MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   25 / 67

72K to 75K   out of 198.3K words

kuma nace
Amman me yasa zata ɗau fishi har ta tsallake yaranta ta tafi, alhalin ba korarta yayi ba?" Hajara tace.
"Ke meye naki ni da nayi tunanin zaki yi murna, wake ƙaunar kishiya in ba ke ba. Ko da yake ta asiriceku ne wallahi tallahi shi yasa ki kai ta mata bauta, da asirin ya karye ba gashi kin botsare ba. Harara na sakar mata naja bakina nayi gum.
Hajara ni wani irin ƙauri nake ji, ko kin ɗaura girkine yake ƙonewa, ga hayaƙi yana shigowa daga tsakar gida. Hajara tace.
"Wallahi ko ɗaya babu abinda na ɗaura, ina tunanin ko taya ake ƙonawa acikin layin, tun safe nake jin wannan ƙaurin. Kafin ta ida magana sai muka ji dam wani abu yayi ƙara. Muka soma jiyo ihun mata da yara suna ambaton gobara_ gobara. A zabure muka miƙe, duk da ina cikin jiri a guje muka fito tare da Hajara. Ashe a cikin gidanmu ne gobarar, a ɗakin Zubaina, wuta ce take ci ba ba ba ba, gashi harya kama kitchen ya kama zaure, babu wata hanyar fita. Sai ambaton Allah nake yi da ƙarfi, hawaye na fita a idanuna. Iyayena kawai nake tunowa, shikenan mun rabu kenan, dan izuwa yanzu wutar harta kama ɗakunan gidan kab, da mugun gudu na shiga cikin ɗakin na zari jakata wacce takadduna suke ciki, hankalina in yayi dubu to ya tashi. Sai watso ruwa mata da matasa suke yi ta katanga, amman a banza man kare, gashi ƙofar gidan da sakata. Mata sai ihu da kururuwa suke yi a waje, hayaƙi ya gama turniƙe mu sai tari muke yi. Da naga muna shirin halaka, ba shiri nayi kukan kura naja hannun Hajara muka shiga zaure. Tururin wuta da zafin hayaƙi duk ya kiɗimamu, numfashinmu na gab da ɗaukewa muka ji an ɓalle ƙofar, matasa sun fincikomu waje. Shanshar na faɗi a wajan, hayaƙi na fita ta hanci ta bakina. Haka ma Hajara. Gidan maƙota mata suka kaimu duk aka kewayemu ana kuka, wuta bata taɓa mu ba sam, amman kuma sai tari muke yi, muna fitar da kaki baƙi ƙirin. Wata tsohuwa tace.
"Ga manja ku shanye, tun wuri ku samu kuyi aman wannan hayaƙin tun kafin ya halaka ku. An auna arziki tunda dai kun fito da rai, kuma wuta bata taɓa ku ba." Wallahi haka matannan suka dinga ɗura mana manja, mu ka dinga kwara amai baƙi ƙirin, muryoyinmu lokaci guda suka dashe dan maƙorona babu abinda yake yi sai zafi tamkar zai tsatstsage.
Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun shi nake ta nanatawa ina hawaye. Wani ɗaki aka shiga damu, sai zuwa jaje maƙota suke ta faman yi. Anci nasarar kashe gobarar amman komai ya ƙone ƙurmus, har ya fara cin gidan maƙota. Hajara sai sambatu take yi.
"Oh ni Hajara Allah na tuba. Shi yasa akace in zaka auri mutum ka aureshi domin Allah, ba dan abinda yake dashi ba. Yanzu jiba ƴan tsunmokaran da muke gadara dasu, da ma komai duk sun ƙone. Muƙami babba da Abban Anisa yake riƙe dashi, motocinshi biyu. Sutura kuwa yasa wancan, ya cire wannan, ya kyautar da wannan. Ni kaina wanne irin facaka ce banyi da dukiya ba. Kasuwanci nake yi, ina juya sama da million amman wata la'ananniya ta damfareni, komai namu ya ƙare sai ci baya da muke sake yi. Allah in wani laifin mu kai ma ka yafe mana. Wallahi ko a iya haka abin ya tsaya munga aya." Ita tana da bakin surutai ma, ni in banda addu'a babu abinda nake yi. Kwayoyi kawai nake burin gani na afa ko zanji sauƙin zugi da tashin hankalin da nake ciki. Ji nake yi tamkar in tsala ihu sabida hayaniyar masu zuwa jajanta mana, jinta nake yi a cikin ƙwaƙwalwata, tamkar zan zare haka nake ji. Wannan tsohuwar ce ta sake leƙowa ɗakin da muke tace damu.
