MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   66 / 67

195K to 198K   out of 198.3K words

zan koma ɗakina. Shine fa hankalinshi ya mugun tashi, sai kirana a waya yake yi yana cewa.
"Ya zanyi da sonki Yahanasu, yanzu kema kin yarda a rabamu?" Ire_iren kalaman da yake ta jifa na dasu kenan duk yabi ya rikice. Ni kuma bansan ma ina sonshi ba, sai da aka sa ranar ɗaurin aure na da Bulama Babba tukunna. Ina kara wayar a kunne sai naji muryar mace.
"Hello Yahanasu Maman Amira ce, kin ganni a Damaturu." Da murna na tareta nace.
Da gaske Maman Amira, kina ina yanzu haka?" Cikin fara'a tace.
"Ina tasha saukata kenan" Ba shiri na zari mayafi na wuce gareji da mugun saurina mota na shiga na fice fuu a gida. Sai tasha, a zaune a wata rumfa na sameta tana jirana. Rungume juna mu ka yi da murna, sai hawaye kuma sai kuka mai sauti ya ƙwace mana. Yana da nasaba da irin rayuwar da mu ka yi a rihab mun ci wuya iya wuya. Janta nayi muka shiga mota. Sai da muka share hawayenmu tas sannan na ta da motata mu ka bar tasha.
"Sai yau kika kirani. Kinsan ku baku bani numbobin wayoyinku ba, sai dai adireshi,. Ina Zainura kuna zumunci dai ko tunda garin ku ɗaya?"
"Muna zumunci sosai ma, ta yi alƙawarin zata zo itama sai mu koma tare in sha Allah. Kin ga yadda kika koma kuwa Yahanasu Bulaman ki ya tsaya miki" Dariya kawai nayi mata nace.
Ke ma kin yi shar dake Maman Amira. Ina Sani ya kuka ƙarke?" Dariya ta kwashe dashi tace. Labari yana gaba, bari in samu in watsa ruwa in ci burabusko zaki ji labari filla_fillah. Da haka muka iso gida. Motar Alh Nura na gani a cikin gareji yazo kenan. Muna fitowa daga mota ya karaso in da muke. Idanu na ƙura mai naga ya rame ainun. Ɗan murmushi nayi mishi carab a idanun Bulama Babba wanda fitowarshi daga gida kenan da halama fita zaiyi. Kallona yayi naga idanunshi sun cicciko da ruwan hawaye. Na shiga tashin hankali sosai. Ƙarasowa yayi in da muke ya ba Alh Nura hannu suka gaisa, jikin Bulama Babba yayi wani irin mugun sanyi. Maman Amira ta gaisheshi na gabatar mishi da'ita. Ya ma kasa magana sai ɗan guntun murmushi yake yi. Yana shiga motar shi, nace ma Maman Amira ta jira ni ina zuwa. Anan na barta ita da Alh Nura. Murfin motar Bulama Babba na buɗe na shiga gaban motar. Kanshi ya ɗago daga kan tiriyarin motar. Idanunshi sun ƙanƙance sun kuma yin ja, take jikina ya mutu. Haƙiƙa nasan Bulama Babba yana sona so na haƙiƙa so mara mis a cikinshi, Alh Nura tausayi yake bani, amman zallar soyayya Bulama Babba nake yi ma. Domun a zaman mu Bulama ya soni, ko da aka tursasashi ya rabu dani sai da ya bini da Alkhairi.
"Na lura ni kaɗai nake ƙwaɗayin yin rayuwa dake a karo na biyu Yahanasu. To bazan miki dole a karo na biyu ba. Tunda kin fi tausayin Alh Nura to ni na haƙura. Inai muku fatan alkhairi Allah ya baku zaman lafiya, zan sanar ma Ba Modu na janye" Hawayene suka gangaro a kumatunshi. Take na rushe mishi da kuka dan bansan mai zance mishi ba. Nasan baya son kukana, kukan kaɗai zan yi ya tsaya ya saurareni.
"Kukan na menene shin ba haka kike so kiji nace ba?"
