Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
37
GHANA ZUBAINA:
A sanyaye na ɗaga wayar tare da karawa a kunne.
"Yaya ake kici Zubaina, ince dai ke kaɗai ce ko?" Kukan dake shirin turniƙeni na haɗiye da ƙyar murmushi na ƙaƙaro nace.
Ni kaɗai ce Mama yanzu Alh ya fita ni kuma na shigo cikin gida kenan ina ɗakina" Ƴar dariya ta saki tace.
"Kin yi abunda boka ya ce kiyin, ya yanayin abun yake kuma, kinsan da zafi_ zafi ake dukan ƙarfe?"
Aiki yaci Mama babu wata matsala, kuma Mama ni yanzu ma naga gidan zama, bansan ina son Alh ba ma sai yau, wani bala'in son shi nake yi sosai." Ni kaina ji nayi zancen ya subce a bakina ba tare da na shirya ba. Duk da dai a yanda nake ji a yanzu, sai naji lallai inason zaman gidan Alh ji nake zan iya rasa rayuwata in bana tare dashi. Ba tare da wani dalili ba, dan babu komai a gidan Alh in ba baƙar azaba ba. Amman ina ganin gara in haƙura kawai in zauna. ( Asirin Alh Liti yayi tasiri a jikin Zubaina. Wannan wani babban darasine, asirin mallaka yayi mata, da soyayya Kamar yadda tai ma Bulama) Mama ce ta katse ni dariyar murna da naji tana yi gami da hamdala.
"Alhamdulillah Zubaina sai yanzu naji abunda ya tokare ni ya faɗa. To kinsan da zafi _ zafi zaki yagi abunda zaki yaga. Ki dinga turowa ana siya miki filaye ana gina miki, ke har tirela ma sai ki siya abunki, ko ki buɗe shago a kasuwa, ko daga ghanan ki dinga turo kaya. Ko Musa sai ya kula miki da shagon. Amman kar kiyi sake, tun kafin gishiri ya fice daga kan kaza zaki haɗa balance ɗinki." Kukan yarinya na ji a kusa da Mama. Ajjiyar zuchiya na sauke ina tunanin yanda zan ɓullo ma zaman gidan Alh.
Mama kukan ƙaramin yaro nake jiyowa, ko su Rauda ne suka zo?"
"Wace Rauda? Hmmmm ƴar dakan kukannan aka zo aka diremun da sassafennan, wai yarinya an yayeta. Ni nama rasa yadda zan tsoma kaina ta ina zan soma renon wannan yarinyar ƴar ƙararrama da'ita? Ke fita ma bazan iyayi ba. Sagiru nake ta aikin nema tun jiya yazo mu tattare mu koma can sabon gida, nima in huta da wannan ƙaddararriyar anguwar." Baki kawai na taɓe abunda yake gabana yana da yawa.
"Mancewa nayi ban sanar dake ba Zubaina Asiya tana son a rushe wannan gidan, wai gidan sama take son tayarwa mai hawa uku ma. In yaso ko haya a zuba." Tana haɗiye yawu ta sake cemun.
"Ba wani abu da zaki turo mana ne Zubaina?" Kai kawai na girgiza nace.