"An sa samarin gidan, sun kira mazajenku a waya, anyi musu bayani. Suna ma hanyar zuwa. Allah yasa da abinda gobararnan ta tare muku. Allah ya mayar muku da arziki.
Ameen Baba mun gode" Shine abinda na iya cewa.
"Ba komai, hakkin maƙwabtakan kenan. Kafin ɗan uwanka yazo kan ka, koma menene, maƙocinka shi zai soma zuwa. Shi yasa akeson a zauna da kowa lafiya. Cikin ku tsakaninmu daku girmamawa ce. Hajara kuwa nanne gidan hirarta. Yahanasu ce ma dai, tun lokacin da kuka shigo kuna sababbin dawowa layin, bata kuma shigowa ba. Abokiyar zamanki dama ita bata zo ba. Ni ina take ne ma tana wajan aiki ko? Oh kome ta bari a kunne a ɗakin sai Allah, daga ɗakinta wutar ta tashi Wuta ta lashe muku komai na tausaya gaya." Carab Hajara tace.
"Ai tayi yaji. Bayan wannan hatsaniya data afku jiya Baba, bata kwana a gidan ba, ƙila wani abun ta bari a kunne kam" Kallon Hajara nayi ina mamakin gulma da munafurcinta, a cikin wannan tashin hankalin da muke ma sai tayi halin nata. Baba tace.
"Kai ai wannan yarinya, jiya wuni nayi ina mamakinta, cin mutuncin miji haka ai babu kyau. Oh yanzu sai dai taji mummunan labari maras daɗin ji" Ni dai bana iya cewa komai. Hanya nake nema in fita ko bashi ne in ciyo na maganin mura in sha, tun kafin kaina ya hargitse asirina ya tonu. Gashi wayata na barota a can cikin gidan, inason inji muryar su Ba Bakura ko zanji dama dama, in sanar dasu halin iftila'in da kuma muka kuma faɗawa."






Zubaina:
Washe gari:
Cikin ƙunci da zafin zuchiya na kwana. Bansan dalili ba nima. Yusuf ma haka ya raba dare yana kuka, nonon ma yaƙi karɓa, Nafisa sai faman tsaki take ja mun, mun hanata bacci. Gashi babu wuta haka mu ka ƙwan ba wuta, wayata a mace ta wuni ta kwana. Zama nayi a kujerar tsugunno, ina goge bakina, Mama kuma tana gaban wake tana wankewa. Daga bayan gida Sagiru ya fito, butar da nake amfani da'ita Sagiru ya saka ƙafa yayi boll da'ita. Ruwan ya tarwatse duk ya ɓata mu.
"Wannan ƴar tashar kuma me take yi a cikin gidannan Mama?" Ni dai idanu na bishi dashi, dan ji nake yi zuchiyata na tunzurani akanshi. Mama tace
"Shine zaka yi mata boll da buta, wannan butar ita kaɗai ta rage a cikin gidannan, sabida duk ka farfasa mana kayan ribobi. A zabura na miƙe tsaye, kokawa ta kaure a tsakanina da Sagiru, dukana yake yi sosai, nima ban tsaya raga mishi ba, na shiga yi mishi dukan manyan ɓarayi. Mama sai zage_ zage take yi, tana ta kiciniyar rabamu, mu kuma sai turka_turka muke yi. Musa da Nafisa ne suka raba wannan taƙaddama da ƙyar, dukkanmu mun daku sai huci muke yi.
"Wallahi ba dan Mama ba saina kasheki har lahira, ko ba komai na rage mugun iri, amman a juri zuwa rafi wata rana za'a fasa tulu, in sanda na yawo, kai na yawo wata rana zasu haɗu. Karki kuskura in dawo in sameki a gidannan, la'ananniyar Allah, sai na zame miki silar ajali. Mama tace.
