MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   50 / 67

147K to 150K   out of 198.3K words

tazo mana da sauƙi ai. Ni dai hankalina bai kwanta da batun ɗaukar Yahanasu daga asibiti zuwa Rehabilitation center ba ( gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye shaye na gargajiya) dan akwai wani labarin daya taɓa faruwa a ɗaya daga cikin ire _ iren gidajennan labarin mummunane. Ana azabtar da mazauna irin wannan gidan azaba mai tsananin gaske. Duk da nasan ba duka aka zama ɗaya ba. Muryar Ya Bagulaji na jiyo tana faɗin.
"Kayi shiru baka ce komai ba Bulama Babba, baka ji abunda Mamanka tace bane? Mama Gana nan ta sauke mun kwandon jarabar dana rasa dame ma zanji.
Naji Ya Bagulaji ina dai tauna zancenne a raina kawai." Buɗar bakin Mama Gana tace.
"Dake ba Bakura bane ya yanke hukuncin ai dole ya tsaya tattaunawa. Da uwarka Hajja Gana wannan koɗaɗɗiyarce ke magana ai da saika bata amsa kafin ka tauna duk abinda kake son ka tauna." Haƙuri na basu dukkansu nace.
Shikenan zanje in samu Ahmad muyi magana kafin goben. Sabida dama a satinnan nake son shi Ahmad ɗin ince mishi ya koma Yobe ɗaya daga cikin gidajena ya zauna da iyalanshi, kafin in gyara mana gidan da zamu zauna. Wannan sha'anin jikin na Yahanasu ne yasa komai ma ya dakata. Amman ba damuwa Allah ya kaimu goben." Ban jima a asibitin ba na fito. Neman Ahmad nayi a waya muka haɗu dashi, a gefen hanya ya ajjiye keken nashi a cikin keken muka zauna. Halin da ake ciki kab na zaiyane mishi, shima yaji girman abun.
Ni Ahmad hankalina bai kwanta da rihab ɗin gargajiya bane kawai, duba da irin tarin matsalolin da ake samu. Amman dole inbi umarnin Ba Modu. Ka taya ni da adda'a Ahmad. Sai batun komawarmu Yobe kuma. Ina ganin ko zuwa jibi ai sai ku wuce ko? Kasan gidan, nasa an tashi ƴan hayan ɗakin da zaku zauna a ciki. 3bedroom flat ne. Ku zauna a ciki kafin in gyare mana ɗayan gidan sai mu haɗu duka muci gaba da zamanmu dan sake haɓaka zumuncinmu. Wannan kamfanin pure water ɗinnan kasan dole sai ka taimakamun da aiki, tunda kaga babbane kamfanin. Ita kanta Hajara ba zata rasa aikin da za'a bata ba, a ƙalla itama zata taimakama iyayenta. Na tura maka nera dubu ɗari da hamsin a account ɗinka naka ne ku ɗanyi siyayyar kayan ɗaki. Wannan million ɗayan kuma kuɗin gidan Yahanasunane dana siyar na tura cikin account ɗinka ka Ajjiye mun." Mun daɗe muna tattaunawa kafin daga bisani muka tafi gidan tare. Kekunan da muke tuƙawa na biya mana ragowar balance ɗin daya rage mu game lone ɗinmu. Munyi da Ahmad zai tura da kekunan Damaturu aci gaba da kabu_ kabu dasu. Washe gari nayi ma mazan gidan sallama na nufi asibiti. Su Bawa Ahmad zai tafi dasu Yobe. Ina zuwa asibitin na tarar da su Mama Gana har sun gama haɗa kayanmu. Takaddar sallama suka miƙamun naje nayi duk abunda ya dace. Dr Halima har gaban motarmu ta rakomu tana ɗaga mana hannu. A hankali nake tuƙin motar ina kallon Yahanasuna ta mudubi, tayi shiru tana kallon gefen taga. A haka batai kama da masu taɓin hankali ba sam. Sai kayi mata magana ta kasa baka amsa ta sako shirme ne mutum zai fahimta. Ko kuma in abun ya motsa ta soma fiffisga tana ihun a bata laka mis in ba haka ba mutuwa zata yi. Ina jin su Mama Gana suna ta hirarsu da Ya Bagulaji. Ni dai hankalina yana wajan tuƙi, zuchiyata kuma tana wajan Yahanasuna. Haɗa idanu muka yi ta mudubi. Murmushin soyayya na sakar mata mai taushi. Abun mamaki itama murmushin ta sakar mun tana mai kafe ni da idanunta. Can kuma sai ta soma zubar hawaye. Haka dama Yahanasu take a koda yaushe tunda wannan lalurar ta same ta. Tafiyar awa hudu ne ya kaimu garin na daura can wani ƙauye, tambayar gidan malam Rilwanu mu ka yi aka nuna mana. A ƙofar gidan muka ga motar su Ba Modu halamar sun iso suma kenan. Malam Rilwanu ne yai mana iso har cikin gidan nashi. Yana gaba muna biye dashi a baya. Gaisawa su Mama Gana suka tsaya yi da matan gidan, ni kuma ya jani zuwa cikin turakarshi inda anan na tarar da Ba Modu da Ba'a Kaka da Ya Innana sai Fanna. Gaggaisawa muka shiga yi, a cikin haka su Mama Gana suma suka shigo a bisa jagorancin wata dattijuwar farar mace.
