MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   65 / 67

192K to 195K   out of 198.3K words

ki sani baki isa ki kawo mana bare ba, gara tun wuri ki sallameshi dan ba zamu aura mishi ke ba in dai nine a matsayin wa a gareki. Ɗakin ki zaki koma, ya kamata ki tausayama yaran ai ko Yahanasu suna bukatarki nasan kin san komai, so kike sonki ya halaka ni, a gabana kike ma wani namijin kallon soyayya, ko dan kin zama tauraruwa shine kike ganin kamar kin fi ƙarfina ko, sabida kinga al umma ke suke son ji da gani?" Fuu ya fice, da sauri na bi bayanshi amman kafin in fita Ahmad ya ja motar fuuu sun bar ƙofar shagon. Kaina na dafe da yake mun mugun ciwo, to ni ya akeso in yi da raina ne, Hajja bata sona kallon ƴar iska ƴar shaye_shaye take mun, gashi tana ganin kamar ni na kashe mata mijinta, har abada bana jin zata dena mun wannan kallon gara in yi aurena nima in huta kawai" Haka kwana biyu na kasance sukuku, Mama Gana sai aukin tambayata take yi inai mata ƙaryar aikine yai mun yawa a wajan aiki. Shi kuma Bulama Babba ya shiga aikin sintiri a tsakanin shago da gida ya hanani yin saƙat, ko yaita kira na a waya, da yaji number busy shikenan zai ta turo tesa_tesai na soyayya. Ga Alh Nura shima kullum a cikin tarairayata yake a waya, duk da dai bamu sake haɗuwa ba, amman kullum yana kirana sau biyu a waya, bama waya mai tsayi sai dai yana zube mun kalamai masu tsaiwa a kahon zuchiya. Ko bikin Ahmad ban je ba, Hajara dai tazo ƙunshi da gyaran jiki shago. Bayan bikin da sati uku Yalewa ta haifi ɗanta Namiji, ban je barka ba, amman na kira Bulama Babba nayi mishi barka, na kira ƴan Damaturu suma nayi musu barka, Hajja da ƙyar take amsa gaisuwata tsabar jin haushina da take yi. Ranar suna na fito cikin sauri inason fita wajan aiki na tarar da Mama Gana a falo tana zuzzuba mun turarukan wuta a kwalabe.
"Har kin fito agogo sarkin aiki? To zo ki zauna mu ɗan tattauna Bulama Babba ne ya kawo mun ƙararki." Gabana ya yanke ya faɗi dawowa nayi a sanyaye na zauna.
"Yahanasu nace ashe samari kike tarawa a shagon naki dama ni banda masaniya?" Da sauri na ɗago na dubeta da mamaki nace.
Samari kuma Mama Gana, ni wallahi bana tara samari"
"To Bulama ne ya ce wai kina tara samari a shago, ya kamata in miki faɗa, shi shine maɗaurin aurenki bazai bari ki auri bare ba. Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba kamar zai yi mun kuka anan. Kishi ya gama rufe mai idanunshi ainun. To mu dai ba zamu hanaki auren bare ba, amman mu munfi son ki auri ɗan gida zancan gaskiya kenan. Akwai maza a cikin gidannan, ga wasu a Damaturu ya kamata ki basu dama su bayyana kansu. Sabida zaman haka bazai yiwu ba ni kuma ko Hajja ta sakko tace Bulama ya mayar dake. Wallahi Allah bazan yarda ba ni, sai dai ayi duk abunda za'ayi ai taci mana mutunci ƙiri_ƙiri muna gani. In akwai wani bare da yake zuwa wajanki ki dakatar dashi kawai tun wuri zai fi miki, anan gidan nawa ma kina da miji ai kin sani sarai yana sonki. Ki tashi ki tafi. Bazaki sunan matar Bulama bane ko kema kishin ne? Ƴan Damaturu suna hanya" Ɗan dariyar yake nayi kawai nace.
Zan zo in na baro ma'aikata labaran safe kawai yau zan gabatar." Adda'a ta bini dashi harna ƙule. Ina tafe a mota ina mamakin Bulama Babba, so yake in ta zama kenan ni kar in yi aure haka yafi so ko? Da ace yau daya rabu dani bai yi wani auren har yayi ma mace ciki ba, da nima sai in zauna in iyaye suka ga zamu tsofe ba auren sa dawo mana da aurenmu. Ni nasan wannan itace ƙaddarata a sakamakon ƙin karɓar ƙaddarata da nayi, ya Allah bazai jarabceni ba? Da banyi shaye_shaye ba nayi imani da yanzu ina gidana ina farin ciki, da yanzu nice na haifama Bulamana yaro. Kukane yaci ƙarfina.


