙuri in dai da matsala kika zo, matsalarki ta kau." Ɗaya daga cikin matan da muka shigo tare tace.
"Baiwar Allah banso na shiga cikin maganarku ba. Amman kin ganni nan,. Sau uku ina kwana a ɗakinnan da mata ƴan uwana musulmai, harma da arnan, babu abunda zai faru dake, da dukkan halamu ke sabon shigan zuwa wajan bokace, ashe sai kin yi fitsari zuwa gobe in kika shiga cikin inda bokan yake. Amman dai in duniya kike nema, ki kwanta kiyi barcinki da munshari dan kin sameta a tafin hannunki. Sai dai fa wannan boka aikinshi akwai tsada, yanzu_yanzu sai ya talautaki, amman ni tsabar iya aikinshi ne ma yasa nake zuwa wajanshi. Dan ban taɓa faɗa mai matsala bai magance mun ba" Ajjiyar zuchiya na sauke, na dubi wannan mata nace.
To ya kuke yi ku yi sallah a gidan waɗanda ba musulmai ba kuma? Kinga ko azahar ba mui ba" Dariya ta saka mun tace.
"Ki nemi waje ki zauna kinji Zubaina. Allah dai ya yafe, gobe in kika koma kya rama sallar a nitse, dan a cikin gidannan baki ba sallah" Rashin sallar ya jijjigani sosai. Amman haka matannan da Mabaruka su ka haɗu su kai ta fahimtar dani, ala tilas nayi haƙuri. A daren ranar nasha labarai daga bakunan matannan, da irin muguntocin da suke ta aikatawa, da kuma nasarorin da suka samu a rayuwa, da burukansu duk da suka cinma. Wannan hira tasu ta ƙaramin kaifin ilmi, dan na koyi darrussa masu tarin yawa a ciki, haka bacci yai awon gaba dani cike da zabarin son ganin gobe. Bulama kuma text nayi mishi cewar aikine ya riƙeni a office, acan zan kwana, amman gobe da safe zan dawo gidan, ya ba su Mama Gana da Amarya haƙuri"
WASHE GARI:
Tun asubar fari uwar gidan boka ta shigo tace.
"Me gida yace wacce zata soma shiga ta je, ku kuma sauran ku koma kan layi" Da sauri nace.
Inason zan zagaya makewayi in kama ruwa" Dan da fitsari tab marata na kwana, amman tsoro da muggan mafarkai sun hanani ko da motsawane" Bayan matar boka nabi, tai mun nuni da ɗan wani lungu. A ƙyamace na shiga nayi fitsarin, gashi ba ruwa, ni tsoron tambayar ruwan nayi tun farko. Ɗan kwalin kayana na cire, shi nasa na goge gabana na miƙe da sauri, dan sai naji kamar ana tawowa. A waje na samu Mabaruka, da Kattume a zaune a layi, Mansa itace ta shiga wajan boka. Tafi awa guda kafin ta fito, Kattume ta shiga.
"Mansa ki tsaya mana sai mu rage miki hanya, ba kince a Ƙauyan Kamuru kike ba? Ai muma kadunan muka nufa" Cewar Mabaruka. Mansa ta yashe bakinta tace.
"Ai kuwa na gode sosai, kunga ma shiga ku ga inda nake zaune ma, mayi zumunci duk da dai na girme muku nesa ba kusa ba. Amman ko babu komai ma dinga bama juna shawarwari. Zama tayi a gefe na, ni dai na ƙosa mu shiga wajan wannan boka. Kattume da yake tace magani da godiya tazo ta yima Boka bata wuce mintuna talatin ba ta fito, Mabaruka tayi mun jagora zuwa cikin bukkar tashi. Muna haɗa idanu cikina ya kaɗa, jikina ya shiga rawa, bokan na ganshi tiƙeƙen gaske sosai, ga idanunshi yayi biyar ɗin na Bulama a ja. Gashi na ganshi ba riga sai zani daya ɗaura, shima zanin iya guiwa, wani irin mugun wari ɗakin yake yi. Ga wasu gumakai masu abun tsoro takota ina a ɗakin ni dai jikina sai rawa yake yi. Uwar gidan boka tace.
"Ku samu waje ku zauna, sai kuyi mun bayanin abunda yake tafe daku, in sanar mishi. Take bakina ya shiga kakkarwa, na kasa furta komai. Bokanne naji yayi ma uwar gidanshi yare, yana yi yana zare idanu, ai cikina sai ya ƙara ɗurar ruwa kamar fitsari zai zubo mun. Uwar gidan boka tace.
"Yara Boka yace ku nutsu, ki faɗi damuwarki, in kuma kina jin tsoro ku fice ku bashi waje. Mabaruka tayi carab tace.