A'a kaima kasan babu wani ɗa namiji da zai iya ture matsayinka a rayuwata balle har ya maye gurbinka. Shin kasan irin ƙunci da takaicin da zuchiyata tai ta shanyewa a kan ka kuwa, kasan yadda naji a karon farko da naga Yalewa da cikin ka kuwa? Ina sonka kaima ka sani, ina farin cikin wannan komen da zanyi, ai yanzu ne zamu yi auren soyayya kayi haƙuri. Alh Nura baza ka sake ganinshi ba. In ƙawata bata da wani tsayayye zan haɗa su in sun amince" Idanu muka haɗa yayi murmushi ya sauke ajjiyar zuchiya. Nima murmushin nayi mishi nace.
Shikenan ƙasusuwan jikin ka sun kwanta ko?" Ido ya kashe mun yace.
"Za dai su kwanta sarauniya in na ganki akan shinfiɗata ina gurzarki" Da sauri na fice a motar ina dariya. Wajan su Alh Nura na nufa.
"Alh ai mun afuwa na barku ku kaɗai. Yanzu dai kaga ina da baƙuwa zamu yi waya ko kuma da daddare mu haɗu" Sallama mu kai ma juna muka shiga ciki. Nuna Maman Amira nayi a cikin gida mu kaita zagaye zagaye. Kafin muka ya da zango a ɗakina. Bayan tayo wanka tana cin abinci ne tace.
"Ni fa kaina duk ya ɗaure Yahanasu. Ni na ɗauka zan ganki a gidan mijinki sai naga saɓanin haka. Kuma naji anata ce miki Amarya meke faruwa ne?" Na ɗauki Maman Amira ƙawa Aminiya. Labarin komai daya faru na bata, tace
"Amman gaskiya na tausaya miki sosai. Hajja bata kyauta ba, amman ta gane kuranta ai da taga za'a hallaka mata ɗa. Hmm ni ai ko ƙuda ya kasa shinshinata, duk wanda yazo wajena ɗaya biyu shikenan baya kuma zuwa, kinsan hausawanmu abu baya wuce musu. Ni kuwa rayuwata nake yi a nitse, ina juya kuɗaɗena bani da matsalar komai. Ai baki sani ba. Ina komawa gida da sati muka soma zurubtun zuwa kotu da Sani. Kinsan sha'ani na maganar kotu mun kai wata takwas ana abu ɗaya. Kab dukiyata ta dawo hannuna harda bashi da nake binshi. Yanzu haka yana gidan kyaran hali zai ɗan yi aiki na wata huɗu haka. Na ji labarin ma ita yarinyar daya aura sun rabu, tun muna sintirin zuwa kotu da ta tabbatar da gaske fa dukiya zata dawo hannun mai ita" Nayi farin ciki sosai da jin wannan labari. Da wannan damar nayi amfani na shigar mata da zancan Alh Nura. Alhamdulillah tayi na'am, ta ɓangarenshi shima ban samu matsala ba, dan maman Amira kyakkyawar mace ce son kowa ƙin wanda ya rasa. Kwanan Maman Amira uku Zainura tazo itama. Bulama Babba ya dinga zaga garin Damaturu damu. Har Yobe mu ka je suka ga gidana da zan zauna. Bulama Babba sai sake gyara gidan yake yi." Naji daɗin wannan zumunci sosai.
Bayan wata biyu muka shiga shagalin bikina, da bikin Wakil wanda sabida rashin lafiyata aka ɗaga. An yi shagali sosai, Hajja ta yi bajinta ainun a wannan biki namu. Bayan an gama duk shagali kuma muka nufi Yobe, amman Ya Innana tace abar mata yaran dukka su dawo Damaturu da zama baki ɗaya. Gida daga ni sai Bulama Babba.
