MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   27 / 67

78K to 81K   out of 198.3K words

nake tunawa Mama, yanzu shikenan na haifi yara, wata banzar bazarace zata moresu harma ƙila asa su mance ni na haifesu? Ni kinji abinda ya dameni har ya hanani bacci mai daɗi. Amman ko ɗar bana ji dan na yar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda. Da sauran ƙuruciyata fa Mama, bari in gama goyo kiga motocin da zasu dinga mun sintiri. Ke dai sai na dawo, zan sai cin cin a layin dutse, ko in sai ƙosan wannan matar ta bakin layin sabo da Allah." Sallama nayi mata na fice. A zaure na haɗu da Sagiru ya bangaji kafaɗata ya wuce yana fito. Ba dan sauri nake yi ba, da zan tsaya muyi uwar watsi ni dashi, dan ba tsoronshi nake ji ba, a matsayina ta Kofur. Ina fita cikin layi,. Munafukai suka soma tambayata yaushe a gari, harda masu tambayar ina na baro motata. Babu wacce ta samu amsar abinda take son ji munafukai kawai. Ƴar ƙumbula na hau ta sauke ni a dai dai layin dutse dandali. Ta cikin layin na ratsa har zuwa makarantar malam sha rubutu. Almajirinshi yai mun iso har cikin gidanshi, wajan matanshi. Izini matar malam ta bani, na shiga ɗakinshi yana zaune akan buzu yana rubutu a jikin Allo.
"Meke tafe dake yarinya? Ki yi mun bayani ina sauraronki." Zama na gyara tare ta bashi labarin sakina da Bulama yayi da ɗanyan goyo.
Malam ni so nake in san yaya maganar iddata take, ni dai in ina shayarwa bana yin al'ada har sai yaro ya dena shan nono. To malam ya sake ni da ɗanyan jego ga shayarwa, yanzu yaya zanyi?" Malam sha rubutu ya dubeni da kyau yace.
"Haƙiƙa bai kyauta ba da ya sake ki da ɗanyan jego. Dan gane da maganar idda kuma, a zahirin gaskiya tunda ke yarinyar mace ce kina yin jinin ba wai bakya yi ba. Dole zaki jira har zuwa sanda zaki yi yayen. Tunda kina yin jinin bawai kin wuce munzili bane. Sai kinyi wannan jini ukun sannan zaki yi aure. Sannan ratayayyen hakkine a wuyan shi uban ɗanki ya ciyar dake sabida yaronshi ta jikin ki yake cin abinci, in bashi da lafiya shi zai bada kuɗin magani. Dan da so samu ne a ɗakinshi zaki zauna kiyi iddarki kamar yadda Allah yace, har sai kinyi yaye kin kammala iddarki sannan sai ki tafi gidan iyayenki kuma" Wata sassanyar ajjiyar zuchiya na sauke, domin har na hango irin gara Bulama da zanyi dan wallahi sai na gigita rayuwarshi da bani bani. Bazan je gidanshi in zauna ba, gashin kaina nake son ci. Godiya nai ma malam, tare da kawo ɗan abun hasafi na bashi. Office ɗinmu na nufa, naima D P O bayanin mutuwar aurena. Ya jajanta mun matuƙa, kuma yaji daɗin dawowa da nayi, sabida ina bada gudunmawa sosai akwai ni da jajircewa akan aiki. A ranar dai ban shiga office ba, sai gobe nake son komawa bakin aikina, in D P O ya gama tattaunawa da na sama dashi kan batun transpa da akai mun da. Kai tsaye na wuce gidansu mabaruka.
"Yanzu nake shirin kiranki a waya ƙawata. Hmmm aikin gama fa har ya gama. Yanzu na gama waya da Adam." Zama nayi daɓas a kujera babu kuzari sam a jikina, tunanina taya zan zauna a gida har na tsawon shekara ɗaya da rabi, ba tare da naji ɗumin namiji a kusa dani ba. Mabaruka tace.
"Adam yana son ya mayar dani ɗakina. Amman na bashi sharaɗin sai ya saki matarshi, ya turo mun da copy na sakinta, sannan zan koma kuma ya shirya mun kayan ɗaki. Ai ƙawata a ƙasa zan jashi tamkar yanda kare yake jan mushen nama".
