MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   35 / 67

102K to 105K   out of 198.3K words

da Aissa ya faru a kanta. Ina mai horarku da kuji tsoron Allah ku riƙe matayenku babu cuta babu cutarwa. Ku duba kuga irin zaman mutumci da muke yi da iyayenku, kuma ku kwatanta akan matayenku. Ku ji ƙansu ƴan uwanku ne, ku tausaya musu. Kuma ko bayan babu ku, sai Allah ya haɗa yaranku da masu jin ƙansu. Ko bayan ƙasa ta rufe idanuwanmu ku daure ku riƙe gidannan, kuma a dinga auren zumunci domun haɓaka zumunci. Dan mutanen wannan zamanin sun yi ma zumunci riƙon sakainar kashi. Hamma da Hewa sun matuƙar bani mamaki, amman babu komai." Tarin shi na tsufa ya soma yi, Ba Modu yana yi mai sannu. Gabaki ɗaya jikinmu duk ya mace, dan duk ranar da Ba Bakura ya yi batun mutuwa, duk sai mu shiga tashin hankali. Hajja tace.
"Modu kwana biyunnan ɗan uwanka baya samun bacci ishasshe, numfashinshi sai inji yana fita sama_ sama. Tunda Bulama Babba yazo, ya kamata a kaishi asibiti a duba lafiyarshi. Ni kaina duk na bi na shiga damuwa, da irin halin da yake ciki. Ba Modu yace.
"Bakura akwai inda yake yi maka ciwo a jikinka ne" murmushi yayi kawai yace.
"Sai ciwon tsufa wanda ko wanne tsoho ke fama dashi, shi kuma mutuwace kawai maganinshi. Baya ga wannan babu abunda ke damuna. Sai rashin baccin dai da ban samu ba, shekaran jiya zuwa jiya, shine kawai. Amman ina haɗiyar ƙwayar bature kullum, ko rabi ma ban sha ba. Yaushe_yaushe muka je ka kaini asibitin.?" Dubana yayi yace.
"Kai ya Yahanasu da yaran suke?" Kai na sosa ina ɗan murmushi nace.
Suna lafiya, amman ita bata ji daɗi ba, taje asibiti amman yau. Ina hanya ma ta kira ni. Wai ciki ne da ita" Kaina na sauke ƙasa. Gabaki ɗaya falon suka yi kabbara, zukata su ka ɗau sanyi. Ba'a daɗe ba kab gidan ya ɗauka Yahanasu na da juna biyu. Ni dai ina faɗa na gudu masauki. Bayan sallar Magriba, Dala ya raka ni muka zagayo ƴan uwa, aka gaggaisa, bani na shigo gidan ba sai wajajen sha ɗayan dare. Washe gari da sassafe na shiga haramar tafiya. Wani ƙunshin baƙar leda Hajja ta bayar tace a ba ma Yahanasu. Haka ma Ya Innana ta bani ƙatuwar keda itama tace a kaima Yahanasun. Ni kuma na ba Ba Bakura dubu ɗaya, ba Modu dubu ɗaya. Iyayenmu mata na bisu da ɗari biyar biyar. Matan ƙannena na bi ko wanne ɗaki da ɗari bibbiyu nace a sayi omo ai ma yarana wanki. Ba'akaka da Wakil ne suka raka ni tasha, har sai da motarmu ta tashi sannan suka tafi suma.




YAHANASU:
A daren jiya, bacci kasa ɗaukata yayi fur, sakamakon bansha komai ba, idanuna na jisu a soye, sai zafi da ƙaiƙayi da suka dame ni dashi. Haka naita faman juye_ juye, yanda naga rana haka darenma ya kasance mun. Da asuba kuwa na tashi da matsanancin ciwon kai, ko idanuna bana iya ɗagowa. A daddafe nayi aikace aikacen yau da kullum wanda suka zame ma ko wacce mace jiki. Muna gama karyawa, na zura ma Maryam kayan makarantarta, Bawa ya saka nashi, ya ɗaukar musu lunch box ɗinsu. Nima na ɗauko jakata na rufe ɗakina, naima matan gida sallama muka fita. Sai da na biya ta makaranta na ajjiye yara, ni kuma na wuce wajan aikina. Haka dai aikin ya kasance mun babu daɗi. Har na baro office muka nufi ɗorayi gidan wata uwar marayu domun tattaunawa da'ita. A daddafe dai muka gama program ɗin, ya ɗauke mu awa guda. Office muka sake komawa. Sai ƙarfe biyu muka tashi.
