Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
dawo." Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Gidanne naji ba daɗi da bakya cikinshi, har wani duhu_duhu nake gani. Bari inzo in same ki a can gidan Kawu Tankon, ma dawo tare." Dariyar farin ciki nayi, lallai Bulama ya kamu sosai.
A'a kayi haƙuri nima da zaran baƙin sun tafi zan tawo. Ka siyo gadon kuwa da nace ka siyo?" Ɗan tsaki yayi yace.
"Nasiyo yana can ɓarayin nata, inna huta zanje in kafa"
Kai da kanka, me yasa ba zaka ce ita ta kafa maka gadon ba? Ai ba aikinka bane. Ka tura Nafisa ta sanar da'ita ta gyara ɗakin. Kaci abincin?"
To shikenan an gama, yanzu zan turata. Abinci kuma banci ba, yanzu ta kawo abincin ma. Wanka zanyi, inna dawo daga masallaci zanci, amman saifa kin dawo" Nan mu kai sallama na ajjiye wayata. Gaggaisawa mu kayi da Goggo Safiya, da Goggo Nafisa. Goggo Safiya tace.
"Ya Jummai tana lafiya da sauran yaran dai ko?" Nace.
Lafiya lau suke. Bari inyi sallah kafin baƙin su iso" Alwala na ɗauro nazo na gabatar da salla. Ina idarwa su Goggo Rakiya, da Mama Zakiya suka shigo cikin ɗakin Goggo Safiya. Ƙannen Mama ne su ɗin. Ashe wai Alhaji Jabeer tare da mata suke, masu kawo akwatin gaisuwa. Ana kan gaishe_ gaishen yaushe gamo, sai ga baƙi mata Musa ya rako su huɗu. Kai da gani kaga hajiyoyin Kano, kuma kana kallonsu kaga masu hannu da shuni, dan manyan atampopine a jikinsu, harda gwal. Tarbar arziki da karamci sosai suka samu a wajan su Goggo Safiya. Akwatinsu na gaisuwa guda uku, shaƙe da manyan atampopi da shaddajo, da mayukan shafawa, da sabulan ruwa, banda katan katan na lemo, da biskit Kaya dai sai son barka. Sunci kaji sun kora da ruwan gora. Bayan sallar isha kuma suka tafi, zasu je su kwana a gidan wata ƴar uwarsu a cikin gari, tukuicin nera dubu hamsin na basu, domun hausawa na cewa tuwon girma miyarshi nama. Bayan tafiyarsu ne, Kawu Tanko da kawu isiya suka shigo.
"To Safiya, Nafisa, Zakiya, Rakiya, Zubaina, da kai Musa ga sadakin Asiya na karɓa. Sunce kuma shi Alhajin sun gama magana da Jummai akan sati uku za'a saka. To mun tsayar a hakan, ranar juma'a za'a ɗaura auren a ƙofar gidannan. Amman wa aka wakilta dan binciken halayya, da nasabar shi wanda Asiyan zata aura? Duba da yanda sharia ta ba da damar ayi bincike in za'ayi aure sabida gudun matsala" Goggo Rakiya tace
"Duk wani bincike sai da babban wanmu Ɗan juma ya gudanar, tun kafin azo wannan fagen ai Tanko" Kawu Isiya yace.
"To ai shikenan tunda kunyi bincike. Ga sadakinnan nera dubu ɗari biyu. Ni naso a rage yawan kuɗin ko dan neman albarkar auren, to amman su suka ƙi, dan sunso su bada abinda yafi hakan ma, mune muka ƙiya, tunda ba siyar da ɗiyar tamu zamu yi ba. Allah ya sa ayi damu. Gobe zan koma muma zamu gudanar da shirye_shiryenmu daga ƙauye in Allah yaso." Kuɗin sadakin suka miƙawa Goggo Rakiya. Daga nan muka ɗebi kayan gaisuwar muka tafi. Bani na shigo gidan ba, sai goman dare, dan sai da na koma gidan Mama, mu ka kai akwatunan, sannan na kai su Goggo gida." A falo na samu Bulama yana zaune yana kallo a NBC 2 Maryam na jikinshi tayi bacci. Murmushinshi ya sakarmun, wanda yake faranta mun rai a ko wanne hali na tsinci kaina. Maryam na zare daga jikinshi, na miƙa ma Asiya wacce muka dawo tare ita. Sannan na fuskanci Bulama.
