MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   40 / 67

117K to 120K   out of 198.3K words

fa, jirgin Lagos kaɗai ya sako mu aka kawo mu. Da ba dan Mabaruka, da yarannan namu ba, in dan ni da Safiya ne, wallahi da sai dai muyi bara a ƙarƙashin gadar Lagos, har zuwa lokacin da zamu haɗa kuɗin motar da zai dawo damu Kaduna. Yaya Jummai tunda muka ci abincin tarar baƙi, bamu sake sa dai _ dai da ruwa a bakinmu ba a cikin gidannan. Nafisa tace.
"Aini Mama tunda aka kawo bushashshiyar jollof ɗin, jikina ya mutu. Domun a yanda Alh yake da mashahurin kuɗi, bai dace ace ma abincin gida zamu ci bana hotel ba. Ki duba fa lokacin da Asiya ta haihu, ba hotel babba Alh ya kama akayi hidimar suna a ciki ba, duk abinda muke so muyi oda kai tsaye daga Kitchen ɗin hotel ɗin. Wallahi na zaci hakan Alh Liti zaiyi mana. Nifa jikina yana bani akwai matsala babba gaskiya." Asiya wacce tayi tagumi tayi jigum tace.
"Matsala kam akwaita. Kuma wallahi ko da na tambayi Alh akan me ya sani game da Abokinshi. Ni fa Mama ce mun yayi bai san komai a game dashi ba, yasan dai mashahurin ɗan kasuwane, kuma yana da kuɗin daya ninka nashi, harkar kasuwancin zuwa ƙasashene ya haɗasu har suka zama abokai. Amman baisan kowa nashi da komai nashi ba. Ni sai naji duk jikina yayi sanyi gaskiya." Mama duk tabi ta ruɗe sosai, ta rasa ta cewa, dan tana tsananin son Zubaina, dan ita bataƙi duk abinda ta samu ta kashe akanta ba, ita kuma zuchiya tana son mai kyautata mata ne.
"Ku kira mun layin Zubainan dai ko Allah zai sa ta ɗauka, muji tana dai lafiya ko?"
"To ai Yaya Jummai tun a Lagos muke kiran wayarta ba'a ɗagawa, har shi mijin mun kira bai ɗauka ba. Abunda ya sake kashe mana jiki kenan" Mama tace.
"Rakiya ku sake kiranta, hankalina bazai kwanta ba, in banji daga Zubaina ba. Ni na shiga uku, karfa son zuchiya ya kaimu tsakar rana. Ni na ɗauka mijin Asiya yasan komai a kanshi. Shi yasa ko da Tanko yayi magana, nace mishi daga ɓangarenmu munyi duk wani bincike" Sun ta kiran wayar Zubaina data mijinta shiru kake ji malam yaci shirwa. Gabaki ɗaya cikinsu ya ɗuri ruwa, an rasa me bacci, gashi ba gari ɗaya ba, balle gobe ai musu dirar mikiya sassafe.




Yahanasu:
Bulamana na juyo na kalla, sai sauke numfashi yake yi, hankalinshi a kwance, amman ni bacci ya ƙauracema idanuna, ga wani irin nauyi da nake ji a kaina tamkar kan nawa zai fashe. Nayi alƙawari a wannan cikin, bazan sha komai daya danganci kayan maye ba, ko dan ganin na samu haihuwa nima, ina nadamar wanda nasha a baya, kuma ina roƙon Allah ya yaye mun wannan bala'in. Kuma babban abunda Bulamana yake so bai wuce ƴaƴa ba. Ko ba komai nima inga jinina, iyayena ma kullum a damuwar rashin haihuwata suke, dan har Ya Innana ta ce in nazo bikin Wakil, zata kaini wajan wani mai magani, in soma shan maganin hausa, ko Allah zai sa a dace. Ga kaina yana barazanar fashewa. A daddafe na miƙe tsaye, nayi alwala a cikin bahun, dan dare ne sosai tsoro bazai barni fita ba. Sallar nafila na tayar, amman wallahi abun gagara yayi, inyi karatun sallah na kasa, sai wani irin ƙara da hauragiya nake ji a kaina da kunnuwana. Zama nayi daɓas, nayi shiru ina tunanin yanda na lalata rayuwata a banza da wofi, har ta kai ta kawo bana iya gudanar da komai, har sai nasha abubbuwan maye. Gashi sallah na kasa karanta ko wacce sura, ni da nake da sittin a kaina. jin kaina nake tamkar ban haddace ko alif ba. Qur'ani na jawo na buɗe, rubutun kawai nake bi da kallo, na kasa haɗa baƙin in karanta, sakamakon ciwon kai da ruwa da idanuna ke fitarwa. A wajan na kife na saki kuka mai gunjin gaske, wanda yai sanadiyyar farkawar Bulamana. Da sauri ya iso inda nake, ya sa hannu ya ɗagoni, na faɗa jikinshi kukan nawa ya sake tsananta. Sai kalmar la'ilaha illallah nake ambato, ina haɗawa da lahaula wala ƙuuwati illabillah, astagarufullah astagarufullah astagarufullah. Ina yi ina kuka muryata na rawa. Bulamana duk yabi ya kiɗime, yana tambayata menene damuwata, ko cikin ya zube ne.
