MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   62 / 67

183K to 186K   out of 198.3K words

wannan baiwar Allah ta nuna musu. Mutanene sosai a cikin ɗakin, ga kuma gadajen kara a jejjere da marasa lafiya a kai. Wasu suna kwance yayin da wasu suke a zaune. Wasu suna sambatu da dariya, yayin da wasu kuma suke shiru, amman kallo guda za kai musu kasan lallai babu lafiya.
"Bayin Allah ga gadon kara can ku shinfiɗe maras lafiyar a kai. Barkan ku da zuwa" Ɗaya daga cikin matan ɗakinne taima su Mama magana. Shinfiɗe Asiya su kayi a gadon kara, wuyanta a goce ya suntuma sai walƙiya yake yi. Hawaye Mama ta shiga sharewa, ɗingisawa tayi da ƴar sandarta wanda take dogarawa tun sanadin Alh Liti.
"Sannun ku baayin Allah mun same ku lafiya ya masu jikin kuma?" Goggo Safiya ce take gaishe da jama'ar da suka samu a ɗakin, bayan sun nemi tabarma sun zazzauna. Nan aka shiga gaisuwa da tambayar masu jiki. Wannan dattijuwar ce ta kawo ma su Mama ruwa a kofin silver.
"Dan Allah muna son zamu kama ruwa zamu yi alwala kuma" Inji Goggo Safiya dan Mama da Nafeesa sun kasa cewa komai, ko wanne cike yake da dana sani a rayuwa. Bayan sun rama sallolinsu ne suka koma ɗakin jira. Goggo Safiya tace.
"Nafeesa taimaka ki ba Asiya ruwa kar ƙishi ya dameta." Nafeesa a sanyaye kamar ba'ita ba tace
"Goggo ko an bata ruwan ƙwaranyewa yake yi, wuyanta a karye yake sosai." Mama cikin muryar kuka tace.
"Ni ban taɓa ganin irin wannan ciwon na Asiya ba. Amman wallahi ba da ban na tuba na koma ga Allah ba da sai na yi shari'a da Alh Jafar da matarshi, dan su suka nakasa mun ɗiyata. Allah ya isa bazan yafe musu ba mugaye kawai" Goggo Safiya ta dubi mama tace.
"Jummai kenan wanzami dama ance bai son jarfa. Wannan duk abubbuwan da suke ta faruwa akufi_akufi girbine na abunda kuka shuka. Ai adda'a zaku yi Allah yasa ya tsaya a haka. Kuma a dage aita tuba zuwa ga Allah, an yi kusa kurai masu tarin yawa, suma mazan Allah ya shiryar dasu baki ɗayansu. Rayuwa kenan duniya juyi_juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi." Mama da Nafeesa sai share hawaye su ke ta faman yi. Suna dai wannan gidan har bayan sallar isha. Da dama an dubasu sun tafi majinyata biyar suka rage a ɗakin, sai ƴan Rakiya. Wannan dattijuwar ce dai ta shigo hannunta riƙe da katon trai mai murtala da tasosi a kan tran na tuwo dana biya. Durewa tayi a tsakar ɗakin, ta fita sai gata da wani tran ta sake direwa.
"Bayin Allah ga abinci, tire ɗaya na marasa lafiyan ne. Ɗayan kuma naku ne. Zuwa gobe da safe malam zai duba ku in sha Allah." Godiya su kai mata, Goggo Safiya ta ce.