"A'a Ungo wannan dai ƙawata ce, tana zaune da mijinta lafiya iyayenshi suka aura mishi ƙanwarshi, sabida basa son ƙawar tawa. Shine muka zo munason a mallaka mana mijin a hannu, sai yanda ƙawata ta juya shi, daga shi har danginshi, kuma a mantar dashi ƴan uwanshi. Ko iyayenshi ne suka faɗa bama so yayi, sai abunda matarshi tace mishi, duk da cewar daman kusan a hakan yake. Gaula dolo muke so a mayar dashi. Itama Amaryar ta zama sai abunda Zubaina tace mata, ta zame mata kamar baiwa, kuma a rufe mata bakinta karta kuskura ta kai ƙarar Zubaina, a sa mata kwarjininta, da tsoronta a zuchiyarta. Sannan muna son a lalata mishi gabanshi, ta yanda in ya je kwanciyar Aure da Amaryar zai koma kamar lagwani, in ya xo kwanciyar Aure da Zubaina sai ya zama namiji. A taimaka mana." Matar Boka data gama ji, sai ta zayyane ma boka dukkannin abunda yake tafe damu. Yayi magana amman ba mai yawa ba, cikin yarenshi na Tubi. Uwar gidan boka ta dube mu tace.
"Yace duk abinda kike buƙata zaki samu, amman da sharaɗin duk abinda zai biyo baya kar ki zargi kowa. In dai mallakar miji da kishiyane kin samu, kuma har ki mutu kece sarauniya a gidanki" Da sauri nace.
Na yarda da duk abinda zai biyo baya in dai ba mutuwa ko hauka, ko rasa Bulama bane, ni kuma a shirye nake ko nawa ne in kashe, ko da zan tafi tsirarane" Uwar gidan boka ta isar da saƙona ga boka. Dariya yayi, ya ɗaga hannayenshi dukka biyu sama, ya dinga wasu surkullen maganganu da ƙarfin tsiya. Sai ga wata ƙwarya ƙarama da wani tsumma ƙulle a hannunshi. Ƙwaryar ya sauke, ya miƙo ma Uwar gidanshi, tasa hannu ta amsa ta miƙo mun. Da sauri nasa hannu na karɓa. Wani irin maganine mai mugun warin tsiya, ga wani irin hunhuna da tsutsa a saman kwaryar. Amman haka uwar gidan boka tace in shanye maganin tas. Dana kafa kaina, na runtse idanuna ban ɗago ba, har sai da na shanye. Ƙwaryar na ajjiye ina ɗaga kaina sama dan wani irin amai ne naji yana taso mun. Wani ƙullukan magani ta karɓo a hannun boka ta ajjiye a cikin tsumma a gabana.
"Wannan wanka zaki yi dashi da kin je gidanki. Wannan kuma kwalline wanda aka haɗa da kitsen maciji, da kitsen biri, shi kuma a ko da yaushe idanunki ya zama yana saye da kwallinnan, sharaɗin shine daya ƙare zaki dawo a baki wani. Wannan kuma hayaƙin gidanki zaki yi dashi, ki tabbatar mijin naki, da ita amaryar sun shaƙi hayaƙin a dai dai sanda yake tashi. In zaki zuba hayaƙin a wuta, ki ambaci sunan mijinki sau uku, kishiyarki sau uku, sai ki zuba hayaƙin. Wannan kuma a abinci zaki zuba musu, an gama in dai sun ci. Shi kuma wannan layar, a bayan ɗakin baccin mai gidan naki zaki tona rami ki birne kuma tsirara zaki yi sanda zaki birne layar, kar ki kuskure, sannan kar ki bari kowa ya ganki. Kuɗinki million ɗaya. In zaki dawo karɓar kwalli da wasu hayaƙin kuma dubu ɗari biyu zaki riƙo duk zuwa." Cike da murna na zuge jakata nayi ƙarkaf, Allah ya soni ma kuɗin sun kai, har da ɗoriyar dubu goma sha ɗaya, duk na tarkata na ajjiye musu. Muka fito da baya, kamar yadda aka umarce mu. Mansa na ganinmu ta miƙe tana yashe baki.
"Har kun fito, sai mu je ko?" Jerawa mu ka yi, muna tafe Mabaruka na yi mun Dariya. Mansa tace.
"Ai daga yanzu kin dena bin ƙananun bokaye, shifa akwai biyan buƙata, sai dai ƴan siyasa da masu sarauta sun ɓata shi da tsadar tsiya, ni yanzu dubu ɗari biyu ya chajeni na magani kawai, banda sauran ƙananun abubbuwa. Sai dai fa zuwa wajanshi na sa talauci. Dan wallahi da mijinmu mai arzikin gaske ne, amman a halin yanzu komai nashi ya ja baya, kuma ya tabtabkar asarori masu tarin yawa manya_manya. Amman wallahi ko nawa ya samu a gabana yake zube mun su, ni ke siya ma kishiyoyina hatsin da zasu ci, in fa naga dama kenan. In kuwa banso ba, sai dai ko wacce ta yi surfau ko wankau ta ciyar da kanta da yaranta." Mabaruka tace.
"Ni kaina sanadin zuwana nan, na rasa abubbuwa da yawa, hatta Adamu sai da samun kuɗinshi ya ragu. Amman babban farin ciki shine ka mulki miji, ka juya kishiya yadda ranka ya so, kuma sai yanda ka tsarama mijinka sannan zai bi" Ni dai bana ma jin me suke cewa sosai, hankalina yana gida, burina in isa gida, ko dan in soma zartar da aikin da boka ya bani"




