MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   67 / 67

198K to 198.3K   out of 198.3K words

mugun kyau, taci wani lace mai mugun kyau, fuskarta tayi sawai, gashi ta saka humrar dana bata. Ahmad sai wani kallonta yake yi yana murmushi yana wani liƙe mata ( in kema kina son mijinki ya dinga niƙe miki ya zamar miki ɗaye manna to ki neme ni) ita kuma sai sakar ma Khairat harara take yi. A wajan mu ka ci mu ka sha akayi hirar nishaɗi. Yara su ka ji daɗin su. Dab magariba muka nufi gida. Washe gari har daki Hajara ta biyo ni tace.
"Jiya na tsugunna a kan turaren tsugunnon nan da kika bani Yaha, hmmm in ana sallah ba'a magana wallahi har kyautar dubu goma Ahmad ya bani, ke a liƙe muka kwana ko ya na motsa zai dawo dani jikinshi, na yi amfani da wannan turaren kwanciyar da humrar matan Aure. Gaskiya wannan setin duniya ne, ya kamata ko wacce mace ta mallaki nata. Shi yasa ku Kanuri da shuwa mazaje suke liƙe muku aita ɗaukar hakkin ku ana cewa asirine, ashe gyaran shedkwata kuka fimu iyawa" Dariya ni ta bani ma sosai. Ƙarin bayani na yi mata ( kina son mallakar naki setin? To ki tuntuɓeni ki yi booking naki) Da daddare ina kwance lamo a bayan Bulamana na yi matashin kai da gadon bayanshi. Hawaye nake tsiyayarwa wannan rashin samun rabo yana damuna ainun. Amman ita rayuwa bata taɓa rabo da ƙalubale. Idanu na lumshe bacci yayi awon gaba dani cike da maharkan jarirai baƙaƙe masu kama da Bawa .






Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen wannan labari. Sai Allah ya sake sadamu a cikin wani sabon littafin zaku jini ba da daɗewa ba in sha Allah.


Masu siyan setikan turare kuma ina maraba daku nagode sosai masoyana.


Yahanasu tana miƙo saƙon gaisuwarta ga masoyanta tana barar adda'arku Allah ya bata rabo da Bulamanta. Ba Modu kuma har yanzu yana nan gadagau dashi cikin ƙoshin lafiya

67 / 67