MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   39 / 67

114K to 117K   out of 198.3K words

in yaso in lokacin shigarshi makaranta yayi, sai ya dawo. Zuwa lokacin abunda kika haifa shima yayi ƙwari. Allah ya raba lafiya"
Ameen nagode. Amman dan Allah kar ka faɗa ma ƴan Damaturu, ka barsu kawai, in na juye abunda ke cikin nawa sa sha mamaki. Tunda a baya kaga abunda ya faru. Muita adda'ar Allah yasa mai zama ne" Yace.
"In zaman nashi shine mafi alkairi ba. Ai dukkan abinda kika ga ya samu bawa, to da sanin Allah, kuma shi kaɗai yasan dalilin faruwar hakan. Sau da dama zaka so abu, kaga Allah ya hanaka. Ƙila ba alkhairi bane a cikin rayuwarka wannan abun da kake ta so. Ki dogara da Allah kawai"








Ghana:
ZUBAINA:
Abunda idanuna yayi tozali dashi ya firgita tunanina. Da sauri na leƙo waje domun tabbatarma da kaina anya nanne gidan Alh Liti kuwa inda uwar gidanshi take ciki? Nan ɗinne kuwa. Jikina na rawa na ɓalle sakatar dake jikin get ɗin na wangale mishi, domun wani irin gigitaccen hon ya soma yi mini. Kunno hancin motar tashi yayi izuwa ciki, da ƙyar na mayar da get ɗin na rufe. Wani irin kwaraɓaɓɓen gidane, mai cike da yara yingu_ yingu, da ƴan madaidaita, harma da ƴan mata da samari. Filin tsakar gidan ba ko filasta, rairayine a tsakar gidan, wasu ɗakuna guda shiga na hango a jejjere kamar gidan aladu, dan basu da tsayi sosai, ginin ya galabaita, haka kwanon da a ka yi rufin ɗakunan a ratattake suke, wannan ana samun ruwa da iska, zai kwashesu yayi awon gaba dasu. Wata mata na gani a gaban tulin tarin uban wanke_ wanke, tana ta aikin wankesu, yayin da nake hango ƙyallin wutar murhu na itace a cikin wani gini ɗan guntu yana tashi, irin kitchen ɗin ƴan ƙauye, ko ince na mutan da. Ƙatuwar tukunyace akan murhunnan, wata mata mai goyo sai iza wutar murhun take yi, hayaƙi na buleta ita da yaron bayanta idanunta tab hawayen da hayaƙin itacennan ya haddasa mata. Hajiya Kubra kuma tana zaune gefe guda tana yima wata ƴar matashiyar budurwa kitso. Kowa dai na harkokin gabanshi, suna cikin wasu irin tsummokarai, yara_yaran kuma wasu ba riga fuskokinsu a mugun bushe kunatukansu duk waskane, manyan kuma a yamushe suke. Kaina yayi wani irin mugun ɗaurewa, anya ba mafarki bane kuwa, to ko dai aljanune suka shafeni?. A tsaye Alh Liti ya sakko ya same ni.
"Kubra banga Rumaisa'u ba, ina fatan ta tattare iya kar kayanta ko? Ga Zubaina zata maye gurbinta" Hajiya Kubra tace.
"Tana cikin ɗaki, tun safe Rumaisa'u take kuka a cikin gidannan, babu kalan rarrashin da ba'ayi mata ba, wallahi bata kula ba" Da mamaki Alh Liti ya kalli Hajiya Kubra yace.
"Dan bura'ubanci nine zan bada umarni, wata ƴar iska ta ketare karar dana gindaya? E lallai Rumaisa'u karanta ya kai tsaiko" Malum_malum ɗin shi ya tattare, ya kutsa kai ɗakin da yake kallomu. Ni dai gabaki ɗaya kaina ya kulle, ikon Allah kawai nake son gani. Ghana most go Alh Liti ya jefo tsakar gidan, tare da jefo wasu tsunmokaran kayan sakawa. Ban gama rufe baki ba naga wata mata ta faɗo gabana Alh Liti ya jefo ta. Kuka kawai take yi tana faɗin.