Dakata Mabaruka naki duk mai sauƙine maganar kome kuke yi. Nifa sai na shekara ɗaya da kusan rabi zan yaye Yusuf sannan in jira in soma jini, shims Sai nayi wata uku, sannan kuma fa zan soma zance ayi batun aure. Ta yaya zan iya riƙe kaina na iya waɗannan lokutan ba tare da ana mun ban ruwa ba? Yanzu daga wajan malam sha rubutu nake, ina zuwa bari in kira Bulama in huce akanshi tukunna" Wayata na ciro a jakata na danna kiran layin Bulama amman harta tsinke bai ɗagaba, kuma kiranshi nayi ruri ɗaya zuwa biyu ya ɗaga wayar, ban jira yace komai ba nace.
Na raina saki biyun da kayi mun. Da ace ka haifu cikin Bakura da Hajjagana da saki uku za kayi mun, kaga ba kare bin damo. Sannan ka sani hakkin ci da sha, da lafiyata yana hannunka har zuwa lokacin da zan yi yayen Yusuf in gama iddata. Dan haka nera dubu biyu zaka dinga turo mun a rana. Sannan naji ta'asar da matarka tai mun kishi yasa ta bunkama gida wuta, babu abunda zance sai abinda kukai mun Allah yai muku." Murmushinshi yayi mun cikin ƙatuwar muryarshi mai kama da sautin duro yace.
Ke ma jahila kika san da wannan hakkin a kaina, ballantana ni mai sittin a kaina. Jahilci mugun ciwo, mai kashe rayuwa. Dubu biyu da kika yanka mun bazan ce zaki samu ba, dan ko kotu kika kaini sai alƙali ya soma da tambayar albashina. Zaki dinga ganin Alert na abinda ya sauwaƙa.... Ƙit ya kashe mun wayata, a madadin in bashi haushi sai shine ya cunkusamun baƙin ciki, yasa kwakwalwata ta cinkushe na rasa tunanin da zanyi. Kuka na fasa tare da ɗaura dukkan hannayena aka, kuka nake yi wi_wi tamkar zararriya. Da ƙyar Mabaruka ta dinga rarrashina harta samu kaina."


Yahanasu:
Misalin ƙarfe bakwai a tashar mota na anguwa uku yai mana. Bamu jima ba sosai motarmu ta cika muka ɗauki hanya. Kaina wani irin yam_ yam_ yam kawai yake yi mini, daidai da motsi ko hayaniyar Maryam da take cinyata, bugamun ƙwaƙwalwata yake yi. Kayan aiki kawai nake son in afa ko ƙwaƙwalwata zata barni in huta. Bulama Babba sai aikin sannu_sannu yake yi mun, a tunaninshi ciwo nake yi. Idanuna suna lumshe na jingina kaina a bayan kujerar mota, hannun Bulama Babba na gugann kafaɗuna, jikinmu a manne yake sosai, kuma naji zazzaɓi kau a jikinshi dan jikin yayi matuƙar zafi. Ana cikin haka wayarshi tayi ƙara. Ina jiyo duk abinda Zubaina ta faɗa mishi, da amsar daya mayar mata. Dukkan wannan abun da ke faruwa idanuna a lumshe suke.
MRS BUKHARI CE
MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
20
A cikin motar nan sai hira suke gudanarwa, yayin da wasu suke ta ciye ciyensu. Mu kuma a baya kowa yayi shiru tunani ya cika mana kayukanmu. A ɗan wani ƙauye muka tsaya dan gabatar da sallar azahar. Tun daga cikin mota na hango wani ɗan kemis ƙarami, ajjiyar zuchiya na sauke, dole in faki ido inje in siyo maganin tari.
"Miƙo Maryam ki fito Yahanasu, ki bi su Hajara gashi can mata na shiga cikin gidan masallaci suna Sallah. Bulama Babba ke mun magana daga ƙasa. Maryam na miƙa mishi, ni kuma na sakko a hankali. Muna haɗa idanu ya sakar mun ɗan guntun Murmushi, duk da da ganinshi a cikin matsala yake. Bakina yana rawa nace
Dan Allah in akwai kuɗi a hannunka ka bani"
"Me zaki yi da kuɗi? Cikin inda_ inda nace dashi.
