Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
siyo, ki fito da kayanki dana yaran da nawa duk zan haɗa in wanke, ke kuma sai kiyi kwalimar da kika ce kinason kiyi. Wannan kuma naman kan saniya ne, nasan kina so shine na siyo miki ayi mana farfesu da farar shinkafa. In Allah ya kaimu sati me zuwa in an yi albashi zan siyo mana gado. Akwai wani gado da katifa dana taya, naji yayi mun sauƙi, amman fa kiyi haƙuri ba sabo bane na hannu ne" Murmushi nayi nace.
Allah ya saka da alheri Bulamana ina godiya sosai. Batun siyan gado da ka ɗan jinkirta ba yanzu ba tukunna, banyi ƙorafin yanda nake ba, Alhamdulillah. Akwai abubbuwan da suka fi gado da katifa mahimmanci a gabanmu, lokacin da ya dace ayi za'ayi. Kace yau zamu goge wuya da farfesu. Amman nasan ba'ayi biya ba ina ka samu kuɗi?" Dariya yayi yana nuna ni da yatsa.
"Dama nasan sai kin tambaya. Fito mun da wankin waje, zamu yi maganar." Tashi nayi na haɗo kayan wankin basu da yawa kala bibbiyu ne, sai zanin gado guda ɗaya. A waje na same shi akan turmi yana kaɗa kumfa. A gabanshi na dure kayan wankin. Gidan cike da mata harda na maƙota anata sharara gulma, sabida rashin abun yi. Ƙazanta tayi musu katutu tun safe in suka fito, babu abinda suke in banda gulma da shewa, tsakar gida duk datti, bayan gida duk zarnin masifa. Ɗakunan biyu dana shiga da suka haihu kuwa, abun ya matuƙar bani mamaki. Wasu tsunmokarai da annakiyoyin datti ne zai soma maka maraba, ga wani hamamin tsami da warin datti da ɗakunan suke yi. Ko da yake da dama a cikinsu ko tsabtar jikinsu basu san ya zasu yi ba. Ɗai ɗai ku a cikin gidanne masu tsabta, dan ko ƙofar ɗakinsu ka kalla kullum fes fes dashi. Kullum sai na share ƙofar ɗakina, kuma kullum saina karkaɓe tokar kurfo ɗina, har mopping ƙofar ɗakin nake yi da tsumma kullum. Wayar Bulamana ce tayi ringing harna juya zan shiga ɗakko naman kai zan ɗaura a wuta tunda akwai ragowar gaushi a kunne. Sai naji inason tsaiwa inji wake kiranshi, dan kwana biyunnan Zubaina na yawan damunshi da waya, jiya sha ɗayan dare ta kirashi a waya. Zaro wayar yayi a aljihunshi ya kara a kunne. Idanu na ƙura mai ƙur ina jin motsin kishinshi a ƙirjina.
"Hello Zubaina ya jikin Yusuf ɗin to?" Bansan me tace ba na dai ji yace
"Subuhanallah abun yayi tsanani haka harda ƙarin jini, amman sun faɗa miki abunda ke damunshin kuwa tun jiya nake tambayarki. Ni dai tsabar kishi ma shigewata ciki nayi, na juyo naman kan a tukunya na zuba ruwa na wanke shi tas, na girgije kurfo ɗina na ƙara gawayi na mayar da naman wuta. Har zuwa lokacin bai daina waya da Zubaina ba, suna maganar kuɗi ina dai jin ana ambaton dubu goma. Jajjayen kayan miya na soma yi. Yana gama wayar ya shiga kallona.
"Kinga jikin yaronnan yayi tsamari fa har jini aka ƙara mishi yau. Inaga dole gobe zan kama hanyar Kaduna in duboshi.
Allah ya kaimu, shi kuma Allah ya bashi lafiya" Iyakar abunda na faɗa kenan na tsuke bakina. Sai da na gama haɗa farfesuna tsab na koma ciki dan soma kwalima. Biyoni Bulamana yayi.
