Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
wani abu daya taɓa faruwa da'ita mai firgitarwa ne, ko kuma mutuwar wani na kusa da'ita?" Ni dai nayi ƙuri ina kallon Dr Halima. Ya Bagulaji tace.
"E likita shekaru uku da suka wuce an taɓa yi mata fyaɗe. Ina tunanin wannan shine gagarumin abun da zance ya taɓa faruwa a famili baki ɗaya mai firgitarwa ."
"Okey an kaita asibiti a lokacin da abun ya faru, ko kuwa a gida aka barta ne" Muƙut Ya Bagulaji ta haɗiyi yawu.
"An kaita asibiti, ta samu kulawar duk daya dace ta samu likita. Dan iyayenta maza tsayayyune kuma ƴan boko ne." Dr Halima tace.
"Yaya kuma Rayuwarta taci gaba da tafiya bayan ta dawo gida, sannan ya al'umma suka ci gaba da kallonta?, Ta shiga wani hali na tsangwamane"
"Sakamakon ta firgita ainun da lamarin daya risketa, ko a asibiti da aka kaita tayi ta fisge _fisge, da yawan firciki, da taimakon Allah da kulawar da likitoci suka bata sai ta samu lafiya, amman an yi ta sauke mata Quri'a. To ko da ta dawo gida sai ya zamana bata son fitowa waje, cikin ƴan uwanta ma bata son shiga. Tayi rama sosai, to ana cikin wannan gaɓar mahaifinta yai mata aure da shi Bulama Babba wannan, dama ɗan uwanta ne." Shiru Dr Halima tayi tana nazari, tayi jim tana kallona, ni kuma duk na gama dibibicewa, tausayin halin da Yahanasuna ta tsinci kanta a ciki a baya ya tsirga mun ainun dan ban taɓa jin wannan labarin ba, tunda dai Mama Gana ta sanar dani an yi mata fyade a lokacin da suka kawo ta gidana, ban sake tayar mata da zancan ba. Dr Halima ta dube ni tace.
"Yaya Yahansu ta kasance a cikin gidanka?" Cikin faɗuwar gaba na zaiyana mata ɗan abunda ya kamata ace na sanar mata,na halin ko in kula data tsinci kanta a ciki, kwanciyar hankalin data samu baifi na shekara ɗaya da ɗoriya ba. Shiru kake ji a cikin ofishin ko wanne cikinmu da abunda yake tunani. Haƙiƙa na muzanta a cikin wannan ofishi sosai, duk da nasan ko a lokacin da nake cusgunama Yahanasu ina jin zafi da raɗaɗin ganinta a cikin damuwa. Amman ƙarfin asirin da Zubaina tayi mun yayi mugun tasiri a jikina. Kuma bana wasa da sallolin nafila dana farilla, bana wasa wajan tilawar Qur'ani da azkhar. Wannan ya farune sabida shine ƙaddarata ni da Yahanasu. Allah ka yafe mun, ka bawa baiwarka lafiya ka dubeni. Haka nai ta tattauna maganganu a zuchiyata, amon muryar Dr ne ya sa na ɗago kaina wanda yake baranar ƙonewa tsabar tsantsar chajin daya ɗauka.
"To ina ganin sakamakon fyaɗen da akayi mata a baya, shi ya jefata a cikin wannan halin data tsinci rayuwarta a ciki. Sakamakon rashin kulawa da bata samu ba, ko kuma ince tarairaya. Ta kamu da cutar damuwa wacce a turance muke kiranta da (Deepretion) Amman ku baku fahimta ba, sai akayi mata aure, ta jima wannan cutar tana cinta, wanna raɗaɗin na fyaɗen da akayi mata shi ya jata ta soma shan miyagun ƙwayoyi domun ta samama kanta nutsuwa da hutun ƙwaƙwalwa. Tana cikin wannan halin aka kuma yi mata Aure, ta fuskanci matsi a gidan aure, hakan ya ƙara sake jefata a matsananciyar ciwon damuwa, ta yanda ba zata ma iya sarrafa kanta ba. Ciwon damuwa ciwone mai girman gaske, da yake buƙatar a tarairayi dukkan wanda ya kamu da wannan cuta. A dinga kawo shi asibiti yana karɓar magunguna akan kari, likitanshi na bashi kalma mai daɗi. Amman mutane da yawa suna tare da cutukan damuwa ba'a sani ba. Matan aure da yawa sun faɗa cikin harkar shaye_shaye tsundum a sanadiyyar ciwon damuwa, wasu kuma gudun kar su kamu da hawan jini ne. Gasu can duk a cikin ɗakin, kaso saba'in duk shaye _shaye ne ya haukatar dasu, kuma a cikin kaso saba'in ɗinnan kaso hamsin matan aure ne, kaso ashirin kuma yawanci ƴan mata da suka tsinci kansu a cikin jarabawar fyaɗe ko wata tsangwama. Kaso goman daya rage kuma masu shafar aljanune duk muna dasu." Ajjiyar zuchiya ta sauke ta kakkafemu da idanuwanta. Har ga Allah sai naji na muzanta ainun. Lallai Zubaina ta cutar dani da yawa. Yahanasu a cikin irin halin da dama aka kawo ta gidana kenan, amman na kasa bata kulawa balle in san a wanne hali take? Kaico, Allah kana gani ba acikin hayyacina na aikata komai ba, Allah ka kawo mana ɗauki ka dawo mun da nutsuwa da tunanin matata."