"Haba Yahanasu, me yasa kike haka, dan cikin ki ya zube shikenan sai ki ta rusa kuka tsakar dare, ƙarfe biyun dare ne fa yanzu. Ki jini da kyau, Allah yana sane dake, kuma ai ya baki bai zauna bane. Kinsan adadin matan da suke son ko ɓarin ne ace sunyi, dan a dena kiransu da juya kuwa? Ke ki godema Allah da yake baki ya amshe. Ni baki ga canji daga wajena ba, kinsan kuma ai baza ki gani a wajan iyayenmu ba, dan haka ki share hawayenki, kizo muje ki kwanta" Miƙar dani tsaye yayi, ina jikinshi muka isa kan katifar, ya kwantar dani, shi kuma ya zauna yana mammatsa mun jikina a hankali. Rufe idanuna nayi kamar mai bacci. A ƙasan zuchiyata kuma tausayin kaina, da tausayin Bulamana ne fal cikina. Ina tausayin kaina a ranar da asirina zai tonu, ƙila hakan yai sale salin ruguza dukkan farin cikin gidana, dama farin cikin dangina. Kab gidanmu babu ɗan shaye_shaye sai gashi an same ni, ina mace, macen aure da shan miyagun ƙwayoyi har yayi sale salin zubewar ciki a jikina har sau huɗu. Nayi ma kaina alƙawarin na dena shan komai, ko dan lafiyata, da lafiyar yaran da zan haifa. Bugu da ƙari ina cikin saɓon Ubangiji, nabi ruɗin zuchiya, idanuna ya rufe ni nitsuwa kawai nake son samoma kaina tsiya tsiya. Na mance dukkan nutsuwa yana ga karatun Qur'ani mai girma, sallah, da tasbihu sune kaɗai ke yayema mutum damuwa, su maye ma da farin ciki. Gani da haddar izifi sittin cib a kaina, musabaƙa naci ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Amman nayi fatali da sanina, na nema ma zuchiyata salama ta hanyar shan miyagun ƙwayoyi, gashi sun kaini sun baro. Ya iyahil alamin, Allah na tuba." Kwanciya bulamana yayi a hankali a gefe na, a tunaninshi na samu baccine. Buɗe idanuna nayi, hawaye sai cika su suke yi tab, suna sulalewa ta gefe da gefen idanun nawa. Bacci kuwa babu dalilin wanzuwarshi"




Ghana:
Ni dai a zaune a inda Alh ya barni, bansan mintuna nawa na share ba. Har ya shigo ban san ya shigo ba, sai da na jiyo amon shegiyar muryarshi, da lalatacciyar hausarshi ta mutan Ghana a kaina yana faɗin.
"Ke ko tunanin me kike yi a rana irin ta yau? Kin mance da tarin alƙawarurrukan da kikai mun a wannan darenne? Ni ko fes suna ƙwaƙwalwata tun daga ranar da kika furtasu kawo i yanzu. Yanzu dai zo mu shige daga ciki ko?" Kallonshi nayi, daga shi sai gajeren wando, da singlet, tumbinnan nashi yayi wani uban tsoro, gashi da nonuwa kasancewarshi mai ƙiba. Ni dai a kiɗime na bi bayanshi muka shiga ɗakin baccinshi. Ɗakin baccin ya haɗu, ga gadonshi babba 6 by 7 katon gaske, yasha lallausan farin zanin gado, sai ƙamshi ɗakin yake fitarwa.