"Yau na ganki sukuku, idanunki sunyi jawur, akwai wata matsala ne Yahanasu?" Kai na girgiza nace.
Ba komai kaina ne kamar zai tarwatse dan ciwo. Gabaki ɗaya komai kika ga inayi ƙarfin hali ne kawai."
"Kina da laka mis ɗin shine har ciwon kai ya addabeki kuma? Yau tunda kika zo aiki banga kin kora komai ba" Shareta nayi bance da'ita komai ba. Ɗan sahu ɗaya muka hau da'ita dan itama zata je kasuwa cefane. Ni kuma zan siyo kayan meat pie da kunun zaƙi. A kasuwar muka rabu bayan mun gama siyayyar da zamu yi. Ina shiga gida na shiga aikin kunun zaƙi bayan na haɗa niƙa na miƙa cikin gida, sai na leƙa gidansu Uwatale ƙawata, tana siyar da goruna. A tsakar gida na sameta tana ƙirga ma wata mata goruna.
"Umman Maryam yau kece a gidan namu? Lallai za'ayi ruwa da ƙanƙara yau" Dariya nayi ma Uwatale inayi ina dafe kaina da nake ji kamar zai faɗi ƙasa. Uwatale ta soni sosai da ƙawance, takan shigo wajena da yamma haka. Amman ni sau ɗaya na taɓa zuwa gidanta, data haifi yarinyarta, shima tare da matan gidanmu muka shigo, sai kuma yau dana shigo. Tun tana ƙorafin harta dena.
Kai Uwatale, wato za'ayi ruwa da ƙanƙara ma ko? " Itama dariya tayi mun tace.
"Sau ɗaya kika zo gidannan, shima tare da su Maman Hassan. Ni har Abban su Fatima na sanarma, nace mishi na lura kamar cusa kaina nake yi gareki, ke bakya so. Shi yasa kika ga kwana biyu na ja baya dake" Baki na buɗe nace.
Wallahi ba yanda kike tunani bane Uwatale, abubbuwanne sai adda'a kawai. Ga hidimar iyali, ga zuwa aiki. Yanzun ma niƙa kunun zaƙi na miƙa cikin gida shine fa nace bari in zo wajan ƙawata in sai goruna" Hararata tayi tace.
"Ba wani aiki ke dai baki yi niyyar yin zumuncin dani bane" Hararar nima na mayar mata nace.
Naji ƙorafinki, zan gyara in sha Allah. Yanzu dai ki bani robobi dozin biyu, dozin ɗaya manya, dozin ɗaya ƙananu." Sai da ta sallami matar da take ƙirga ma gorunan, sannan ta ƙirga mun nawa gorunan ina daga zaune. Sai da muka taɓa hira kafin nace.
Zan tafi gida sai na sake shigowa" Tace dani.
"Ai kuwa nagode sosai, duk da ba takanas danni akazo ba, amman nagode. Kuma zan sa Khalifa ya shishshiga maƙota ya sanar musu kina kunun zaƙi Muma kullum in Abbansu ya dawo yana aikawa can shagon ɗan fulani a siyo mana. Kinga ma dinga siye a wajanki, matan gidannan namu ma, da zaran yamma tayi zaki ga suna aikawa a siyo musu abun sanyi.
