Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
Qur'ani duk sati, kinga dai yadda nake yi ai. Karki bari sanadinki a ɓata wannan zumuncin. Kome zai faru dake ki jure, kar ki tunkari kowa da ƙorafi, Bulama Babba ɗan uwanki ne, duk abinda ya miki mara daɗi ki shanye. Ki nutsu ki riƙe gidanki da mijinki. Ga Fanda, duk abinda ya shige miki duhu ki sanar da'ita. Ke kuma Fanda kiji tsoron Allah ki ba ƴar uwarki nagartacciyar shawara. Yahanasu ki nutsu ki zama mai girman daraja a idanun mijinki. Karki gaza wajan yi mishi hidima. Aljanna kika je nemowa, duk wuya ki ɗau jumurin shanyeshi. Ki samama Ba Bakura da Hajja Gana farin ciki. Ki shirya Wakil ya kaiki gidan Yanunu ƙanwata, tai miki gyara, sabida kina buƙatar gyara na musamman. Zata baki wasu surrukan da dabarun zama da miji, da abokiyar zama." Gabaki ɗaya nasihar Ya Innana ta ɗaure ƙashi da jijiyoyin jikina. Dajin muryarta kinsan tana cikin tsananin tashin hankali da damuwa.
Ya Innana, na rungumi zaɓi iyayena, ina fatan ya zame mana alkhairi baki ɗaya. Ƴan uwana gudunmawar da zaku bani shine adda'a, ku yawaita mun sadaka da nufin Allah ya kareni da dukkan wani sharri." Kuka na rushe dashi mai ciwo. Dan har wani ɗaukewa numfashina yake yi. Sai yamma Wakil ya fitar mun da akwatina, ni kuma na shiga cikin gida yima matan gidan sallama, sannan na fito muka tafi
Ya Innana:
Wayarta taja bayan fitar su Yahanasu ta doka kiran ƴar uwarta. Ƙara ɗaya_biyu aka ɗauka.
"Assalamu alaikum Yaya, an wuni lafiya, ya Ƙarfin jikin Yahanasu?" Ajjiyar zuchiya Innana tayi tace.
"Jiki da sauƙi, sai rashin sakewa, da rashin son magana yanzu da take fama dashi. Ga wani babban al'amari daya ɓullo cikin rayuwarta. Bansan ta inda Yahanasu zata iya wannan rayuwar ba. Ba Bakura ne ya haɗata da Bulama na wajanshi, zai musu aure. Shi kanshi Bulaman sai yanda matarshi tace mai fa yake yi, shine za'a aura mishi mace,macen ma Yahanasu, ina cikin damuwa Yanunu, yanzu haka ma Wakil zai kawo miki Yahanasun, suna hanya, amman zasu biya su sauke ƴar uwar tasu a gidanta. Ta zauna a wajanki. In bikin ya gabato, ta dawo cikin gidan, ki yi mata dukkan gyaran da zai farfaɗo mata da darajar gabanta." Yanunu tace.
"Kuma Yaya haka kina ji kina gani za'a bama yaronnan Auren Yahanasu, bakwa tunanin makomar rayuwarta ne, koko me? A cikin zafi da raɗaɗin fyaɗe take fa, yarinyar da take cikin tsananin damuwa shine za'ayi mata auren dole, a wannan halin da take? Yaya asiri fa gaskiya ne, tunda yaci ma'aikin Allah."
"Yanunu nasan asiri gaskiya ne, tunda yaci ma'aiki Arrasul ( S A W) amman bani da ikon yin jayayya da umarnin da Ba Bakura ya yanke. Ko Modu bashi da wannan ikon balle ni. Wallahi ni kaɗai nasan a irin tashin hankalin da nake ciki, dukan yayi mana yawa, shi yasa ma na turo miki ita, in ina ganinta tausayinta zai iya ingizani in bijirema Modu." Sun jima suna tattaunawa, amman mafita dai basu da ita, sun shige damuwa ainun"
Yahanasu.
Tunda muka fito, zazzaɓi ya rufeni mai zafi, zuchiyata sai naji kawai tana raya mun, in kashe kaina kawai in huta. Wata zuchiyar tace, gara in gudu. Wata tace mun in buɗe murfin motar da nake ciki in faɗo ƙasa.
Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun itace kalmar da naita jaddadawa a hankali, ina dafe da ƙirjina. Ahankali nake jin ina dawowa dai'dai. Amman har muka iso gidan Yanunu ban dawo haiyacina ba. Muna shiga na zarce ɗakinta, bance dasu komai ba. Su kansu basa son cewa dani komai. Zama nayi a bakin gado, ina tunano fuskar Bulama Babba, da matarshi Kofur Zubaina. o ikon Allah, a ƙirji da cinyar Bulama Babba na gama wasannina, domun ya kasance mai son yara. Daga mazan har matan, babu wanda bai goya ba. Ni kuwa, ina tuno lokacin da ake goya ma Bulama Babba ni, muje kai niƙa. Hawayena na share .
Na rasa darajata, farin ciki ma gashi ina dab da rasashi, wato haka rayuwa take faruwa, dole mutum mai rai, wata rana ya faɗa cikin jarabawar rayuwa, duniya juyi juyi kwaɗo ya faɗa a ruwan zafi, duniya zancen banza, duk wanda ya bari duniya ta ruɗeshi yayi wawa, duniya mai idanu a tsakar ka. Yanunu ce ta shigo hannunta riƙe da plate cike da wani irin farfesun nama.
"Cinye wannan cicciɓin Yahanasu. Ki share hawayenki, da kaina zanje in samu Ba Bakura ɗin, muyi magana, aurennan bazai yiwu ba, ai wanna ma zalunci ne, kuma mahaifinki ya zura idanu ya kasa cewa komai." Dubanta nayi nace.
Dan Allah Yanunu karki je, zan aureshi, nima na amince, babu bawan daya isa ya zaɓarma kanshi rayuwar da yake so, kuma ace ya samu hanyar ba gargada. Ƙila aurena da Bulama Babba shine abunda yake rubuce a allon ƙaddarata. Na rasa ma darajata, na fauwalama Allah komai. Babu wani zafi da raɗaɗin da zanji wanda ya wuce zafin fyaɗen da akayi mun." Ina kaiwa nan sai kuka. Na tashi hankalina sosai. Ni kenan a cikin kuka, da kulle kaina a ɗaki. Yanunu ta rasa yanda zata sani. Ni kaina fatan mutuwa nake yima kaina sosai. A hakan take ta gyarani da magunguna, wasu naci, wasu nasha, wasu kuma na wanka. Ga kullekham ta matan aure, da shu'umar humra da nake shafawa, sabulun wankana ma, ƙamshinshi bana wasa bane. Ni ɗince dai bana cikin hayyacina. Kullum a cikin kai kukana ga Allah nake. Ƴan gidanmu duk wanda ya kawo mun ziyara da kuka yake tafiya. Hakan da na gani ne yasa na daddage na aro nutsuwa na ɗamfara ma kaina, shine na soma ganuwa. Nasiru kuwa bai ƙara ganina ba, bai kuma jin muryata ba,ni banma san yanda aka ƙare da zancenshi ba. Wata ranar juma'a ina zaune a uwar ɗakin Yanunu, na jiyo muryar Hajja Fati ƙawata, suna gaisawa da Yanunu kamar a mafarki.
"Ki shiga tana ciki, sai kika ji abunda ya faru da'ita ko?" Hajja Fati tace.
"Wallahi jiya na shigo gari, ummanmu take labarta mun abunda ya faru, Allah ya kiyaye gaba."
"Uhmm Ameen, ki shiga tana cikin wancan ɗakin" Ni dai ina jiyosu, saiga Hajja Fati ta shigo da gandamemen ciki a jikinta. Ganin cikin ya sani jin sanyi da farin ciki a raina. Dan Shekara biyar da auren Hajja Fati, amman ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Magunguna babu irin wanda bata sha ba na samun ciki, daga na Gargajiyar, harna asibitin. Har aure mijinta ya sake sabida rashin haihuwar nata. Hajja Fati ƙawata ce ta ƙut da ƙut, maƙotanmu ne, kuma tare mukai karatu, tun daga primary har sakandare, Ba Bakura ne ya biya mata kuɗin karatu, kasancewar mahaifinta ya jima da rasuwa.
Hajja Fati kece da safennan haka, sai kace wacce tayi mafarkina? Sai naga abun arziki ashe an samu, shine ko a waya baki bani labari ba" Jikinta a mace ta zauna.
"Yahanasu kece kika rame kikayi duhu haka, kin ganki kuwa yanda kika zama? Ki ɗauki dangana mana Yahanasu, ki yi fatali da abunda ya faru dake, ko dan kwanciyar hankalin Ya Innana. Naga ita kanta tayi rama sosai sai wuya" murmushi nayi mata kawai, sannan nace.