"Nazifa a kawo musu ruwa da abinci, baƙine daga Kano wadannan kuma daga Damaturu, marar lafiya suma suka kawo." Wannan dattijuwar tace.
"Marabanku lale da zuwa. Me jiki kuma Allah ya bata lafiya, jiya ma wasu bayin Allah suka kawo ɗansu daga Kaduna can hayin rigasa." Tafiya tayi bata jima ba sai gata da ruwa cikin kofunan silver. Da dambun rama cikin wata ƙaramar kwalla. Godiya Ya Innana tayi mata, sannan ta dube mu tace.
"To bismillah muci abinci ko, sai mu sa haramar komawa." Ni dai loma biyu nayi na ajjiye cokalina, cike zuchiyata take tab da tsantsar alhinin rashin Yahanasuna. Ita nake kallo, sai kama kanta take yi, tana wata iriyar zabura. Suna kammala cin abincin malam Rilwanu yace.
"Sai muje can bayan gida in nuna muku inda muke ajjiye marasa lafiyanmu ɓangaren mata. Da kuma nasarorin da muka samu na warakar wasu daga cikin waɗanda aka kawosu suna hauka tuburan. Duk da naga taku marar lafiyarma tana jin jiki, ƙila ta jima tana shan miyagun ƙwayoyi masu cutar da ƙwaƙwalwa." Yana gaba muna bin bayanshi. Bamu fita waje ba, ta cikin gidan nashi muka shiga wata ƙofar, munyi tafiyar kimanin minti goma sha biyar kafin muka iso wata ƙofar. Muna shige wannan ƙofar muka soma ganin guggun mata a zaune a wata baranda ana koyar dasu darasin lissafi wato Maths. Matane manya da matasa. Ɗakunan da suke kwana ya shiga nuna mana ɗakuna, ko wanne ɗaki mutum shida ke rayuwa a ciki, katifar yayi ce ƙanƙana a shisshinfiɗe a cikin ɗakunan ko zanin gado babu balle matashi. Babu ƙazanta dai a wajan amman kuma babu wata tsabda ta azo a gani. Wasu ɗaure suke a mari, yayin da wasu suke a sake. Kana ganin wasu da halamar haukar sosai ta bayyana a jikinsu, yayin da wasu kuma tabarallah kamar irin waɗanda muka samu a can baya suna karatu. Wani godon ɗaki malam Rilwanu yasa wata malama Fahiƙa ta shigar damu. Keken ɗinki muka gani, da keken saƙar setin kayan sanyi na jarirai. Sai kuma katakwaye irin dai na haɗa gado kamar kafinta dai zance. Shi kuma wannan ɗakin na koyon sana'a ne, wanda ya zama wajibi akan ko wanne marar lafiya. Amman da halamar kamar ana ɗan azabtar dasu, dan na ga manyan dorinaye. Kuma duk ɗakin da muka leƙa sai inga ƴan ɗakin sun zabura da zaran sun ga malam Rilwanu. Daga ɗakin koyon sana'a kuma ana nuna mana wajan da suke motsa jikinsu atisaye, sai ɗakin shan maganin bature, inda wani matashi yake zaune a gaban teburi shi da wata dattijuwa. Gaggaisawa mu kayi, yai mana ɗan bayani a taƙaice na irin gudunmawar da suke basu ta fannin ilimin likitanci, su ɗin likitocin ƙwaƙwalwa ne. Duk wannan zagayen da muke yi Yahanasu tana riƙe gam a hannuna, sai matse mun hannu take yi tana shigemun. Da muka zo rabuwane ta fashe da kukan da sai data raunata zuchiyoyinmu dukkanmu. Matan suma kuka suke yi, tuni idanuna suka sake kaɗawa su kai jawur dasu.