MRS BUKHARI CEGAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 60
















Sai da nayi kuka ishasshe sosai sannan na share hawayena na shiga ma'aikata domun gabatar da labaran hantsi. Haka dole na ɓoye damuwata na soma ragargazo labarai ina yi ina jinjina irin yadda ƙasarmu ta lalace da tsadan abubuwa, masara wannan kuɗinta ya ninku, ga kayan miya yayi tashin gwauron zabi, al'umma sunfi ta'amali da bushasshe a halin yanzu fiye da ɗanye. Minti arba'in na ɗauka ina labarai kafin na ƙarƙare na fito. Yau ban tsaya ɓata lokaci ba sam shago na wuce bayan nayi cike_ciken takaddu a wajan aiki. Wata mai jego nai ma gyaran jiki, zuwa azahar muka kammala, na bar shagon za'ayi mata ƙunshi da kitso, ni kuma na nufi hanyar gidan Bulama Babba. Tun safe su Fanna suka kirani suna sanar dani isowar tasu. A bakin wani kanti na tsaya na durzarma jariri kaya masu kyau guda uku da takalmi, nera dubu arba'in da hudu na kashe musu sannan na kama hanya. A babban falon gidan na tarar da ƴan uwana an baje anata tiƙar hira. Ƴan uwan mai jego sai kai komo suke a tsakankanin ciki da falo. Cikin ƴan uwana na ƙule na saki jiki muna ta hira kamar bani da damuwar komai. Amman a baɗini ji nake kamar in fasa ihu. Ana cikin haka Ya Bagulaji ta fito falo in da muke, zamanta ke da wuya aka biyota kici_kici da abincinan suna. Fried rice su ka yi da coslo, sai tuwon shinkafa miyar egusi da ganda, sai kuma biski da miyar taushe, banda lemukan gora da ruwan gora, ga sobeniya da suka yi na jaka shaƙe da tarkace, buhu ɗaya aka bamu an san yawa ne damu ga haɗin kai, ɗaya bazai yi amfani dashi ba in ɗan uwanshi bai samu ba. Sai da aka ƙirgemu tas. Ni dai ruwa kawai nasha, banci wannan abincin sunan ba. Bayan sun kammala na ja Fanna ta raka ni wajan mai jego. Hamshaƙiyar dana ganta tsurewa nayi, har wani mugun zazzaɓine ya rabkeni lokaci guda. Tayi kyau gaskiya sai dai maƙiyi gata fata irin ingarmun matan Kanuri, tasha adon lace da ɗan ƙaramin gwal a wuyanta. A daddafe ta amsa gaisuwata ni dai nayi barka muka fito, sai wani harararmu take yi tana yatsina. Ni dai nasan a yanzu nafi ƙarfin yatsinar fuskar wata mace, danni a cikin kanurin ma ƙamshina ya fita daban, ƙamshina ya na kwana biyu a waje in dai na shiga na zauna ƙyan fata kuwa baza'a nuna mini ba, sai dai a fini farar fata. Kayan dangin miji muka soma haɗawa a falon. Sai da akayi mata turamen zani kala arba'in, kayan yaro kuwa ba'a magana, sabulu omo jingim haka famfas ma. Surukan gidanmu ne suka ɗauka Ya Bagulaji da Ya Gaji suka jagorancesu wajan kai kayan ciki, a hannun manya suka danƙa kaya