Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
ƙwarai irin Ahmad. Ko babu komai ya kwantar mun da kaso hamsin cikin kaso ɗarin damuwata. Ban gushe ba sai da nayi sallar nafila tare da roƙon Allah ya bani mafita, bacci nayi mai nauyin gaske. Washe gari na tashi da niyyar kama hanyar Yobe dan komawa bakin aiki. Ko da nayi ma Hajja sallama sai da ta tuna mun da batun zuwa gidan Kawu Bature, Yalewa na nan tana jiran isowata. To kawai na iya ce mata na ajjiye mata dubu ɗari a gabanta na fita. Su Bawa na turo mata nace suyi mata sallama in sun fito su sameni a garejin mota. Da wakil naci karo a tsakar gida yana nufar hanyar turakar Ba Modu. Tare muka jera dashi yana tambayata jikin na Yahanasu. Yaran gidan sai kallona suke yi, kafin in wuce sai da na rabama yaran gidan dubu ɗaɗɗaya, iyayensu kuma na basu dubu bibbiyu yaran suka kai musu. Wani irin girma na musamman matan ƙannen nawa suke bani, kuma hakan na da nasaba ne da yanda ƙannen nawa suka ɗaukeni da mahimmanci. A turaka muka samu Ba Modu shi kaɗai yana lazimi. A kusa dashi daf na zauna kamar yadda nake yi da a lokacin da bana auren Yahanasu. Kallona yayi cike da so da nuna kulawa yace.
"Ji yanda ka rame akan Yahanasu, ya kamata ka sassauta ma kanka, na ganka a cikin sabuwar damuwa" Bansan sanda na fara yi mishi bayanin yanda mu ka yi da Hajja ba. Murmushi kawai naga Ba Modu yana yi, yana girgiza kanshi. Wakil kuwa miƙewa yayi yanason ya bamu waje. Dubanshi nayi jikinshi duk ya mace nace.
Dawo ka zauna Wakil" Baiyi musu dani ba, domun ba tarbiyyar gidan bace. Ba Modu kallonmu yake yi yana karantar yanayinmu dukkanmu, can yace.
Mrs Bukhari ce[16/08, 9:05 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B (GIDAN ƘAMSHI)
46
"Dama da ganin take _ taken Hajja nasan wannan abunne zai biyo baya. Tunda Innana ta sanar dani kowa ya shigo mata banda Hajja. Duk da nasan tana takaba ne, amman ai Yahanasu tata ce, ko babu aure daya gibta a tsakaninku nayi imani zata damu da halin da Yahanasu take ciki. Ballantana kuma kai ke aurenta. Danginta na ɓangaran mahaifinta su suka zugata kan wasu al'amura bayan rasuwar Bakura. Wanda dani da'ita da Kawunku Bature muka zauna harda ma Hamma. Kan batun gidanmu da ake haya a ciki na waccan anguwa. To ni dai nasan gidan namu ne mu biyu da Bakura. Amman gudun matsala yasa na bar muku ku magada, domun Hajja tace bata amince ba, sabida babu shaida, kuma takaddun gidan da sunan mijinta aka saka. Ba zaku san anyi dukkan wannan abun ba, kuma abunda na lura Bature shine yake mata ingiza mai kantu ruwa. Dan rankatakab dukiyarta ta tuminin takaba, gidajen Bature ke kular mata dasu. Ni dai na ɗakko idanu na zuba, Bature ya kai mari ya kai gwauro a cikin gidannan. Hatta mata dake cikin gida basu da masaniya kan komai. Ni dai abunda zance maka kayi mata biyayya dan a zauna lafiya. Ko kusa bana fatan zumuncin gidannan ya tarwatse. Wannan dalilin yasa matan Baana na hana ko waccensu tafiya nace su share waje su zauna. Toh Bakura ya jaddada wasiyyarshi a gareni kan, lallai lallai in haɗesu dukka biyun in auresu. Nima da nayi wannan tunanin tun rasuwar Baanan, amman ganin cikinmu babu wanda ya samu nutsuwane yasa ban fitar da zancan mata sun sani ba. Amman yau nake shirin tunkararsu da zancan, in muka sasanta kanmu dasu, sai kuma iyayenku su samu labari. Ko bayan raina Bulama Babba ka kasance jajirtaccen uba a Cikin zuriyarnan. Kar ka bari ayi wasarairai da zumunci. Ashirin ga wata akwai taron ƴan uwa da aka saba yi, zamu ɗaura daga inda aka tsaya. Ku tashi ku tafi, Allah ya tsare maka hanya. Kai kuma Wakil sai ka dawo." Jikkunanmu a sanyaye muka fito dukkanmu. Sallama nayi da kowa, na samu su Bawa a gareji su da Ba'a Kaka, sai zabga mishi surutu suke yi. Shi kuma ya biyesu sai dariya yake faman yi musu. Hannu na miƙa ma Ba'a Kaka, cikin girmamawa ya miƙo hannunshi muka gaisa.