Mama ni yanzu bani da kuɗi, kuma turo kuɗi daga Ghana zuwa Najeriya akwai wuya. Shi yasa fa nace kuɗin hayar gidana in kun karɓa ku dinga amfani dashi kawai Mama." Yarinyar Musa ce ta hana mu ƙarashe wayar, sai kuka take yi. Ƙit Mama ta kashe wayar ina ji sai ƙundumama yarinyar zagi take yi. Ɗan latse_latse nayi a wayar na ɗan shiga whatapp ɗina. Saƙonni barkatai na tarar. Da yawan saƙonnin na murnar aurenane, dan su Asiya da Mabaruka sun watsa zafafan hotunana kafafen sada zumunta. Wani sabon group naga an adding ɗina mai suna MATSALOLIN MU, wata tsohuwar ƙawata Bilki ce ta adding ɗina. A hankali na soma bin saƙonnin cikin group ɗin. Sai na fuskanci gidan shawarwari ne, zaka turo da matsalarka, ko na wanin ka, sai ka nemi shawara a baka. Idanuna na runtse hawaye suka sulalo mun. Kokkonnan na ɗaga na soma sha a hankali ina gutsurar ƙuli_ƙulinnan, sai kawai na fashe da kuka. Tunanin gidan Bulama na soma yi. Da farfesun naman rago, ko kan saniya dashi nake karyawa. Rana ɗaɗɗaya ne nake karyawa da kakkauran tea da biredi, da wainar ƙwai harda bota a jikin biredin. Amman yau nice kokko da ƙuli _ƙuli ya zama abun karyawata. Ɗaga kaina nayi na kalli ɗakin nawa, ɗakin da kishiyata ta gama zamanta ta haifi yara har biyu. Nima gani a ɗakin a kan gadon. Ɗakina na gidan Bulama na sake tunowa, yanda gadona yake babba gashi da tsadar gaske. Bayan ya auro Yahanasu ya sake sake mun kayan ɗaki harda fenti. Na sake tuno da kayan ɗaki daya ciyo bashinsu ya samun a ɗaki a lokacin da na haifi Yusuf, dan kawai yaga walwalata Oh Allah rayuwa kenan duk da hakan kuma sai nake jin inason zama da Alh, bana fatan abunda zai rabani ma dashi. Ni bansan ina sonshi ba, sai yau dana ga ya fito cikin kwalliyar nunawa sa'a. Amman wajan wata budurwar ma zashi, na tabbatar itama aurota zaiyi, shine dalilinshi na sakin Zakiya. Ina cikin wannan tunanin na jiyo sallamar Zakiya zata tafi Najeria. Fitowa nayi tsakar gidan tana tsaye da akwatin kayanta. Tana sanye da wata jemammiyar atamfa shuɗiya, da wani farin ɓulallen mayafi, takalmin ƙafarta ma ƙarewarta a tsinke yake ta ƙulle da wani jan zare.
"Zubaina ni kam zamana ya ƙare, abunda naita nema yau yazo kaina, a gabana an saki wasu matan. Ina muku fatan fitowa da wuri ba ma sai kun kaini jemewa ba. Ga yara nan na barsu." In yi magana ma na kasa, wani irin hakine yake taso mun, ina jin wani jiri na ɗibata.
Wannan wacce iriyar rayuwa ce na shigar da kaina? Ina zaman_ zamana. Manya da yaran gidan sai sallama suke ma Zakiya, ɗan yaronta da bai wuce shekaru uku ba yana tsaye ba wando sai zandara ihu yake yi. Goyon da Zakiya take yi kuma yana hannun Nabila, ita kanta sharar hawaye take yi. Nima hawayenne yake zuba a kumatuna. Haka rayuwa taci gaba da garani. Uƙubar da nake ciki ko maƙiyina bazan so ace ya faɗa ba. Wayata ma baki ɗayanta kasheta nayi na jefa a jakata, dan katin cikin wayar ya ƙare, kuma haushin kowa nake ji. Musamman Asiya da Nafisa da in suka kirani suke mum wani shegen iyayi da feleƙe. Wanka a ƙyanƙyame nake yi, sabida ƙyamar da bayan gidan yake bani. Rashin Alh Liti a gari ya sanyaya mun zuchiyata. Ina kwance a kan gadona ina cikin duniyar tunani, tare da tausayin yarinyar da naji Alh Liti yana waya zaije wajanta. Ko kurkuku yafi gidan Alh Liti daɗin rayuwa. Bulama ne ya faɗo mun a raina, wanda hakan sai da yasa ni murmushi. Bawa da Maryama na na tuno saina fashe da dariya, ina dariya ina share ƙwalla. Nasan duk talaucin da Bulama zai tsinci kanshi, babu abunda zai sauyashi wajan bautawa matarshi. Kaicona da na bar gidan Bulama, da zamana nayi muka rayu rayuwa mai daɗi. A ranar dai tunanin Bulama da zugin zuchiyane suka hanani bacci, sai wajajen asuba ɓarawon bacci ya ɗebeni.
Asibiti. Bulama Babba.
A wasu dogayen binci muka samu waje muka zauna. Babu mai cewa da kowa komai. Ward ɗin a cike yake maƙil da masu kawo ziyara, lokacin shiga suke jira kawai ya cika su shiga su duba majinyatan da suka zo dubiya. Hajara ce ta iso inda muke kici_kici da kaya da sauri Ahmad ya miƙe ya karɓeta ga goyon Yusuf a bayanta.
