MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   23 / 67

66K to 69K   out of 198.3K words

tsaye a ƙofar ɗakina ina kullewa, Yusuf yana goye a bayan yarinyar dana ɗakkota zata dunga kula mun dashi a office, ina biyanta duk wata. Murhun da Yahanasu take girki na duba, naga tukunyar ruwan wanka ne kawai a kai, da mamaki nace da Hajara dake zaune tana fifita wuta.
Hajara, yau waccan yarinyar bata yi abun kari bane?" Dariya Hajara tayi harda girgiza kanta tace.
"Ai kuwa tayi, yanzu ta tafi wajan aiki a gurguje fa"
Kusun uwa ta fita fa kika ce, tana nufin ni da yarana ba wanda zaici abinci kenan ko me take nufi" Hannaye Hajara ta haɗa ɗaya ya daki ɗaya tace.
"Wannan tambayar taki ai bani da amsarta. Amman dai ta fita wajan aiki. Yanzu naso in leƙo inyi miki magana, kar yara su sani latti naga har bakwai saura basu karya ba" A fusace na shiga ɗakin Yahanasun cike da ruwan bala'i da masifa na durarma Bulama. Yana zaune yana cin wani ƙazamin ɗumamen tuwo da ruwan bunu.
Meye haka Bulama, wanne irin bura ubancine yasa ka bar matarka ta tafi wajan aiki ba tare da ta yi ma yara girki ba? Wannan ai wulaƙanci ne, kuma kana ganinta. Yanzu yaya kake son nayi? Operation ne dani a sabon gari da safennen, ya kake son nayi da yaran, ga Yusuf kwana yayi yana kuka." Miƙewa yayi tsaye ya fuskanceni yace.
"Ai ina ganin taci ai mata uziri tunda ta kwashe tsawon shekera guda ita ke yin komai a gidan, kama daga girki, shara, wankan yara, wankinsu, da nawa da naki, gyaran ɗakinsu. Dan yau ɗaya data fita bata yi ba, ai kema sai ki kama. Ni nafa gaji da wannan fitinar taki, ya kamata ki san ni ba yaronki bane, balle kiyi ta takani. Sabida yanzu bani dashi shine kika kasa yin haƙuri dani. Dai dai da nera biyar ɗinki bana ci a gidannan. Matsa mun ni" Yasa hannu ya tureni gefe, ya fito. Ni mamaki ma yasa na kasa motsi gani nake yi, kamar mafarki nake yi ba gaskiya bane.
Asirin ya karye kenan ko me, dan kwalli na ya ƙare, jiya nake magana da Mama akan ta aro mun ko da dubu ɗari biyar ne, inason in je wajan boka. yarinyarnan wato zuwa tayi aka karya mata asirin da na kashe uban kuɗi wajan yinshi?" A haukace na fito. Cukume Bulama nayi, ina ihu ina jijjiga kamar ƴar tasha, ina faɗin.
In ka cika cikin uwarka baƙarnan da ubanka ka sakeni, ni dai kai ɗan halak ne, ba zina akayi aka haifeka ba. Bazan zauna da kai ba. So kake yi talauci ya kasheni kome. Bulama sake ni, nace ka sake ni ko." Ahmad ne ya fito da sauri ya iso wajan.
"Baki da hankaline Zubaina kanki ɗaya kuwa, Bulaman kika cukume kina mishi irin wannan ihun kamar a gidan magajiyar karuwai? Ai kaga illar auren ƴar bariki wacce ta saba cin kwalar maza kenan" Cikin rufewar idanu, da zafin kishi nace.
Ai nafi magajiya ma ni. Ya sake ni, in yana son kanshi da arziki, kar ka kuma sa mun baki a magana kuma tsohon munafuki"
"Ki sake ni ko in daka ki a tsakar gidannan jahilar banza wacce bata san darajar aure ba, maras tarbiyya. Ko da yake a ina za'a koya miki tarbiyyar ma" Dariya na saka kamar mahaukaciya nace.