Kaina ne yake ciwo zan sayi magani" Baice mun komai ba yayi tafiyarshi. Hannun Maryam naja nabi ayarin matan cikin motarmu zuwa cikin gidan masallaci. A zaune nayi sallah dan ji nake kaina kamar zai tarwatse mun.
"A masha Allah, Yahanasu an shiga ayarin ƴan laulayin ciki kenan. Allah ya raba lafiya" Hajara ce take magana tana washe mun baki. Da kallon takaici kawai na bita, na kama hannun Maryam muka fito, hannuna dafe da kaina. Mota na koma na zauna, hannuna dafe da kaina me barazanar tsagewa. A haka Bulama Babba ya shigo ya tadda ni.
"Ga nama da yogurt ki daure kici, sai ki sha maganin ciwon kan ko? Kawo Maryam ɗin Zulai ta riƙeta, kiji da kanki. Ɗaukar Maryam yazo yi, hannunshi ya gogi ƙirjina sosai. Wata guguwa ta taso mun daga kaina ta rufemun idanuna, sai kawai jin idanuna nayi a lumshe. Shi kanshi da halama baisan ya saki ajjiyar zuchiya mai nauyi ba. Zulai ya miƙa ma Maryam, sannan ya ɓare maganin ya bani na kora da yogurt. Bayan kowa ya shiga mota muka ɗauki hanya. Kowa a cikin motar nan sai da ya taɓa bacci, Amman ban da ni, dan idanuna sun bala'in soyewa har wani yaji yaji suke yi mun, duk sun ƙanƙance. Wajajen la'asar sakaliya muka shiga Damaturu, jefin shiddan yamma muka shiga cikin gida ni da Bulama Babba da yara. Ahmad yayi mana sallama zaije ya ajjiye Zulai da Hajara a gidan mamanshi. Ajjiyar zuchiya na sauke dana ji ƙafafuna suna taka farfajiyar tsakar gidanmu, zuchiyata cike da zabarin son ganin iyaye da ƴan uwana. Shi kanshi Bulama Babba naga wani irin annuri a fuskarshi, duk da dai akwai tsoro a tattare dashi, ni kaina inajin tsoro shin wacce iriyar tarba za'ai mana ne." Hango su Ya Innana nayi ko wacce tana zaune akan tabarma a ƙofar ɗakinta, suna wannan hirar tasu da suka saba, sai dariya suke yi.
"Oyoyo oyoyo Yahanasu Bulama kune tafe da yamma sakaliya haka? Cewar Ya Bagulaji kenan. Da sauri duk matan gidan suka juyo kowa ya zuba mun idanuwa. Muryar Ba Bakura muka jiyo a bayanmu yana cewa.
"Su waye nan a tsaye kamar Yahanasu?" Hantar cikina ce ta tattake ta kaɗa, da sauri muka juyo ni da Bulama Babba. Ba Bakura ne da Ba Modu, sai Hajja a gefensu, Bulama fari kuma yana riƙe da jakar Hajja da key ɗin mota da ganinsu unguwa suka fito. Kallon kallone ya shiga tsakaninmu dasu na wasu daƙiƙu. Bulama Babba yana kallon iyayenshi cikin so gami da nadamar duk abubbuwan da suka faru. Su kuma sunai mishi kallo mai cike da kewar ɗan nasu a kusa dasu. Ni kuma Ba Modu nake kallo, shima ni ɗin yake kallo, kallon tausayawa da lallashi. Ba Bakura ne ya katse shirun da cewa.
"Daga ina haka bagatatan ba sanarwa, da kunzo bama nan fa uhmm?" Turus dukkanmu mu kayi, Bulama Babba take ya soma zubar da ruwan hawaye, Bulama Babba sau ɗaya na taɓa ganin hawayenshi sai kuma yanzu. Dan ko sanda Kaka Yahanasu ta rasu, shine kaɗai bai zubar da hawaye ba, sai dai shine ya kwanta ciwon rashinta.