Yaya iyalan naka kowa lafiya ba wata matsala ko?" Kai ya sosa yace.
"Ba komai Bulama Babba, kowa yana lafiya. Yanzu ma aka kwashe kab yaran gidan zuwa makaranta, shine na tsaya a wajan su Bawa muke hira. Murmushi gajere nayi mishi, kana na shiga mota. Kowa ya ganni yasan ina cikin matsananciyar damuwa babba. Wakil ne ya tura su Bawa mota, dubu bibbiyu Ba'a kaka ya basu. Wakil kuma ya basu ɗari biyar biyar. Har sai da na ɓace na daina ganin hannayensu da suke mun adabo dashi. Cike da tunane_tunane kala_kala na ƙarasa ƙofar gidan Ba Bature, nama mance da zancan zuwa gidan umman Ahmad kan batun Yahanasu. Kaina yayi zafi da yawa, sai dai in na gama da nan in koma baya. A gefen kwatar gidan na ajjiye motata na fito, su Bawa suka fito muka shiga baki ɗaya. Suna tsakar gida dukkansu karyawa suke yi da kokko da ƙosai. Ba Bature yana ganina ya shiga washe bakinshi. Goggo Bulu tace.
"Me gidan da ba cefane yau kaine a gidannan? Rabonka da gidannan tun sanda uwarka ta zo da goyonka, sai yau kuma da Bulama Babba ya kawo ka. Ga kuma kishiyata Maryama ba. Dariya mu ka yi duka, kan ƙaton kafet ɗin da suke nima na hau. Kokko da ƙosan dake gaban Ba Bature ya turo mun, bakinshi cike da kokko yace.
"Bismilla sha Bulama Babba. Su kuma saji da yaran. Banyi musu ba naja kwanon ƙosan gabana naci biyu, na kora kunun. Sannan muka shiga gaisuwa.
"Zaina yaushe kika shigo Damaturu? " Zaina yar Yalewa ce, itama batai aure ba. Ma'aikaciyar banki ce a bankin FCMB dake hijar Yobe. Acan take da zama ta kama gida, sai dai ta kawo musu ziyara. Mai sunan Hajja kuma tana karatun mastars dinta a jihar Borno, ƙanwarsu ce itama batai aure ba, sai ƙaramarsu Yana ita kuma digree take haɗawa a fannin kasuwanci. Zaina tace.
"Jiya nazo, yau da yamma zan wuce. Ya jikin Yahanasu kuwa? Kwanaki dana zo Ba Bakure yake sanar dani taɓin hankalinta." Yaƙe nayi nace.
Ayya, jikin da sauƙi, jiya ma muka je dubota da yaran duka. Goggo Bulu tace.
"Allah ya bata lafiya. Ka shiga daga falo Yalewar wanka take yi, inta kintsa zata sameka a ciki" Bance uffan ba na miƙe nabi umarninta zuwa cikin madaidaicin falonsu, wanda yaranta suka cika mata tab da kayan alatu. Zama nayi a saman kujera ina karanta wasiƙar jaki. Nafi minti talatin a zaune kafin Yalewa ta buɗe labule ta shigo. Idanu muka haɗa, ta wani yamutse fuskarta kamar taga kashi, ko wani mugun abun. Doguwace Yalewa sosai, fara sol da'ita kamar ba Kanuri ba, gata da gashi irin na matan Kanuri, maganar diri kam in yana yawa to yayi mata yawa, akasarin matan ƙabilar Kanuri Allah ya azurtasu da kyakkyawan zubi da tsari ta ɓagaren jikinsu dama fatarsu, sai dai basu cika kyau ba, kuma da wahala kaga farin Kanuri. Gogaggiyace sosai riƙaƙƙiyar mace wacce ta zama minista a gidansu tsabar girma. In ban yi kuskuren lissafi ba Yalewa zata kai shakara talatin da bakwai shekarun haihuwa. Sanye take da baƙar lafaya mai adon jan zare. Tayi kitson gaba irin na al'adunmu. Waje ta samu nesa dani ta zauna. Ƙur na zuba idanuna a nata ina ƙare mata kallo, gami da karantar yanayinta. Da dukkan halama ita kanta tursasa mata akayi saurarata kamar yadda nima a kaimun. Ni ina ma zan kai wannan tsohuwar guzimar.