"To bayin Allah ga fa abinci nan. A samu aba marasa lafiyan tukunna. Mu tamu ko ruwa aka bata dawowa yake yi baya zama. Nafeesa ke da kike fama da juna maza ci abinci. Adda'a zaki dage da yima ƴar uwar taki, ba wai kita tagumi ba Allah zai bata lafiya in sha Allah." Haka su ka ci tuwannan na dawa da miyar kuka ko maggi babu sai gishiri, tako ji daddawa sosai sai ƙamshin kalwa take yi. A zazzaune suka kwana wasu kuma a kan taburmin suka shinfiɗe. Da safe aka tare su da ɗumamen tuwonnan da ruwan kokko. Misalin ƙarfe sha biyu layi ya iso kan su Mama. Zuwa wannan lokacin jama'a sun sake cika ɗakinnan da marasa lafiya." Da Goggo Safiya da Nafeesa ne suka tattagi Asiya, Mama na biye dasu tana ɗingishi tare da cije lebɓa dan kullum ƙafarnan sake yin ciwo take yi mata a ko da yaushe, gashi sai kumburi take yi, rashin nitsuwa dangane da ciwon Asiya ne ya hana Mama zuwa asibiti domun a duba ta. A falon malam suka shinfiɗe Asiya suka zauna daga gefe. Malam ja'e ya ƙura mata idanu sosai ya taso ya dubi wuyanta yanda ya kumbura yai suntum gashi a gefe. Addu'a ya soma yi yana tofe ta dashi tub_tub. Daga bisani ya ɗakko wani garin magani ya kwaɓa da wani irin kitse ya shafe mata wuyanta dashi, ya yayyafa mata wani ruwa a ƙwarya.
"Allah ya bata lafiya, amman dole zamu riƙeta anan domun ace za'aita tiri_tiri abun bazai yi muku kyau ba jikin nata zaiyi laushi. Akwai magunguna da zan sa mata su dafa, akwai na sha da na wanka in sha Allah. Ga wannan shi kuma sau uku za'a dinga shafa mata a rana. Allah yasa mu dace, ku ɗauketa in kun shiga cikin gidan kuce Hanne ta nuna muku ɗakin jinya zata nuna muku. Akwai masu kawo abincin siyarwa dandali zaku iya sayen duk abunda kuke so, dan ba lallai bane abincin namu yayi muku ba." Da godiya suka kinkimi Asiya zuwa ɗakin jinya da Hanne ta nuna musu. Akwai majinyata har guda biyar a cikin ɗakin. Goggo Safiya tace.
"Nafeesa zuwa gobe sai ki yi azamar komawa ɗakin ki, kya dinga zuwa dubiya lokaci zuwa lokaci tunda bamu san yaushe zamu bar nan ba" Nafeesa sai ta fashe da kuka tace.
"Wallahi Goggo Safiya ko bacci bana iya yi a cikin gidan, firgita nake yi sosai. Sannan shi kanshi mai gidan kar ki so ki ga irin tsawar da yake daka mun ni bazan koma ba" Mama ta yi wuf tace.
"Ki ma kan ki Alam nashara ki koma ɗakin ki bakin ki a likkafa Nafeesa, da kinga halin da Zubaina take ciki da yanda ta zama kuma kice me?" Nan su kai ta lallaɓata washe gari ta kama hanya ta koma. Su kuma su ka ci gaba da zaman jinyar Asiya, babu dai wani canji, abinci da ruwa ɗura mata akeyi, baya wani shiga, ba um ba um _um haka dai take kwance kamar gawa bata dai sauya zane ba. Mama kuwa ƙafarta kullum a cikin ciwo take sai da malam Ja'e ya ɗaurata itama akan magani, dan magashiyan ta kwanta jinya, bata ko iya motsa ƙafarta guda ɗaya balle har ta takata. Oh Duniya mai ido a tsakar ka kenan, ku dubi yanda rayuwa take juyawa wannan kaɗai ya ishe mu jin tsoron rabbil sama wata wal ardi. Ubangiji ka bamu dama da ikon cinye jarabawarmu.






Mrs Bukhari ce
[20/08, 10:01 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
DUNIYA
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI IBRAHIM B4B GIDAN ƘAMSHI 57








GHANA:










ZUBAINA:
Haka na ci gaba da rainon ƴan biyu na, ga jego ga aikin gida, gashi ko ishasshen bacci bana samu. Gabana kuwa duk ya ɗaɗɗaye tsumman ƙunzugu ya cinye mun wajan sosai, a tattale nake tafiya. Rashin kyan abinci da rashin lafiyayyen abinci yasa na sake ficewa a hayyacina, suma yaran ruwan nonon babu maiƙo baya isan su sam, shi yasa kullum a cikin tsala kuka suke, ni kenan a cikin rarrashinsu, in abun ya isheni in ta faman kuka nima. Musa ne ya kira wayata, tun shekaranjiya nake mai filashin sai yau ya kira.
