MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   34 / 67

99K to 102K   out of 198.3K words

ne kawai bata yi ba. Wasu hawayene suka sulalo kumatuna masu ɗumi. Wata nadama ce ta shigeni sosai.
Mrs Bukhari ce
[07/08, 9:42 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
27


*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*


























Tare da taraddadin in na mutu a cikin wannan halin me zan ce ma Allah, ya iyayena zasu ɗauki wannan abun, daga ranar da asirina ya tonu, ya Bulamana zai kalleni daga ranar da wannan ɓallin zai ɓalle, yarana da wanne ido ni zan kallesu? Ƙila ma a haukace zan ƙare, duk wannan abubbuwan bazan gansu ina cikin hayyacina ba.
"Hajiya mun zo fa" Muryar mai ɗan sahun da nake ciki ta doki dodon kunnuwana. Cikin rashin kuzari na fito na zaro kuɗinshi na bashi. Duk wanda ya kalle ni yasan nayi kuka. Da na shiga gidan babu wanda na yarda na haɗa idanu dashi. Hajara na bakin ƙofar ɗakina a gaban wani deepfreeza babba, mai ruwan toka, amman da gani na hannune kuma ya sha jiki, dan har tsatsa ne a ƙasan shi."
"Kin dawo kenan Yaha? Ai ina nan tun tuni ina ƙarema wannan firji kallo. Gaskiya Bulama ya gwngwajeki, Allah ya baki miji mai zuchiya ba mai dukiya ba." Wani farin ciki ne ya lulluɓeni kamar wacce aka biya ma umara. Nan na shiga washe bakina ina dariya. Matan gidan duk suka rufu ana taya ni murna. Ahmad ne ya shigar mun da shi ɗaki, na kuwa yi sa'a da wuta. Mintuna kaɗan da shigar mun na kunna, na jejjefa pure water a ciki. Allah sarki Bulamana akwaishi da ƙoƙari dama shi haka yake tun yana ma yaro, yana mugun son ɗan uwa, ballantana ni da na zame mishi uku a ɗaya( 3 in 1 ) Ƙanwa, ƴar uwa, mata. Gahi ina shirin zama uwar ƴaƴanshi. Cikina na shafa ina farin ciki, na kalli tumbina a raina nace. Yanzu nasan ina haihuwa tumbina zai ƙara girma, ƙila har ƙiba in ƙara tunda ni mai jikin ƙiba ce. Sai na tuno da Fanna sanda ta haihu, sai da ta ninka ƙibarta ta da sau biyu, ga tumbi, ga kumatu. Har yanzu kuma tana nan da ƙibarta bata sauka ba. ( Amman ina tunanin in kira Maman Amal in sai constifree tea na kamfanin G H T maganin rage tumbi sadidan, harma da ƙibar. Sannan ta haɗamun da female care domun ya tado mun da komaɗata, tunda in mace ta haihu tana rasa abubbuwa da yawa. Kuma magungunan G H T ingantattun magungunane da aka samar dasu daga itatuwa. +234 703 777 8458 ga number ta ga me buƙata.) Duk da nasan irin tanadin da Kanuri suke ma mai jego wajan gyaran matantakarta abun sai son barka. Amman hausawa suka ce kogi bai ƙi daɗi ba. Da rana garin kwaki da ƙuli na jiƙa mana da ruwan sanyi. Na shinfiɗa mana tabarma a tsakar gida, dan zaman ɗakin bazai yiwu ba sabida zafi aka shiga, kuma ya sauka da ƙarfinshi sosai. A tsakar gida nayi sallah, nan na kishingiɗa bacci yai awon gaba dani. Sai la'asar Hajara ta tasheni tana zolayata.
"Shi kuma wannan na sa bacci ne kenan, tun ɗazu sai sharara baccinki kike hankali kwance." Murmushi nayi mata. Na yunƙura na miƙe. A nan na kuma yin sallar la'asar, daga nan na soma haramar ɗaura abincin dare. Ina tsaka da yin girkin ne Bulamana ya kira ni. Da sauri Bawa ya ɗakko mun wayar. Karawa nayi a kunnena bayan na ɗaga.