Tunda baki da bakin gaisheni ni bari in gaisheki. Ina kwana?" Kallona tayi rai a haɗe tace.
"Baƙin gaisheka nayi ba, ina shirin yin hakan ka katse mun hanzari."
Kinsan dalilin zuwan nawa ai, dan nasan Ba Bature yayi miki bayanin abinda suke son ƙullawa. Duk da ni bani da ra'ayin haɗa matsayin Yahanasu da kowa. Amman sabida iyaye da gudun rushewar zumunci dole in amsa umarninsu. Amman ke ta ɓangarenki meye ra'ayinki game dani da kuma auren? Kar ki cuci kanki ta hanyar kasa faɗin abunda ke ƙasan zuchiyarki. Ki sani Aure ba abun wasa bane. Kuma Hajja tace babu mai yi miki dole, in banyi miki ba ki sanar tun kafin tafiyar tayi nisa." Zuba mata idanu nayi ina karantarta.
"Zahiri ni ban taɓa jin ina ra'ayin ƙulla wata alaƙar data wuce ta zumunci a tsakaninmu ba. Da ace kayi mini, ko kana daga cikin zubin mazajen da nake buri. Tabbas da ita kanta Yahanasu da bata same ka ba, tunda a gabanmu suka taso. Tun a jiya da Hajja ta kira tana sanarma da Ba Bature zuwanka. Ban ɓoye musu komai ba, ba kai mun ba. Kar azo ayi abunda duk rai bazai yi daɗi ba. Aini a ganina aurena sai babban mutum sosai wanda ya ƙara rabi akan shekarunka. Kuma ina nan akan bakata, babu wanda zai mun auren dole. Ina da wanda muka gama maganar aure dashi, da zaran ya dawo umara zan gabatar musu dashi." Wani daɗi da farin ciki ne ya ziyarceni, harma ya kasa ɓoyuwa a fuskata. Zama na gyara na dubeta ina ɗan dariya nace.
Kin kyauta, lallai kina son zumuncinmu yaci gaba da ɗorawa, nima zan yima Ba Bature bayani ta yanda zai fahimceki, suyi haƙuri ki auri wanda kuka yi alƙawari kawai. Na kuma gode da baki yi wani rufa_rufa ba." Dariya itama tayi mun tace.
"Haba da wayewata zan tsaya a tauye mun hakkinane? Ai aure dole hatta a addinance bai dace ba, ballantana a zamana ce. Mastas gareni fa, ma'aikaciyace ni tsawon shekara goma ina cin gumina."
Hakane kam. To Allah yasa mu dace. Ni kam zan kama hanya, sai in na kuma shigowa garin kuma" Tare da'ita muka fito faram_faram. Ganin mu hakan ya ƙara ma Ba Bature ƙarfin guiwa. Sai bayan da muka keɓe a waje nayi mishi bayanin da ita Yalewa tayi mun, nan kuma ya gintse fuskarshi, har yana dakatar dani a zafafe.
"Kar ka faɗamun maganar banza Bulama Babba. Ita uwar taka abunda ta turoka kenan kayi, jin ra'ayin Yalewa? Alhalin ni mahaifinta na zaɓa mata mijin da yafi dacewa da'ita. Ko so kake ka nuna ma duniya modu ne kaɗai yafi kowa a duniyar ka mutunci?" Kaina na sauke ina jimamin wannan sabon lamari dake shirin yi mana kutse cikin zuriyarmu. Haƙiƙa Ba Bature shike zuga Hajja kamar yadda Ba Modu ya sanar dani. Bazan taɓa auren Yalewa alhalin nasan ba sona take yi ba, gata da buɗaɗɗen idanu. Mace me buɗaɗɗen idanu ta shani harna warke." A fili kuma nace dashi.