"Kai mun rai Alh Liti ina son zama ko dan goben yarana. Gidannan babu wadatacciyar tarbiyya, yaro mahaifiyarshi ma na tsugunne a gidan ya ya cika, balle bata nan. Ni inma ba zaka barni in zauna ba, ka bani su in tafi dasu" Huci naga Alh Liti yana yi, gabaki ɗaya ya sauya ya zama abun tsoro.
"Ni zaki tafi ma da yara? Buyagi, to na baki nan da mintuna goma ki bar farfajiyar gidannan, tunda babu kuɗin ubanki a ciki, kwaɗayayya, ai duk wanda ya hau motar kwaɗayi, yasan a tashar wulaƙanci motar nan zata ajjiyeta. In kika sake na dawo na tarar dake anan zaki fita da gudu, ƙila ko arzikin sutura ma bazaki samu ba. Ke kuma daga yau wannan shine ɗakin ki, zaki soma zuwa kwana turaka daga daran yau." Fuuu ya nufi babbar ƙofar da zata sada shi da ɓangarenshi. Ni kuwa da kallo na bishi, idanuna suna tsiyayar ruwan hawaye masu ɗumin gaske. Mata da yaran gidan ko wacce kanta a ƙasa da dukkan halamu Alh Liti boss ne a cikin gidanshi, kowa tsoronshi yake yi. Hajiya Kubra ta matso kusa da Rumaisa'u da take ta kwashe kayanta tana turawa a Ghana most go ɗinta tace.
"Rumaisa'u da kin bi shawarata da duk haka bata faru dake ba. Domun irin wannan korar karen a gabanki anyi ma mata uku, kuma kinsan Alh bazai sauya ba. Ke da zaki yi hamdala kin rabu da ƙwallon mangoro kin huta da ƙuda, yara Allah zai raya su, zasu neme ki a duk inda kike." Wannan mata mai goyo, wacce take aikin girki ta fito tace.
"Wallahi ni naso ace ta kaina sakinnan ya zagayo, domun inda kika san a kan ƙaya haka nake. Danni wallahi babu zaman iddar da zanyi a wannan ƙaddararren gidan ma. Amman nasan sakin ki da Alh yayi, shi ya bani damar matsowa layi, ana tafe za'a isa." Wannan mata mai goyo na kalla, ruwan jiri na shirin ɗibata in faɗi tsabar yanda nake ji jikina takota ina rawa yake yi. Alh Liti to matan aurenshi nawa ne, ni da yace mun matarshi ɗaya tilo da ƴan ƴaƴayenshi shida. Sai gashi nazo na ga saɓanin abunda yace mun. Ga ni, ga Hajiya Kubra, ga Rumaisa'u, duk da dai a iya fahimtata na fahimci aurensu ne ya ƙare ita da Alh liti, ga kuma mai goyo. Kuma Hajiya Kubra tace an kori mata uku a gaban Rumaisa'u, ɗaurewar da kaina yayi yafi gaban misali.
Wannan wanne irin gidane na kawo kaina" Haka nake ta maimaitawa a zuchiyata, ban gama ta'ajibi ba, muka hango Alh Liti da ƙaton gora irin ta bugun ɓarawo ya nufo mu gadan gadan da wani irin mugun gudu, iska cike da malum_malum ɗinshi. Habawa kowa take ya dare, yayi ta kanshi mata da yara sai rige_rigen gudu suke yi. Ɗakin da Alh ya nuna mun yace in shiga, nan na faɗa da mugun gudu ba shiri, harda tura ƙofa A jikin bango na jingina, hannuna na dafe da ƙirjina, a firgice nake ainun, idanuna suna zubar da ruwan hawaye. Har izuwa yanzu gani nake yi tamkar ba ni bace. Ina tsaye ina jiyo yanda Alh yake kutumtumo zagi ɗuma_ ɗuma irin na Sakkwatawan Shehu. Gidannan yayi tsit tamkar babu ƙwayar halitta mai rai. Abubbuwan da suka faru a tsakar gidan, tare da maganganun da suka faffaru, su kaina ƙwaƙwalwata ke ta juya mun, a ƙoƙarinta na son ganin gano bakin zaren. Ni dai abunda na fahimta shine. Alh Liti matanshi uku banda Rumaisa'u daya saka, yaranshi kuma suna da yawa naga halama, domun ko iyakar waɗanda na gani a tsakar gida za su kai dozin uku in ma basu fi ba. Kaina na dafe wanda yake saramun, ahankali na sulale akan ledar tsakar ɗakin, na saki kuka mai gunji. Tuni na shiga hasashen makomar rayuwata a cikin ƙasar da banda kowa, gidan da kamar kowa ta kanshi yake yi. Me yasa ma tun farko na aminta da Alh Liti ne? Wata zuchiyar tace mun.