"Hello barka da gidan Yahanasu Maman Hajja, yaya gidan da fatan saƙo ya iso miki ko?' Dariya nayi nace.
Yauwa barka da hanya, ina fatan ka sauka lafiya?"
"Ah lafiya ƙalau ina tasha ma ina jiran isowar Wakil, kinga yanzu na gama cin burabusko a tasha. Ya kinje asibitin, wata nawa suka ce?" Sai da na kyalkyale da dariya sannan na bashi amsa.
Sati takwas suka ce dani. Naji ma har an sa mata suna, to in Namiji ne kuma wa zaka saka?" Cikin dariyar farin ciki yace.
"Ba Baana zan saka in dai namiji ne, nima in yi mai takwaran da zan dinga tunashi da shi. To ya kika ga firji?
Hmmm firji yayi matuƙar kyau, harfa na kunna dan zumuɗi, kuma gashi yana aiki da kyau. Naji daɗi sosai Bulamana ubangiji Allah ya yauƙaƙa hannayenka duk abinda ka taɓa ya zama mai albarka. Nagode sosai " Da jin yanda yake murmushi na tabbatar adda'ar ta sanyaya zuchiyarshi.
"To sai a soma yin su kunun zaƙi da jinja ɗin da akeson a soma siyarwa. Rannan ina jinki kuna hira da matan gida kina cewa da zaki samu hali da kin sai firji dan cin kasuwar lokacin zafi da aka shiga. Shine ƴan kuɗaɗen da nake tarawa sabida komawa makaranta duk na ƙundume na siyo miki" Ji nayi Bulamana ya mayar dani tamkar sarauniya. Hausawa sunyi gaskiya a hikimar zance da suka ce, gaya ma mai zuchiya ba mai dukiya ba. Daga jin hirarmu a tsakar gida shikenan sai ya aiwatar da abunda yaji inason? Madallah da samun miji mummuna, mai kyakkyawar zuchiya, mai sauƙi, da faram faram. Godiya da adda'a na dinga kwararo mishi, har sai da ma ya gaji da amsawa ya kashe wayarshi.










BULAMA BABBA:
Girgiza kaina nayi, ina mamakin irin godiyar da Yahanasuna ta dinga ragargazo mun, tamkar wacce aka biya ma aikin Hajji.
Allah ka hore mun in biya ma Yahanasuna aikin Hajji, in siya mata dalleliyar mota" Ina cikin wannan taɗin zuchin na hango Wakil a cikin motarshi 4.0.7, miƙewa tsaye nayi, na biya yarinya mai abinci kuɗinta, Wakil ya iso inda nake ya karɓi ƴar jakata. Cikin sosa kai yace.
"Bulama Babba kayi haƙuri, wallahi kasan ƙarfen nasara bashi da tabbas, motar ce ta samu ɗan matsala, sai da na tsaya a gefen hanya na gyara." Hannuna na ɗaura a kafaɗarshi na ɗan jijjiga irin na wa da ƙaninshi.
Ba komai Wakil, ya ka baro su Ba Modu?" Tafiya muka soma yi dan kama hanyar gidansu Aissa. Sai bayan da motar mu ta hau kan titi wakil yace.
"Ba Modu suna lafiya dukkansu, kafin ma in fito sai da muka yi magana dashi, yana cewa in kai zuchiyata nesa duk abubda Aissa zata ce in dai ba'a bani damar magana ba karma ince komai. Sun ɗauki abun da zafi har Ba Hamma ya kira Ba Modu wai ranar litinin zasu turo mota ta kwashe kayan Aissa ɗin." Da sauri na kalli Wakil ɗin.
Har matsalar ta kai haka ashe, to wai meye yayi zafi haka a tsakaninku, ko dai ya wuce maganar ƙazanta ta yawan gantali ne?" Na tambayi Wakil tare da tsatstsareshi da idandunana.