MRS BUKHARI CE. Ina siyar da turaren wuta da humra, da KULACCHAM, ƙamshi nauyi da ban daban. Akwai shu'umar humra ma, ga turarukan tsugunno, ga turaren turara jiki, dana turara kaya, mopping musk, Arebian Roomfresher, turaren kafet da dai sauransu Mrs Bukhari ta tanadar muku domun samun nutsuwarku. Mai buƙata ya tuntuɓeni (08179523215) ina maraba da masu sayen ɗaya ko sari.




_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 July 20 in sha Allah._






_1-NIHLATUL-KHAIR_
👇🏽
*(Ummu Affan)*




_2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*




_ZULFA_
👇🏽
*Ummu maher(miss green)*




_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_


Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank


Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽


08104335144


Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽


08104335144




*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽


08104335144
07068606171
08179523215


Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽


2K
sati biyu
3k


idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.






Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼


*MAMAN ZEE ƘAMSHI AND KAYAN MATA!*
Shahararu goma kenan aduniyan kayan mata munsan kanmu munsan kayanmu bah ako inazakisamu kayan shahararu goma aduniyan kayan mata sai awajen m zee kamshi kayan mata available online
Gakayanmu kamarhaka
Tafi budurwa duniyane
Tsumin lahaula
Gombar bujenki jagab
Shu Umar zumarmu
Mumuna da,aeki
Makalemata
Hadin me jego d amarya d uwar gidan d bazauwara
Dahuwar kaza cicibin kala kala
Shu,mar humra baka d Fara namatan aure ne kawai akwai Nayan mata
Turare wuta kala kala saiwanda kikazaba kayanmu batarkace kayane na matan kwairai kumakunsani shahararu goma aduniyan kayan mata m zee ce dakanta 08063845136 ko 07019551505 Kar abaki labari.
Sannan maganin sanyi ba Sai kinada infection zakiyi amfani dashi ba Dole ne ga KOWACE mace maganin sanyi ya zama daya daga cikin abinda ba a rasata dashi a gidanta sannan kuma
AMARYA
MAI JEGO
WACCE ZATAYI KOME
Dolene kiyi amfani da maganin sanyi kafin ku hadu da miji wannan Dole ne indai kinason kiji dadin muamala da miji.
Duk amaryar da aka kaita dakinta batayi amfani da maganin sanyi ba toh tabbas tayi babban kuskure hakama duk Mai jego data haihu har ta Bari tayi arbain suka Hadu da mijinta batasha magani sanyi ba itama ta tapka babban kuskure.
Wllhy kaya na aiki kinga ikon Allah Wai😂🔥🔥🔥🔥🔥ance wanda y iya y huta toh wanda y siya ma wllhy yafi kowa hutawa Allah dai y biya. Ku tuntuɓe ni a wannan number domin ƙarin bayani, muna aika kayanmu ƙasa-ƙasa gari-gari. Sayen nagari mai da kuɗi gida. 08063845136 sai kunzo.
[26/07, 2:35 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
GAWURTATTU UKU
9




Yahanasu:
Tun asuba su Yanunu suka kammala shirin tafiyarsu tsab, harma su Bulama ƙarami ya saka musu jakunkunansu a mota. Ni kuwa ina kwance ina hawaye, ga wani irin mayen zazzaɓi wanda dashi nake tashi a bacci. Wakil ne ya leƙo ɗakin da muke yace.
"Yahanasu mu kam sai Allah ya ƙaddara saduwarmu, sai kun zo ganin gida, aita haƙuri. Ba Bagulaji Bulama Babba ya ba mai gadi dubu hamsin wai a baku, shi ya tafi wajan aiki. Matar gidan ma a wajan aiki ta kwana, ƙannenta da yaranta ne a cikin gidan. Mama Gana wacce ke tsaye tana gyara tsaiwar lafayarta tace.
"Kamar yadda ya bar ma mai gadi sallahu, nima ga sallahu ka bayar a ajjiye mishi. Dan ubanshi tun kafin yazo duniya muke ta'amali da kuɗi, da wannan kuɗaɗe aka gina mishi rayuwarshi ta fannin ilimin addini dana zamani, dan haka ba kuɗi bane ya kawo mu, a bar mishi kuɗinshi.

11 / 67