Kana zaune har goma baka je ka kwanta ba Bulama, kana da aiki fa gobe" jajayen idanunnan nashi ya zuba mun, yana wani ƙanƙantar dasu, na riga da nasan me hakan ke nufi. Dan irin wannan kallon mayatar daya saba yi mun kenan a duk lokacin da yake buƙatar shaƙar ɗumina. A daddafe muka ci abinci, kai tsaye muka wuce ɗakinshi, yai mun rumfa. Ni kuma na saki jikina, na kula dashi sosai, kamar yadda na saba, shi kuma ya zame mun tamkar mafaraucin zaki. Goma da rabi na rakashi har ɗakin Yahanasu. Tana zaune a falo ƙwalam, ta jiyo sallamarmu. Da idanu ta bimu, ciki ciki ta amsa sallamar. Ni kuwa sai baki nake washewa.
Amarya sannu da aiki fa, mun haɗaki da aiki. Ga angonki na kawo miki." To kawai tace dani.
Bulama muje inga fasalin ɗakin naka ko? A wajan muka barta da sakakken baki, hawaye tab gurbin idanunta. Ɗakin yayi kyau, har sababbin labulaye da santa kafet ta saka, sai ƙamshin turaren wuta ɗakin yake yi. Ni dai inata dariyar da na tabbatar haushi nake kuma cusa mata. A haka nayi musu sallama na fice.
Hmmm dani kuke zancan, wallahi in dai ina numfashi haka zaki ci gaba da zama a cikin gidannan tamkar poster, ko status shashasha."
Yahanasu:
Wani irin suya ƙirjina yake yi mun. Tunani da damuwa sun damu rayuwata, na rabu da iyayena da ƴan uwana, an kawo ni nan dan inyi zaman aure, amman da dukkan halamu sai dai in zama ƴar aikin gidan kawai. Bana son in yi ƙorafi tun yanzu, idanu nake son in zuba in gani, Baluma Babba dashi za'a haɗa kai a cutar dani da gaske, kokuwa dai mafarki nake yi?" Hawayene suka sakko a kumatuna jikina a mace mus na shige ɗakina. Jakata na jawo na ciro maganin da Hajja Fati ta bani, guda biyu na watsa a bakina nabi da ruwa. Ina kwance ina karatun Alqur'ani, ina hawaye, nadamar shan maganin maye take ya shige ni, kuka na shiga rerawa mai ban tausayi. Bansan ma sanda wani irin nannauyan baccin da bansan anayin irinshi ba ya ɗebeni. Har wani tashi naji inayi sama, ina daga kwancen tsabar nauyin baccine ko meye oho. Bani na farka ba, sai biyar ɗin asuba, shima bawai dan baccin ya isheni bane, a daddafe da bango na shiga toilet, saida nayi wanka sannan naji ƙarfin jikina, kaina kuwa tamkar an sauke mun wani ginginemen dutse mai ɗan karen nauyi, nauyin dake danne da ƙirjina kusan rabi ya washe, sai na ke jin kaso ɗari cikin damowoyin da suka hanani sukuni, kaso talatin da ɗoriya sun kau. Ina idar da salla na yi kitchen da sauri. Doya da miyar ƙyai nayi musu na kumallo, sai tea mai haɗin kayan ƙamshi. Shida da rabi nayi sallama a babban falonsu, ƙanwar Zubaina ce ta leƙo, na bata kayan abincin, har zata koma nace mata.
Dan Allah bari in ɗakko miki kayan wankinsu, ki adana musu" Ban jira ta amsa ba, na juya na ɗakko mata kayan wankin ƙunshi biyu. Sannan na shiga aikin wankin mota, ban dai iyaba amman haka na dinga dirjewa ina watsa ruwa, dana gama wanke na Kofur Zubaina, saina wanke ta Bulama Babba. Duk jikina yayi laushi, a jiƙe sharab na koma ɗaki na saki wani irin kuka mai gunji. A wajan ya fito ya sameni ina rawar sanyi, ina kukan fitar hayyaci. Cak ya tsaya a kaina, bai tambayeni meke damuna ba, baice inyi shiru ba, baice komai ba. Idanunshi sun kuma kaɗawa sunyi jawur, ni banbi ta kanshi ba, kukana naci gaba dayi. Bai bar kaina ba, har saida yaga bakwai da rabi na shirin gotawa, sannan yace mun.