Ni zaka daka? Ai sai dai mu daki juna ba dai ka dake ni ba wallahi, shege ɗan iska." Kafun in rufe baki Bulama ya yanka mun mari mai zafi. Banyi wata wata ba, na dunƙule hannayena na luma mishi a ciki, irin naushin da muke ma ɓarayi a cikin sell cikinsu ya ƙulle. Nan kokawa ta ɓalle a tsakaninmu, sai zibgata yake yi. Ni kuma sai cunkusama iyayenshi ashar nake yi, bakina duk jini, shi kuwa dukana yake yi kamar Allah ne ya aiko shi. Maƙota suka taru a cikin gidan. Maza su ka lallaɓa Bulama ya rabu dani, jikinshi har rawa yake yi, idanunshi ɗaya na fitar da hawaye. Ahmad ya ja hannunshi suka fice. A guje na shiga ɗakina, na tattaro kayana da kayan Yusuf na fito, bakina da hancina duk a dauje suna tsiyayar jini, gaskiya na daku irin dukan da babu mahalukin daya taɓa mun irinshi. Kunce goyon Yusuf nayi a bayan Zuwaira mai kula mun dashi, na mayar dashi bayana. Na kulle ɗakina na ɗauki jakata.
"Zubaina in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Kar ki tafi gida Zubaina. Maganar gaskiya kece da laifi, irin zagin iyayenshi da kika dinga yi, ba dan yana da tunani ba, ai da tuni ya sauwake miki. Ni in banda a Lagos ban taɓa ganin irin wannan tsiya da wasali ƙasan ba. Mata ki haukace mana a gida sai kace a agege ko a ƙarƙashin gadar C M S"
MRS BUKHARI CE


wasa farin girki. Yanzu ne zamu shiga asalin labarin gadan_gadan. Ina masoyan Yahanasu ku fito ku taka rawa. Yau Kofur ta daku."
[30/07, 7:32 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
17




*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*
















Rufa mun baki munafukar Allah ta'ala, masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki. Ke da munafikin mijinki. Sai ku hanani tafiya ai, shegiya sai shegen tsigudidi" Ina faɗar haka Hajara ta tashi, ta soma jijjiga tana zage_ zage. Ni da ita sai da muka ci uwar sabada sannan na saka kaina, daman a kusa nake, na kuwa zage na kirɓeta sosa.i Kai tsaye tasha na zarce. Cikin awa ɗaya motarmu ta cika mu ka nufi kaduna. Sai huci kawai nake yi. Gashi bani da isassun kuɗin da har zanje wajan boka yaimun wani sammun, sai dai nayi dabarar ɗebo manyan zannuwan dana samu a sunan Yusuf. Ina zaune ina tunane_ tunane, sai ga kiran Mabaruka. A hanzarce na ɗaga nace.
Dama ko baki kira ba, zan kira ki, so nayi sai na sauka a mota tukunna. Gani a hanyar zuwa Kaduna, waccan matsiyaciyar ta ruguzamun shirina, yau dambe mu ka yi da Bulama, ya dake ni na dake shi, baki ga yadda ya farfasamun fuska ba." Wani namiji ne a kusa dani ya wani juyo da sauri ya kalleni. Harara na galla mishi, ba shiri ya kawar da kanshi. Mabaruka tace.
"Hmmm Zubaina ni kaina a cikin matsala nake mai girma, kin ganni a gida yau kwana uku kenan. Adam ne ya turo mun da takaddar saki a waya. Gashi nera biyar bana magani balle in je wajan boka, kayan ɗakina nayi tunanin ko in siyar, sai in je dama, sai kuma na tuno dake, kinji dalilin kiranki da nayi. Ashe kema asirin ya lalace?" Ƙwafa nayi nace.
Ki rabu dasu, daga Adam ɗin har Bulama sai sun yaba ma aya zaƙinta, ƴan aiki sai sun fisu daraja, bari dai in shigo kadunan" Sallama mu ka yi, na sauke wayata. Awa huɗu ya shigar damu kaduna garin gwamna. Mama na zaune jigum na shigo gidan da kuka wiwi. Da sauri ta miƙe.