"Dan Allah karka barni anan wajan. Nifa lafiyata ƙalau. Kar ku barni su cutar dani." Sake rushewa da kuka tayi ta faɗa jikina tana kukan fitar rai. Da sauri na cireta a jikina sabida su Ba Modu. Tsugunnawa nayi a ƙasa ina mata magana ƙasa_ƙasa.
Zan dinga zuwa dubaki kinji? Ki dinga shan maganinki, sannan duk abunda akace miki kiyi, kar kiyi musu gaddama kiyi kinji? Zan dinga zuwa. Da dabara na share hawayen daya zubo kan kumatuna. Yahanasu ta rungume Mama Gana tsam ta dinga kuka. Da ƙyar na ɓanɓareta a jikin Mama Gana na damƙata ga malama Fahiƙa nace.
Amanarta tana hannunki, ki kular mun da'ita dan Allah." Malama Fahiƙa tace.
"Amanoninsu duk a hannuna suke. In sha Allah bayan wata ɗaya in kuka kawo mata ziyara zaku yi farin ciki a bisa sauyin da zaku gani daga gareta. Allah ya basu lafiya. Dan Allah kubi doka. Talatin ga ƙarshen ko wanne wata ne yake zama ranar zuwa ziyartarsu, in ba dai kunji kiran gaggawa daga garemu ba kar kuzo." Sallama mu ka yi musu muka fito tare da malam Rilwanu. A bakin motacinmu muka tsaya. Bayana na juya ina share hawaye dake zubowa a idanuna.
"To Malam Modu nagode sosai. Zuwa nan da wata uku ina tunanin kuɗin hidima da'ita zai iya ƙarewa, in ma ya wuce wata ukun duk zan sanar muku. Nagode da kayan abinci da aka sauke mana, ku sauka lafiya, sai ƙarshen wata in Allah ya kaimu cikin rayayyu.' Sallama su kai mishi muka shiga mota. A wannan karon bani da kuzarin da zan iya tuƙi. Zama nayi a gefen mai zaman banza, Dala ne ya riƙe motar. Mama Gana da Ya Bagulaji suna baya. Ba'a Kaka kuma ya tuƙa Ba Modu da Ya Innana. A jere muke tafiya, a masallacin daura mu kai sallar azahar kafin muka ɗauki hanya. Sai magriba muka isa Damaturu, kowa jikinshi a mace mus. Ɗakin Dala na samartaka na shiga na keɓe kaina, bayan na zaga iyayen nawa mun gaisa na ƙara musu ta'aziyyar Ba Bakura. A ranar baccin kirki ban samu damar yi ba. A sallaya na raba dare ina roƙon Allah ya bama Yahanasu lafiya. Haka dai al'amura su kai ta motsawa. Ahmad sun shiga Yobe sai da ya ajjiye Hajara da yaran acan sannan ya tawo damaturu. Kwana biyu mu ka yi a Damaturu muka koma Yobe. Gadan_gadan na shiga gyaran gidan da zamu zauna, bayan ƴan hayan gidan duk sun tashi. Fasali me kyau nasa akema gidan. Duk wannan aikin ƙarfin hali kawai nake yi, babu nutsuwa a tare dani. Na rame sosai, ko da yaushe inna je Damaturu sai Ba Modu yayi mun faɗa tare da nasiha. Cikin kwana ashirin da biyu da Yahanasu tayi a Daura, kullum na kwanta sai nayi mafarkinta. Ranar juma'a ya kama talatin ga wata, a daren da washe gari zamu tafi Daura, bacci ɓarawone ya ɗaukeni. Tun asuba kuwa na shirya tsab harda yaran da Ahmad muka nufi Damaturu. Acan ma mun same su a shirye tsab. Hajja ta bada cincin da alkaki tace a kaima Yahanasun. Ya Innana kuma tayi mana lafiyayyen buski da miyar kuka da taji kaza. Sallama mu ka yi musu muka kama hanya. Wannan karon da su Yabulu, da su Gunsum muka tafi, sai Fanda. Mun isa Daura dab sallar juma'a. Sai da muka gabatar da sallar juma'a sannan muka ƙarasa ƙauyansu malam Rilwanu. Motoci da dama muka riske a ƙofar gidan Malam Rilwanu. Da halama motocin iyaye masu zuwa ziyartar yaransu ne. Kai na jinjina, ina biye da Ba Modu a baya har zuwa cikin gidan farfaɗo da rayuwar masu shaye shayen.