MRS BUKHARI
[07/08, 9:43 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
28
































Sai da Uwatale ta raka ni har zaure, mu kai sallama na koma gida. A lokacin ne naji kaina kamar zai tsage mun, wani irin amai na taso mun. A guje na ƙarasa kwatar data raba tsakar gidan, na dinga amai, ina jin kaina da tsigar jikina suna bubbuɗewa. Matan gidanmu suka taru a kaina. Daga masu cewa ta tabbata ciki ne dani. Sai masu yi mun sannu. Da ƙyar na tashi na shige ɗaki, bayan na tace ƙullin kunun zaƙi na. Laka mis na buɗe na shanye gora guda na yar da gorar a tsakar ɗakin, a wajan na sulale ina kuka. Ke nan haka rayuwata za tai ta tafiya, duk ranar da ban sha wani abun ba, babu zaman lafiya?" Na kai kamar minti talatin a zaune a wajan, a hankali na dinga jin kaina yana daidaituwa. Jin hakanne yasa na fita a ɗakin na ɗauro alwala nazo nayi sallar la'asar. Sannan na koma tsakar gida bakin aikina. Ina haɗa kunun zaƙi, ina girki. Ina gama haɗa kunun zaƙin na kai firji dan yayi sanyi sosai, na dawo naci gaba da aikina. Shida da hamsin na fito wanka a gurguje, dan Bulamana ya kira ni, sun shigo gari, yana hanyar dawowa gida. Sai da aka kirayi sallar isha ya shigo niƙi _niƙi da kaya. Da sauri na tarbeshi, yara suka isa gareshi a guje, ya rungume Maryam tsam a jikinshi, yana shafa kan Bawa da ɗayan hannun nashi. Ni kuma sai Murmushi nake yi ina musu kallon sha'awa.
"Bulama ka shigo ne?" Muka jiyo Muryar Ahmad a ƙofar ɗakinmu.
"E yanzu na shigo, kaya na shigo ajjiyewa, naji ana kiran Sallah." Dubana yayi yace.
"Bari in je masallaci, kafin in dawo ki zuba mun ruwan a bokiti zanyi wanka" Yana faɗar haka ya sauke Maryam ya fice shi da Bawa. Taburma babba na baza mana a tsakar gida gefen ɗakinmu, dan ɗakin in ba wutar nefa bane akwai, baya iya shiguwa a zauna a ciki. Gashi tunda aka shiga wannan zafin suka soma hanamu wuta. Kayan abinci na ajjiye, ina shirin zama kamar wasa aka soma shigowa siyan kunun zaƙi, kowa na son jiƙa maƙoshinshi da abun sanyi, dama Hajara ta aika yara sun shisshiga maƙota sun sanar. Haka masu sayen pure water ma sai shigowa suke suna siya a wajan maƙociysta Wani yarone yazo siyan kunun zaƙi na shiga ɗakko mishi kenan Bulamana suka dawo daga masallaci, ganin kayan abinci akan tabarma yasa ya zauna. Ina fitowa naga ashe sun dawo. Yaron na miƙa ma kunun zaƙin da canjin shi.
"Kice har an soma cabkar kuɗi?" Dariya nayi mishi, na nemi waje na zauna nace.
Har nayi ɗari uku da hamsin, ga kunun zaƙin har wasu sun soma yin ƙanƙara, firjin yana da ƙarfi sosai, ni har mamakin ƙarfinshi nake yi, a haka kuma yaji jiki sosai. Muna cin abinci, yana labarta mun yanda akayi da Ba Hamma. Nayi mamaki matuƙar mamaki. Bulamana yace.
"Ai wannan mamakin kowa ne yayi shi, ba mu kaɗai ba. Amman ita Aissan ta gaji da Wakil ɗinne, gara data nuna mishi halinta tun wuri, yarinya ɗaya ce a tsakaninsu. Da yayi wannan maganar sai na tari numfashin shi da cewa.
Yauwa dama ina son in tambayeka, yaushe zaka je ka dubo Yusuf ne? Ya kamata ka je kaga lafiyarshi, tunda su basu zo sunga lafiyar su Bawa ba, kuma ko a waya ba wanda ya taɓa kira da zummar yanason yaji muryarsu. Ƙanwar mahaifiyar tasu da take nan Kano itama bata taɓa zuwa ba" Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya ɗaga kofin dana zuba mishi kunun zaƙi ya kafa a bakinshi, bai cire ba har sai da ya shanye tukun.
"To nima jiya nayi tunanin zuwa ganin Yusuf, kawai sai naji ya faɗo mun inason in sa shi a ƙwayar idanuna. Mu bari zuwa ƙarshen wata in anyi biya sai in je in dubo shi. To ya Baby na yana lafiya ko?" Dariya nayi mishi, na shafa cikina tare da numshe idanuna, ina jin son cikin sosai a zuchiyata, ashe dama haka iyaye suke ji a lokacin da suke ɗauke da ciki?"