"To yanzu dai ƙwaƙwalwar Yahanasu ta gama birkicewa tuƙuru. Sakamakon wani magani ko allurar doki da suke yi ma kansu masu ƙarfi, hakanne yasa cikin dake jikinta ma ya fita. Zamu riƙeta a nan asibitin mu bata kulawa tare da ƴan uwanta masu taɓin ƙwaƙwalwa, har zuwa lokacin da zata warke, shekara guda ko ƙasa da hakan. Ku yi haƙuri nasan da ciwo, kuma duk abubbuwan sun faru ne a bisa rashin sanin ita a wanne halin take bayan fyaɗen da akayi mata. Ciwon damuwa cutace da ita ke sarrafa mutum, itama tana kamanceceniya da taɓin ƙwaƙwalwa. Da yawan matan da kuke jin labarin sun soka ma miji wuƙa, sun kashe kishiya, sun ƙona miji, yawanci ciwon damuwa ke ɗawainiya dasu, ya taɓa ƙwaƙwalwarsu ba'a sani ba, ko sun aikata zaku gansu a kafafen yaɗa labarai suna ba da labarin yanda suka yi kisan. Mai hankali ai bazai yi irin wannan aikin ba mata da aka sanmu da taushi. Shaye_ shayen mata ya ta'azzara a wannan ƙasar tamu, musamman a garin Kano ( kuyi haƙuri wannan zancan gaskiya ne. Shaye_shaye yayi yawa a Kano, musamman na mata) Kuka Ya Bagulaji ta fashe dashi, ni kaina hawaye nake zubarwa dan zuchiyata ta riga data tsinke sosai, na kasa sarrafa kaina bansan sanda na soma zubar da hawayen ba. Dr Halima ta ja fasali tace.
"Ba kuka zaku yi ba. Ku bita da adda'a dan ƙwaƙwalwata ta taɓu sosai, ta jima tana ta'amali da waɗannan miyagun ƙwayoyin, a hankali _ a hankali har suka ƙarashe rikita mata ƙwaƙwalwarta. Kamar yadda na faɗa muku zamu riƙeta a nan muci gaba da bata kulawa, zata samu kulawa daga ƙarƙashin ofishina in sha Allah. Mutum biyu zasu zauna su yi jinyarta mata, sabida jinyar masu taɓin ƙwaƙwalwa akwai wahala sosai. Sannan akwai lokuta da aka ware na zuwa dubiya, bama son ana yawan zuwa ana ganinsu, sabida hakan wani lokaci ka iya sake rikirkita mana majinyatanmu. Ga wannan takaddar ka fita ka samo mana wannan allurar, bamu da ita ta ƙare, kuma muna buƙatarta da gaggawa, in ka kawo ta sai ka kawo mini. To Allah ya bata lafiya, maman Yahanasu ayi haƙuri." Ina riƙe da hannun Ya Bagulaji muka fita, dan tama kasa tashi sam. Zaunar da'ita nayi a benci, sai faman haki take yi. Ahmad da Gunsum suka shiga tambayata me Dr tace. Sun fahimci ta tabbata Yahanasu na ɗauke da taɓin ƙwaƙwalwa duba da yanda suka ga duk na fice a hayyacina. Takaddar allurar da Dr ta bani na miƙa ma Gunsum.