"Zauna a kan gadon mana, ai ranarki ce yau, a gadonnan zamu ci uwar sabada" Idanu na zare, na zama kurma dai. Wutar ɗakin ya kashe duhu ya gauraye ko'ina a ɗakin. Muryarshi na jiyo yana cewa.
"Ki cire komai na jikinki ki hayo mana, naga kina ta yin wani abu kamar wacce aka zare ma laka a jiki ne" Ƙululu cikina ya ba da ƙara, kuka na sakar mishi mai gunji. Wutar ɗakin ya kunna muka haɗa idanu, babu komai a jikinshi, miƙewa nayi da sauri zan gudu, hannuna ya riƙo ya yarɓani a kan gadon ji kake yib ya bugani a katifa ya kashe wutar ɗakin. Gauramun mari yayi, yana huci.
"Baki da hankaline dan ubanki, ni zaki haramta ma kanki, duk maƙudan kuɗin dana kashe a kanki, zaki tuɓe ki kwanta ne, ko sai na banƙare miki ƙafa kamar yadda ake banƙare kazar gidan gona?" Jikina na rawa na shiga kiciniyar cire kayan jikina, tsoron Alh take ya ɗarsu a zuchiyata, dan daga marin daya wankeni dashi, nasan in nayi wasa zansha jibga a darennan. Jikina na rawa na haye gadon kusa dashi, ina runtse idanuna. Mirginowa Alh Liti yayi, kawai ya danneni, banyi auneba naji yana neman hanya, ba tare da ya taɓa komai na jikina ba, sai kace wata jaka ya hauni. Da sauri nace.
Dan girman Allah, Alh kayi wasa dani, kar ka afkamun haka kamar jaka." Idanu na runtse tsabar tsoronshi, gashi Mabaruka tasa naje asibiti an ɗinkeni. A wannan daren Alh ya majigani sosai, ko tunkuza bata kaini shan matsa ba, nasha azaba sosai. Shirim Alh ya sauka a kaina, yana mayar da numfashinshi. Ni kuma ina kwance ina kuka mai ƙarfin sauti, dan wallahi ko kasheni zaiyi yau ni sai ya sake ni a darennan.
"Ke wannan wanne irin bura'ubanci ne haka, zaki tusani gaba kinai mun kuka kamar wacce akai ma fyaɗe. Ko so kike dole ki sani in koyi iskanci ƙarfi da yaji. Shikenan kinaso in sha miki nono, in shafa miki mazaunai sai kace wani ɗan bakiri, ko ƙaramin yaro, ko an ce miki ni ɗan iska ne? To ni ban taɓa yin hakan ba akan ki kuma bazan yi ba, kija bakin ki ki mun shiru ni dallah"
Dan Allah Alh ka rufa mun asiri, ka sake ni in koma ƙasarmu. Wallahi bazan iya rayuwar aure dakai ba, na roƙe ka da Allah ka sake ni" shiru naji yayi, ina juyowa naga baccinshi ma yake yi ashe, sai gwarti yake sha. Ihu nayi tare da bubbuga gadon, dole ya buɗe idanunshi ya kalleni. A zabure ya tashi yana ƙoƙarin wawuroni, banci nasarar guduwa ba, dan zafin nama ne dashi. Danneni yayi ya sakarmun nauyinshi yace.
"Kin ɗauka ni irin ɗan iskan mijinki na baya ne ko, ƙila kin saba yi mishi rashin daraja yana ƙyaleki ko? In na kuma jin muryarki saina baki mamaki a cikin darennan, kinsan koni waye ma kuwa? Oh son duniya ya rufe miki idanu ke da kilakin uwarki, shi yasa kuka kasa bincike a kaina. Gidannan kuma kin shigoshi kenan, babu saki, babu yaji." Da ƙyar nake numfashi sabida nauyi ya sakar mun, sai da yaga fuskata ta dawo jazur sannan ya rabu dani. Ya mirgina ya kwanta, ko minti biyu baiyi da kwanciyar ba yayi baccinshi hankalin shi a kwance, sai gwarti yake sakarwa. Ni kuwa ina kwance ko ƙwaƙƙaran motsi tsoron yi nake yi, dan gudun kar Alh ya farka, bansan irin buyagin da zai tare ni dashi ba. Tun ina hawaye a wannan dare, har hawayen nawa ya ƙare, kaina ya ɗau caji, tashin hankali ya ziyarceni, mafita kawai nake nema koma wacce iri ce in dai zata fitar dani a wannan ƙaddarennen gidan. Idanuna biyu aka yi kiran sallar asuba. Lumshe kumburarrun idanuna nayi, na sakko daga kan gadon, jikina yayi mugun tsamin gaske. Ban ɗakin dake manne a cikin ɗakin na shiga, na tari ruwan zafi a bokiti na gargasa jikina, ina jin wani jirin yunwa, da zazzaɓi a jikina. Na gargasa jikina sosai, sannan nayi wankan sallah na fito. A ƙasa na tsince kayana na mayar jikina. Na soma sallah kenan Alh ya sakko daga kan gadon. Dariya naji yayi. Ko ta meye ohon mishi.