"Kin shiga tunani, kinƙi amsa ni ko?" Kafin in yi magana, Hassan ɗin Maman Hassan yazo siyan kunun zaƙi na nera ɗari. Bulamane ne ya shiga ya ɗakko mishi. Ahmad ya tuntsure mishi da dariya, dake suma suna zaune a ƙofar ɗakinsu.
"Ka zama me sayar da kunun zaƙi kenan kaima, gaskiya wannan ƙanwar tawa ta shanyeka da yawa Bulama" Dariya yayi mishi yace.
"In ban kula da'ita ba, dawa zan kula, ka mance laulayi take yi ne?" Dariya Ahmad yayi yace
"Ban isa in mance ba, kuɗin rago na wuyana ai. Kuma ina yi ma Walid kamu in macece ce" Haka dai sukai ta zolayar junansu. Kafin daga bisani Bulamana ya fuskanceni yace.
"Ga kaya Hajja, da Ya Innana suka ce in kawo miki, ni bansan ma kayan meye ba. Babbar ledar shine na Ya Innana"
Allah ya saka musu da alkhairi, ai kasa duk sun kirani, sai murna suke yi, ni kuma Kamar in nitse dan kunya wallahi, ai da baka faɗa musu ba." Murmushi yayi mun kawai, ya kakkafeni da idanunshi. Haka mu kai ta hirarmu gwanin sha'awa, kafin mu tashi a wajan kunun zaƙi ya ƙare har ana zuwa nema, kasancewar da sanyi sosai, kuma nayi shi da kauri dan ban bi riba mai yawa ba, albarka nake nema. Haka dai rayuwar tai ta turawa ahankali. Wata ranar juma'a na dawo gida a gajiye, gashi nasha wata ƙwaya da ban taɓa sha ba, kaina sai juyawa yake yi da ni, da ƙyar na iya kawo kaina gida. Ina shiga ɗaki jini ya ɓalle mun, take marata ta shiga jujjuyawa tana murɗewa. Tsugunnawa nayi ina nishi da ƙyar, hankalina ba ƙaramin mugun tashi yayi ba, take na shiga kuka wiwi domun na fahimci ɓari nayi. Da ƙyar na iya tashi na gyara jikina, maganin mayen da nasha yana kuma ɗibata. Kintsa jikina nayi na koma kan katifa na kwanta hannuna dafe da marata, hawaye sai bin kuncina yake yi. Wasa wasa ciwo yaci gaba da tsananta. Dole na kira Hajara da ƙyar nake magana.
Hajara ki taimaka ki kira mun Rabi nose da naga matan gidannan na kiranta. Marata zata fashe ki taimakeni". Ina kaiwa nan na fashe da sabon kuka.
"Sannu Yahanasu, subuhanallahi, Allah yasa dai ba ɓari kika yi ba. Bari in kira Maman Iklima ta zauna dake kafin in dawo" Da sauri ta fita. Bata jima da fita ba Maman Iklima ta shigo. A lokacin na kusan fita daga hayyacina bibbiyu uku_ uku nake ganinta. Daga hakan ban sake ma sani inda kaina yake ba. Farfaɗowa nayi cike da matsanancin ciwo, da zubar jini sosai. Rabi nose ta dubu Hajara tace.
"Cikin jikinta ne ya zube, ga jini na zuba a jikinta ni ina ganin kuje asibiti mafi kusa zaifi. Ko Asibitin Dr Bala ku kaita." Basu yi wata wata ba, suka taimaka mun na miƙe suna riƙe dani, jini duk ya ɓata katifar da nake kwance a kai, ya ɓata mun jikina. Hijabi na zura a jikina na tuɓe kayan daya ɓacin na sake wasu, tare da yin ƙunzugu. Jikina sai wani ɓari yake yi,sanyi na ratsani. Haka suka riƙe ni muka je ɗan kemis ɗin Dr Bala inda anan matarshi take duba marasa lafiya, harma ta basu gado in ta kama, amman ba'a kwana a wajan. Sun buɗe wajanne domun taimakon marasa ƙarfi. In sun dawo asibiti sai su buɗe kemis ɗin dan duba marasa lafiya da siyar da magani. Kwanakin baya ma a nan Uwatale ta haihu. Muna isa Dr Hauwa tana ganinmu ta riƙe ni.