To ni zan koma Ba Bature, duk yanda kuka yanke da Hajja ni mai yin biyayyane a gareku." Murfin motata na buɗe na shiga, su Bawa suna bayan mota a zaune. Ficewa nayi daga anguwar na dawo da baya zuwa gidansu Umman Ahmad. A gindin bishiyar mangoron dake tsskiyar gidansu na sameta a zaune a tabarma. Ta tarbemu cikin girma da karamci, Mahaifiyar Ahmad akwai kirki da son mutane. Harna tuno sanda nake biyo ma Ahmad zuwa makaranta. Kullum sai ta ƙulla mana gyaɗa a leda ta bamu nera bibbiyu. Bayan mun gaisa ne na sanar da'ita maƙasudin zuwana wajanta.
"To Bulama Babba, sha Allah zanje yau ba sai gobe ba, zanyi magana dashi Modun. Duk yanda mu ka yi zan bugo maka waya. Yaya jikin na Yahanasun amman?"
A jikin da sauƙi, tunda har ta gane mu ma da muka je. Banji ɗuriyar Zulai Amarya ba Umma." Umma tace.
"Au Zulai ai tana Yobe jiya taje, Hajara tace taje ta zauna a wajanta, satin bikin sai su rankayo su dawo. Zan sake yi maka godiya da kayan ɗaki da kayi ma Zulai Allah ya saka da Alkhairi.
Haba umma Zulai ai ƙanwata ce, me yasa zaki ta godemun ne, ni banaso Umma. Sai anjima ma." Dariya tayi tace.
"Ɗan nema kamar ba jiya_jiya kake shigowa neman Ahmad hanci du majina ba, ga hawaye kullum a idanka." Dariya nayi sosai. Kullum sai Umma ta yi wannan maganar, sai dai in banzo dubata ba. Kuɗi na ajjiye mata a gabanta, nayi mata salllama. Tuwon madara ta ƙullowa yara a leda muka yi mata sallama muka fito. Gidan mahaifiyar Hajja Fati naje nayi musu ta'aziyyarta kamun na kama hanyar Yobe kuma. Yaran kawai na ajjiye a gida, na juya na samu Ahmad a kamfani. A kujera na kwanta hannuna dafe da kaina. Da sauri Ahmad ya iso inda nake yace.
"Kai karfa kaje ka halaka kanka a banza, ka sassauta ma kanka. Zama yayi a kujerar dake gefena yace.
"Ya kuka ƙare da Yalewa?" Labarin yanda muka yi na bashi. Cikin zolaya yace.
"Yaushe Yalewa zata yarda ta aureka baƙiƙƙirin da kai, ga shegen jan ido, kai hatta dasashinka fa baƙine" Dariya mu ka yi dukkanmu, duka na kai mishi ya kauce a hanzarce.
Wallahi nima a zuchiyata haka nace. Gata kyakkyawa son kowa. Ina ni ina samun irinsu, ai wannan sai mijin novel. Yanzu da a novel ne, ina zuwa zata ruɗemun. Allah na tuba mummuna dani yaushe zan ruɗa Yalewa, ai ni ɗin na Yahanasu ne kawai. Ko Zubaina son duniyane yasa ta aure ni, har ga Allah nasan kyanta yafi ƙarfin ace nine mijinta. Shi yasa ma ta garani." Ahmad yayi dariya harda buga ƙafa yace.
"Kai dai ka tsorata da mata masu kyaune kawai, amman Zubaina bata fi ƙarfinka ba tunda kaga har ta aureka. Da iliminka da degree dinka kace ƴar talakawa tafi ƙarfinka? Haba kar ka ba da maza mana. Gara Yalewan in kace tafi ƙarfinka kana da hujja mai ƙarfi." Nan mu ka shiga hira muna dariya kamar ba ni ba. Ahmad ya rage mun zugin abubbuwa da dama. Ƙarfe huɗu da rabi muka bar kamfani. Kai tsaye muka nufi ɗayan gidan namu da akeyin gyara. Saura kaɗan ya rage a kammala gyaran, komai yayi kyau. An farfasa ɗakunan an jonesu. Ɗakin Yahanasuna ciki da falo, da bayan gida. Nima nawa haka, sai ƙaton falo a tsakiya wanda anan kitchen yake da ɗakin yara, da ɗakin wasansu. Ɓangaren Ahmad ma haka tsarin yake. Ga filin tsakar gida yalwatacce. Ta baya akwai babban B Q, sai sai wani ɗan fili da aka malala jan kafet.