Ina zaune a inda nayi sallar ya fito ɗaure da tawul, a gurguje ya zura jallabiyarshi ya fice. Fitarshi ke da wuya na ji wayarshi ta shiga kuka, ko in kula ina zaune ƙwalam, da naji kiran yayi yawa ne dai na miƙe na isa bakin gadon. Jummai naga an rubuta, dana kalla da kyau sai naga kamar number Mama. Baki na riƙe dana tabbatar numbern ne. Da sauri na kara wayar a kunnena, kafin tace wani abun na ɓalle mata da gigitaccen kuka, duk na tashi hankulansu, dan ina jiyo Asiya tana cewa.
"Kinga ni ba, ai ni nasan ba Lafiya jikina ya bani" Inyi Magana ma na kasa cewa komai.
"Zubaina akwai matsala ko? Ki buɗe baki kiyi mun magana ko zan samu sassauci, dan jiya ko runtsawa banyi ba. Cewar Mama, cikin shessheƙar kuka nace da Mama.
Alh Liti azzalumine macuci maha'inci ya yaudareni. Gidanshi yafi kurkuku muni da wahala. Mama ki tawo ki tafi dani dan Allah, dan Allah Mama kizo, dan in kika wuce kwana biyu baki zo ba, wallahi zan kashe kaina kowa ya huta" Motsin shigowarshi ne yasa na zabura naja baya, tare da datse kiran Mama. Tinƙis tinƙis ya iso gare ni, yana wani zazzare mun idanu.
"Na lura kina da taurin kai ko? Ko da yake Rumaisa'u tayi hauka a cikin gidannan na sama da kwana biyu, babu wanda bata kutuntumama ashariya ba, amman daga baya ai kinji roƙo take yi ma in barta ta kula da ɗiyoyinta, kar su zama ƴan tsakar gida kamar sauran. Ni kuma baiwar da Allah yai mun, sau ɗaya nake kwanciya da mace ta samu ciki. Zubaina inaso ki kiyayi shiga gonata, ki kiyayeni bani da daɗi" Tsugunnawa nayi ƙasa, akan guiwowina ina roƙonshi ya sauwaƙe mun aurenshi. Dariya yayi mun yace.
"Ki shirya ki caɓa ado, yau lahadi rana ce ta musamman da nake ganawa da kab mata da yaran gidana, in gansu su ganni, waɗanda suke da ƙorafi duk yau suna da dama. Ki shirya ki same ni a falon ƙasa an kawo abun kari." Wayarshi ya karɓa a hannuna, ya harareni kafin ya fice. Ina hawaye na biyo bayanshi har zuwa falon ƙasa.
Inason in duba kayana yana can ɗakin" Na nuna mishi ɗakin da hannuna"
"Ki shiga ki sake kaya, kayan akwatunan kuma kar ki taɓa su, ki barsu a ɗakin. Kayan da kika tawo dasu daga gidan iyayenki, sun isheki kiyi amfani dasu, danni ba almubazzari bane. Akwatunan kuma na kaima ƙanwarki da zan auro ba da jimawa ba, domun kayan akwatunannan da kike ganinsu na cizo ne, waɗan da kika ɗinga Allah ya ci dake, sauran kuma a cikin ɗakin zaki barsu, dama daga ɗakin aka fitar dasu. Tunda na shigo gidannan nake ganin abubbuwan almara iri daban_ daban. Inason yi mai tambaya, amman bata da amfani, ni da ba zama nazo yi ba ma. Shigewa nayi ɗakin, hawayen idanuna da halama sun ƙare tas, doguwar rigar leshi na saka, na shafa mai na na MAKARI, na fito falon. Da idanu ya bini, yana lasar bakinshi, ni kuma na sake haɗe raina tamau. Kujera na nufa zan zauna ya dakatar dani.