"Me zan gani Zubaina? Asirina ya tonu meya same ki a baki da hanci haɗarin mota ki ka yi ko me?"
Hmmm Mama Bulama ne ya dakeni. Tsinanniyar yarinyar nan sai da tayi kwanta_kwanta ta karya duk wani sihirin da ke jikin Bulama. Yau ba dan maƙota ba Bulama da kasheni zaiyi. Mama ta shiga salati tana tafa hannayenta.
"Oh ni Jummai, to wai mema ya haɗaku har ta kai da duka, kaji mun matsiyaci sakin ki to yayi?"
Ina fa bai sake ni ba, barin mishi gidanshi nayi. Sai na mugun gasashi kafin ya koma, sai yayi ta zubda hawaye, yana saka guiwarshi a ƙasa kafin na yadda in koma. Zama nayi na kunto yaron bayana, mama ta karɓeshi.
"Kafin ki tawo kin sanar ma da ƴar uwarki kuwa, kar taje gidan bakya nan Bulama ya dakata itama. Kafin in bata amsa, muka jiyo sallamar wasu mata su biyu. A tare suka shigo, da gani uwa da ƴa ne.
"Nanne gidan su Musa ko, kece mahaifiyarshi? Mama tace.
"Nice baiwar Allah lafiya kuwa"
"Sakina nemi waje ki zauna, yaro yazo gidan ubanshi. Kin ganta nan, ɗanki Musa ne yai mata fyaɗe, ta hanyar yaudararta da sunan zai kawo ta gaisuwar surukai yasa mata maganin bacci a lemo, naso in shigar da ƙara tun lokacin da abun ya faru, amman mahaifinta ya dinga lallaɓani dan gudun zubewar mutuncinshi a idanun duniya, bai duba hakkin yarinya ba. Tun daga ranar da Musa ya biya buƙatar shi da Sakina ya dena Zuwa zance wajanta. Kwatsam sai ga ciki ya ɓullo a jikinta har na tsawon wata uku. Shine na kawota ta haife yaron a gabanku, domun ku ke da alhakin ciyar da ita da abunda yake cikinta." Mama bata gama jin zancen ba ta miƙe nan suka soma buyagi da wannan baiwar Allah, itama naga halama da shirinta ta zo.
Mama wannan hayaniyar duk ba ita bace mafita. Halin Musa babu wanda bai sani ba a unguwarnan. Ciki dai nashi ne, amman baiwar Allah ki tafi da Sakina, zamu ɗauki alhakin ciyar da'ita har zuwa ta yaye abunda ta haifa, sai mu karɓi abunmu. Mama ta dura tace
"Akan me zaki ce musu haka Zubaina lafiyarki kuwa?"
Mama case ɗin fyaɗe case ne babba wanda in ya je gaban ƴan sanda kai tsaye kotu ne, daga nan sai gidan yari. Mu lallaɓa a samu a rabu lafiya, ɗan kuka mai jama uwarshi jifa" Da ƙyar wannan baiwar Allah suka koma tare da bamu kwatancen gidan da suke. Mama ta fashe da kuka tana.
"Ni na shiga ukuna wannan yara so suke su kasheni su huta kawai, kullum hawan jinina baya sauka sai kuma hawa, ni inaga gidan zan bari." Sagiru ne ya shigo da fito, sai wani cije baki yake yi kamar shugaban ƴan tauri, butoci da bokatan ƙarfen gidan ya soma yin boll dasu. Mama ta ƙura mishi idanu yana ta buyaginshi, kallona yayi.
"Ke kuma yaushe a garin ne?" Banza nayi dashi, nan ya gama zage zagenshi ya wuce mu.