sai son Barka. Muna zaune su Bulama Babba suka shiga tare da su Bulama ƙarami, da su Ahmada. Tsakiyarmu suka shige anata hira. Ni da Bulama Babba sai kallon_kallo muke aikama da juna na tsantsar soyayya. In nace bana tausayinmu nayi ƙarya, Bulama Babba ya rame sosai a kullum baya cikin walwala da nutsuwa sam, baya rasa nasaba da rashin zaman lafiyar da suke yi da matarshi, da kuma rashina a kusa dashi. Haka dai mu ka gama suna aka watse, wajen motata Bulama babba ya biyoni yace.
"Yahanasu wallahi sau ɗaya tak na kusanci Yalewa shima rabon yaronnan ne yasa har na kusanceta, a daren da abun ya faru ji nayi kamar in ban kusanci mace ba mutuwa zanyi. Sai naga ai bani da zaɓi daya wuce in kusanci Yalewa ko ba komai ai matatace. Amman naga kin ɗauki fishi dani, babu macen da ta'isa kai ki matsayi a rayuwata. Na soki kuma da sonki zan koma ga mahaliccina. Ki ma Allah ki dena ƙona mun zuchiya ta hanyar sauraron Alh Nura. Ni dai ban iya ce mishi komai ba, a wajan na tafi na barshi ya saki baki yana mamakina. Ni da Alh Nura abu sai gaba yake yi, tun bana damuwa dashi harna soma, tun bana jin sonshi har na soma ji dai, daga haka soyayya ta ɓalle a tsakaninmu. Ana cikin haka muka tashi da mummunan labarin Bulama Babba yana asibiti Yalewa ta farke mai ciki da wuƙa ta tsallake ta gudu gidansu, shi kuma yana babban asibiti rai a hannun Allah. Ranar munji tashin hankali bana wasa ba. Kan kace me ƴan Damaturu suka ɗau motoci suka nufo Yobe. Ni da Mama Gana da yaranta mu muna asibitin, anƙi barinmu ma mu ganshi. Ahmad ne da Hajara suka kawo shi asibiti, sai da suka kira ƴan sanda tukunna aka yadda aka karɓeshi. Har dai su Ba Modu suka iso ba'a shiga ɗakin da Bulama Babba yake, bamu san a wanne halin yake ba. Ba Modu yana hawaye yace.
"Wakil kaini ɗakin ganawa da likita muji shin mutuwa yaronnan yayi ne suke ɓoye mana ko yaya? Ke kuma Hajja ki sani sai nayi shariya da wannan yarinyar ke in ma ta kama harda ke zanyi shari'a baki isa kin ka an kashe mun yaro ba.."
Wakil ya kama hannun Ba Modu suka tafi ganin likita Ba Modu sai haki yake yi. Nan Mama Gana ta dinga ma Hajja jaraba ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Ana cikin haka Ba Bature ya ƙaraso shi da Hewa. Muna nan jigum muna jiran me kaje kazo. Su Ba Modu ma basu samu damar ganawa da likita ba. Ni dai adda'a kawai nake yi. A firgice wani Dr ya fito daga cikin ɗakin da Bulama Babba yake. Gabaki ɗaya shi muke kallo, Ba Modu kuwa harya ƙarasa in da yake. Buɗar bakin Dr yace.
"Baba ayi haƙuri"
Wani irin zabura nayi na isa gaban likita nace.
Me kake nufi da ayi haƙuri mutuwa yayi ko me?"