"Haushi kike ji sabida ina waya da Zubaina ko? Kishi kumallon mata. Ai matsayinki ya kere matsayin ko wacce mace a zuchiyata. Zubaina kuma dole zamu dinga waya sabida akwai ɗana a hannunta, amman kinsan ko yarona baya hannunta zata iya kira ta wayata tace abata yaran zasu gaisa ko? To kiyi haƙuri ki dena fishin, Ahmad zaije ya dubo Yusuf ɗin in ya kama ni kuma ina manne dake. Haka yaita jana da wasa harna sake, daga baya ma na dinga jin kunya. Bulamana yana wanki ni kuma inata share share, matan gida aka kafa dabarshi sai zuwa wucewa akeyi dan a tabbatar da wankin yake yi mana ni da yaran. Shi kuwa bai san anayi ba. Ni da na sani sai janshi da hira nake yi muna dariya, yana aikinshi ina girkina, yara kuwa sai wasan gare gare suke a tsakar gidan. Shanya kayan yayi a igiya, ya zari bokiti ya tafi ɗebo ruwa. Nan fa surutu ya ɓalle, daga masu cewa ba banza na barshi ba, sai masu cewa ya basu mamaki, sai masu cewa Kanuri gidan asiri. Ni dai duk wacce tai magana sai in kalleta kawai. Yana gama jidan ruwan yayo wanka. Cikin shirin fita ya fito.
"Zanje makaranta sai bayan isha zan shigo." Da adda'a na bishi, har sai da yayi nisa na yi shiru. Wayata ce ta soma ringin a ɗaki. Ko da na shiga sai naga su Dala ke kirana. Mun kuwa jima anata waye_ waye, suka sanar dani matar Dala ta haihu yanzu. Cikin jin daɗi da taya murna nayi ma Dala murna, bayan mun gama waya dasu na kira su Ya Innana da su ya Bagulaji nayi musu barka, na kuma kiran su Ba Modu nayi musu barka, hakan akeyi a gidan namu in aka samu ƙaruwa. Ba Modu yace.
"Amman kiyi haƙuri ki yi zamanki tunda baki daɗe da komawa ba. In wani sha'anin ya taso kwa zo, sha'ani baya ƙarewa a gidannan ai" Naso zuwan, amman inna tuna bani da suturar mata da zan fita taro dashi, da wasa bana fatan aga gazawar Bulamana a kaina. Tunda yana bakin ƙoƙarinshi, ko farin ciki daya bani ya fiye mun duniya da abinda ke cikinta. Damuwata shaye shayennan ne da ya zamemun ƙarfen ƙafa, ina tsoro gami da jimamin ranar tonon asiri, bansan da wanne idanu zan kalli mijina da iyayena, da ƴan uwana ba. Bansan da wanne ido zasu dinga kallona ba, ƙila ma igiyar auren da nake alfahari da ita ta samu targaɗe, astagarufullah." Da haka mu kai sallama dai _dai ana kiraye kirayen sallar Magriba. Kulolin tuwo da miya na fito dashi tsakar gidan. Na zuba ma mijina nashi shinkafa da farfesun, yarama na zuba musu nasu, suka zauna a tabarma suna ci, kwanon Hajara na karɓa na zuba musu nasu, sai fara'a take yi da taga farfesun. Ruwan wanka na mayar, bayan na ɗauro alwala na shige ɗakina na yi sallar Magriba. Ina idarwa nayo wanka. Kasancewar garin zafi zafi akeyi bansa wasu kaya masu nauyi ba doguwar rigar bacci na saka har ƙasa, bayan na cakuɗe jikina da sassanyar Humra. Bawa yana zaune sai gyangyaɗi yake yi an sha gagamniya.