Na riga na dangana, dan da'ace ban dangana ba. Da yanzu na biye ma sharrin zuchiya na halaka kaina. Hajja Fati wannan ramar tana da nasaba da rayuwar dake tunkaroni a gaba, abunda ya faru a baya ya shige ai, mikin dai yana cikin zuchiyata abadan. Ta yaya zan soma rayuwa da Bulama Babba, alhalin sai abinda matarshi tace mishi. Duk da kullum a cikin adda'ar neman dacewa nake, amman kuma zuchiyata a cikin zulumi, da taraddadi take a ko da yaushe Hajja Fati" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
"Zahiri maganarki abin a duba ne Yahanasu. Auren soyayyarma yaya yake cikawa balle auren dole? Ni kaina abubbuwan da nake fuskatanta a wajan Ahmad ai abun bana wasa bane. Yahanasu tunda Ahmad yayi aure, na zama banza, sharar gidana ta fini daraja a idanunshi. Allah ya dubeni ya soma bani ciki kafin amaryar. Nayi tunanin hakan zai sa Ahmad a farin ciki. Amman wallahi ta cikin amaryarshi yake yi. Kwanakin baya na dawo gida ai nayo yaji. A ranar Umma ta mayar dani. Yahanasu Umma taƙi ta saurareni in faɗa mata halinda nake ciki ma. Sai cewa take yi in riƙe maraicina in dubeta. Ke ga ciki, ga damuwa, hawan jini ya rufar mun, da naga zan mutu ba shiri na soma shan kayan maye. Su kaɗai nake sha in samu nutsuwa a zuchiyata Yahanasu, to in ban sha ba, mutuwa zanyi, takaicin ɗa namiji dubi yanda ya zubar mun da ajina, duk gaye na. Amman yanzu dubeni fa" Da kallon mamaki na bita. Da ace a bakin wani naji labarinnan bazan taɓa gasgatawa ba. Hajja Fati da Ahmad wata soyayya suka gudanar mai ban sha'awa kafin aure. Duk wanda yasan Ahmad, to dole yasan Hajja Fati. Haka itama duk wanda ya santa, ya san Ahmad. Amman yau shine ya juya mata baya, har take shirin halaka kanta sabida shi?
Haba Hajja Fati, me ya kaiki shan kayan maye, adda'a ya dace ki kama, amman ba ki kama abunda zai iya taɓa duniyarki ba. Ya kike ganin randa Umma zata san halin da kike ciki zata ji? Karki bari ki halaka kanki a kan namiji" Dariya tayi mun.
"Bafa zaki gane bane Yahanasu. Sai lokacin da tsananin damuwa ya kamani ne, nake shan abun maye, da zaran nayi bacci na farka, sai kiji zuchiyata sawai da'ita, shi kanshi kaina sai yayi fayau. Kuma raba dare nake yi, ina adda'ar Allah ya bani mafita Yahanasu. Takaicin ɗa namiji, da kishiya yafa wuce tunaninki. Balle ke mai mugun sa abu a ranki, maganar da ba wata magana ba ma, saita hanaki bacci. Harfa Deepretion ne ya kamani lokacin cikina yana wata na huɗu." Dubanta na kuma yi cikin sarewa nace da'ita.
Ki dai kiyaye, kuma ni ina ganin ki koma makaranta ki haɗa digiri ɗinki, ki ɗan samu aiki. Rashin lokaci zai iya rage miki matsala. Amman sai anyi biki zaki koma dai ko?" Dariya tayi.
"Har Kaduna saina kaiki ai Yahanasu." Ganin Hajja Fati yasa na ɗan saki jiki na, sai hira muke yi na yaushe gamo. A wajena ta kwana, sai washe gari Sannan ta koma gida.
Innana:
A ɗakin Bagulaji matan gidan duk suka taru, harda Innana, Mama Gana tana ta tsara yanda al'amarin bikin ƴan matan zai kasance.
"Ni ina ganin ayi jeren yarannan da wuri sabida a huta. Maganar kayan katako kuma, zuwa gobe Ni da Bagulaji zamu je Kasuwa, sai mu zaɓa musu abunda ya dace. Ke kuma Yaguji, ke da Ya kura. Sai ku duba mana kayan kitchen. Ɓangaren Labulaye da su kafet kuma, sai Innana ta ɗauka, tunda ta iya zaɓe, mu samu mu gama komai cikin tsanake, Ba Bakura ya tura mun kuɗin duk abunda za'a buƙata. Cewar Mama Gana kenan. Innana tace.