"Zaƙin bakinshi, da abun hannunshi su suka rufe miki idanuwanki" Ni sai yau ne na sake ganinshi da kyau, na kuma gane lallai ko kusa bamu dace da juna ba." Nafi awa biyu a zaune ina aikin karanta wasiƙar jaki, ni kaina bana ce ga abinda nake tunanowa ba. Kiran sallar azahar da na soma jiyowa daga masallacin cikin unguwane ya dawo dani kan doka da oda. Ajjiyar zuchiya na sauke, na sa hannu na shasshare hawayen dake ta faman sintiri a kumatuna. Sai a lokacin na shiga karema ɗakin kallo. Gadone ƙarami a ɗakin, sai wadrope mai ƙofa biyu shikenan abunda yake cikin ɗakin, ƙaramine sosai ɗakin, filin tsakar ɗakin bazai wuci mutum uku su zauna su miƙe ƙafafuwa ba, hatta windon ɗakin ƙaramine sosai, hakama ƙofar shiga ɗakin itama ƙarama ce. Har aka idar da sallah a masallaci ina zaune dirshen bani da guiwar da zan iya miƙewa tsaye, jikina yayi mugun sanyi kamar wacce aka watsa ma ruwan firji. Da ƙarfi naji an doko ƙofar ɗakin, a zabure na miƙe tsaye nima, dan na gama tsorata da sha'anin Alh Liti. Wannan matashiyar yarinyar ce da Hajiya Kubra ke ma kitso ɗazu. Hannanunta riƙe da kwanon silver da kofin silver na ruwa. Ɗan Murmushi tayi mun kaɗan, ta ajjiye mun kwanon da kofin.
"Ga abincinki nan Anti Amarya, Hajiya ce tace in kawo miki." Harta juya zata fita da hanzari nace.
Dan Allah inane bayan gida inason zan kama ruwa in yi alwala?" Bata juyo ba tace.
"Muje to in nina miki bayan gidan" A tsorace na biyo bayanta muka fito. Su Hajiya Kubra duk suna tsakar gidan, abinci suke ci, a manya manyan tire. Hajiya Kubra tace.
"Kin fito yin alwala ba Amarya"
E" Shine amsar daya fito a bakina, wata ɓagurarriyar buta wannan matashiyar ta ɗakko ta cika mun ruwa a ciki, ta bani.
"Ta lungunnan bayan gidan yake, da kin shiga zaki ganshi" Wuce wa nayi lungun da take nuna mun, bayan nayi mata godiya. Bayan gidan babu laifi a tsabtace yake, yasha sumunti sumul sumul, sai ɗan zarni da baza'a rasa ba. Ina hawaye na kama ruwa na fito. Ni da nayi tunanin bayan gidana sai ya zama abun kallo, sai gashi na lalace a shiga bayan gida mai daɓen siminti. A tsakar gida nayi alwalar inda naga wata ƴar yarinya da bata wuci shekaru uku ba tana alwala. A kusa da su Hajiya Kubra na tsaya nace.
Dan Allah Hajiya inane gabas?" Da fara'arta tace.
"In kika shiga ɗakin ki, ƙofar shiga zaki kalla nanne gabas ɗin" Godiya nayi mata na koma ciki, sai gauraye hanya nake yi. Yaran gidan kuma abun kallo na zame musu, sai uban hayaniya da sowa suke yi, wanda wannan kaɗai ya isa birkita ƙwaƙwalwa. A zaune nayi sallar, dan tsaiwar ta gagara babu guiwa a tare dani. Cikina sai murɗamun yake yi, rabon da ya samu loma tun jiya da yamma. Kwanon abincin da aka kawo mun na jawo. Ina buɗewa naci karo da farar shinkafa sol da manja da yaji, sai albasa ɗanya da aka yayyanka a saman abincin. Ina hawaye ina tura abincinnan a bakina, loma huɗu nayi na sha ruwa, na ture kwanonnan gefe. Tunanin hanyar guduwa na soma yi, domun bazan taɓa iya rayuwa a cikin irin wannan gidan ba, in ma na zauna tamkar na kashe rayuwata ne baki ɗaya. Tunano ƙannena da ƙawata Mabaruka na shiga yi, da su Hadiza da duk suke auren masu sukuni, suke fantamawarsu, babu ma kamar Mabaruka a cikinmu. A wannan ƙaddararren ɗakin na wuni, tunani ya kaini har bayan magriba. Duhu dilim a ɗakin, amman kasancewar gangar jikinane kaɗai a cikin ɗakin ruhina baya wajan yasa banga duhun ba. Turo ƙofar akayi da fitilar ƙwai a hannun mai shigowar. Hasken haƙorin makan Hajiya Kubra na gani tana yi mun Murmushi, hannunta riƙe da kwanon abinci. A gabana ta dure kwanon, ta nemi waje gefen gado ta zauna.