Bawa tawo kayi sallar isha sai ka kwanta ko? Maryamana taso muyi Sallah. Muna idar da sallar isha duk yaran su kai bacci, laka mis ɗina na ɗaga na shanye rabin gora, kafin minti goma na soma jin network ɗina yana kawowa, da ya ɗan sauka ƙasa. Zuchiyata fes da'ita. Na daɗe da lura kwanciyar hankalina shine in sha kayan maye, sai in dinga jin wani farin ciki mara yankewa. In kuwa ban sha ba na wuni guda, sai in dinga jin tamkar an ɗauramun gingimemen dutse a kaina. Hayaniya a kunnena kuwa kamar kasuwar kurmi. Ina ninke kayayyakin wankin mu, Bulamana yayo sallama hannunshi riƙe da ƴar leda baƙa. Ledar na karɓa tare da yi mishi maraba da dawowa. Lemo ne guda uku a cikin ledar ya siyo mana. Murmushi nayi mishi, shima ya mayar mun. Muna hira muna cin abincinmu, har muka gama na raka shi yayo wanka, mu kai brosh a tsakar gida, nan muka bar Ahmad da Hajara a zaune a waje suna hirarsu suna shan iska. Maman Hassan ma suna ƙofar ɗakinta ita da mijinta, suna hira suna shan rake. Bayan mun yi mu'amala aure mun nitsa ne, Bulamana ya zo mun da wata magana."
"Yahanasuna, ni ina ganin zan jona mastas a B.U.K badan komai ba sai dan in samu aiki me kyau. Ko da lecturing suka ɗauke ni ina laifi duk da na jarraba hakan ma ya gagara, amman ƙila in nayi mastas dasu zasu bani koyarwar Kinga kullum fa sai mun fita neman aiki ma'aikatu_ma'aikatu, duk inda muka je sai ace babu aikin. Ni na yanke shawarar bazan sake zuwa neman aiki ba. Hajja ma ta ɗan tuntuɓamun a wajan yayyunta, aikin bai samu bane. Amman shawarace me kika ce?" Gyara kwanciyata nayi a jikinshi, ina wasa da gemunshi nace.
Wannan magana taka tayi Bulamana, amman ka sani yanayin karatu yanzu ya zama sai adda'a kuɗin registration anan matsalar take, in ka samu gurbin karatun dame zamu biya registration?" Ajjiyar zuchiya ya sauke ya ce.
"To ni ina gani zan shiga adashe hannu biyu, akwai wanda akeyi a gidan yari. A kwai wanda malaman makarantar da nake koyarwa zasu kafa sati mai zuwa. Ina ganin duk zan sa hannuna ayi tare dani. Bani kaɗai zan koma makaranta ba Harda ke kema, gara mu shiga tare kawai." Dariya nayi mishi tare da muskutawa nace.
Wasa kake yi dai, in yi yaya da aikin nawa da yaran?"
Pa time zaki dinga zuwa makarantar, gara mu shiga tare kawai Yahanasu na. Ko koyarwarne ai sai mu yi tare ko ya kika ce?"
Hakane Bulamana, zamu ci gaba da shawara a tsakaninmu kafin zuwan lokacin, duk da dai watannine ya rage, Allah ya tabbatar mana da abinda yafi alkhairi" Da "Ameen" ya amsa, muna ta taɓa hira har bacci yai awon gaba damu." Haka al'amura suka ci gaba da turawa, har yanzu Ba Bakura bai gama sakewa da Bulamana ba, amman yana ɗaga wayarshi, yana amsa gaisuwarshi harma ya tambayeshi lafiyarshi da tamu lafiyar. Ni kuma haka naci gaba da kasuwancina ina jijjuya kuɗi, duk da ba wani mai yawa nake yi ba, amman babu laifi ina samun alkhairi sosai, kayan fulawa akwai riba sosai. Kuma ina bama yara su tafi dashi makarata, ina ƙunsama Bulamana da Ahmad suma su tafi dashi, duk da haka sai dai hamdala. Wannan watan ina ɗaukar albashina, na cire nera dubu biyar muka sai bulo ni da Binta, itama ta sai ƙaramin filinta a kusa da nawa. Harma mun kira magina sun haƙa: ginshiƙi, ko wacce ta zuba bulo ɗinta a filinta ƙanin Binta na kular mana da wajan. Ragowar kuɗin kuma na yo cefane, na siyo ma yara da Bulamana takalmi. Ni kuma na siyi wata atamfar roba na ajjiye, dan ko kuɗin ɗinkin bani dashi, sai dai in jira wani watan.