"Ku kwantar da hankalinku, aiki zamu shiga dashi yanzu, Baba kaine zaka sa mana hannu ko waye? Amman fa sai kun taya shi da adda'a dan da ƙyar bawan Allahn nan yayi rai" Ajjiyar zuchiya na sauke, hajja kuma tana gefe sai kuka take yi Ba Bature na rarrashinta. Ba Modu ya shiga yasa hannu a takaddar aiki suka fito.
"Wakil inaso kai tsaye ayi magana da lauyoyi a shigar da kara kotu, dole mu ɗau matakin shari'a, da yanzu wannan abun yazo da tsautsayi shikenan yaronnan da mutuwa zaiyi lokaci ɗaya? To wallahi bazan yarda ba, yanzun ma ai kunji abunda likita yace, cewa fa yayi ba lalle ya tashi ba." Ba Bature yana jin haka yace.
"Modu kai mun rai dan girman Allah. Wallahi ni bazan so hakan ta faru ba wannan abun duk na gidane, yarinya bata kyauta ba kuma zamu ɗau ƙwaƙƙwaran mataki akan hakan. Ku yi haƙuri. Hajja kuyi haƙuri dan girman Allah ban taɓa tsammanin ƙiyayyar da Yalewa take ma Bulama ta kai rabin haka ba." Da haka dai magana ta mutu da ƙyar duk da Ba Modu yace sai an ƙwato ma Bulama hakkinshi, haka muka wuni a asibitinnan, bayan an fito da Bulama Babba daga ɗakin tiyata zuwa ɗakin hutu, nan aka buƙaci za'ayi mishi ƙarin jini. Wakil da Ahmada ne suka ba da jininsu aka ƙara ma Bulama Babba. Ba Modu yai ta hidima da Bulama Babba, dan karewarta shi ke jinyar shi. Hajja kuwa sai kuka take tana roƙon a yafe mata a bisa sawa da tayi Bulama Babba ya sake ni. Ita tayi nadama, ita sai dai a dawo da aurenmu kafin ma Bulama Babba ya farfado. Ni kuwa nayi fur nace ai ina na riga nayi ma wani alƙawari na bushe idanuna. Ba Modu shi kuma yace babu mai yi mun dole a karo na biyu. Mama Gana tace nayi mata dai_dai , sai an ga Bulama Babba a cikin wani hali akeson ni in raɓeshi dan ayi amfani dani kamar yadda akayi a baya. Haka dai akaita jinyar Bulama Babba, yana farfadowa ya rubuta ma Yalewa takaddar sakinta, Wakil aka wakilta ya kai musu har Damaturu. Satin Bulama Babba shida a asibiti aka sallame shi, kai tsaye Ba Modu yace a wuce mishi dashi damaturu. Hakan ko akayi muka ɗunguma sai Damaturu, a turakar Ba Modu aka ajjiye Bulama Babba, sai nan nan Ba Modu yake yi dashi. Kunyar duniya ta ishi Hajja. Gashi Ba Bature ya turmushe mata kuɗaɗenta, wasu kadarorin ma ya sasu a kasuwa ya karɓi wasu kuɗaɗe daga ciki. Sai Ba Modu ne ya biya kuɗin kadarorinta suka dawo hannunta. Wallahi kunyar wannan abun yasa ta kwanta jinya zanga _zanga, a lokacin Bulama Babba ya warke fes yana shirin komawa Yobe, ni kuma soyayya muke ci da Alh Nura sosai. Rashin lafiyar Hajja ya ɗagama kowa hankali dan harta soma barin wasiyya."