"Abban Anisa akwai filo da tabarma da bokiti na ajjiye su a wajan mai gadi kayan sunyi mun yawa." Cewar Hajara wacce ta zauna tana mayar da numfashinta. Ahmad baice mata komai ba ya nufi hanyar dogon falon.
"Sannu Bulama yaya me jikin? Kun samu ganin likita kuwa naga har azahar ta kusa?" Cikin tawakkali nace mata.
A'a sai zuwa shiddan yamma likitar da zata dubata zata shigo. Amman dai ta samu gado. Sannu da ɗawainiya ga Yusuf ma yayi bacci." Kafin tace wani abun muka jiyo ihu da dambarwar wata baiwar Allah ita da nursses da halama itama mai taɓin ƙwaƙwalwarce, sai ƙunduma ashariya take yi, wani dattijo kamar mijinta yana riƙe da'ita yana.
"Hauwa kiyi shiru dan Allah, a asibiti muke fa" Amman wannan matar taƙi yin shiru sai naushi take kaiwa nursses ɗinnan. Allura wata nurse ta fakaiceta ta tsira mata. Kafin ma a zare allurar tuni tayi laushi sai ido. Da taimakon wannan dattijo aka shige da'ita ɗakin da Yahanasu take ciki. Ni dai nayi tagumi ina kallon ikon Allah. In baka je asibiti ba, ba zaka gane ana fama da cuta ba.
"Ohh ni Hajara ji wannan lamari abun tausayi ya Allah." Ahmad ne ya iso da kaya a hannunshi.
"Ungo Hajara ki shiga ki ajjiye a gefen gadon da Yahanasu take kai. Sai ki zauna a gefenta, inta farka ki kira mu." Karɓan bokitin da tabarmar tayi, ta shige ɗakin da saurinta har tana bige wata nurse.
"Gunsum sun kira ni yanzu ina hanyar shigowa, suna dab da shigowa cikin garinnan da Gunsum, da Bagulaji, sai Asissa tamu ba tsohuwar matar Wakil ba. Na dai ce da zaran sun shigo su kira ni sai in yi musu kwatancen asibitin da muke, gudun kar in ɗaga musu hankali in nace muna dawanau."
To Allah ya kawo su lafiya. Leɓena na lasa wanda ya bushe kamar zai tsage.
"Bulama muje masallaci lokacin sallah yayi, na baro maza anata alwala." Miƙewa nayi muka jera ni da Ahmad, babu Mai cewa uffan. Ko da mu ka idar da sallah a wani ɗan masallaci a tsallaken titi. Zaune nayi ina tasbihi a hankali. Bayan na gama na nufi durowar Qur'anan masallacin na ɗakko Qur'ani na dawo na zauna. Karatun Qur'ani na shiga yi domun in samu ƴar nutsuwa dan zazzaɓi ne yake shirin kayar dani, ko yanzu da likitoci zasu yi aune_aune a jikina na tabbatar zasu bani gado a matsayin mara lafiya. Wayar Ahmad dake ajjiye a ƙasan kafet ɗin masallacin ta shiga kuka, ƙarfe biyu dai_dai na rana.
"Gunsum kun ƙarasa shigowa gari kenan? Cewar Ahmad dake waya. Bana jin me Gunsum yake cewa, na ji Ahmad yace.
"To kayi amfani da map ya kawo ku asibitin Dawanau, in kuka iso sai ku kira ni" Kallon Ahmad nayi naga yayi jim ga wayar a kunnenshi da dukkan halama magana Gunsum yake yi mishi. Numfashi yaja yace.
"Gunsum ba abunda kuke tunani bane sam. Daga asibitin Murtala aka turo mu yin wani gwaji, kai dai sai kun ƙaraso kawai." Ya sauke wayar yana girgiza kanshi. A sanyaye nace.
Tambayoyi ya shiga yi maka ko Ahmad?"
"Wallahi kuwa kai dai ka bari, ina jiyo muryar Bagulaji da Aissa suna rabka salati. To amma tunda sun shigo garin ai dole su san koma me ake ciki ai. Mu dai fatanmu shine Allah yasa da zaran Dr Halima ta gama gwaje_gwajenta ta mayar damu asibitin Murtala."
Ameen Ahmad" Na ce a raunace. Mun shafe kamar minti talatin muna jiran su Gunsum, suna kira muka fice a masallacin muka koma cikin asibitin. Sai dube _dube muke yi ko zamu hangosu, can wajan ajjiye motoci naji muryar Gunsum yana kirana.