"Baki da tarbiyya ne, ina kujera zaki zauna a kujera, in ubanki ne a zaune a kujera ai bazaki zauna a kujerar ba. Bake ba ko wacce matata a ƙasa take zama in ina gabanta. Na lura dake tun jiya kamar baki horu da tarbiyya ba, amman zaki samu tarbiyya a nan gidan." Ji nake kamar in kutuntuma mishi ashar, in yi fashe _ fashe a falon, ko in mutu ko in yi rai. Dannewa nayi, na zauna a ƙasa.
"Ga abun karyawarki nan, ki karya kafin iyalan gidan su zo" Muguwar yunwa nake ji dama, kofin silvern daya nuna mini na jawo, na buɗe wani ruwan kokko na gani tsararo a ciki, sai ƙuli ƙuli mai suger, irin masu faɗinnan guda uku, da mazar ƙwaila rabin_ rabi, wato kwata. Ɗagowa nayi na kalleshi, yanda yake shan kunun yana kallon labarai. In ya gutsiri kuli kulin, da mazau ƙwailar sai ya guntsi kunun. Kasa yin hakan nayi, iya kar ruwan kokkon nasha kawai na rufe. Kallona yayi yace.
"Bakya cin ƙuli ƙuli ne?" Kamar in zageshi haka nake ji, da ƙyar na daure nace.
Ina ci" Kai ya gyaɗa yace mun.
"Kinga dukka matan jikin hotunannan? Matanane dana auresu, dukkansu munyi rayuwar aure dasu, wasu sun haifamun ƴaƴa, wasu kuma ɗaya suka haifa. Biyu daga cikinsu ne Allah yayi musu rasuwa, a wajan haihuwa, suka mutu tare da abinda ke cikin nasu." Kallon hotunan na shiga yi, ina ƙirga yawansu a zuchiyata. Mata rai goma sha shida na ƙirga cib harda nawa hoton da aka kafe a kusa da wata kyakkyawar matashiyar bafulatana mai ƙuruciya. Kafin in fita daga mamakin lamarin Alh Liti, su Hajiya Kubra su ka yo sallama, su uku suka shigo. Da idanuwa na bisu, yanda naga sun durƙusa suna kwasar gaisuwa a wajan Alh, sai kace wani adalin sarki. Ya ɗauke kanshi shi kuwa gogan kallo wannan basu isheshi ba, amman ya tambayesu ya yaran suke, sannan a cikinsu wacece bata da lafiya"
"Nice Alh bani da Lafiya, juna biyu gare ni, sai dai yazo mun da ciwon mara sosai, kwana biyu kenan bana runtsawa" Sai lokacin ya juyo ya dubeta, baice da'ita komai ba. Dawo da kallonshi yayi gareni yace.
"Waɗannan sune abokan zamanki Zubaina, Kubra, Nabila, Zakiya, sai ke cikwaton ta huɗun.
MRS BUKHARI[09/08, 11:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
33














Da idanu na bi matan Alh Liti gasu nan a zaune su su uku. Al'amarin gidan Alh Liti da shi kanshi mai gayyar ƙoƙarin tarwatsa mun zuchiya yake yi. Dukan yayi mun yawa tako ta ina. Wato gadar zare Alh Liti yai mun, ni kuma kwaɗayin abun hannunshi yasa na zurma wannan gadar, gashi gadar na shirin halakar dani. Amman nasan da zaran Mama tazo ƙasarnan ƙafarta_ ƙafata, in ma bata zo ba a cikin kwana biyu, to tabbas zan shiga duniya, da in zauna wahala da takaicin gidan Alh Liti ya hallaka mun rayuwata, ya sukurkuta ƙuruciyata, na gwammaci in fantsama duniya a neme ni a rasa. Alh Liti ya ce.
"Kubra ina yaran suke to?"
"Suna waje suna jiran ai musu iso. Sai dai mummunan abu ya faru da Rashida,

40 / 67