"Kaga nan yara nake son a zuba ma kayan wasan yara su lilo da sulu haka." Na dubeshi nace.
Banda ɗakunan wasan da suke dashi a ciki?"
"Wancan ɗakin karatune haɗe da wasa ai. Zasu fi sakewa a tsakar gidan ai" Haka mu kai ta zagaye a cikin gidan. Abinda ya rage filasta ne, sai fenti, da kuma kayayyakin cikin bayan gida da tails ɗin ɗakunan da za'a sake. Haka lamura su kai ta tafiya. Umman Ahmad taje ta samu Ba Modu tayi mai magana. Amman haƙona bai cimma ruwa ba. Dan Ba Modu kirana yayi a waya yai mun tas. Ta ɓangaren Hajja kuwa ta buɗe mun wuta sosai akan batun Yalewa tace dole ko muna so ko bama so sai anyi bikinnan. Sannan ta bani umarnin in dinga zuwa gidan Yalewa zance. Al'amura duk suka bi suka cuɗe mun. Har wata uwar rama nayi. Ranar da naje Damaturu ɗaurin auren Ba Modu da matan Marigayi Ba Baana, ranar Hajja ta tusani gaba ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
"Ni dama na san dole Modu ya mallakeka kamar yadda ya mallake mahaifinka. Komai ya kwaso Modu, Modu dai. Ko kai baya maka son da yake ma Modu. Kuma ai auren Yahanasu da aka baka da biyu ne. Wata munaƙisa Modu ya ƙulla shi yasa. Dan haka baku isa ba daga kai har Modu, ina dai _ dai da kowa a cikin gidannan. Aure dai sai an yi shi". Haka na koma Yobe cikin damuwa. Har kwanciya nayi a gadon asibiti jinya mai mugun tsanani ta kada ni. Hankalin ƴan Damaturu duk ya bi ya tashi. Na jima ina jinya kafin daga bisani aka sallameni. Nanma ban tsira a wajan Hajja ba. Bugomun waya tayi take cewa dani.
"Da ace ka yarda kayi auren ai da ba Ahmad, da Wakil bane zasu dinga kwana da kai a asibiti ba. Ka sa sun baro matansu sunzo sun tare a asibiti. Na ji likita yace hawan jinine yake son kama ka. Sabida wannan dalilin zan sa Bature ya ɗan jinkirta batun aurenka da Yalewa zuwa wasu ƴan watanni. Amman kafa sani babu wani makawa aure babu fashi." Idanu kawai na lumshe na sauke wayar a kunnuwana. A hankali jikina ya soma warwarewa harna koma bakin aikina. Kullum inna farka naga babu Yahanasu a gefena, da damuwa nake ƙarashe wunin ranar. Duk da dai alhamdulillah jikin nata da sauƙi nima na gani. Allah _Allah nake yi watan ya kai ƙarshe, dan inga Yahanasu in kuma nuna mata gidanta yanda aka gama komai hatta da sutura na jibge mata a wadrope, na sai mata dogayen abayoyi na ijib da aka kawo mana tallarsu har kamfani.
YAHANASU:
GIDAN FARFAƊO DA RAYUWAR MASU SHAYE_SHAYE:
Idanuna na runtse hawaye na ambaliya a kumatuna. Haƙiƙa zuchiyata cike take tab da nadamar rayuwar dana tsinci kaina a ciki. Ni kaina bazan iya cewa meye mafarin abunda yasa nayi watsi da tarbiyata ba, na faɗa cikin kogon da babu mai iya fiddani ba. Yau nice a gidan mahaukata, kullum a cikin uƙuba da duka nake, bayana duk ya farfashe da bulala, ko zaman kirki bana iyayi tsabar irin yanda ake azabtar damu. Ba kayan maye bane suka fice mun akai kaɗai ba. Hatta rayuwar da nake yi ta fice mun a raina, bazance ire iren gidajennan basu da amfani ba, domun na zauna tsawon wata biyar, kuma na samu