"Tunda gidan na ubanka ne kai kaɗai ba, mitsiyacin yaro wanda baya ƙaunar dukkan wani farin cikina, Allah dai ya tsine maka akbarka, ita da gidanta ko ka mance mijinta ne ya sai mana gidan. Ubanku me ya mutu ya bar muku in banda riguna uku da rediyo sai tabarau da lofe." Harya soma tafiya ya juyo yace ma Mama.
"Allah ya tsinemun albarka, to na nawa kuma? Tun ina yaro kike tsine mana ai, waye zaiga haske a rayuwarshi kin gama kwashe mana Albarka. Kinga wata rana sai inyi ajalinki. Gasu ɗan Mama su da suke yanka kare su gasa su ci, mahaifiyarshi da yake mai tarbiyya ce kullum albarka take saka mana. Amman mu Baba ya auro mana uwa ƴar buyagi babu abinda ta sani sai ashariya, Mama in ku kai wasa fa wallahi duk zan sa kawunanku gabas in yanka." Yana dasa aya ya fice yana gauraye hanya, sai zage _zagen rashin mutumci yake yi. Ni kuwa tsaki naja na wuce na ɗebo ruwa a kofi na ƙarashe brosh ɗina, na koma ɗaki goya Yusuf nayi, na fito tsakar gida.
Mama maganar atampopin Tafarkiya zata siyanne ko in kai kasuwa kawai? Banason mabaruka tazo tai ta aukin jirana, ni kaina na tsagu inje ai mun maganin Bulama da matsiyaciyar ƙanwarshi, zasu ɗanɗanama aya zaƙinta wallahi."
"To kinsan Tafarkiya inta faɗi kuɗin kamar saukar wahayi bata ƙara ko sisi akai, in kina ganin zaki siyar mata a hakan da tace, ai sai in kai yanzu ta caske miki kuɗinki, nima da kuɗaɗe a hannuna duk sai a gagganɗa, na aro miki dubu ɗarin ma da kika ce." Cikin juyayi nace
To Mama akai mata banda zaɓi, biyan buƙata yadi dogon buri. Mama ta shiga ɗaki ta ɗakko ledar kayan, ta haɗa da robar niƙan waken da take son yin alala ta fita. Nafisa na kalla tana zaune a tsakar gida tana faman chartting ɗinta na jaraba sai dariya take yi tana buga ƙafa. Duk yanda naso in gyara rayuwarsu sunƙi su hau layin seti, duk sun watsar da karatun dana tsaya a kansu nake son ganin sunyi, kowa ya shiga aikin ɓel_ɓel kawai, kuɗine suke shigoma Nafisa faca _faca, gabaki ɗaya ta canja, kalarta ta sake fitowa, hutu da gigewa sun kuma bayyana a tattare da'ita. Ko ba'ace ba da ganin buɗewar idanun Nafisa da irin mazan da suke mu'amula da'ita, nasan tuni ta jima da sallamar musu da budurcinta, karenta take ci babu babbaka kawai. Musa kuwa, tun Mama na faɗan mata da yake kawowa cikin gida su kwana, harta zuba mishi idanu kawai, gashi har ta kai za'a ajjiye mana ɗan dakan kuka a cikin gidanmu. Sagiru kuwa tuni ya jima da gagarar kowa. Ina cikin wannan tunanin Mabaruka tayo sallama ta shigo, idanu na zuba mata ina nazartar yanayinta. Har wata ƴar rama naga tayi, tayi wani zuru zuru da'ita.
"Ƙawata yauwa kin shirya ko? Muje maza dan mu samu mu dawo yau"
Mabaruka ni ko ba zamu dawo yau ba, in dai buƙata zata biya ai an gama. Kuma ai boka gangaranne kafi gwani, Mama nake jira ta kawo mun kuɗi sai mu wuce, ni ko ishasshen bacci ban samu ba." Muna cikin mamana Mama tayo sallama ta shigo, Nafisa kuma ta miƙe da gudu kafin ta ƙarasa magudana ta shiga sheƙa amai, tamkar zata amayar da ƴan hanjinta baki ɗaya. Murmusawa nayi, ai dama da ganin zaki zaici mutum, irin canjawar da Nafisa jikinta yayi dole da walakin, ashe wake ta ciyo, dole kuwa tayi kumburin ciki. Salati da tafa hannaye Mama ta shiga yi tana jijjiga kamar beyerabiya, cikin hanzari nace.