KOFUR ZUBAINA:
Gida ya cika ya batsa tab da jama'ar biki. Yanzu aka gama ɗaurin auren a can gidan kawu Tanko. Mu kuma a cikin gida muna ta fama shirye shiryen halartar walima abokan ango suka haɗa. Na fito nayi wani irin mugun kyau da murjewa na sha make up rantsatstsiya, ina saye da wani tsadaden farin lace, da farin takalmi mai tsini. Mabaruka da Hadiza Aliyu, da Mariya Buba da su ka zo mun biki ko wacce saye take da farin leshi mai tsada, dan Mariya wani hamshaƙin Alhaji take aure Haka zalika Hadiza Aliyu itama mijinta me akwai ne. Mota Alh Liti ya ɗakko a ciki ya ɗebeni da ƙawayena, Mariya Buba tana biye damu da yaranta a cikin tata motar. Ni na kasance mace mai mugun baƙin ciki, nifa bana son a fini nafi son ace ni nafi kowa. Amman naga halama ƙawayena kamar duk sun kere mun, dan ko irin kuɗin da Salisu yake kashe ma Mabaruka Alh Liti baya kashe mun irinsu, duk da yana mun ɓarin kuɗi sosai, dan ko a hidimar bikinnan dubu ɗari da hamsin ya ba Mama, banda buhunhunan shinkafa biyar da yasa aka turo gidan, yace ayi abincin biki dasu, ni kuma dubu ɗari biyu nayi mishi total bai yi musu ba ya bani. Amman naga yanda Mariya Buba ta zama wata hajiyane, gashi tace mun zata sake komawa hajji wannan shekarar ita da mahaifiyarta, duk da shekara biyu kenan da dawowarta, taje Dubai, ta je Qatar, amman ni iyakata Najeriya. Hadiza Aliyu ma tayi aikin hajji tayi umara. Ohhh zuchiyata wani zafi naji tana yi mun, munfashina ya shiga bazaranar tarwatsewa. Bansan mun kawo holl ɗin ba, sai da naji fitar su Hadiza Aliyu daga cikin motar tukunna na ankara. Alh Liti na ƙura ma idanuna da suka rune tsabar baƙin cikin da nake yi da ƙawayena da ƙannena.
Wai da gaske kuwa Alh Liti kana sona, kuma zaka aure ni a hakan?" A rikirkice ya kalleni, babban abunda ya tsana a duniya bai wuci ɓacin raina ba. Dan ko a waya ya ɓata mun rai, ba ƙaramin birkicewa yake yi ba, sai ya kira Mama ya dinga roƙonta akan ta bani haƙuri. Magana yake yi, amman ni hankalina ya koma wajan Asiya dana hangota ta sake zama wata wayayya, harda ƙawayenta biyu tazo bikin, wasu wayayyu matan alhazai, sun sha kwalliyar gwalagwalai. Tsaki naja a fili, na dubi Alh Liti a tsawace nace.
Kai nifa na gaji da baƙar rowarka, Allah ya haɗa kowa da rabonshi. Ina kaiwa nan na ɓalle murfin motar na fice, harara na sakar ma Asiya da ƙawayenta na shiga na samu su Mariya Buba a ciki"
MRS BUKHARI CE
[07/08, 9:42 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
26
Da ƙyar na daidaita fishin fuskata, na zage mu kaita hira da su Hadiza Aliyu. Alh Liti sai faman kiran wayata yake yi, data katse daya kuma danna mun kira. Kashe wayar nayi dan dole. Ba shiri ya shigo buguzun_ buguzun da ƙaton ciki a gaba, malum_ malum ɗinshi cike da iska. Shaddace mai tsada fara sol a jikinshi. Agogon hannunshi, takalminshi da jar darar hularshi ita ta sake fito da tsantsar haskenshi. Gefena ya tsaya ya dinga magana dani, sai da su Mariya Buba suka sa baki sannan na biyo bayanshi zuwa waje, muka jingina a jikin motar da ya kawo mu.
"Wai ni kam Gimbiya lafiya me ya birkita mun ke haka, yanzu ni me nayi miki da har zaki ce kin fasa aurena? Wallahi haɗari zan shiga mai girman gaske, ashe baki san girman sonki a zuchiyata ba ko, me kike so, waya taɓaki?" A yatsine na soma magana.