"Maganar cincin, da su nakiya kuma, nayi ma Umman Hajja Fati magana, tunda dama ita ke yi sana'arta ce. To na faɗa mata gobe Wakil da Bulama ƙarami zasu kawo mata buhun fulawa bakwai, na cincin, da dublan, buhu ɗaya na alkama domun yin alkaki, sai buhun sikari. Sai buhun shinkafar tuwo,da rabin buhun suga, da kayan ƙamshi. na siya an kai gidan Baba Gwamma, maganar nakiya da zata yi. Sabida a samu a kammala komai, kafin gidan ya cika da Baƙi. Abincin biki kuma Hajja gana tace. Tayi ma wata mata, mai yin sana'ar abincin biki. Zata yo abinci kala uku ranar ɗaurin auren, sabida baƙi. Bagulaji tace.
"E nima tayi mun magana, sabida ta bani wasu atampopi da lace tace in ba telana ya ɗinka ma Yahanasu su. Shine da nake karɓan kuɗin dinkin take sanar dani maganar abincin ƴan ɗaurin auren. Allah yasa ayi damu wannan bikin. Ba Bakura yana kashe ma wannan biki kuɗi sosai gaskiya. Kamar ba'a taɓa yin biki ba a gidan haka yake ji. Dariya suka yi dukkansu. Shirye_shirye sosai suke yi, abun babu kama hannun yaro. Ana biki saura sati guda, gabaki ɗaya an gama komai, amaren anje anyi musu jeransu. Mazan kuma, ko wanne ya gyara inda zai ajiye matarshi. Gida ya soma cika da baƙi, ƴan Pataskum ne, ƴan maiduguri ne, ƴan yobe ne, jama'ar Yola ne. Duk kowa ya tawo,duk inda ka gilma yaren kanuri da kamshin humra ke tashi, duk matar da ka gani, zaka ganta saye cikin lafaya, hannu da ƙafarta kuwa yasha ƙunshi baƙi. gidan kuwa yasha fenti sabo. Iyayen amare, da angwayen kuwa ko wacce ɗanta ya gyare mata ɗakinta, anyi musu fenti. Atampa super sukaima iyayen nasu Anko, na ranar ɗaurin auren kenan. Dan akwai walima da zasu gudanar a cikin gidan ranar ɗaurin auren kamar yanda dama suke yi, duk aure. Ga tarin al'adun auren Kanuri da ake gudanarwa, babu ko guda ɗaya da ake bari, sabida al'adune masu dogon tarihi, a cikin yaren Kanuri.
Yahanasu:
Tun biki saura sati guda, Yanunu ta dawo dani gida. Can ɓangaren Ya Bagulaji kishiyar Ya Innana ta kaini, sabida kara. Ƙawayena duk muna can, Yaguji ƙanwata ɗiyar Ya Bagulaji ita kuma ta koma ɗakinmu ita da nata tawagar. Ni dai na dawo kalar tausayi, babu wuya sai kuka, gabaki ɗaya na sare. Ga gidan ya cika dam babu masaka tsinke, duk inda ka ratsa yare ke tashi. Hajja Fati tana tare dani, da ƴan tsirarin ƙawayenmu data gayyata. Haka aka shiga gudanar da al'adun biki iri daban daban....✍🏻
Mrs Bukhari ce.
Ya kuka ji labarin? Yawan comments zai iya sawa zuwa yamma ku sake jina da sabon feji, dan kuji yadda wannan biki zai kaya...
Ina da humrori da turarukan wuta irin da kanuri da sudanawa, siyan na gari mai da kuɗi gida, kayana ingantattune sai kin gwada zaki tabbatar.