"A'a Bulama Babba, akansu ne kawai. Kuma ni gajiya nayi da ƙazantar tata. Hatta ɗan kanfanta fa sai ta ajjiyeshi a bayan gida kaca kaca da jinin al'ada. Haka data haihu, kusan kullum sai na ga jinin biki, har amai nake yi, amman nayi mata magana taƙi gyarawa. Mu da muka saba da ƙamshi amman Aissa ko wacce kusurwa a jikinta tsami. Data haihu sai abun ya haɗe da ƙarnin nono. Ni gani nake yi ƙawayenta na wajan aiki suke hure mata kunne" Tsahirta maganar mu ka yi, dan mai gadi ya wangale mana get ɗin gidan su Aissa. Ba Hamma yana zaune a kan kureja a cikin baranda, ga shinfiɗu anyi da lallausan kafet a wajan. Cikin girmamawa muka isa gareshi. Rai a murtuke ya amsa mana gausuwarmu, ya nuna mana wajan zama, sai daddanna waya yake yi. Wayar ya kara a kunnenshi yace.
" ki tawo da Aissa ga Wakil da Bulama Babba sun iso. A kawo musu ruwa" Iyakar abunda yace kenan ya kashe wayarshi. Jim kaɗan sai ga wan Aissa Bukar da ruwan gora a tire. Hannu ya mimmiƙa mana aka gaisa kadaran kadahan. Bayan mun sha ruwa, sai ga Ya Hewa da Aissa sun ƙaraso. A kan idona ta watsama Wakil wata uwar harara, yayin da yake miƙa mata hannu akan ta bashi Yahanasu ƙarama. A cinyarshi ta dangwarar da yarinyar. A taƙaice aka gaisa, na soma magana.
Ba Hamma dama munzo ne game da batun Wakil da Aissa. Domun a sasanta tsakaninsu ta koma ɗakinta." Ba Hamma yace.
"Bulama Babba kenan, shi Bakuran ne ya aiko ka ko kai ka kawo kanka?" Kallonshi nayi a mamakince.
Ni nazo da kaina a matsayina na babban wa a gidan. Koma me ke tsakaninsu ayi haƙuri dai ta koma ɗakinta, ga zuria sun soma shiga tsakani, gudun kar zumunci ya samu tangarɗa." Gyaran murya yayi irin ta manya.
"Zumunci ya riga da ya taɓu. Domun nayi mamakin yanda Bakura a gabanshi Wakil yake horar da Aissa da yunwa, harma da duka in yaso. Amman ace ya kasa ɗaukar mataki akan Wakil. Ko ranar da yarinyarnan tazo mun cikin gidannan ga Bukar gashi, fuskarta a kumbure duk shatin yatsunshi sun kwanta a kan fuskarta. Kuma ta tawo Modu ko Bakura aka rasa wanda zai taso yazo cikin gidannan sai kai. Ai ko baiwace ita a gidannan bazan bari ta koma ba. Litinin za'a kwaso mata kayan ɗakinta aure a tsakankaninsu ya ƙare. Tunda kazo sai ka rubuta mata takaddarta ai." Cike da mamaki na dinga rarraba idanuna a tsakankanin Ba Hamma da Wakil, harma da Aissa ɗin."
Duka da yunwa a cikin gidan namu? Amman Ba Hamma aba shi Wakil ɗin dama ya faɗi abinda yasan ya haɗasu, ni nasan Wakil bazai doki Aissa ba, balle yai mata horon yunwa ba. Domun hatta maƙotanmu da suke da buƙata Ba Bakura bai barsu haka ba. Har gobe yana ɗaukar ɗawainiyar karatun marayun yara da marasa galihu da yawa. Aissa ai ƴa take a gidan." Bukar yace.