Musa ya ake ciki ne wai, wayar su Mama bata fa shiga kwata_kwata ranan kace zaka je can ƙauyan ka dubo jikin na Asiya tunda Nafeesa ta maka kwatance ko, to baka je ba?" Musa yace.
"Gobe zan je in sha Allah tare da Kawu Tanko zamu je da Kawu isiya zai tawo daga Rano yau, gobe sai mu wuce. Wallahi Zubaina rayuwar na gama tsorata da'ita kin ganni ina nan ina istigifari wallahi bani ba zina, wallahi duk waɗanda naga suna aikatawa ma zan musu faɗa ni islamiyya ma zan koma ko da ta dare ne, bazan so abunda naima yaran wasu nima ai ma yarana ba. Yanzu ga Sagiru yana firizin kuma rayuwarshi zai gama gaba ki ɗaya a can. Rai suka kashe, kuma ran yana da gatan shi. Sati guda kenan da aka gama zaman kotu, har Kawu Isiya ma ya tawo daga Rano. Amman an yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai, ni faɗa miki ne banyi ba, kuma kuji da musibar dake gabanku, Mama ma sai mun je ƙauye zamu faɗa mata. Ba network ne a garin" Da kuka na ajjiye wayar, na sake shiga wani mugun tashin hankalin sabo. Ji yanda rayuwarmu ta dawo abun tausayi kamar ba damu ake damawa ba a da. Ni nawa ma da sauƙi dubi Asiya da Sagiru yanda rayuwarsu ta juye cikin ƙanƙanin lokaci. Oh Allah na tuba ka gafarta mun, Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar. Ƴan biyu na haɗe a bayana su biyun na goya su na dawo bakin aikina. Zarah sai zage_zage da habaice habaice take ta faman yi. Ina gaban murhu ina iza itace Alh Liti ya shigo yana ihun kiran sunan Nabeela, sai uban sauri yake yi. A guje Nabeela ta fito.
" Na sauwaƙe miki aure na, Zarah kema ki je na sakeki tunda baki da ciki, kwanaki dai naji labarin kin yi ɓari. Ku tattare ku bani fili zanyi sabbin zubi" Salati muka shiga zabgawa, saki shi bashi da daɗi sam, duk buyagin gidan Alh Liti in ya saki mace sai ta ci ɗan banzan kuka, ko dan sabida yaranta da zata tsallake ta barsu. A ranar Nabeela ta kama hanyarta, ni ina kuka ita tana kuka, yaron da take goyo ta miƙo mun, hannuna yana rawa na amsa.
"Gashi dan Allah ki haɗa ki shayar dashi shima, nono yana da matuƙar hamimmanci ga jikin yaro, watan shi biyu zaki dinga haɗa mishi da kokko. Hajiya Kubra saduwar alkhairi, Allah ya ƙaddara saduwarmu, ya haɗa fuskokinmu da Alkhairi" gidan gabaki ɗaya a ranar hautsine mana yayi ni da Hajiya Kubra. Washe gari sassafe Zarah ta tattare inata inata itama tayi gaba. Abubbuwa suka sake cakuɗe mun, ga yara har uku, ga aikin gidan ya ƙaru mana ainun. Da yamma ina zaune a ƙofar ɗakina nayi jigum yaran yanzu na gama basu nono duk sun yi bacci. Sai ga wayar Musa. Ina ɗagawa na jiyo muryar Mama cikin rishin kuka. Gabana ya yanke ya zube hankalina ya tashi ainun cikin kakkarwar murya nace
Ta mutu ko? Innalillahiwainnailaihilrajiun kaico har ga Allah banso Asiya ta mutu ba tare data yi istigifari da aiyukan alkhairi dan wanke laifukanta a wajan Allah ba" Ina gama faɗar haka na ƙule ɗaki da wayar a kunnena.
"Bata mutu ba Zubaina amman dole ki tausaya ma Asiya in kika ganta, duk da dai muna ganin canji sosai dan ta soma karɓar abinci. Sai dai ba um ba um um. Jiya Zakiya da Rakiya suka koma sun zo dubamu, Nafeesa ma tana nan tare damu, mijin yayi mata kafurin duka ya korota, amman bai saketa ba dai. Mun yi kiran wayarshi kiran duniya ya ƙi amsa kiran namu. Ga ƙafata ciwo take yi. Ni dai ku yafe mun dan Allah duk ni na sa ku a wannan ukun na tuba na tuba." Idanu na lumshe wani hawaye mai zafin gaske ya yanko mun. Tausayin kanmu dukka ya kama mu, a hakan ma bata san abinda Sagiru ya aikata ba.