"Baiwar Allah kina ta zaune sai wasiƙar jaki kike ta karantawa ko? Tun ɗazu nake ta jiran fitowarki domun in faɗa miki ƴan ƙa'idojin gidan namu wanda ya kamata kiji a bakin nawa, sauran kuma Alh zai faɗa miki domin shi dake ya shafa kai tsaye.
MRS BUKHARI CEMAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
32




















Amman kafinnan inaso in soma da baki shawara. Abu mafi sauƙi da zaki yi shine ki kwantar da hankalinki, karma tunanin tawaye, ko guduwa ya zo zuchiyarki, in kika watsar da komai, kina zaune haka a cikin ɗakinnan, in dai Alh ne zai leƙo ya ce ya sake ki, in ya samu wata. Kamar yadda ya saki Rumaisa'u daya same ki, haka ne yake gudana a cikin lamarin rayuwar Alh, sake mace yafi mai sauƙi fiye da cire hula a kanshi. To dokokin gidan sune. Alh ƙarfe takwas na dare yake shigowa cikin gidannan, yana so kafin ya dawo wacce take da girki ya zamana ta kasance a bakin barandar turakarshi domin tsaiwar jiranshi. Ƙin yin hakan ka iya sawa ki fuskanci fushinshi, fishinshi kuma babu kyau a gareki. Sannan in ya buɗe kofa kuka gaisa, saiki zo ki gabatar mishi da abinci, wanda dama tun magriba abincinshi zai kasance a ɗakin wacce take da kwanane. Girkin gidannan yana da matuƙar yawa da wahala hakan yasa ko wacce mace bata da wani hutu a cikin gidan kullum. Wacce take da girki ita zata yi girki ita kaɗai, mu kuma zamu kama shara, wankin bayi, da wanke wanke. Yaran gidan kuma aikinsu shine ɗibo ruwa da ɗan aike da dai abunda baza'a rasa ba. Abincin gidan kullum iri ɗaya ne. Da safe abunda ake dafawa shine dai, haka ma da rana, da daddare ma haka. Ranar juma'a ne kaɗai ake yin tuwon shinkafa da miyar kabewa da rana. Baya ga wannan rana babu wani sauyi a abincin gidan.Sai da sallah ƙarama ko babba ake dafa shinkafa da jar miya wato miyar sutu, Ina ganin abunda ya kamata kiji daga gareni kenan, sauran bayanan shi zai miki, in ma da abinda na mance ban sanar miki ba, sannu a hankali zaki gane ki fahimta. Hawaye na bin fuskata nace da'ita.
Na gode da bayananki, amman da kin adanasu zasu yi ma wacce Alh zai kawo gaba amfani. Domun Allah ko kwana bakwai bazan yi a cikin gidannan ba, ƙasarmu zan koma" Wani murmushi taimun mai fassara, ta miƙe tsaye.
"Irin wannan taurin kan, da ikirarin nayi a shekaru Ashirin baya da suka wuce, kuma wannan dalilinne ya bani lasisin zaman dirshen a gidan Alh Liti. Da ace ban yi rigima dashi ba, da tuni nafi shekara goma sha tara da rabuwa dashi, na tafi wani gidan na gina kyakkyawar rayuwa mai inganci. Sakin da yaga shine kaɗai abunda nake nema yasa shi kuma ya ƙi sakina dan tsabaragen muguwar mugunta. Kuma wannan shawarar na kan ba duk wata Amarya da Alh zai kawo ta cikin gidannan." Miƙewa tsaye nayi, nayi tsaiwar daka a gabanta nace.
