MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   30 / 67

87K to 90K   out of 198.3K words

aure, tare da yi mun adda'ar Allah yasa yayi ajjiya a marata. A daren naci kuka sosai, ba kukan kasancewa da mijina ba, kukan keta mun darajata da wani banza yayi. Gani nake yi tamkar ban gamsar da Bulamana ba, domun banga yayi irin wannan abun da nake karantawa a littattafan hausa ba. Asalima sai da ya barni naci kukana na ƙoshi sannan ya bani haƙuri. Dama Hajja Fati ta faɗamun duk wannan rubutun first night da marubuta suke yi yaudarace kawai. Dududu a cikin minti goma Bulamana ya gama jin daɗinshi dani, saɓanin su da suke rubuta gabaki ɗaya daren aikin da akeyi kenan. Da asuba da zan shiga wanka, bayan Bulamana ya fito, na ɗauka bazan iya tashi ba sai ya tallafamun. Abun mamaki a kan ƙafafuna ras na shiga bayi, nayo wankan tsarki, sannan nayi wankan soso da sabulu na fito."
A tsaye na same shi yana goge jikinshi da towel. Haɗa idanu mu ka yi, a tare muka sakarma da juna murmushi, inajin sonshi na sabunta kanshi a zuchiyata, Aure kenan mai sa duk girman namiji ka ganshi babu wando. Mai sawa duk ƙanƙantar mace ta ɗauke babban namiji.
MRS BUKHARI CE




💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻MAI IDO A TSAKAR KA
( DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI (B4B)
22






*UmmuAffan Collection*
_DUK ABIN DA KUKA GANI ANAN MUNA DA SU, DOMIN ƘARIN BAYANI 08104335144_
Royal jelly big
Royal jelly 30 pieces
Royal jelly small one 60 pieces inside the pack
Vitamin C-100,
Vitamin E big
Pesona
Dara
Cantik ayu
GLUTA white
Khusus ibu
Sugar wanita
Majakani 3 in 1
Eve Care
Juliet eve
Phyton buster
Phyton collegen
Glute sparkling
days ginger oil for hair
Papaya oil for breast
Garlic oil for hips
Vitamin C serum
Vitamin E serum
Busty blend
Gluta prime
Collegen+C
*Ƴan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan UmmuAffan collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08104335144*


