Kinga Mama sanlameni mu wuce, uzirin dake gabana yafi na Nafisa, ita daɗine yai mata yawa. Dama bata shiryaba ta soma" Mama taja ajjiyar zuchiya, tare da miƙo mun kuɗina, ta shiga ɗaki ta tarkatomun ƴan kuɗaɗen hannayenta da wanda ta ciyo mun bashi, ba laifi kuɗin sun tashi sosai. Daga gida kai tsaye muka wuce television garej anan muka hau motar Jos, masu bi ta kafancan. Bamu daɗe ba motarmu ta cika, kasancewar ɗaya a gaba uku a baya suke sakawa, amman kuɗin motar yafi na kawo tsada. Cikin awa uku da rabi muka iso Jos, kasancewar hanyar taana da kyau ba irin ta samunaka ba. Bamu muka isa ƙauyan boka ba, sai gaba da azahar, bamu ci komai ba, sai atile da muka siya da masara a bakin titin shiga Maza. Mun tarar da cincirindon layi sosai, maza da mata. Muna zaune wani Alh ya fito yana ɗingishi, jini face face a bayan malum malum ɗinshi, da ganinshi wani babban mai muƙamin ne. Bai jima da fita ba, sai ga Hama ta fito.
Ah Hama ashe rai kan ga rai? Sama da shekara guda ba ɗuriyarki, number ki a kashe in na gwada" Hama ta kama haɓarta halamar mamaki da jin daɗin ganinmu, ta dubeni tace.
"Masha Allah, haihuwa kika yi kenan Zubaina?" Dariya nayi duk da ina cikin damuwa da tunanin lalacewar da ƴan uwana suka yi.
Haihuwa nayi hama na samu Yusuf gashi a baya" Daga nan muka ɓalle da hirar yaushe gamo, ita kanta Hama abubbuwa da dama sun caɓe mata fiye da tunani, gashi duk wani arzikinta ya ƙare, harma an sako mata ɗiyarta ɗaya tana gabanta tana zawarci. Nisawa Hama tayi bayan mun gama bata labarin halin da muke ciki, tace.
"Shi zuwa wajan boka ko ƴan bori akwai biyan buƙata, sai dai bazaka taɓa yin arziki ba, sabida kullum a cikin matsaloli kake baka da aiki sai na samun biyan buƙata. Gashi bin bokaye tamkar sigari ko goro yake baka iya denawa, har sai kaga abinda ya ture ma buzu naɗi. Amman wannan karon tarwatsa gidan zanyi gabaki ɗaya, ni in zauna ni kaɗai ya fiye mun, na gaji da wannan yaƙin,na kashe kuɗi sosai yau, sabida aikin boka kullum a cikin ƙara farashi yake. Ƴan siyasa da masu neman duniya kullum kuma lalatashi suke yi, amman aikinshi ba dai yayi, baki samu abinda kike so ba. Mabaruka tace.
"Sosai kuwa Hama shi yasa ni bana jin tsadar ma wallahi, tunda zaka samu biyan buƙata, bokayen ƙaryar ma ai tsada garesu, sai rashin biyan buƙata yadda kake so. Ai ni kaina Adam a wannan karon sakin Sagira zaiyi kawai in huta, na gwammaci in ɗauki ƴar aiki, ko da kuwa ni zan dinga biyanta. Da ƙyar Hama ta yakice hira tai mana sallama, tare da bamu sabuwar lambarta, dan waccan wayar tace sace mata ita akayi. Bamu muka samu shiga ɗakin Boka ba sai wajajan bayan la'asar. A gurfane muke a gabanshi, muna shigowa ya soma yima matarshi yare yana nunoni da ɗan yatsa, take naji jikina ya soma rawa dan bansan hau ɗin da zata hauni ba. Matar boka ta dubeni tace.