_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023
_1-NIHLATUL-KHAIR_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-ME IDO A TSAKAR KA duniya_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFA_
👇🏽
*Ummu maher(miss green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼
[26/07, 2:34 p.m.] +234 806 874 8984: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
4
*BABBAN ALBISHIR GAREKU MASOYA LITTATTAFAN GAWURTATTU UKU. AKWAI KYAUTA TA MUSAMMAN DA MUKA SAKA DOMUN KU MASOYANMU. WAƊANDA SUKA JAJIRCE WAJAN TAYA MU SHARE ƊIN LITATTAFAN MU DOMUN SOYAYYA. AKWAI KYAUTAR BAN GIRMA DA MUTUM UKU DAGA CIKI ZASU SAMU. BUGU DA ƘARI ZASU SAMU DAMAR KARANTA LITTATAFAN GAWURTATTU UKU NA WANNAN ZANGON KYAUTA. BUGU DA ƘARI MUTANE BIYAR DA SUKA BIYA KUƊIN BOOKS ƊINSU DA ZARAN MUN GAMA FREE PAGE, SUMA SUNA DA KYAUTAR BAN GIRMA DA GAWURTATTU UKU ZASU BASU. AMMAN BIYAR ƊIN FARKO BA. AN RIGA AN DAƊE DA SOMA BIYAN LITTAFIN GAWURTATTU UKU, TUN KAFIN MU SOMA POSTING. WANNAN MUNA MAGANA NE DA WAƊANDA ZASU BIYA BAYAN MUN KAMMALA FREE PAGE ƊINMU. ( FATIMA SULAIMAN ITACE TA FARKO DATA SAI LITTAFAN GAWURTATTU UKU TUN KAFIN MU SOMA. TATA KYAUTAR TA MUSAMMAN CE) DOMUN ƘARIN BAYANI SAI KU TUNTUƁEMU A NUMBOBIN WAYAYOYINMU. MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU ✍🏻*
Yahanasu:
Haƙiƙa Kanuri suna ɗaya daga cikin ƙabilun da suka fi ko wacce ƙabila iya riƙon aure, dama gudanar da Al'adu a yayin Aure. Al'adun nasu sun haɗa da.
*BAWARAM* Kalmar Bawaram tana nufin Iyaye maza. Idan kuma a aure ne aka ce Bawaram tana nufin kayayyakin da ango yake yi wa dangin Amarya, waɗanda suka haɗa da kayan. Uwa, matar uba, da ma ƙannen uba, da yayyensu, babbar yar Amarya, kakannin, mai kitson Amarya, da uwar ɗakinta in tana dasu, duk sai ango yayi musu kaya.
*FAFURAI* Fafurai kuma, wani akwati ne da gidan Amarya suke yiwa Ango, abunda ake sawa a cikin akwatin sun haɗa da, shaddaji, da yaduna, huluna, da, takalma, agogo, turare, sallalaya, Qur'ani da sauransu. Kuɗi ake kashewa bana wasa ba, sabida dangin amarya suna son yiwa ango bajinta.
*WUSHE_WUSHE* kuma bikine da ake gudanarwa tsakanin ɓangaren amarya da ɓangaren ango, ana gobe ɗaurin aure. Ɓangarorin biyu sukanyi shigar al'ada irin ta Kanuri su haɗu a wani farfajiya, ko, waje mai fili dan gudanar da wannan bikin Al'ada. Mu a gidanmu muke gudanar da wannan biki, kasancewar gidan da girma. A wajan bikin ana keɓe Amarya da ango, a wani ƙayataccen gado, sa'ilin da makaɗan gargajiya ke kiɗa. Ƴan mata da abokan ango kuma, zasuita rausayawa a gaban ango da Amarya, irin rawar al'ada. Daga nan kuma sai liƙin kuɗi tare da yin hotuna kuma. Wushe_wushe na ɗaya daga cikin bikin auren Kanuri da yaruka da dama suka ara suka yafa a Najeria.
*QLATUL* Yana nufin wanke kai, mata kaɗai ake yima. Ana gudanar da wannan bikine, idan aure ya rage saura kwana uku. Yadda ake yinshi shine, Iyayen Amarya ke wanke mata kai da karkashi. Bayan an kammala wanke kan, ana yin kiɗan ƙwarya, wanda tsofaffin mata ke waƙa cikin harshen Kanuri. Shi wannan kiɗan ƙwaryar, irin na al'adar ƙabilar hausawane sak.
*KALAWA* Tamkar shaɗi yake, sai dai shi ba'a duka. Yanda ake yinshi, akushi ake tanada, da bushasshen karkashi, da ɗanyar shinkafa. Sai a ɗaura ango da Amarya akai su zauna. Dama an riga an ɗaura tuwon buski a wuta, ana saukewa da zafinshi za'a ɗebo, a zuba a tafukan Amarya da ango. Amarya da ango, sai su juye wannan buskin na hannunsu a cikin akushi. Ana yin haka har sau uku, sai a goge musu hannayensu, a shafe musu da