MRS BUKHARI CE[15/08, 11:55 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)


GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
43
GHANA














ZUBAINA:
Yau gidan mun tashi da hidimar abincin masu kawo Amaryar Alh Liti daga sokoton Shehu. Kaji bakwai ya kawo, da shinkafa forin kwana biyu, ruwan roba katon hudu da lemun gora katon biyu. Tun asuba da mu ka yi sallah muka duƙufa aikin. Hannuna har zuwa wannan lokacin bai warke ba, bayan sake ɗaurani da akayi a asibiti, sai da aka sake yi mun ɗaurin gargajiya dan dana koma asibitin cewa su ka yi hannun bai haɗeba sai an sake karyawa an dorani. Gashi ba kuɗi a hannuna, na roƙi Alh Liti roƙon duniya ya taimaka mun, amman yace mun bashi da kuɗi. Hajiya Kubra ce ta sake raka ni gidan wani mai ɗori acan wata anguwa mai nisan gaske. Takalmi da jakata wanda naci bikina dashi, shi na bayar a matsayin kuɗin gyaran karayan. Ina cikin jinyar hannuna na shiga laulayin ciki, gashi wannan karon cikin ba ƙaramin jigatani yake yi ba. Duk wanda ya sanni a lokacin da nake kofur Zubaina, ko mrs Bulama sai ya sha mamaki, domun ba ƙaramin lalacewa nayi ba, nayi baƙi na wani ƙanjame kamar ba ni ba. Mama kuwa kullum a cikin yi mata filashin nake amman bata kirana. Asiya da Nafisa suna kirana jefi_jefi mu gaggaisai. Mabaruka kuwa tana ƙasar ingila ita da mijinta ta rakashi wani aiki. Amman tayi mun alƙawarin zata zo ta ganni kafin su koma Najeriya. Kullum a cikin mafarkin gidana na da nake da yarana da Bulamana, ina da number Bulama a kaina, amman kona danna da zummar in mishi filashin in ya kira ince ya bani yara mu gaisa, dan gudun karsu mance wacece uwarsu, sai in fasa kiran sabida kunyar jin muryar Bulama nake yi, tare da taraddadin in Alh Liti yaga na kira wayar Bulama bansan wanne hukunci zai mun ba."
"Yauwa masha Allah, Zubaina komai ya kammala, Nabila sai wanka kuma, mu tsimayi jiran manyan baƙi. Cewar Hajiya Kubra kenan, tana riƙe da tsintsiyar data gama share wajan girkin tsab. Rashida wacce take gaban kular da aka zuba kaji tace.
"Wannan rayuwa ta ƙaddara, Baba bashi da aikin daya wuci Aure da saki sai kace mai bakin uwa, ko kuma wanda akaima asiri. Taya ma mazajenmu zasu riƙemu da daraja? Ai ko alhakin matan da yake aurowa ya gana musu azaba, bazai sa mu mazajenmu su tarairayemu ba." Tsaki ta dinga jerawa. Mu dai babu wanda ta tanka mata, a cikinmu ko wacce ka kalla a cikin ƙunci take da yawan tunani. Wanka mu ka yo ko wacce ta shirya tsab dan sauraran isowar baƙi. Ai kuwa dab magriba sai ga Alh Liti ya shigo ɓarayinmu faram _ faram da farar shadda ɗinkin malum_ malum, hula a karkace, sai kwaɗa mana kira yake na rashin daraja. Ina kwance na jiyo kiran da yake yi mana, babu shiri na miƙe a zabure dan ba ƙaramin tsoronshi ya ɗarsamun a zuchiyata ba. Har bana ƙaunar kwanana ya zagayo dan ina gurzuwa kamar babban bargo. Gashi sai ya gama yai ta mun mita wai shi bai gamsu ba, babu ni'ima sam a tare dani, ai aurena asanar kuɗine, babu irin maganganun da baya yaɓamun. A tare muka firfito ko wacce kanta a kasa.