"Zan fita Yahanasu, akwai abunda kike buƙatane?" Kai na girgiza mishi.
Babu, Allah ya tsare gabanka da bayanka, ya kareka daga sharrin masu sharri, adawo lafiya karka manta da addu'ar fita daga gida"
"To Yahanasu nagode, ki share hawayenki ki dena kukannan." Yana gama faɗin haka ya fice a ɓangaren nawa. Haka rayuwar gidan taita tafiya cikin ƙunci da matsi. A haka Bulama Babba ya gama kwanakinshi bakwai a ɗakina. Kullum inayin waya da ƴan gidanmu, ko basu kirani ba ni zan kirasu a gaggaisa, ana washe gari zan soma zuwa aiki Ba Bakura ya kirani, yake cewa dani in shirya da wuri ƙarfe bakwai za'a zo a ɗaukeni. Naji daɗi sosai ko babu komai na rage raɗaɗin zaman gidan, dan ma ina afa magungunan da Hajja Fati ta bani, kuma inajin daɗin baccin sosai, tun ina tunanin sha, har na dena, domun zuchiyata sai sake ingizani take yi, shaiɗan kuma yana ƙara ƙawata mun maganin. Ibada kuwa, na ƙara ƙanƙameta gam, da naji sauyi a jikina, zan ɗauro alwala in shiga salla, ko da yaushe ina kai kukana ga mahaliccina. Iyayena kullum a cikin rufesu nake, da sunan lafiya lau nake zaune tare da Bulama Babba. Washe gari, ranar ya kasance a ɗakina Bulama Babba yake, bayan na gama duk ayyukan da nasan nike yinsu, yau tun bakwai na sallami kowa, cikin shiri na fito tsab, a kan kujera na samu Bulama Babba yana ɗaure igiyar takalminshi. A gabanshi na durƙusa nace.
Bulama Babba" Ɗagowa yayi ya zuba mun jajayen idanunshi, nayi sauri na sauke kaina.
"Lafiya Yahanasu menene?"
Dama yau zan soma zuwa aikine, shine nace bari in faɗa maka. Hajiya zata zo ta ɗauke ni mu tafi" jim yayi, kana yace.
"Wacece kuma Hajiya?" Nace.
Matar Alhaji Munka'ilu aminin Ba Bakura"
"Oh su suke aurenki kenan ko?" Nace.
A'a kayi haƙuri"
"Dalla rufa mun baki, to da izinin wa zaki soma zuwa aiki?" Kai tsaye nace.
Da izinin Ba Bakura zan soma zuwa aikin, tunda shi ya ajjiyeni, kuma dokar gidanmu itace duk wanda zai auri matan gidanmu, akwai sharaɗin zasu ci gaba da aiki, kuma kasani." Iyakar abunda na faɗa kenan. Bulama Babba ya dinga zazzaga mun ruwan jaraba, yana caccakama iyayena maganganu kaifafa, akan basu bani tarbiyya ba ashe. Kuka kawai na saki, ni bansan dame akeso inji ba, da damuwar da take damuna, ko da masifar da Bulama Babba ya tsiro da'ita kwana biyunnan.
"Babu inda zaki je, inga ubanda zai tilastamun akan saina barki kinyi aiki. Inace a garin zuwa aikinne kike zuwa yawon iskancinki, har kikai ma iyayenmu ƙaryar an miki fyaɗe ko? Sabida kin saba da bin maza shine kike son ki koma ruwa ko? To babu wannan ƙofar a gidannan. Tunda har suka bani ke bana so, bazaki taɓa jin daɗina ba, na faɗa miki." A wajen ya barni a durƙushe ina kuka kamar zan haɗiye zuchiyata. Ina jiyo muryar Zubaina tana tambayarshi ba'asi. Fyaɗen da akaimun ya dawo ɗanye a zuchiyata, dama mikin kullum a cikin nuƙurƙusata yake. Duk irin tarbiyyar da iyayenmu suka tsaya akanmu suka bamu. Yau ni Bulama Babba yake kira da ƴar iska, mara tarbiyya kuma, har Bulama Babba zai iya buɗe baki ya aibanta Ba Modu a gabana? Ai halin shi ya kula dashi ya bashi tarbiyya. Sallamar Hajiya Ramlatu ne ya katsemun kukan da nake, amman na kasa shanye yanayin da nake ciki, dole ta kutso kanta ta sameni a zube a ƙasa fuskata sharkab da hawaye duk ta kumbura.