"Aissa ba zata yi mana ƙarya ba muma Bulama Babba, domun babu maƙaryaci a cikin gidannan. Nine babba a cikin gidannan kamar yadda kaima kake babba a naku gidan. Aissa ba zata koma gidanku ba, mu mun haƙura da wannan auren duka da yunwar. Dai dai da famfas bai san ya siyama ƴarshi Yahanasu ba, sai dai ita ta siya da kuɗin aikinta. Ko kuma ni in siya mata wata rana." Iya wuya na kai wuya sosai. Amman duk wuyan da na kai bai kai na Wakil wanda jikinshi har rawa yake yi ba. Idanuwanshi sun cika da hawaye tab. Na rasa ta cewa ni kam kaina ya ɗaure, nayi mamaki da iyaye basu cika bincikeba da zaran yara sun haɗo ƙarya da gaskiya sun ɗaura iyayensu a kai sai su hau. Soyayyar iyaye da yara sun rufe musu idanu, gani suke yaran basu iya ƙarya ba ma. Ni wanne kalan maɗe da munafurcin mace ne ban gani ba?"
"Na sake ta saki ɗaya. In ni na cuceta Allah ya saka mata. In ita ta cuce ni Allah ya saka mun. Bulama Babba muje" Furucin Wakil sun yi tsauri amman sunyi dai dai, ƙila a sasanta bayan wani lokaci in zukata su ka ɗauki sanyi" Ba Hamm ya nunfasa yace.
"Za kaci gaba da ciyar da Aissa da kula da lafiyarta har zuwa lokacin da zata yaye maka ƴarka. Zan turo a ɗebi kayanta." Jikinshi sai naga yayi sanyi, ita kanta Aissa ta yi laushi. Sai nayi amfani da wannan damar nace.
Ba Hamma, a bisa tsari na musulunci Allah yayi magana akan zaman iddar mace a ɗakinta, da fa'idar hakan. Gashi Aissa goyo take yi. Ni ina ganin ku daure ta koma ɗakinta ta zauna har sai in ta yaye ɗiyarta sai ta dawo. In kuma sun dai dai ta kansu falillahil hamdu. Kar mu ƙetare maganar Ubangiji dan baza mu ga da kyau ba. Wasu matan ma basa yin jini a yayin da suke shayarwa har sai sun cire yaro a nono. Wasu ma bayan sun cire yaro a nono su kan jima basu yi jinin ba. Kuma in dai mace ba ta wuci yin jini bane, dole sai ta yi wannan jinin uku shine ta fita idda. In Aissa tana daga cikin irin matan, tofa har sai ta yaye Yahanasu tayi jini uku shine ta kammala iddarta. Ratayayyen hakkine akan Wakil ya kula dasu." Jikin kowa yai sanyi a wajan. Ni kuma banma kuma cewa komai ba, na zuba ido in ga zasu sa ƙafa su shure gaskiya ne ko yaya.
"Aissa ki shiga ciki ki haɗo kayanki ki bisu, kije ɗakin ki ki yi idda acan. Umarnin Allah ne." Kuka ta fashe dashi wiwi. Mu kuma mu ka yi sallama dasu akan muna jiranta a mota."
Me yasa kayi saurin sakinta baka da hankali ne? Kasan in Ba Modu yaji zai ɗau fishi da kai, ni meye amfanina to?"
"Ba haka bane Bulama Babba. Aissa maƙaryaciyace wallahi ko kallon banza ban taɓa yi mata ba. Balle duka, ko barinta da yunwa. Store ɗinta a cike yake da kayan abinci fa."
Barta ai ta yaba ma aya zaƙinta. In kana son matarka a zaman iddarta sai kayi ƙoƙarin ku sasanta kanku. In kuma baka sonta shikenan in ta gama iddar sai ta tafi gidansu. Ba Hamma ya bani mamaki matuƙa," Wakil yace.
"Iddarta zata gama ta koma gidansu, ni kafin ta gama iddarma zanyi aure. In naci gaba da zama da'ita ƙila zumuncinmu ya rushe da ƴan gidansu ta sanadiyyarmu. Babban abunda Ba Bakura ya tsana kenan, shi yasa ya fi son ayi auren zumunci. Sai dai yana zuwa shima da nashi matsalolin. Ƙila ƙannenmu mata suma suna can suna fuskantar tasu matsalar a wajan mazajen nasu, ko mazajen na fuskata a wajansu." Aissa ce ta ƙwanƙwasa glass ɗin motar. Wakil ya fita ya saka mata kayansu a both. Ta shiga gidan baya sai runtuma kuka take yi. Ya Hewa na bata baki.