"Dan bura'ubanci ina kiranku kunyi kunnen uwar shegu dani, kunfi son inyi rashin daraja baƙi su jiyoni ne ko yaya? Ai wannan iskancine da daƙiƙanci irinna mata." Kallonshi nayi kalmar daƙiƙanci da iskanci daya faɗa ya huda zuchiyata zafin. A zuchiyata nace.
Ai uwarka ma ƴar iska daƙiƙiyace tunda macece." A zahiri kuma jikina har rawa yake yi wajan ba Alh Liti haƙuri, kamar ingizashi muke yi, haka ya tusamu gaba yai ta ɗebe mana albarka, inda sabo mun riga da mun saba. Wata iriyar rayuwa Alh Liti yake gudanarwa ta rashin jinƙai da tunani.
"Sai ku kwashi kayan abincin ku kai ɓangarena wajan baƙi. Ban yarda kowa ya gabatar da kanshi ga dangin Amarya ba. Ni da kaina zan gabatar daku a wajenta, tunda dukanku zamana kuke yi. Ƴan iska a haka kamar na Allah. Cikinku ba wacce bata cuceni ba lokacin muna nema, kun ɗauka irin santolon namijinnanne, wasu ma har romiyo suke kirana a waya in na kira wayarsu." Ya gama buyaginshi ya wuce buuu kamar kububuwa. Numfashi naja tare da share hawayen idanuna, kaina na jinjina kawai. Na duƙa na ɗauki babbar kular kajin, su Hajiya Kubra da Nabila, da Rashida suka ɗebo ragowar kayan muka bi bayan Alh Liti zuwa ɓarayinshi. A ɗakin da aka saukeni a lokacin da aka kawoni a nan ya ajjiye Amaryar tashi da danginta. Ko da muka shiga, dangin Amarya sai wani gani _ gani suke yi mana, sun ganmu hajaran majaran. A raina nace.
Kwana nawa ne maye yayi Amarya zai lashe abunshi." Da ƙyar suke amsa gaisuwarmu, Amaryar ma bamu samu ganinta ba wai tana sama tare da Alh Liti. Wata dattijuwace tace.
"Ammm nace dan Allah a cikinku wacece uwar gidan Alh Litin?" Murmushin da Hajiya Kubra ya zame mata jiki a wannan karon ma shi tayi tace.
"Nice uwar gidan nashi, sunana Hajiya Kubra" Nan kallo ya dawo wajenta, amman babu wanda dai yace wani abu. Muka jawo tsumman rayuwarmu muka dawo ɗakunanmu. A daren ranar nayi kukan marar iyaka, kukan da bansan me yasa nake yinshi ba nima. Haka naita tubka da warwara da ƙyar bacci ya ɗebeni. Da sasafe na fito na haɗa itacen dama kokko, yau nice da aiki, ga ciwon hannu ga lallauyin karamin ciki, amman babu mai taimakamun in ranar aikina ta zagayo duk abunda yake a wuyana saina yi shi. Babu babban tashin hankali irin dafa dokunu/ kenke. Wani irin tuwone mai azabar wuyar aiki. Da farko garin masara ake jiƙawa a ruwa ya kwana biyu a jiƙe, sai a juye ƙullin a tukunya rabi a barshi yaita dahuwa, in ya dahu sai a juye a ƙaton bahun, a sake zuba ɗanyen jiƙakken ƙullun masarannan a cikin dafaffen aita gaurayawa har sai ya haɗa jikinshi, sai a samu ɓawon masara a dinga zuba wannan tuwon a cikin ɓawon ana nannaɗewa, Ana mayarwa cikin tukunya akan wuta, bayan an gama za'a zuba ruwa a tukunyar abar tuwonnan yaita dahuwa har na tsawon minti arba'in. ( Da soyayyan kifi ake cin tuwon a ƙasar ghana, da ƴar miyar jajjagen attahuru da albasa) Amman a gidan Alh Liti kayukan kifi ake siyowa na ɗari biyar a watsa a jajjagen, kowa ya dinga lasawa. Hajiya Kubra ce ta fito tana salati tsakar gidan, har tana hawaye. Da ƙyar na miƙe bayana a kantare na dubeta nace.
Lafiya Hajiya

50 / 67