"Yahanasu lafiya kike rusa irin wannan kukan? Na haɗu da bulama shima na ganshi a cikin fishi sosai, ba dai har kun soma samun saɓani ba, daga auren naku ba?" Hawayena na shasshare nayi ƙasa da kai nace.
Sannu da zuwa Hajiya, ina kwana?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
"Lafiya lau Yahanasu, ki taso dai yanzu mu kama hanya, tunda naga a shirye kike tsab"
Kiyi haƙuri Hajiya, na gode da ƙoƙarinki a gareni. Amman Bulama Babba yace bazanyi aiki ba, abunda ya ɓata mishi rai kenan" Dubana tayi cike da maɗaukakin mamaki tace.
"Ya baza kiyi aiki yake ba? Naga yanzu ya fice wajan aiki, matarshi na mara mishi baya da kayanta na ƴan doka zasu tafi aiki, kuma tunda nasan mahaifiyarshi ma'aikaciya ce, har sai da tayi ritaya sannan ta zauna a gida. Akanme zaice ke bazakiyi aiki ba, alhalin yasan ku ƴan boko ne, kuma kab ƴan gidanku babu mai zaman kawai. Ai wannan in dai Bulama Babba yayi haka baiso zaman lafiyar iyayenshi ba, kuma bai ɗakko hanyar haɗin kan gidan nashi ba ma. Ai wannan zalunci ne Babba, ina zuwa." Fita tayi, ta ɗanyi waya na mintoci, sai gata ta dawo ciki.
"Zan tafi Yahanasu, zuwa gobe komai zai daidaita zanzo in ɗaukeki mu tafi aikin, ki dena kukan ya'isa haka" Har bakin motar ta na rakata ta ja ta tafi. Ni kuma na shiga aikace_aikacen cikin gida kamar yadda na saba. Wankin da nayi yau bana wasa bane, nasha wahala sosai. Na rame matuƙa, hakan yasa na ɗan washe kaɗan, ni kaɗai nasan irin zafi da raɗaɗin dake gasa ruhina. Misalin ƙarfe biyun rana na shiga kasuwa nayo cefane na, nazo na ɗaura miyar dare. Na fita tsakar gida zan kwaso shanya, dan garin hadarine sosai ya sauko, ruwa ne ma ke shirin kecewa. Mota na gani ta kaya, cike da sababbin kayan ɗaki, suna saukewa ƙasa, wasu na fito da tsofaffin na ciki, wanda suma sababbinne dan babu abunda ya same su. Sai lokacin na lura an sake ma ma ɓarayin sabon fenti mai kashe idanu dan ƙyalli. Kaina na girgiza na kwashe kayan na tafi ɗaki da abuna. Sai wajajen biyar na yamma na gama girkin dare. Tuwon alkama miyar ganye nayi da kayan ciki da stock fish. Ruwane ya ɓalle kamar da bakin ƙwarya. Akaita tabka ruwannan, ina zaune ina ribatar lokutana da tulawar Qur'ani mai girma. Har magriba ruwannan bai tsaya ba, amman ya ɗan dakata kaɗan.
Ba Bakura:
Tun ƙarfe huɗun yamma suke tsaye a bakin get ɗin gidan Bulama Babba, amman mai gadi ya hanasu shiga, duk da bayanin da Dala yayi mishi na cewar, mahaifan mai gidanne a cikin motar. Haƙuri ya basu kan cewar su kira mai gidan a waya in ya bada damar su shiga, sai ya buɗe musu. In bai ba da damar shigan ba sai suyi haƙuri. Ba Bakura ya kira kiran duniya Bulama Babba bai ɗauka ba. Ba Modu ma ya kikkira bai ɗaga ba. Hajja gana itama ta kira shiru. Gabaƙi ɗaya ran kowa ya dagule da irin halayyar ko in kula da Bulama Babba yake yi musu. Dab magriba Bulama Babba ya dawo wajan aiki yaga motar Ba Bakura a ƙofar gidan. Ji yayi da yasan zai dawo ya samu motar a wajan dama bai dawo yau ba baki ɗaya. Da gudu mai gadi ya buɗe mishi get ya shige. Mai gadi yabi bayanshi a cikin lema da sauri.