"Yace a faɗa miki akan mijinki da kishiyarki kikazo, domun a lalata musu rayuwarsu. Sai dai abunda baki sani ba shine tun daren jiya ya turo miki da saƙon saki a wayarki ya sake ki saki biyu. Yau kuma suka wayi gari da gobara babu abinda suka ɗauka a gidan, dan haka sai dai in kina son komawa gidanki sai kiyi bayani" Zuface ta wankeni tas, wani irin duhu_ duhu nake gani, gabana sai harbawa yake yi. Ni Bulama zai saka haka kawai a kyauta? Tabb lallai na yarda da tsubbace_ tsubbacen Kanuri da ake faɗa yau, yarinya ƙarama lokaci ƙanƙani ta rushe mun duk ƙoƙarina na sama da shekaru. Tabb yau ake yinta ana dara ga dare yayi. Tunani na shiga mai mugun zurfin gaske, domun ina son yin nazari shin in koma gidan Bulama da ƙarfin asirine, ko in rabu dashi kawai in buɗe ma kaina wani kyakykyawan shafi na sabuwar rayuwane? Yanda nake da ƙuruciyata da dirinnan, kuma rayuwa ai yanzu na soma, naga zawarawa suna gara zarensu yanda suka so, har su kanyi dace da mijin daya kere mijinsu na baya ma. Yanzu Bulama ba koman komai bane fama da takauci yake yi, gandirobane ba wata tsiyar ba, ni ina ganin rabuwa dani da yayi tamkar wata ƙofa ya buɗa mun ta ginin sabuwar duniya. Ta wani fannin kuma ina gani tamkar na faɗi babu nauyi in har Yahanasu da iyayen Bulama suka samu abinda suke so. Wani shashe na lokon zuchiyata shi kuma sai hasko mun yarana yake yi. Yanzu haka zan tafi in barsu su kaɗai, zasu taso ba tare dani ba, yanzu duk irin shaƙuwar dake tsakaninmu da mama ba lallai bane su Maryam su shaƙu dani fa ko? Daɗiin abun haushin shine, duk tarin tulin tsadaddun suturuna wannan matsiyaciyar ta bunka mun wuta sun ƙone, dan ina da tabbacin dan sabida ɗakina ya ƙone ta kunna wutar dama sun ƙone dukka gidan uban kowa ya rasa"
"Zubaina meye haka wannan tunani haka har an kammalamun aikina amman sai faman karanta wasiƙar jaki kike yi. Ki faɗi abinda kike so mu tashi mu kama hanya" Mabaruka ce take yi mun magana, nisawa nayi na kalli uwar gidan boka nace.
Bana buƙatar komawa gidanshi, tunda har ya sake ni. Amman inason a sashi yaita asara duk abinda ya taɓa ya lalace, dukiya ko nawa ya samu ya zama mai rariyar hannu, tunda ya yageni a jikinshi, yaita cin karo da bala'en iri daban daban kawai" Wawuyar ajjiyar zuchiya ce ta ƙwace mun wacce bansan dalili ba. Wata laya boka ya miƙo mun, Mabaruka ta amsa ta bani. Bai jima yana magana ba uwar gidan boka ta dubeni tace.
"Wannan layar aikinta yana da laulayi sosai sai kin kula. Ki samu titi mai fuska huɗu ki tsaya a tsakiya, sai ki saki layarnan a tsaye ta faɗi, cikin dare amman zaki yi. In dai kika yi hakan shi da arziki sai dai yaga anayi. Kuɗinki dubu ɗari da ashirin" Kai wannan boka akwai shi da tsadar aiki gaskiya, sai dai fa akwai shi da aiki gaskiya. Dubu ɗari da ashirin ɗin na ƙirgo na miƙa mata. Muka fito daga cikin ɗakin. Wani irin ƙududun takaicine ya tokare mun maƙoshina da ƙyar nake haɗiyan kakkauran yawu.
"Yanzu Zubaina shikenan yarinyarnan ta ƙone miki kaya ta ƙone banza kenan, babu wani hukunci da zaki ɗauka akan hakan?"
MRS BUKHARI CE






😍🤍🤍🤍🤍
MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
19




*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days

25 / 67