Ka fita ka nemo wannan allurar, bazan iya tafiya ba Gunsum." Da sauri ya amshi takaddar ya fice. Ahmad ya zaunar dani dan ya lura da yanda jikina yake ɓari. Haƙiƙa Zubaina ta cutar da rayuwata. Ta zalunci kowa nawa, amman nasan Allah zai mun sakayya, fit duniya wal akira. Ina dafe da kaina na ji Ya Bagulaji tana waya, na dai ji ta ambaci Wakil, tiryan_tiryan ta soma yi mishi jawabi, take na soma haki, ina ambaton Allah a fili, saitin zuchiyata na dafe bugawa yake yi kamar zai Burma mun kirjina.
"Kasan yadda za ka sanar ma Babanninku musamman Innana, wacce daman na barota a cikin damuwa. A taya mu da adda'a. Sannan a sanar ma da Mama Gana halin da ake ciki, in yaso in zaku tawo ku tawo da'ita sai mu zauna mu kula da ita Yahanasun kafin mu ga abinda hali zaiyi." Bana jin abunda Wakil yake faɗa mata. Da haka ta ajjiye wayar tata. Cikin ƙanƙanin lokaci aka dinga kiran wayar Ya Bagulaji, duk ƴan gidane tun tana ɗagawa har ta gaji ta maka wayar a silent, dama ni tuni na" kashe wayata, wayar Yahanasu kuma tana gida. Minti talatin da fitar Gunsum sai gashi ya dawo da ledar allurar ya sayo. Tare dashi muka kaima Dr. Allurar tazo taima Yahanasu da bata ko motsawa. Kallona tayi tace.
"Ina ganin ku kam zaku iya tafiya gida, ba kasafai muke son ganin mutane ba. Masu kula da'ita kaɗai zaku bari. Gobe kwa dawo da misalin biyun rana ne kaɗai zaku iya ganinta." Ya zanyi dole haka mu ka yi ma su Ya Bagulaji salllama. Gunsum ya ciro kuɗi ya miƙa mata taƙi karɓa.
"Akwai kuɗi a hannuna Gunsum. Ku je abinku. Bulama Babba abunda zan faɗa maka shine ka daure karka bari ciwo ya kwantar da kai, dukan yai mana yawa, dan naga jikinka har rawa yake yi. Ka yi hakuri. Ba Bakura yasa anyi mata sauka jiya. Yau ma za'a kuma yi. Gobe wasu zasu tawo daga can Damaturun, harda Innana. Da mahaifiyarka. Hankulan ƴan Damaturu ya tashi ainun. Mata matam da suke gidan miji duk kowa so yake sai ya zo. Amman Ba Modu yace mota biyu kawai za'a zo dubiya, washe gari su koma. Ku tafi Allah yayi albarka. Ahmad Allah ya bar zumunci sannunku dukkanku da ƙoƙari. Ka gaishe mun da Hajara inai mata ban gajiya." Sallama mu ka yi muka fita. Ahmad ya ja ɗan sahu, mu kuma muna biye dashi a mota har zuwa na'ibawa. Muna shiga layin ana kiraye_ kirayen salla, sai da mu ka yi sallar magriba, mu ka zauna a masallacin ƴan anguwa suna tai mun jajen ashe Yahanasu ta samu lalurar taɓin ƙwaƙwalwa. Nasan aikin Hajara ne uwar kusasu. Ahmad ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba dannewa kawai yayi. Sai da mu kai sallar isha muka kuma nufi gidan."
GHANA:
ZUBAINA
Allah yayi dare gari ya waye. Tun duku_duku hayaniyar bataliyar yaran gidan ta tashe ni a nannauyan baccin da ban daɗe da samun shi ba. Yau da bala'i da masifa ƴan matan gidan suka farka. Wai akan wata tayi ma wata ƙwacen saurayi a cikinsu. Shine suka kaure da damben mafisa, wanda dama a cikin kwana biyun da nazo kullum sai yaran sunyi rikici. Da naji ihun yayi yawa ne na fita a guje. Abunda na gani ya razanani. Walida kamar yadda naji ana kiranta a gidan na gani da wuƙa a hunnunta jini na ɗiga. Yayin da wata farar budurwar da ban san sunanta ba, na hangota a ɗurƙushe dafe da kunnenta jini na zuba. Dan ba duka yaran gidan na san sunansu ba, Allah yayi yawa dasu. Hajiya Kubra da Nabila sai salati suke zabgawa.