"Kin ganshi nan, ƙwaƙwalwarshi ta gama lalacewa ya haukace, wataran haka zaki ji yana danna ihu a tsakar gida haka sittan. Shi kuwa Musa ko Ayu dole ya sara mishi, ɗakinshi baya shiguwa kullum da mace, kinga gashi ya bankama wata ciki, shikenan muma mun samu ɗan dakan kuka a gida." Ni gabaƙi ɗaya ma sai naji zazzaɓi na shirin kwantar dani. Mabaruka ce tayo sallama ta shigo.
"Lallai Mabaruka yau kece a gidan namu, idanki kenan? Dariya Mabaruka tayi tace.
"Mama ayi haƙuri damu, yanayin aikin asibiti ne sai a hankali, babu lokaci. Ina wuni Mama" Da fara'a Mama tace.
"Lafiya lau, ya gyatumarki, da mai gidan naki?"
"Duk suna lafiya Mama " Mama tace.
"To madallah Allah yayi albarka" Hannun mabaruka na kama muka shiga ciki. Nan muka shiga tattaunawa, mun tsayar da matsayar gobe zamu shiga Jos, ni zan siyar da atampopina Mama zata ranto mun wasu kuɗaɗe in haɗa, mabaruka kuma zata siyar da Kayan ɗakinta tas mu rankaya mu je wajan boka, faɗa da cikawa.






Bulama Babba:
Jikina yana rawa muka fita daga cikin gidannan, mata sunyi cirko_citko a ƙofar gidan, haka muka rakuɓe gefe muka wuce, sai ambaton Allah nake yi, jikina na ɗaukar wani irin zafi irin na mashasshara mai ƙarfi. A dai dai ta sahu Ahmad ya tare muka faɗa. Jingina nayi a jikin kujerar a daidaita sahun, na lumshe idanuwana a hankali ina jin wani sanyi na huda dukkannin wata mafaka ta gashin jikina. Ƙwaƙwalwata ta shiga tariyomun irin wahalhalun da Zubaina ta dinga sani inayi mata, da irin wulaƙanta mahaifana, da ƙanwata Yahanasu da nayi, da irin ɓarin dukiya da naita ma makirar uwarta, da marasa kunyar ƙannenta. Dukkannin wannan al'amura dawomun suke yi kamar yanda ake tariyo faifayin filet sidi. Na tuno lokacin da na bijiro da zancan auren zubaina kalmar da Ba Bakura ya faɗa mun.
"Bulama ni dai yarinyar nan ko da naga hotonta hankalina bai kwanta da'ita ba. Idanuwanta sun buɗe da yawa. Tunda mahaifiyarka ta ga hoton yarinyar, ta shiga tunani mai zurfi. Jiya ƙarfe biyun dare ta tasheni a bacci sabida zancan. A zahiri daga ni har ita hankalin mu bai kwanta da yarinyar ba, taya ma da hankalinka da tunaninka zaka auri ƴar doka?. Bance maka aikin doka ga mata haramun bane, ko ɗaya. Amman a zahirin gaskiya aikin yafi dacewa da maza, duk wani aikin kaki yafi dacewa da maza, duk da matan suma akwai muhimmiyar rawar da suke takawa. Domun dasu ake shigowa gidajen mata, su riƙe hannayen mata su tafi dasu. Buɗewar idanunta da gogewarta shi yafi ɗaga mana hankali. Mace mai wayewa da buɗewar idanu da yawa, tana da wuyar sha'ani, da wuyar sarrafawa. Amman bance ka auri ƴar ƙauye ba, dan gidanku duk ƴan boko ne, amman wanda suka ƙoshi da karatun addini, tunda a tsarina duk sai da kuka sauke Qur'ani mai girma, kafin kuka soma jami'a. Ina jiye maka me ka je ka zo, kuma kaine ka fita zakka a dangi. Dan babu wanda ya taɓa auro mana bare"