"Lafiya me ya same ta take zubar da jini haka?" Hajara a tsorace tace.
"Rabi nose ce ta turo mu nan, tace ɓari tayi jini ya ɓalle mata." Dubana ta yi da kyau. Bata ce komai ba ta shigar dani ɗan ɗakin da a ciki suke kwantar da marasa lafiya. Gadaje biyu ne jol a ciki. Taimakon gaggawa tayi mun, tamun wasu allurai, tare da bani wasu magunguna nasha. Take jinin da nake zubarwa ya dai dai ta sai dai cikin har zuwa lokacin yana murɗa mun.
"Nace akwai wata ƙwayar bature da kika sha wanda ba likita bane ya rubuta miki, misali maganin ciwon kai, maganin mura, da sauransu? Domun irin wannan jinin da kike zubarwa yayi yawa. Ko dai maganin zubar da ciki ma kika sha ne, ko ƙwayar maye. Ina mijinki inason yin magana dashi gaskiya" Hankalina in yayi dubu ya tashi, a tsorace na dubeta, itama ni ta zubama idanu tana karantar yanayina.
Likita babu abunda nasha wallahi. Ki rufa mun asiri dan Allah, wallahi ban sha wani abu dan cikina ya zube ba, inason abuna ƙaddarace wacce ta riga fata" Wani kallon banza tayi mun, ba tare da tace komai ba ta fita a ɗakin. Kuka na fashe dashi, hankalina a tashe yake ainun. A cikin wannan halin barci yaci ƙarfina. Bani na farka ba sai wajajen goman dare. Bulamana yana zaune a bakin gadon da nake, ya zabga tagumi ni kawai yake kallo. Ina buɗe ido dashi na soma tozali. Hawaye ya soma bin gefen fuskata. Hannayena dukka biyun Bulamana ya riƙo cikin ƙasa da murya yace.
"Haba Yahanasu menene ma abun kuka dan kinyi ɓari, ina kuma ga masu renon cikin tsawon wata tara su yi naƙuda, amman ɗan yazo babu rai fa, su me zasu ce? Addu'a ya kamata mu yi akan Allah yasa hakan shine mafi alheri a gare mu. Allah ya bamu wanda ya fi wannan" Ƙarfin guiwa naji sosai, kuma na tabbatar likita bata faɗa mai wani abun ba. Ajjiyar zuchiya na sauke a hankali nace.
Su Ya Innana sun sani?" Kai ya gyaɗa mun yace.
"Sun sani, tun ɗazu Ba Bakura yake kira yaji ko kin farka ma. Bari in yima Likita magana, dan tace kina farkawa zamu koma gida, ina zuwa ko?" Fita yayi da hanzari, na bi bayanshi da kallo, ina fargabar kada likita ta faɗa mishi wani abun da zata jefa zuchiyarshi a doron zargina. Amman abun mamaki har muka baro kemis ɗinnan wannan likitan bata faɗi wata kalma guda ga Bulamana ba, dangane da tambayoyin data mun farkon zuwan mu. Ahankali nake tafe Bulamana yana riƙe da hannayena. Matan gidanmu duk a tsakar gida muka tarar dasu, yayin da wasu ke hira, wasu kuma bacci ya kwashe su. Muma a tsakar gidan muka ya da zangon mu. Sai gaisheni da jiki suke yi, tare da yi mini adda'ar samun wani rabon da gaggawa. Su Ya Innana ne suka yi kiran waya, haka na dinga amsa ya jikin iyayena da ƴan uwana. Sai hawaye kawai nake sharewa dan fitar cikin ya mun ciwo, sakamakon shaye _shayen muyagun ƙwayoyi ya salwantar mun da farin ciki na. Nayi matuƙar nadamar shaye _ shaye a rayuwata. Kuma nayi ma kaina alƙawarin da zaran na samu ciki zan jingine komai a gefe ko da hakan na nufin tonon asirinane, inason nima inga jinina. Babban abinda ya fi komai tada mun hankali shine

35 / 67