"Ku fice mun da gani, har Yahanasun. Tabi mijinta tayi biyayya, bana buƙatar sake ganinka. Modu ka tabbatar sun bar gidannan, ke kuma Hajjagana wuce mu tafi ciki." Jiki a sanyaye tabi bayan mijinta sumi_ sumi tana kuka. Ba Modu na kalla. Shima mu yake kallo a tsanake, matan gida kuwa kowa yayi tsit dan abun ba nasu bane."
"Yanzu sabida Allah Bulama me ya kawo ku cikin gidannan, kai da baka ƙaunar ganin danginka sun raɓeka? Ku kama hanya ku fita tun kafin dare yayi muku" Da sauri Bulama Babba ya isa wajan Ba Modu. Tsugunnawa yayi guiwarshi a ƙasa, amman ya kasa furta komai sai hawaye kawai yake zubarwa, tun yana hawaye har ya shiga kuka mai sauti, da ƙatuwar muryarshi. Hakanne ya jawo hankalin surukan gidan suka soma baro shashinsu dan gani da jin abinda ke wakana." Jikina a sanyaye naja ƙafafuna zuwa cikin gida.
"Ina zaki je Yahanasu, ba kiji abinda Babanku Bakura yace ba ko?" Ya Innana ce tayi maganar cikin sarewa.
Inason inga Ba Bakura ne kafin mu wuce" Iyakar abinda nace kenan, na shige ciki da sauri. Ko da nayi sallama ban jira an amsa mun ba na faɗa falon. Ba Bakura yana tsaye sai zazzagama Hajjagana faɗa yake yi. Ita kuma sai kuka take yi, ganina ne yasa duk su kai shiru. Zubewa nayi a ƙasa na kama ƙafar Ba Bakura.
Ba Bakura ka yafe mishi dan Allah, wallahi ba laifinshi bane sharrin azzalumar matarshi ne. Ba Bakura kai ka hore mu da yin haƙuri, tare da yin afuwa ga duk wanda ya nemi yafiyarmu. Bulama Babba wallahi yana buƙatar adda'arku, da yafiyarku ko dan yaga haske a rayuwarshi. Abubbuwa da dama sun faru damu. Yanzu haka gidan da muke ƙurmus ya ƙone bamu ɗauki ko tsinke ba a ciki, dai dai da suturar jikinmu ƴan uwa musulmai ne suka bamu." Ina kaiwa nan na kuma fashewa da kuka mai sauti, zuchiyata sai sake tunzura kukana take yi. Tsit babu wanda yayi ko da tari, sautin kukana ne kaɗai yake tashi a falon, na tsawon minti uku. Daga bisani Ba Bakura ya ja nunfashi, a sanyaye yace.
"Yahanasu ke kinsan komai da yake gudana a cikin gidannan, da irin watsar da mu da Bulama Babba yayi. Ga uwarshi nan kullum sai ta yi hawaye sabida shi, har da hotonshi take kwana, ta zaci ko ban sani bane ba. Hatta aiki da Bature ya sa aka bashi na gandiroba duk ina da labarin komai. Matsawar Bulama yana tare da matar shi, to ba zan yafe mishi ba." Cikin sarƙewar murya nace.
Ya saketa ma Ba Bakura, ko gobarar data faru bata gidan ta koma gidansu" Hajja ta miƙe da sauri tace.
"Alhamdulillah Allah na gode maka daka ƙwato mun ɗa na daga hannun wannan makirar azzalumar yarinyar. Allah kana ganin irin rikici da damuwar data haddasa a cikin wannan ahalin, Allah ka saka mana abinda tayi mana" Ba Bakura ya wani kalleta, babu shiri ta zauna. Murmushi yayi mata tare da girgiza kai, kallona yayi yace
"Na yafe mishi Yahanasu uwata amman da sharaɗi" sujudur shukur nayi a tsakar ɗakin ina kuka. Ba Bakura yasa hannu ya ɗagoni tsaye.