Wata iriyar rayuwar soyayya da jin daɗi muke gudanarwa tamkar zamu haɗiye junanmu. Lallai Bulamana yayi kewata kewa mai yawa, ni kuma na saki jiki na faranta mishi ranshi sosai. Shi kanshi yayi mamakin yadda na zama ƴar duniya ƙarfi da yaji, yanzu ne muka san munyi aure a baya wasa muke yi na yiyyi amfani da maganguna ingantattu da wani haɗin turaren tsugunno ina na matan Kanuri wanda yake maida tsohuwa yarinya, wannan turare ko wacce matar Kanuri da matan shuwa dashi suke bugun ƙirji, yana tattare da wasu irin surruka na musamman ne. ( Me so ta tuntuɓeni 08179523215) Kasancewar ni kaɗaice a ɓarayina, kullum cikin shigar ƙananun kaya nake, gyaran jiki da kwalliya sun sa na zama mai kyau, mata da yawa sai suke sha'awar fatata. Kullum gidana a cikin ƙamshi mai ni'ima yake, ƙamshi mai kwantar da hankalin mai gida, asalin ƙamshi na manyan mata, wasu irin turarukan wuta na al'adar Kanuri na haɗa masu dogon tarihi da surrukan kwantar da hankalin mai gida kana da kara danƙon soyayya ( shima akwaishi mai so tayi magana) Bayan wata guda da aurenmu muka tafi umara ni da Bulama Babba. Rayuwa ta warware na sake zama Hajiya ƙarfi da yaji. Aikin gidan TV ɗinma Bulamana ya hana, sai na mai da hankalina kan shagon gyaran jiki. Bulamana ya sake ƙawata mun shagona ya zama shahararren shago, turarukan wutanmu, da asalin ɓakar Humra mai taushin ƙamshi ta kabilar Kanuri ba ƙaramin cinikinsu muke yi ba, gyaran jiki mukam samu a ƙalla mata ashirin a rana, goma, takwas, in kamar ranakun Alhamis ne aikin kacame mana yake yi sosai. Maman Amira kuwa Allah yayi Alh Nura ta aura aka kawota Yobe zumunci ya saƙe karfi, muna zumunci sosai da su Zainura da Hadiza ma. A Damaturu kuma surukan gidan sunata hayayyafa, yara kullum sai cika gida suke yi. Fanna yaranta uku yanzu haka, Fandau kuma yaranta bakwai. Jikoki a cikin gidannan ba dama. Duk wutu in an samu Bulama yana kaima Zubaina yara su yi mata hutu. Muna waya da'ita muna zumuncinmu kamar babu abinda ya faru ma, rayuwa kenan. Tunda nakoma gidan Bulama Babba ban ko yi ɓarin wata ba, abun duniya duk yabi ya isheni, duk inda naji mai magani sai na karɓa, kuma a asibiti sun ce lafiyata ƙalau. Tun ina nema harna haƙura da naga shekaru nata shurawa, saina fauwalama Allah. Wata ƙila iyakar ƴaƴan nawa kenan waɗanda na zubar dasu a sanadiyyar shaye_shayen muyagun ƙwayoyi. Yalewa kuma har zuwa wannan lokacin batai aure ba babu ma wanda yake ko shinshinarta. Hajja wani irin so da kulawa take nuna mun, kullum saita kira ni a waya mun gaisa, in kuma ta samu masu zuwa Yobe zata aiko mun da saƙo. Mama Gana tun tana fishi harta sakko rayuwa ta dawo dai_dai zumunci yaci gaba da tafiya kamar Lokacin da Ba Bakura yake raye. Hankalin kowa a kwance yake sosai muna rayuwarmu cikin aminci gwanin sha'awa.


MRS BUKHARI CE
[23/08, 12:00 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: Gawurtattu uku
62




Ƙarshe.




Zubaina:
Tunda dai na roƙi gafarar su Bulama Babba suka yafe mun sai naji sanyi a raina. Yaran dana tawo dasu naji daɗi sosai. Suka gama hutunsu aka turo mota aka tafi dasu. Haka rayuwa tai ta shurawa. Kawu Tanko ya sai mun gidaje manya guda biyar na haya, aka zuba ƴan haya duk shekara ana karɓar kuɗaɗe masu yawa, sai ya bamu shawarar zuba hannun jarin wani kasuwanci. Shima na cire million uku na zuba. Anata dai juya ma marayu kuɗinsu. Muma nu na ci muna sha. Yarona na da wata tara sai ya yaye kanshi ya dena karɓar nonon kwata_kwata. Sai na yaye shi. Mabaruka ta samu ƙwari jikinta babu laifi, sai magani da take zuwa karɓa. Muna zumuncinmu dai dai yadda muka saba. Ana cikin haka wani ɗan kabu_kabu ya fito neman auren Asiya. Dake Allah yayi mijin nata ne cikin wata uku aka gama komai muka ɗau amarya mu ka