"Bulama Babba gamu nan" Juyawa nayi nayi ido huɗu da ƴan uwana, naji sassauci sosai dana gansu, saidai ganinsu ya sake haifarmun da mutuwar jiki ainun. Wajansu muka nufa, suma tawowa suke yi, a hanya muka ci karo . Bagulaji ta zuba mun idanuwanta tana karantata, ni kuma na sauke kaina ƙasa ina murmushin dole. Aissa tuni ta soma shessheƙar kuka. Gunsum yace.
"Nifa dama nasan halinki muguwar raguwace, ni banso akayi tafiyarnan dake ba ma. Bagulaji ce ta katseshi da cewa.
"Ahmad yaya mai jikin? Cikin inda_ inda Ahmad yace.
"Jiki da sauƙi Bagulaji, ya hanya, ya kuka baro mutan gidan kuma?" Tsugunnawa nayi a guiwowina na gaishe da Bagulaji cikin tsantsar mutuntawa. Jikinta a sanyaye salab ta amsa mun, idanuwanta cike da tsantsar tausayina. Miƙewa tsaye nayi, muka yi musabaha da Gunsum, Aissa tana kuka ta gaisheni ni da Ahmad da yake gaisawa da Gunsum.
"Muje ku kaimu muga Yahanasun ko zamu samu nutsuwa" Cewar Bagulaji kenan. Gaba mu ka yi mu uku, su suma su Aissa suna biye damu, har zuwa dogon falon da zai sada mu da ward ɗin da Yahanasu take. Babu cinkoso yanzu a falon, sai ɗaiɗaikun mutane da suke zaune a kujera wasu ma a tabarma suke zaune. Ɗakin na leƙa naga masu zuwa dubiya suna ciki.
Bagulaji mu shiga ga ɗakinnan" Gaba na soma yi suka mara mun baya har zuwa gadon da Yahanasu take kwance. Hajara bata zaune a kusa da Yahanasu kamar yadda Ahmad yai mata umarni. Tana can gadon ƙarshen ɗakin inda muka ga an cika, wata baiwar Allah sai ihu take yi. Bagulaji da su Gunsum idanu kawai suka bi Yahanasu dashi, kowa jikinshi ya sake macewa mus, babu wanda yayi magana duk suna tsaye jigum dasu. Ahmad wucewa yayi wajan Hajara a fusace, ya finciko hannunta suka dawo inda muke.
"Taka_ mai_mai me ke damun yarinyarnan wai, kuimun bayani. Ni duk na ganku a rame ne sosai" Inji Bagulaji wacce tayi Maganar a tsanake.
Bani da zaɓi, labarta mata yanda abun ya soma nayi, harxuwa tsintarta a cikin kwata da mu kayi, zuwa kaita asibitin Murtala da mu ka yi, da abunda Dr Ruƙayya ta faɗa a kanta, da batun lakasera da take sha kullum." Salati Bagulaji ta shiga rerawa tana tafa hannayenta, idanuwanta suka cicciko da hawaye.
"Yanzu Yahanasun ce ake zargin tana ta'amali da kayan maye, harma ita likitar tace muku waɗannan kwaya suke zubar mata da juna in ta samu? Shine kuka tattagota kuka kawota asibitin mahaukata sabida kuma mahaukatanne ko? A cikin zuriyarmu maza ma ba sui shaye_ shaye ba, sai mace za'ace tana shaye_shaye? Ni nafi danganta lamarin da shafar jinnu gaskiyar magana." Duk dai shiru mu kayi muna kallon Bagulaji sai faɗa take yi. Gunsum yace.
"Amman Ya Bagulaji ni ina ganin kiyi haƙuri mu bar likitoci su gama dukkan bincikensu a kanta kafin mu yanke hukunci, tunda shi ma Bulama Babba yace tana shan lakasera kullum, a cikin lakaserarnan samari suke narkar da ƙwayoyi fs suna sha. A koda yaushe halin ɗan adam ka iya canjawa da irin halinshi da kuka sani na baya. Kuma shaye_shaye ya zama ruwan dare a cikin wannan zamanin da muke ciki. Kar ku manta Dr Ruƙayya likitace wacce ta shafe tsawon shekaru tana karatu a fannin ilimin jinya. Kuma ƙila ta daɗe tana aiki, Asibitin Murtala, babban asibiti ne shima, banyi tunanin zasu yi binciken da ba dai _dai bane. Kuma cikinmu babu wanda shaiɗan ba zai iya cin nasara a kanshi ba. Mu yi haƙuri mu ba likitoci dama su gudanar da aikinsu." Wata nurse ce ta ƙaraso inda muke tace.