Bulama Babba:
Jim nayi a cikin motar, na kasa motsowa sam, dan nasan ba lafiya bane ya kawo su gidan ba, kuma nasan zuwan nasu ba ɗa mai ido zai haifar ba. Ni kuma duk abinda zai ɓata ran Zubaina bana fatan ya raɓeni. Amman a wannan karon zan ja musu layi akan irin wannan zuwan na bagtatan da suke yi mun, suyi zamansu a inda Allah ya ajjiyesu kawai. Buɗe murfin motar nayi, mai gadi ya ƙaraso.
"Mai gida, waɗancan bayin Allahn sun jima sosai a tsaye a ƙofar gida, tun la'asar suke jiranka kuma sunce daga can Damaturu suke. Ɗan tsaki naja a hankali nace.
Kace su shigo kaji" Da sauri ya koma Motar Zubaina ce ta shigo gidan a guje, sannan motar su Ba Bakura ta shigo itama. A hankali na buɗe lema na fito ina tsaye a kusa da motata, Zubaina tayi wuf ta fito. Sannan su Ba Bakura suka fito a cikin Motar. Kallonsu na shiga yi, inajin wani abu na motsa mun zuchiyata, Ni kaina bansan menene wannan abun ba, amman har ƙasan zuchiyata naji daɗin ganinsu, idanuwa da zuchiya suna kewarsu sosai. Sai dai kallo ɗaya zaka yi musu kasan a cikin ɓacin rai sosai suke.
Sannunku da zuwa, kune a tafe haka? Irin wannan ai saiku sanar kafin kuzo, in kuka zo bananan kuma fa?" A ɗan daƙile na furta kalmar. Ba Bakura ya ƙura mun jajayen idanunshi, wanda suka kere nawa runewa, fuskarnan tashi murtuk yace.
"Kayi haƙuri da zuwan bazata da mu kayi maka, na mance bamu da wannan ikon ko? Hakan ba za ta sake faruwa ba" Baki na buɗe zanyi magana amman Ba Modu yayi saurin ɗaga mun hannayenshi, ɗan harararshi nayi ƙasa ƙasa, dan mugun haushinshi nake ji shi fiye da kowa. Hajja gana hawaye naga tana sharewa ko na miye oho. Baki na taɓe dan nasan daman zuwansu ba alkhairi bane sam.
"Nuna mana ɗakin Yahanasu, in da hali a raka mu. Mahaifinka baya son sanyi, ruwa na dukanshi" Cewar Hajja gana kenan. Juyawa nayi, suka bi bayana, ruwa sai dukansu yake yi, ni kuma ina cikin laima ina tafe kamar agwagwa tsabar taƙama. A bakin ƙofar ɗakin na tsaya nace
Ga ɗakinnan" Ina faɗa nayi wucewata na barsu a tsaye a wajan suna doka sallama. A tsaye a tsakar gida inda na bar Zubaina nan na sameta, tana ganina ta saki ajjiyar zuchiya mai ƙarfi. Wucewa muka yi. Daga ni har ita a falo muka zube.
"Bulama amman ya kamata ka sanar da su Ba Bakura su dena irin wannan tafiya ba sanarwa. Su yi kiran waya mana kafin su zo, gudun kar su zo bama nan." Tagumi tayi tana sharar hawayen da yasa duk na rikirkice da ganinsu. Nan na shiga tambayarta ba'asin zubar hawayenta.
"Abban Maryam na rasa abunda nayi ma iyayenka da suka ƙi jinina. Ka duba fa, ko sannu da zuwan da nayi musu basu amsa ba. Cikin su babu wanda ya kalleni, nasan sai sun gama ci mun mutunci ma kafin su tafi" Kuka ta kuma raushewa dashi. Tsam na matseta a ƙirjina na shiga aikin lallashinta, santa da ƙaunarta na huɗa tsokokin jikina."
Babu mai wulaƙanta mun mata in barshi. Ki dena kuka bazan bari sam su faɗi mummuna a kanki ba. Kuma zan faɗa musu kar su sake zuwa har sai sun kirani na ɗaga tukunna. Ai naga kiran nasu ban ɗaga bane kawai. Ashe a lokacin suna ƙofar gidan, dan mai gadi yace