Mama ki gode ma Allah daya ganar damu, lokaci bai ƙure mana ba. Muita roƙon Allah gafara, shi ɗin mai yawan afuwa ne. Bani Musa " Mama ta miƙa ma Musa waya.
Musa so nake ka kira wayar Bulama kaji ya su Bawa suke, in da hali kaje ka dubo mun su. Wallahi kwana biyunnan sun tsaya mun a raina. Ban ma yaran adalci ba yanda nayi fatali dasu, kai mun wannan taimakon." Ya amsa mun akan zai kira duk yanda su ka yi zai sanar mun. Ya ba Goggo Safiya mu ka gaisa, Nafeesa ma muka gaisa, nayi mata ƴan nasihu a matsayina ta babba, daga haka mu kai sallama dasu. Rayuwa tai ta kulawa watan su Mama biyu a gidan mai magani, hatta da gidana da suke ciki sai da aka siyar da ɓangaren da aka zuba haya, ɗakin mama da ɗakin Musa kawai ya rage. Ni kuma ina da wannan ɗanyan goyon, bala'i na yau da ban na gobe da ban. Kwatsam na tsiri laulayi, ga yara uku, ga ƙaramin ciki ga fargaba, ga bautar gidannan abubbuwa suka sake dagule mun. Ɗan sauƙin dana samu shine yaran suna shan kunu sosai, kuma ina mamula musu tuwon dokunu suna kuma karɓa. Bayan tafiyar su Nabeela da wata uku Alh Liti ya fello Amarya zuƙeƙiya kyakkyawa yarinya shatab da'ita. Ni dai baya gabana ina fama da laulayina. Asiya jiki da sauƙi sosai, mai maganin ma yace musu sati mai zuwa zai basu sallama, harma an bani ita a waya mun yi waya na ji muryarta sai naji sanyi a raina. Musa kuma ya sanar dani yayi waya da Bulama, amman yace mishi sun koma Yobe da zama. Take hankalina ya kuma tashi sosai, sai Musa ne yai ta kwantar mun da hankali akan da zaran su Mama sun dawo shi zai je Yobe ya gano mun su, shine na samu dama dama.








Yobe:




Yahanasu
Ina zaune a kan kujerar falon Mama Gana, ga akwatina, da jakar kayan Mama Gana a kusa da ƙofar shigowa. Sai mu ka jiyo sallamar Bulama Babba. Gabana naji ya harba, dama sukuku nake jin kaina yau tunda na tashi, dan da ƙyar nayi wanka na kintsa ko karyawa Mama Gana tayi_tayi in karya naƙi, nace mata in naje gida zan karya. Carab muka haɗa idanu da Bulama Babba, yaci ado dama can shi gwanin adone gaskiya rayuwace ta mayar dashi baya talauci babu abinda baya haddasawa.
Sannu da zuwa Bulama Babba " na katse kallon ƙudan da muke ma juna. Bai kai da amsawaba Mama Gana ta fito daga ɗaki ta cokara ɗan kwali tayi shar da'ita."
"Au kazo ashe? Ke taso mu tafi karmu ɓata ma ango lokaci." Shi dai kai ya sosa ya zube ya shiga gaishe da Mama Gana, nima na gaisheshi muka ɗunguma cikin motarshi. Mama Gana ce ta shige gaba abunta ni kuma ina baya na lumshe idanuna ina ambaton Allah hawayene ke shirin tsinke mun ni kuma sai daddaurewa nake yi kar hawayennan ya zubo in kunyata. Dan Mama Gana ba ƙyaleni zata yi ba. Zama yayi a kujerar direba bayan ya zuba mana jakunkunan mu a bayan but.
"Masha Allah mota tayi kyau rangaɗi kenan, a kashe lafiya, ango mijin Yalewa kenan. Ni ko Ahmad da matarshi fa ba za je bikin bane?"