Nifa in kwanciyar hankali kake nema wallahi ka game mun ginina kawai so nake in zuba ƴan haya, kaɗan ma ya rage . Sannan inason zuwa umara da zaran munyi aure, kuma ka siya mun mota." Murmushi yayi yana dubana da mitsimitsin idanuwanshi kamar an ƙwantali kabewa.
"Shikenan abinda kike buƙata ai miki Gimbiya?"
E ai kaji na faɗa ma yanzu" Wayarshi ya ciro a aljihu ko wa yake kira oho. Na dai ji suna maganar aje a duba ginin nawa ayi mishi estimet na kuɗin da gidan zai ci, komai a zuba masu tsada, dama damuwata kayan tails da kayayyakin cikin bayangidun, da wayaring sune suka rage kuma ba ƙaramin kuɗi zasu lashe ba. Wani farin ciki naji a cikin zuchiyata, amman a zahiri sake haɗe rai nayi.
"Gimbiya a saki ran mana uhm ko so kike dai ki sukurkutani a wajannan ne? Ki bani nan da wata guda za'a kawo miki key ɗin gidanki, za'ayi miki komai, ɓangaren da kike son saka Mama kuma za'a zuba furniture masu tsada, Maganar umara in munyi aure wannan ai baki da buƙatar sai kin ce. Zamu zagaye ƙasashe sosai in kai ki yawo buɗe idanu. Mota kuma sai kin zaɓi wacce tayi miki, amman da direba zan haɗaki ya dinga kai ki ko ina. Ki yi haquri dan Allah a saki ran mana inji daɗi uhm?' Haka yaita faman lallaɓani da ƙyar na sakko, muka ɓalle da hirar soyayya. Haka dai aka gama walima duk muka watse. Washe gari akayi yinin biki, a ranar muka wuce Abuja gidan Nafisa, ni dai da ƙyar nake shaƙar nunfashi dan ji nake yi kamar zan zautu dan baƙin ciki. Sai cikin dare masu kawo Amarya suka iso. Washe gari da sassafe muka tattare ina mu ina mu muka nufi Kaduna. Nafisa kuma ƙarfe sha ɗayan rana girjinsu zai tashi zuwa ingila. Al'amura sukai ta garawa dai. Yanzu zaman gida ya sake yi mun rashin daɗi, daga ni sai Mama. Dan ma ina zuwa aiki shi yasa abun yazo mun da sauƙi. Maginan da Alh liti ya ba kwangilar ginin gidana suna ta aikinsu. Harma na kai Mama da Musa munje mun ga gidan, sai santi Mama take yi. Ni kuma sai jin daɗi nake yi. Burina in gama wannan idda data riƙe mun wuya in zama mallakin Alh Liti ya huta, in huta nima.
Yahanasu:
Yau tun dana tashi nake jin kasala sosai a jikina, a ciccije na kammala aikina, Bulamana sai tambayata yake yi abunda ke damuna. Na samu dai na lallaɓa naje wajan aiki. Sai bacci da bin sanyi a haka na wuni har muka tashi. Binta ta kalleni tace.
" Ki sai P T ki yi awon ciki, gaskiya cikine dake. Wani farin ciki ya lulluɓeni, nayi murmushin jin daɗi.
In kuwa hakane nasan Bulamana zaifi kowa farin ciki. Haka ƴan Damaturu zasu yi farin ciki."
Zan siya kafin in shiga gida. Amman ba kince zamu je sabon gari siyan kaya ba?" Binta tace.
"Aji garau zaki ce. Yanzu kuwa can muka nufa muje ko?" Muna cikin ɗan sahu Binta tace.
"Matar da zaku je gidanta ku tattauna, a kurna take, zan baki lambarta in kunje kurnan sai ki kirata. Nima gobe zamu halarci wani taron ƴan siyasa da za'a gudanar a cikin gari. Zamu je ayi damu mu kwaso rahoto." Kallon Binta nayi nace.
Uhm aikin jarida akwai wuya, wallahi aikin ya fice mun a kaina, musamman program ɗin nan da yake hannuna, rana ɗai ɗai ne fa bana zubar da hawaye a gaban matan da naje tattauna dasu fa. Sabida labaran nasu gwanin ban tausayi. Duk da labaran wasu matan gwanin ban ƙaye. Ki ga dai labarin mai shari'a Hajiya Turai.