kaita hayi. Itace ta uku a gidan, ɗakuna ɗaɗaɗaya ko wacce mata take dashi, sai falo wanda a cikin dalon ɗakunan suke. Ashe wannan bawan Allah baya iya ciyar da matanshi da abinci, su suke sana'a su ke ciyar da kansu da ƴaƴansu. Kuɗi na ware dubu hamsin na ba Asiya nace taja jari karta zauna haka. Bai fi wata ɗaya dana ƙarama Nafeesa jari ba itama sana'ar take yi, ita ke ciyar da ƴaƴa. Ko rabon kwana bayayi da'ita amman Mama tace tayi haƙuri komai mai wucewa ne tayi ta adda'a tana istigifari. Haka dai mu ke ta gurgura rayuwar. Musa ma yanzu babu aiki sam a hannunshi, kullum yana gida, matarshi kuwa a gaban Mama sai ta cukume shi, mu dai bama ce musu komai. Da shekara ta zago sai na cire dubu ɗari huɗu na sai ɗan sahu na ba Musa nace ya dinga kabu_ kabu dashi, ya kula da iyalanshi. Ana cikin haka Mama ta kwanta jinyar da ashe bana tashi bane. Kwananmu arba'in da shida a gadon asibiti. Wata ranar juma'a da safe Allah yai ma Mama rasuwa. Shikenan maraici ya ganmu ba uwa ba uba. Amman Kawu Tanko ya zame mana makwafin iyayenmu, shi ya tsaya a kanmu. Ya haɗani da wani almajirin gidanshi da ya yaba da hankalinshi. Mu kai aurenmu na tare a ɗaya daga gidajena, yana da mata tana rigasa da yaranshi huɗu. Ni kuma ina gidana da yarana. Ni ke musu komai, ƴan biyu sun kai shiga makaranta, na samu makaranta mai kyau na saka su a ciki. Nafeesa cikin amincin Allah mijinta yayi mata afuwa sun dawo suna zaune lafiya, yaci gaba da rabon kwana da'ita. Asiya kuma ta kama sana'arta tana ta jujjuya kuɗi. Har kasuwannin ƙauye take sarin kayan masarufi. Abun ya kankama sosai tana juya kuɗi. Ko data haihu ita da kanta ta dinga yi ma kanta hidima. Nima haka dana haihu ni na ɗauki nauyin komai hatta ragon suna ni nayi ma kaina, Auwal babu ruwanshi, sai dai ran kwanana yazo yaci abinci ya kwanta dani. Amman muna zaune lafiya na rungumi ƙaddarata kuma na gode Allah. Har wani rawar kai yake yi in kwanana ya zagayo,dan nafi matarshi nesa ba kusa ba, ko banza yazo yaci abinci da nama ai, to da kuɗina gaskiya muna cin abinci mai kyau ni da yara. Nayi ɓul_ɓul abuna, sai dai haskena ya disashe yaƙi dawowa sam. Mu kan kai ma Sagiru ziyara gidan yari. Shima ya shiryu ya zama kamar ba shi ba, sai karatu yake yi na addini a gidan yarin. Ni ma ina zuwa islamiyyar matan aure ina karatuna, kuma Alhamdulillah ina fahimta Auwal ma yana ƙaramun Quri'a a gida duk sanda yazo, rayuwar auren ina jin daɗinta gaskiya. Matar Musa ta sake ana zumunci da'ita tunda yanzu ko suna ko biki in ya tashi na family da'ita ake komai. Ko wancan satin Mama Zakiya ɗanta yayi aure da'ita mu kai ta jigilar komai. Hajiya Kubra Ghana muna waya sosai da'ita, haka Nabeela, ita kam har Zariya naje gidan da take aure. Muna zumunci sosai, dana sake haihuwa ma da'ita akayi hidimar suna tsab har aka gama kafin ta koma Zariya. A bakin Hajiya Kubra nake jin labarin Jaɓa ya haukace tuburan bola ma yake bi, sauran yaran Alh Liti kuma duk dukiyar da suka samu ta galgance ta hanyar neman matan banza. Wasu kuma sun gaji mahaifinsu ta fannin shahara a kasuwanci.
Rayuwa kenan in kaga ta wani sai kace taka da sauƙi. Wasu in suka ga yadda muke rayuwa tausaya mana suke yi. Mu kuma sake godema Allah muke yi a ko da yaushe. Dukiyar marayu sai sake burunƙasa take yi, ni kuma inata hidintama karatunsu da wannan dukiya, da ƙannensu wanda suke uwa ɗaya. Na dawo nayi fes dani kamar bani ba, haskena ya dawo nayi ƙiba sosai sabida cin daɗi. Bana dani za'ayi aikin Hajji in Allah ya nufa, na biya mana ni da Auwal. Mabaruka ta samu wani mai irin lalurarta ta rufa ma kanta asiri tana zaune lafiya dashi suna shan maganin akan ka'ida. Mu kan ziyarci juna, amman ƙawancan namu ya ja baya sabida sungulloli da su kai ma kowa yawa.