Kema yaudararki kenan Alh Liti yayi ya baroki da ƙasarki da danginki?" Murmushin da na lura ya zame mata jiki ta kuma yi mun.
"Yarinya, son zuchiya da kwaɗayin abun hannun Alh shi yai sababin shigowar duk macen da Alh ya auro, da waɗanda zai auro nan gaba ma. Dukkanmu kwaɗayayyune daga mu har iyayen namu ke kin sani nima na sani, Alh Liti hatsabibine ki kiyayi jayayya dashi. Ɗakina yana jikin naki, in Alh ya dawo ko sai ki zo ki karɓa mai abincinshi, takwas saura kwata yanzu" Tana kaiwa nan ta fita, ta bar mun fitilar ƙwan. Ko kallon abincin data kawo mun banyi ba, kan gado na faɗa, wani mugun wari da zarni ne yasa na tashi da sauri. Zirga _ zirga na shiga yi a harabar ɗakin, na dunƙule hannuna na dama, yana nausar na hagu, ina neman mafita da tunanin dabarar da zanyi ma Alh ya sauwaƙe mun cikin ruwan sanyi. In kuma yaƙi sauwaƙe mun, in gudu da auren nashi a kaina, in shige duniya." Agogon hannuna na duba da sauri, takwas saura minti biyar. Mayafina dake ƙasa na ɗauka na fito tsakar gidan. Matan gidan da yaran gidan duk suna tsakar gidan, suna shan iska, kowa da sha'anin da yake yi. A yanzune naga tulin bataliyar yaran nashi, manyan maza da manyan mata, waɗanda bamu haɗu ba, sai gaisheni suke yi, yayin da mata _ matan suke ƙunshe dariyarsu. Tsakar gida kamar anacin kasuwar monday ta Kaduna, ace duk wannan bataliyar yaran na mutum ɗaya ne, kuma kai zaka yi musu girki kai kaɗai su ci? Tab wannan daka gama ai sai mutuwa. Ƙara tsurewa nayi sosai. Salalab_salalab na wuce su, na nufi ƙofar da zata sadani da ɓarayin Alh. Ina shiga cikin ɓarayin, naga hasken wutar mota, sai hon ake dannawa da ƙarfi, a jajjere kuma. Ni kuma ina jinjine ina kallon ikon Allah, Ƙaramar ƙofar shigowa cikin gidan aka buɗe da Alh mu ka haɗa idanu, yana huci yace.
"Dan bura'ubanci kina jin ina hon, uban wa kike tunanin zai buɗe mun get in ba ke ba, bauta kika zo yi gidannan, dolenki kuma kiyi bautarnan, dan igiyarki tana hannuna." Kai na gyaɗa kawai, ƙafafuna na rawa na isa bakin get na buɗe mishi ya shigo da gudu. Mayar da get ɗin nayi na rufe, na nufoshi, fitowarshi daga cikin motar kenan, idanu na ƙura mishi ina mamakinshi, shima ni yake kallo bakinshi a yashe, har yana wani lashe leɓe.
"Amarsu ta ango, farar mace alkyabbar mata" Ni dai na kasa cewa komai, a baya na bishi zungui_ zungui, har zuwa sama. Muka shiga wani haɗadɗen falo a sama wanda ya take na ƙasa. Ƙasan kafet ya nuna mun da hannunshi.
"Zauna a nan ki kijira ni ina fitowa ko?" Har ya juya nace.
Abincin ka fa?" Wata dariya yayi, wacce ta ƙara mishi muni yace.
"Ai kece abincina a cikin wannan daren, yau zan fanshe wahalar da kika dinga bani. Hidimar yarana kuma zata fanshe dukiyar da kike tunanin bani da hankaline shi yasa na dinga ɓarnatar miki. Yaro _ yaro ne ko da ɗan giwa ne." Da wata mahaukaciyar dariya ya kece, ya shige wani ɗaki ya barni da sakakken baki da hanci.




Kaduna:
Mama tana zaune a tsakiyar su Mama Rakiya, da Nafisa, suna mayar mata da yadda akayi"
"Aini Yaya Jummai da ganin abubbuwan da suka faru ko, wallahi ba lafiya ba. Bawan Allahnnan

39 / 67