"Kai Bulama ina tunaninka ya tafi ne, sai kiranka nake yi baka ko ji? Da sauri na kalli Ahmad harya fita daga cikin ɗan sahun yana tsaye. Jiki a saɓule na fito nima, muka sake hawa wani abun hawan. Da ni dashi babu mai cewa da wani kanzil, kowa da abinda yake tunani, a haka har muka iso wajan aiki. Kowa ya nufi block ɗin da yake kulawa dasu, dan soma gudanar da aikinshi, bayan mun cika takaddar shaidar zuwanmu, da lokacin da muka iso aiki. Zirga_ zirga nake ta faman yin ina duba mazauna cikin gidan yarin a hankali, amman babu nutsuwa da kuzari a jikina ko kaɗan. A hankali na zaro wayata tare da lalubar number Ba Bakura, cikin faɗuwar gaba da taraddadin me ka je kazo na kara a kunnena. Amman harta ƙaraci kuka ba'a ɗaga ba. Na kira sama da so bakwai, daga ƙarshe naji wayar a kashe. Da ƙyar na mayar da hankali na bakin aikina, na tabbatar da maganar bada abincin karin kumallon block ɗin dake ƙarƙashina, sai da na tabbatar kowa ya samu, sannan na koma gefe na kira layin Ba Modu shima ya ƙaraci kuka ba'a ɗaga ba. Idanu na lumshe ina jiyo wani ɗaci yana ratso huhuna har izuwa kan harshena, da ƙyar na fisgo numfashina daga huhuna zuwa ƙofofin shan iska na. Hajja Gana na kira, ban sameta ba, na kira Dala bai ɗauka ba.
Ya Allah ka kawo mun agaji, nasan na cancanci ko wanne irin hukunci daga magabata na, ya Allah ka bani juriyar rashin iyayena har su sake yarda dani a karo na biyu, in sake zama ɗansu. Allah kana ganin komai, dukkan abinda ya faru bansan musabbabin faruwarsu ba, sharrin shaiɗaniyar mace ne yai tasiri a kaina. Zunaina kin cutar da rayuwata, Allah ka saka mun." Sauke kaina nayi wanda yake yi mun wani irin mugun ciwo, dole in ɗauki hutun aiki, in tafi Damaturu domun roƙon gafarar iyayena ko zanga dai_dai. Wasu hawayene suka gangaromun a kumatuna masu mugun ɗumi. Dana tuno da hawayen da mahaifiyata ta dinga zubarwa, a ranar da nayi musu iyaka da zuwa gidana, da irin tashin hankalin da na gani a fuskar Ba Bakura. Zubaina koma meye tamun ta rabani da farin cikina ta cuceni, wallahi Allah bazai barta ba. Ina komawa gida zan sallameta ta tafi gidansu, zama da'ita ya ƙare, dan rabuwata da'ita shine farin cikin iyayena da dangina baki ɗaya. Kaicona dana shigo mana da bara gurbi cikin zuriyarmu, kaicona da na zamto silar ɓacin ran iyayena da dangina. Abubbuwa sukaita dawomun kaina, inajin tamkar zan zare ne. Ƙarfe goma aka kaɗa ƙararrawar fito da fursinoni cikin yadi, sannan a lokacin wasu suna da ajujuwan ɗaukar darasi, akwai kuma ɓangarorin koyar da sana'o'in hannu iri daban_ daban. Juyawa nayi dan zuwa ɗakin hutawa, zazzaɓi ne mai zafin gaske a Jikina. Ina cikin wannan halin Ahmad ya shigo shima dan ya huta.
Ahmad kana ganin Ba Bakura zasu yafe mun kuwa, kana ganin zasu sake dani har in zama kamar da a zuchiyoyinsu? Ahmad Zubaina itace ta raba ni da kowa nawa, dukiyata ɗan wani abu ƙalilan iyayena da ƴan uwana suka samu. Amman Zubaina da makirar uwarta su naima aiki. Kuma sanadiyyarsu na rasa aikina na tsiyace. Dubi irin ɗiban albarkar da yau Zubaina tai mun a tsakar gida?" Daurewa nayi da ƙyar na mayar da wani irin kuka da yake ƙoƙarin amayo kanshi. Ahmad ya dafani yace.
"Alhamdulillah babu abunda zamu ce da Allah sai godiya.

23 / 67