"Baki da hankaline zaki yanki ƴar uwarki da wuƙa sabida ɗiban albarka. Ashe har yanzu baki dena wannan harkar daban ba. Nabila duba muga kunnen nata." Hajiya Kubra ce tayi waɗannan maganganun a zafafe. Walida tace.
"In kika ga na dena daba sai dai in raina ne ya tsaya. Nifa babu matar data isa dani a gidannan danni nake yi ma kaina komai, zaman kaina nake yi. Kullum mahaifiyata tana samun albarka a waya."
"Hajiya Kubra, kunnen shingin kaɗan ya fice daga jikinta, ga jinin sai tsananta zuba yake yi dole a kaita asibiti. Amman walida baki kyauta ma ƴar uwarki ba." Walida ta katse hanzarin Nabila da cewa.
"Ita da tayi ƙwacen saurayi ba a ce bata yi dai_ dai ba. Sai ni dana hukuntata shine banyi dai_dai ba? Ko da yake dama ba wacce taƙe ƙaunata a cikinku. Kafin ta rufe baki Rashida ta zabgeta da mari tace.
"Ki shiga taitayinki wallahi kin gane ko? Akan wani ɗan iska zaki raunata Yayarki dan ba ciki ɗaya kuka fito ba? Nan faɗa ya dawo kan Rashida, faɗan da sai da suka dangana da ƙofar gida, filin tsakar gidan yayi musu kaɗan. Mazan gidan daga masu tsaki, sai masu cewa su kashe kansu talauci da Babansu ya sasu a ciki ne sanadi. Nabila da Bala kuma suka kama wacce aka jima rauni suka nufi asibiti. Ni dai ina riƙe da haɓa ina kallon ikon Allah.
Wannan wanne irin ƙaddarren auren ne haka? Gida sai kace gidan kazo nazo gidan karuwai.? Ina cikin wannan tunanin muka jiyo muryoyin maza a waje, sai magana akeyi. Babu shiri muka nufi ƙofar gidan, Rashida ce ta shigo da mugun gudu ta bangajeni na faɗi akan hannuna ɓaras na karye a tsintsiyar hannuna. Wan Rashida ne ya shigo da shegen gudu shima hannunshi riƙe da wuƙa. Yaran gidan suma suka shigo. Duk suka tumurmisheni suka wuce. A wajan Hajiya Kubra ta tafi ta barni ina riƙe da hannayena. Ihun kuka na saka ina faɗin.
Ni Zubaina na mutu na lalace ina zan tsoma kaina ne a cikin wannan tsinannen gida, tun asubar fari mun tashi da jarfa.? Miƙewa nayi da ƙyar kafin kace me hannuna ya suntuma har ƙyalli yake yi. Ƙurar faɗan kuma ya lafa. Har wan Rashidan yazo ya fice, ko kallon banza ban isheshi ba, ballantana yai mun sannu. Ɗaki na koma nayi zaman ƴan bori tim a ƙasa ina kukan fitar rai. Ji nake Inama ace mutuwa tazo ta fige mun rai na ko zan huta. Hannu ciwo sai gaba _ gaba yake yi, na rasa me ke mun daɗi. Da ƙyar muryata take fita, sai kiran Hajiya Kubra nake yi da muryata wacce ta dashe sabida yawanta kuka. Labule ta ɗaga tana cewa.
"Ni bana mance ma na ganki a yashe a ƙasa ba ɗazu." Bata hadiyi yawu ba taga hannuna yana reto. Ba shiri ta shigo tana duba hannun.
"Karyewa kika yi Zubaina?" Wani kukane ya tunkudo mun, ban iya bata amsa ba.
"Ki taso mu je gidan madori ya ɗoraki. Amman kina da kuɗi ko kayan kuɗi ko?" Kallonta nayi da mamaki. Murmushi tayi mun tace.