"Ki dena kuka kamar yau zaki gama iddarki ai ki dawo gida. Ƴan uwanki zasu dinga leƙo miki, in Zaina ta dawo hutu zan turo miki ita. Ki dena kukan hakanan" Da yare take mata magana, sai da ta matsa a jikin motar, naja motar mu ka fice a gidan. Ni nake tuƙin motar dan Wakil yana cikin damuwa mai girman gaske, dan yana son matarshi, auren soyayya su ka yi." Babu wanda yace da ɗan uwanshi wani abun. Na mayar da hankalina kan tuƙin da nake yi, Wakil kuma sai ajjiyar zuchiya yake saukewa kawai. Take Zubaina ta faɗo mun a raina. Nasan yanzu tana can tana jiran jini ya soma zuwar mata, domun ta gama iddarta, wani mai ƙarar kwanan shima ya kwasa. Gata da daɗin baki da yaudara, halayyarta ɗaya da mahaifiyarta. Su Nafisa na tuno dana dinga yi musu dawainiya, da kaisu manya manyan supermarket, in danƙaro musu siyayya, dan kawai in faranta ranta. Take naji inason ganin Yusuf, nasan yanzu yayi wayo sosai. Ɗan guntun murmushi nayi kawai na girgiza kaina. A haka muka isa Damaturu, na shiga gareji na ajjiye motar, muka nufi ɓarayin Ba Bakura, Aissa kuma ta wuce ɓangaren surukan gidan fuu da jakarta a hannunta, da ɗiyarta. A falo muka samu Ba Bakura da Ba Modu suna shan shayi suna hirar kasuwanci. Ganina yasa Ba Bakura ya gimtse fuskarshi, yayin da Ba Modu ya faɗaɗa murmushinshi.
"Bulama maraba da zuwa, har kun kammala kun dawo, ince dai an sasanta ko?" Cikin biyayya na gaishesu. Ba Bakura kadaran kadahan ya amsa mun gaisuwata. Anan na labarta musu duk yanda akayi. Salati suka ɗauka dukkansu, har da Hajja data shigo yanzu. Waje ta samu ta zauna tace.
"Yanzu yarinyarnan ƙazafin da za tai ma yaronnan kenan, a gidannan ai ko ƙadangarun da suke shigowa cikin ƙoshi suke, ballantana ita, meta nema ta rasa? Kuma shi Hamma haka akeyi babu bincike ba komai, yarinya ta faɗi magana ku hau ku zauna haka akeyi ne?" Ba Bakura nan ya shiga zazzaga ruwan faɗa akan sai da yace dama kar aje ai, amman Ba Modu ya goyi bayan lallai aje ayi sasanci.
"To ai shikenan, ni bazan ce komai ba. Kuma Hamma ya kyauta wulaƙancin da yayi mana. Yarinya in ka sasanta da'ita kaji zaka iya sake yin zaman aure da'ita to. In kuma ka haƙura shikenan daka nutsa sai ka tafi can gidan kawunku Bature, akwai ƴaƴa mata guda uku acan sai ka zaɓi wacce tayi maka. Ka aureta ku zauna. Yarinya kuma ta ajjiye maka abunka, iyayenka mata zasu riƙe. In ta tafi da'ita shikenan sai abar mata can ma gidane, sai kayi ƙoƙarin sauke nauyinta a kanka, ka kula da rayuwarta. Hukuncin daka yanke a wajan na sakin yayi dai_dai, dan sai an tauna tsakuwa aya ke jin tsoro. Dan Dala ya kawo mun ƙorafin matarshi kan irin zaman da suke yi. In tana son mijinta ta shiga taitayinta dan gudun kar abinda ya faru

34 / 67