MRS BUKHARI CE[23/08, 12:00 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: Gawurtattu uku
61




Kaduna:




Kofur Zubaina:
Yau da safe na shirya na koma asibiti domun duba jikin Mabaruka. Jikin babu laifi na same ta a zaune tana shan tea. Bayan mun gaisa da Mama sai ta bamu waje, a gefen gadonta na zauna.
Ya jikin Mabaruka inata zuwa amman kina halin da baza ki iya gane wanda yake kan ki ba" Buɗar bakin Mabaruka tace.
"Ki matsa Zubaina kar in shafa miki cutar ƙanjamau ƴan uwana ciki ɗaya ma ƙyamata suke yi. Kinga yanda rayuwa ta mai dani ko? Naki mai sauƙi ne Zubaina, ni ciwo yaci ƙarfina ba lallai bane in rayu. Zubaina ki nemi Bulama ya yafe miki da danginshi. Adam da Sagira sun yafe mun jiya da suka dawo dubani, naci albarkacin yarana." In banda kuka babu abunda nake yi, tsoron Allah ya sake shigata sosai na sake tsinkewa da lamarin duniya ainun. Ina asibitin har yamma, sallama aka basu tare dani muka je gidansu bani na baro gidan ba sai bayan isha. Ina komawa gida na jawo jaka na soma haɗa kaya.
"Wannan jakar fa Zubaina" Mama ta tambayeni.
Inaso gobe in Allah ya kaimu ne in je Damaturu gidan su Bulama in roƙi gafararsu da su yafe mun Mama, in da hali Mama ku raka ni dan Allah." Mama na share hawayenta tace.
"Zamu je dukkanmu Allah ya kaimu goben. Amman wannan kuɗi na gadon yarannan me kike ganin ya dace ace anyi dasu Zubaina kinga muna ta zara?" Jim nayi mata nace.
Ina ga kawu Tanko zan je in danƙama ya dinga juyawa ana tarama yarannan riba, in ma bazai yi ba zai bamu shawara mama.
"Hakan yayi gaskiya dan Tanko mutum ne harda ɓari, to shikenan"
Washe gari.
Sassafe muka fice a gidan ko sallama ba mui ma Musa ba balle matarshi. Tasha muka nufa muka shiga motar Damaturu. Mun sha tafiya sosai, wajajen bayan azahar muka isa cikin layin su Bulama. Gabana sai faɗuwa yake yi, ji nake kamar ƙasa ta dare in faɗa ciki dan kunya. A mugun kunyace muka shiga cikin gidan. A falon mahaifiyar Bulama aka saukemu, muna zaune Bulama ya shigo da Sallama idanu muka haɗa dashi gabana ya yanke ya zube. Idanu ya bimu dashi kamar bai sanmu ba, shirin shigewa ciki yake yi Mama tace.
"Bulama wajanka muka zo dan Allah ka tsaya ka sauraremu" Cak ya tsaya, amman fa bai juyo ba. Ba Modu ne yayo sallama ya shigo falon, dan jiranshi akayi akan yana da baƙi. Waje ya samu ya zauna, Bulama ya juyo ya samu waje a ƙasa ya zauna. Yahanasu ta shigo da sallama hannunta riƙe da Bawa da Maryam Yusuf ne ya soma shigowa da gudu ya je wajan Ba Modu. Idanu na ƙura musu su ukun dukkansu. Itama ni take kallo ta kasa motsa ƙafarta ma.
" Uwata zo ki zauna. Bawa ga mahaifiyarku kuje gareta maza " Sakin yaran tayi suka zo wajena yace ma Yusuf ma yazo, ita kuma ta nemi waje ta zauna kanta a ƙasa. Ba Modu yace.
"Hajiya ina saurarenku" Mama tace.
"Yafiyarku mu ka zo nema a bisa kuskuren da muka aikata, ko kuma in kirashi son zuchiya. Domun duk wani alkhairi Bulama yayi mana. Mu kuma da sharri muka nufeku. Amman munga rayuwa, ku da ganinmu ba sai ance muku ba. Bulama ku yafe mana dan girman Allah. Mahaifinka da mahaifiyarka duk muna neman gafararsu a taimaka a yafe mana" Hawaye nake tsiyayarwa sosai. Ba Modu yayi gyaran murya yace.
"To babu komai. Dama ko da yaushe anason mutum ya gane kurenshi sai ya gyara. Naji daɗi da kuka tako zuwa neman gafararmu, domun kun yi mana zalunci sosai. Ta sanadiyyar auren ƴarki abubbuwa da yawa sun faru a cikin wannan zuriyar. Ni dai ta ɓangarena na yafe. Bulama uwata ku yafe musu kuma, ubangiji yana son masu yafiya da afuwa" Yahanasu tace.
"Ban riƙe kowa a zuchiyata ba Ba Modu. Amman duk da haka na yafe musu Allah ya yafe mana baki ɗaya. Nima in a zaman mu na zalunceki ki yafe mini" Bulama shima yace ya yafe mana. Mun nemi ganin mahaifiyar Bulama da Ba Bakura. Anan Ba Modu ya sanar mana rasuwar Ba Bakura. Hajja kuma bata da lafiya tana kwance a ciki. Da kanshi yai mana jagora har inda Hajja take muka roƙi gafararta ta yafe mana itama ba tai ko musu ba. Zuchiyata tayi sanyi sosai, sai naji kamar an sauke mun wani gingimemen dutse a kirjina. Kwana ɗaya mu ka yi a gidan washe gari muka yi azamar komawa. Ba Modu yace mu tafi da su Bawa su je su yi mun hutu tunda ana hutun makaranta, yai mana goma sha tara na arziki, har tasha yasa aka kaimu a mota akan in hutu ya ƙare Bulama zai je ya kwaso yaran."




Yahanasu:
Ina kwance a ɗakin Ya Innana wayata tayi ringin. Da sauri na ɗaga na yi tunanin Alh Nura ne, dan tun jiya ni dashi muke abu ɗaya. Wai Ba Modu ya kirashi ya bashi haƙuri akan

65 / 67