Yahanasu:
Ina tsaye hannuna riƙe da kaskon turaren wuta sai na jiyo sallamar Bawa da ƙannen nashi. Da gudu yazo ya rungume ni. Ya girma sosai shekararshi goma sha uku yanzu, yana SS 2 a fannin boko, a fannin islamiyya kuma yayi sauka.
Daga ina kuke haka ƴan samari? Na tambayesu shi da Yusuf. Maryam ce ta shigo ita da Ba'a kaka.
Ba'a kaka ashe tare kuke, anyi hutu sai Kaduna ko?" Muna cikin haka Bulamana ya fito daga ɗaki yana sanye da jallabiyya yau Sunday ne yana gida. Yaran ya kira su ka je suka same shi. Ni kuma na shiga fito da abincin karyawa. Sai da na gama nace.
To ku sakko mu karya dukkanmu." Bulamana yace.
"Wai yaranki fa wannan karon su baza su je gidan uwarsu ba, a wajanki zasu zauna. Wai Babansu Maryam ƙarama baya son kulasu, kuma in suka je kullum shi Baban a cikin rikici da uwar yake" Haɓa na riƙe nace.
To Allah ya kyauta. Kasan wasu haka su ke yi. Ku dai sakko mu ci abinci, sai mu fita siyayya ko?" Nan suka soma murna muna cin abinci da yara ina jansu da hira. Su kuwa sai surutu suke faman yi mun. Ashe Bulamana mu yake ta kallo ko ƙibtawa babu. Murmushi nayi mishi na soyayya. Bayan mun kammala karyawa sai Bawa yayi wanke wanke, Maryam kuma tayi shara na fito na sameta tana sake turaramun falon da turaren wuta. Ɓarayin su Hajara na nufa. A bakin kofa na samesu suna yankan nama, anayi Hajara na ma khairat jaraba. Dariya nayi dan Hajara ba zata sauya halinta ba sam, ba karamin chabta suke yi ba, ita Khairat akwaita da gwalangwaso, shi kuma Ahmad sabida wanna gwalangwason ma kamar yake jin ya kara sonta, Hajara kuma kullum a cikin rikici ake da'ita. Yanzu ne data nutsu na bata wasu surrukan turaren wuta, na ɗaki dana tsugunno, dana turara kaya, da humra uban ubansu. Tana ganina ta shiga yashe baki.
"Hajiya Yahanasu ni dai bazan dena mamakin irin wannan kyau da ado da kike zugawa ba. Kinsan Allah kamar canja ki akayi. Ki ganki fa a Kano lokacin muna gidan su maman Hassan" Ahmad ne ya fito ɗaga ɗaki yace.
"Faɗi ba'a tambayeka ba kenan tazo ko ki barta ta zauna kin tareta da soki burutsun zance" Ni dai dariya nayi kawai. Muka gaisa da Ahmad kana nace.
Fita zamu yi da yamma zuwa park mu ɗan huta sai ku shirya zuwa bayan la'asar da yaran duka. A kunnen Hajara nayi mata raɗa"
Ki tabbatar kinyi amfani da wannan humrar dana baki."Nan na bar su, Aneesa anata murna. Da yamma kuwa muka shirya tsab, na soya mana kaji, nayi mana babban cake da fried rice ƴar kaɗan sai drinks. Yara suka saka a mota da dadduma duk suka fice suka barmu cikin ado Bulama Babba ya fito. Rungumeni yayi yana mun raɗa.
"Kece farin cikina sanyin idaniyata uwar ƴaƴana" idanu na lumshe hawaye suka gangaro kan kumatuna. Allah na gode maka daka barni da raina da lafiyata, da Bulamana kuma. Rashin haihuwa Allah yasa hakan shine mafi alkairi a gareni." Fita mu ka yi mota biyu. Na gaiyaci Maman Amira ma acan muka same su. Yau ɗaya Hajara ta ɗauki shawarata tayi

66 / 67