"Kukan yayi haka uwata, na yafe ma mijinki, amman ki sanar mishi ni bani da buƙatar ganinshi, bana son yazo inda nake. Allah yayi mishi albarka, kema Allah yayi miki albarka uwata kici gaba da haƙuri, naso ace zan iya cire kuɗi in miki wasu kayan ɗakin, amman kash bazan iya kashe muku ko sisin kwabona ba. Kuma na haramta a baku kuɗi ko wani taimako, ai shi jajirtaccene nayi imani zai kula dake, mun yi na mu, a cikin gidannan kullum a cikin adda'a muke akan Allah ya kuɓutar dashi daga hannun azzalumar matarshi. Duk juma's kinsan anayin sauka ayi sadaka nan ma kuna cikin addu'o'in mu babu dare babu rana." Godiya nayi ma Ba Bakura sosai a bisa yafe ma Bulama Babba da yayi, duk da banso sharaɗin daya gindaya ba, amman dole inyi mishi adalci, Bulama Babba yayi musu abinda ya cancanci fiye da haka, duk da ba cikin hayyacinshi yake ba, amman fa akwai zafi. Kuma babu wanda yaci dukiyarshi, sai Zubaina da danginta. Hajja ta rungumeni a jikinta tana jin wani tsananin farin ciki. Hannuna taja muka koma tsakar gidan. Dai dai lokacin da Bulama Babba ya kama hannun Maryam da Bawa suka juya zasu fita.
"Tsaya Bulama" Hajja ta faɗa da murya mai ɗauke da sautin farin ciki.
"Bulama fari ka shiga da su Bawa ɗakin Innana ko Bagulaji. Shi kuma wanku ka buɗe mishi ɗakin ka na da dashi da Yahanasu su sauka acan." Murmushi Ba Modu yayi yai mun kallon na kyauta kuma na burgeshi. Farin ciki naji sosai da naga farin ciki shinfiɗe a fuskar Ba Modu. Kan ka ce me matan gida aka soma nannan damu, matan su Bulama ƙarami kuwa kowacce sai tace ɗakinta zan shiga. Ni kuma burina shine su barni tare da Ya Innana mu ɗanyi taɗi irinna ƴa da uwa. Hajja tayi dariya tace.
"Yalewa ku barta da shiga ɗakin gyatumarta ta huta, duk zata biku ɗai_ɗai ku gaisa, uwata maza je kiyi wanka kizo ki kaiwa mijinki abinci" Kunya sai ta kasheni a wajan. Shigewa ɗakinmu nayi ina dariyar murna. Gyara naga anyi ma Ya Innana sosai an sake mata komai na ɗakin, ina tsaye ina santi sai ga bulama ƙarami, da Dala, da Wakil sun shigo suna tsokanata.
"Mummunar gidanmu kune a tafe? Munyi kewa" Cewar Wakil kenan sai dariya yake faman yi mun. Dala yace.
"Kunzo a dai dai ɗazu matar Wakil ta haihu mun samu me sunanki, suna asibiti ma. Daga wajansu su Ba Bakura suka dawo, sanda suka same ku a tsakar gida. Amman kowa yayi farin ciki da haƙurin da Ba Bakura yayi, wallahi muna kewar Bulama Babba sosai, ɓuya fa muka yi sanda yake kuka kamar ranshi zai fita." Bulama ɓaki yace.
"Tunda fa Ba Bakura ya soma fishi da Bulama Babba gabaki ɗaya gidan ya dena ma kowa daɗi, to Bulama Babba ai shine uba a gidannan." In banda murmushi babu abinda nake yi ma ƴan uwana, maganganunsu daɗi yake yi mun. Bulama Babba abin so ne ga duk wani yaro daya taso a cikin wannan gida. Domun ko wanne yaro ɗan gata ne a wajanshi. Barkar haihuwa naima Wakil cikin sakin fuska. Sai jana da hira suke yi. Lokacin sallah ne yasa dole suka fice zuwa masallaci, lokacin kuma Ya Innana ta shigo, kallon juna mu ka yi mu kai Murmushi ko wanne yana farin cikin ganin juna.
"Kin kyauta da kika kawo ƙarshen wannan turka turka, wanda duk a sanadiyyar aurenki kaso mafi yawa ya faru Allah yayi miki albarka. Ki shiga ki watsa ruwa sai kiyi Sallah. Harna wuce Ya Innana tace.
"Gobe kuke da niyyar komawa ne na ganku ba kayan sawa, kuma har yaran baku ɗebo musu

27 / 67