"Lokacin dubiya ya ƙare, zaku iya fita daga waje dan Allah, mutum ɗaya muke da buƙatar gani a nan. Sannan ɗaya daga cikinku ya biyo ni domun yankan kati." Ya Bagulaji ce ta ja kujera ta zauna tana sharar hawaye.
"Kuje ni zan zauna da'ita. Yaran du suna gida kenan" Nace mata.
E suna gida, ga Yusuf a bayan matar Ahmad Hajara." Hajara ta matsa suka gaisa da Ya Bagulaji ta shafa kan Yusuf, idanshi biyu sai kallonta yake yi. Fita waje mu ka yi, mu ka bar Ya Bagulaji ita da Yahanasu. Gunsum da Ahmad kuma suka je siyan kati. Tabarma Hajara ta ɗakko a ciki ta shinfiɗa musu, ta koma ta kawo musu abincin data dafo.
An ɗiba ma Ya Bagulaji abincin ? Na tambayi Hajara.
"Na zuba mata amman kaɗan tace in zuba mata. Ga naku kaima ka daure kaci abincin tun safe rabonka da abinci. Aissa ta dubeni cikin yare ta dinga yi mun nasiha. Dole na zauna ta zuba mun abincin, kaɗan naci na sha ruwa. Ina zaune su Ahmad suka dawo. Abincin suma su ka ci. Ana kiran sallar la'asar Hajara ta soma azamar tafiya. Mu kuma muka nufi masallaci mu ukun. Misalin ƙarfe shidda Dr Halima ta shigo asibitin. Muna zazzaune jigum ta shiga ɗakin da Yahanasu take, tana saye da kayan likitoci. Ajjiyar zuchiya na sauke, tare da roƙon Allah yasa ba taɓin hankali Yahanasuna ta samu ba." Fitowar Ya Bagulaji muka gani, dukkanmu muka tashi muka nufeta, sai sharar hawaye take.
"Da gaske fa Yahanasu kamar shaye_shaye take yi. Dan yanayin muryarta tafi kama da muryar ƴan maye ba wanda Jinnu suka shafa ba. Amman in dai hakanne wannan yarinya ta ɗakko hanyar tarwatsa mana sunan gidanmu wallahi, zaku ma ta ci ubanta a wajan iyayenta maza. Tunanina yanda za'ayi ma su Ba Bakura jawabi har tunaninsu ya ɗauka, kar Ba Bakura ciwonshi ya tashi nake jin tsoro." Dam gabana ya yanke ya faɗi, kuka Aissa ta fashe dashi tana ambaton Allah. Nima Allah na shiga ambatowa, dan wani irin harbawa xuchiyata ta shiga yi ba ƙaƙƙautawa. Hankulanmu duk ya sake tashi ainun. Da ƙyar muka rarrashi zukatanmu muka nemi waje a benci muka kafa muka tsare, muna jiran fitowar Dr Halima. Su Ya Bagulaji suna zaune a tabarma tana amsa wayar matan gida da suke ta faman tambayarta jikin Yahanasu."
MRS BUKHARI CE[13/08, 9:33 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI)
38
Sama da mintuna arba'in Dr Halima ta fito daga cikin ɗakin. Da sauri na miƙe na isa gareta.
"Ka same ni a office yanzunnan" Tana gama faɗar haka ta wuce. Ya Bagulaji tace.
"Muje mu sameta, su kuma su jira mu, Aissa ta koma wajan Yahanasun. Gunsum yace.
"Ya da kin zauna mu muje."
"La ba haka mu ka yi da Babanku ba. Yanzu ni suke jira in kirasu in sanar dasu halin da ake ciki. Bulama muje" A sanyaye nayi gaba, tana biye dani a bayana har zuwa ofishin Dr Halima dan muna hangota ta shige wani ɗaki da muke kyautata zaton nanne ofishin nata. Da sallama muka shiga ofishin. Bayan ta amsa sallamarmu ta bamu wajan zama tace.
"Mama kece mahaifiyar Yahanasu?" Ya Bagulaji murya a sarƙe tace.
"E likita Yahanasu ƴata ce." Kai ta jinjina tace.
"Akwai