"Nasan baki fahimce ni ba, kasancewar ke sabuwar zuwa ce a gidan. Ai Alh iya ci da shayarwa, da kwanciyar aure shine kaɗai yake shiga tsakaninshi da matanshi. Da sallah zai bi matanshi da yaranshi mata da atampa ko yadi kala ɗaɗɗaya. Sai kuma in kin haihu kuma. Amman ko haihuwa a asibiti ba'ayi anan gidan. Duk yawan yarannan iyayensu a cikin gidannan sukai naƙudarsu, wasu sai da suka fi kwana biyu suna naƙuda da taimakon unguwar zoma ta gargajiya. Yace a haka shima mahaifiyarshi ta gama haife_,haifenta. Dan haka in kina da abun siyarwa faɗa mun inda yake in ɗakko miki, in munje ma ba mai ɗorin a madadin kuɗin." Hawayena na share, na nuna mata ƙaramin akwatina da hannuna.
Akwai atampata me ruwan ɗorawa ki ciro mun a cikin ƙaramin akwatinnan. Sai mayafina kuma yana kan gado." A gurguje Hajiya Kubra ta ciro, ta taimaka mun ta samun mayafi muka fito. Rashida ta bama izinin kula da yaran gidan da kokkon karin kumallo, kafin mu fita. Munsha ɗan karen tafiya mai nisan gaske. Sakamakon nera biyar da Bama magani, nayi tafiya har ƙafata nayi mun zugi. Gashi ko sallar asuba banyi ba. Muna isa gidan ɗorin muka tarar da layi har mutun uku. Da wata dattijuwa ɗaya, sai yara uku duk suna zaune a wani ƙaton falo suna jiran izini. Mu na zaune aka kawo mana fanke da ruwan lipton. Ni da Hajiya Kubra cin nama mu kai ma fankennan kafin kace kwabo mun lamushe muna siɗe man dake hannunmu. Muna zaune har layi yazo kanmu. Har fitsari sai da nayi a zaune dan azaba. An ɗorani irin ɗorin gargajiya wanda ake jera karere, ya bani wasu garin magunguna na sha, yace bayan sati biyu mu dawo a kwance mini. Godiya mu ka yi mai, muka dire mishi atampar da muka tawo da'ita. Da zazzabi kau a jikina muka shiga gidan, ina shiga na kwanta na shiga rawar sanyi, kafin kice kwabo na soma suma kala_kala. Ciwo nake har bana iya gane wanda yake kaina.
"Hajiya Kubra ki kira mun Mamana in zan mutu in mutu a kusa da wani na." Wayata Hajiya Kubra ta kunna tai ma Mama flashing, ba a jima ba kuwa ta biyo kiran. Hajiya Kubra tayi mata bayanin halin ciwo da nake ciki da karyewa da nayi. Mama tace sha Allah gobe zata biyo jirgin safe ta tawo."
MRS BUKHARI CE
[13/08, 1:11 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(,DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B ( GIDAN ƘAMSHI)
39
Kaduna:
Mama.
Zirga_zirga Mama ta shiga yi a tabkeken falonta na sabon gidan da suka koma. Tana goye da Maryam yarinyar Musa a bayanta. Ta gama jibgar yarinyar kenan kiran Zubaina ya shigo wayarta. Dama kwana biyu cir tana kiran wayar tata sai ta ji ta a kashe. Wayarta ta ɗauka ta kira Nafisa. Ringin ɗaya biyu wayar ta shiga.
"Nafisa so nake ki biya mun jirgin Lagos, daga Lagos in hau jirgi zuwa Ghana. Zubaina bata da lafiya ta samu karaya a hannunta, ko magana bata iyayi, kishiyarta ce tai mun bayanin halin da take ciki. Mijinsu kuma ya tafi kasuwanci." Nafisa tace.
"To shikenan Mama bani nan da awa ɗaya zan sa a gama miki komai. Zuwa gobe sai ki tafi. Allah ya bata lafiya, zan kira inji jikin nata. Muma muna shirin tafiya misra kenan, akwai wani semina da Alh zashi can. Uwar gidanshi ma taso ta kunno wuta, kan cewar sai dai itama wannan karon a tafi da'ita. To da yake na samu wajan zama a zuchiyar Alh Mama kar kiso kiga diban albarkar da yayi mata. Har wanke ta da mari yayi a gabana." Shewa Mama ta saka tace.
"Shegiya ba, ai gwanda daya nuna mata matsayinki. Kar dai kiyi sake da bin malamai.duniyar ba'a zama haka. Ita kanta Zubaina zanje wajan sabon malamina yai mun aiki in kai mata, in yaso in na dawo na biya shi." Haka dai hirar tasu ta ƙare. Mama na kashe wayar ta saɓi tsadadden mayafinta, da tsadadden takalminta ta rufo ɗakinta, a