"Zasu je, suna hanya shi da iyalan nashi." Ya bata amsar a taƙaice, ta sake jefo mishi tambaya.
"Tare zaka tawo da Amarya bayan an gudanar da hidindumun bikin ko, iyayenta ne zasu kawo maka ita" Sai cewa yayi.
"Ni fa ban san komai game da tsare_tsaren su ba. Kinga ina gadon asibiti suka tsara koman su. Duk yadda ku ka yi dai_dai ne." Mama Gana tace.
"Ni kaza duk yadda uwarka tayi dai. Kai Hajja tayi ƙarkon kifi daga ruwa zuwa wuta wallahi, kuma ta tsinka Modu. Duk irin so da kulawar da Modu ya baka a rayuwa yau shine zata tozarta mishi ƴa. Allah ya bamu lafiya, za ku sha mamakin irin mijin da Uwata zata aura." Tai ta surutu ratatata, mu dai kowa yayi shiru kamar ruwa ya cinye mu. A haka muka isa Damaturu gida batse da jama'ar biki kowa ka gani cikin lafaya, tsakar gidan sai ƙamshi turare yake zabgawa. Da halama gagarumin biki Hajja ta shirya bana wasa ba. Ni dai na shige cikin ƴan uwana, amman babu walwala ko kuzari a jikina sam, amman haka nai ta daddaurewa anata sha'anin bikin Bulama Babba da wakil da zai auri ƴar wan Ya Innana da suke zaune a Biu. Biki aka gudanar cancaɗeɗen gaske, Hajja tayi ɓarin kuɗi sosai. Ba Bature suma ba ƙananan kuɗi suka kashe wajen haɗa akwatin ango ba, wasu irin tsadaddun yaduna da shaddajo aka zuba mishi, agogon hannu ma sai da suka zuba hannu bakwai, banda turaruka da sauran tarkace. Irin yanda muke gudanar da bikin al'ada haka akayi wannan biki shina. Zuchiyata sai suya in na ga Bulama Babba cikin adon kece raini, duk da baya cikin walwala Amman sai nake ganin ai yana son matarshi. Ni kuma fa a cikin taron bikinnan sai nuno ni akeyi, daga masu kaɗa kai sai masu nuna sun tausaya mun. Hankali ya tashi ainun. Ranar da za'a kai Amarya Yobe Ba Modu ya kirawoni har ɗakinshi, na zauna a ƙasa kaina a ƙasa ina sharar hawaye. Allah shine masanin tsantsar son Bulama Babba dake raina.
"Uwata kiyi haƙuri ki nutsar da zuchiyarki waje guda. Kifa tuna da baya ko a mafarki na tabbatar baki taɓa mafarkin zaki auri Bulama Babba ba. Ki koma wajen Mama Gana da zama uwata, ki tafi da motarki sabida in kin samu aiki ki dinga tafiya da motarki. Kuɗinki kuma uwata na ƙara miki dubu ɗari biyar akwai. Yayyenki maza suka haɗa miki dubu ɗari shidda suma. Uwata ki soma sana'a kina haɗawa da aikin ki na jarida. Sai ki ga kin samu nutsuwa. Kije kiyi tunanin abunda zaki yi na sana'a. Mama Gana zata kai ki wata ma'aikatan talabijin na kan tauraron ɗan adam zaki ci gaba da aikin ki. Kiyi haƙuri duk ke kika jawo ma kan ki, ban yi tunanin zan iya jin na tausaya miki ba, da baki yi wannan shaye_shayen ba ba lallai bane Hajja ta bijiro da wannan halin ba. Amman ina baki haƙuri."
To Ba Modu nagode sosai da kulawarku gareni. A gaskiya na cuci kaina a bisa halin dana jefa kaina a ciki. Ƙaddarallah. Kuma inaso zan buɗe babban shagon gyaran jiki da gyaran kai irin na Kanuri, da su ƙunshi, da turarukan wuta da humra. Abinda nake son yi kenan" Ba Modu yace.
"To kinga ta kwana gidan sauƙi, gidan da Bulama Babba ya baki akwai shaguna kinga har uku a jere. Sai ki sa a haɗe miki shagunan, a gyara miki shi tas. Sai ki soma gudanar da harkar kasuwancin naki. To amman aikin naki zai baki damar yin

62 / 67