"Zan tafi masallaci, ki yi ƙoƙari ki shirya da wuri, ƙarfe bakwai mu ka yi da Ahmad zamu fito. Inason zanyi magana dake inna dawo masallaci, naso tun jiya muka tattauna, amman ganinki ya susutamun tunanina bamu samu zama ba balle mu tattauna komai. Amman inna dawo kafin mu fita sai mu tattauna, saina dawo ko mai daɗi" Kunya da daɗi yasa nayi saurin rufe fuskata da tafukan hannayena. Dariya ya sakar mun ya fice. Bayanshi nabi da kallo har sai da na dena ganinshi. Ajjiyar zuchiya na sauke, ina mamakin kaina akan sabon son Bulamana da yake bijiromun. Yau nice namiji yake rawar kai a kaina duk rashin kyauna, har na kai macen da zata susuta mijinta harma ya rasa gane kan nutsuwarshi? Lallai rayuwar aure sirri ce, soyayyar gaskiya babu ruwanta da muni. Ni kaina nayi mamakin yanda Bulamana ya dawo a idanuna, ganinshi nake yi tamkar yafi ko wanne namiji kyau a duniyarnan, duk wani muninshi da jayayen idanunshi bana gani yanzu, idanunshi har wani narkomun da sha'awarshi yake yi inna kalla. Allah kenan, Allah na gode maka daka bani ɗan uwana a matsayin abokin rayuwata. Jina nake yi tamkar nafi ko wacce mace kyau a duniyarnan. Daurewa nayi na mayar da kayana nayi sallah, ina kan sallaya Bulamana ya shigo da sallama. A kusa dani ya zauna jikinmu na gugar na juna. Idanunshi ya zuba mun, nima shi nake kallo zuchiyata cike da sonshi.
"Meye sirrinne naga kin sake yin wani kyau, har haske kika sake yi fa uhm" Ya kafeni da jajayen idanunshi, sai wani lumshe su yake yi. Lallai Bulamana ya iya soyayya, da tarairayar mace, ba banza ba ashe Zubaina ta mallakeshi ita kaɗai.
Kaine sirrin ai, kulawar dana samu a wajanka shine ya kwantar mun da hankalina, baka ga na ciko bane?" Hannayena ya kamo yace.
"Na gani sosai ma kin ciko sosai. To bani labarin yanda sona yake a cikin zuchiyarki, sannan da fatan na gamsar dake, na kore miki ƙishin ruwanki, kamar yadda nawa ƙishin ruwan ya koru ko?" Sake sunne kaina nayi, zuchiyata sai tsalle take yi mun, daurewa nayi na faɗa mishi kalamai masu kwantar da zuchiya, amman da ƙyar nayi yaƙi da kunya. Nan muka shiga fallasama juna asirin zuchiyoyinmu, kamar zamu koma ruwa dai, da ƙyar na samu na lallaɓashi ya barni, amman bai rabani da jikinshi ba, yana kwance ni ina gefen kafaɗarshi
"Yahanasu na" Yanayin muryar da yayi amfani da'ita wajan kiran sunana, yayi tasiri sosai a gangar jikina, ayau sai naji sautin babbar muryarshi na neman rikirkitani, saɓani da da in yayi Magana nake shiga taitayina.
Na'am Bulamana " na furta a sarƙe.
"Mun samu gida mun kama a can wata anguwa, to amman gidan gidan yawane sosai, mata zasu kai ashirin in ma basu fi ba. Kiyi haƙuri a yanzu iya abinda zan iya kenan, sabida ina buƙatarki a kusa dani, da yara ma su samu su koma makaranta, kema ki koma bakin aikin ki. Na je ma'aikatar taku na sanar dasu abinda ya faru, na kuma faɗa musu kin tafi gida amman ɗaya ga sabon wata zaki dawo bakin aikin ki. Gemunshi na kamo ina wasa dashi nace.
Haba Bulamana, ni banji daɗin yanda kake bani haƙuri ba. Nifa matarka ce, duk inda kaga damar ajjiyeni ai anan zaka ajjiyeni, dolena ne in yi biyayya a gareka, ai babu komai" Kwanciyata ya gyara mun ya ɗaura da cewar.
"Ina kuma baki haƙuri akan ɗaki ɗaya na kama a ciki zamu zauna harda yaran, sakamakon rashin lafiya da Yusuf yake fama dashi, duk kuɗaɗen nawa sun ƙare akan maganar lafiyarshi, sannan na ɗan siya mana katifa da ɗan abunda ba'a rasa ba......" Hannu nasa na rufe mishi baki.
Shishsh.. baka da buƙatar yi mun dogon bayani, mu ci gaba da adda'a Bulamana. Bari inje in haɗo kayana, kaga ƙarfe shidda, kuma bakwai zamu tafi" Ƙoƙarin sauka nayi a jikinshi, da sauri ya dawo dani, gam ya riƙeni a ƙirjinshi.
"Allah yayi miki albarka. Bani da kuɗi, bani da kyan da zan burgeki, anma zan baki kulawa da soyayyar da sai kinyi alfahari dani."
Nima bani da kyau, bani da diri, bani da hasken da zan burgeka. In sha Allah zan yi maka biyayya, zan zame maka tamkar baiwa." Ina kaiwa nan na miƙe na fita ba tare da na waiwayo ba." Ina shiga ɗakinmu na taradda Ya Innana ta gama haɗa mun kayana tsab a jakarta, kayayyakine nata ta bani, sai sababbi kala uku da Ba Modu ya ɗinka mun. Wakil ya siya mun zanin gado, Dala ya siya mun labulaye ƙofa huɗu, Fanda ta siyamun lafiya guda uku, fanna ta bani takalmi ƙafa biyu. Ƴan uwana suka haɗa mun goma sha tara na arziki. Babu dai wanda ya bani ko sisin kobo, sai Ba Bakura daya bani, yayi ma su Bawa ɗinki, harda ƴan kanti duk ya sai musu. Hajja ta kuma ta haɗoni da kayan ƙamshi, dana gyaran jiki. Kowa dai da abunda ya bani. A tsaitsaye muka karya ni da yaran. Na ɗauki na Bulamana na kai mishi. Yana gamawa muka fito, ƴan uwa da iyaye sunata mana addu'ar isa lafiya. Wakil ne ya ɗauke mu, muka biya gidansu Ahmad muka ɗakkosu, wannan karon an bar Zulai a gida wajan Baba. Wakil bai bar tasha ba sai da yaga motar mu zata tashi, hannu yasa a ajjihu. Yana zarowa ya kamo hannun Bulama Babba ya damƙa mishi ya juya. Da idanu Bulama Babba ya bishi, har idanunshi na cika tab da ruwan hawaye. Motarmu ce ta fita da gudu a tashar, wakil sai ɗaga mana hannu yake yi, har sai da muka dena ganinshi muma muka sauke hannayenmu "










KOFUR ZUBAINA:
Ina zaune a tsakar gidanmu ina daddanna wayata, Nafisa na ɗaki tana baccin asara. Yau bani da aiki ina hutu. Su Mama kuma yau kwanansu biyar da tafiya Umara, sai jiya ne ma suka samu damar kiranmu. Mabaruka ce ta shigo gidan a birkice kamar an jefota. Hawaye caɓe_caɓe a fuskarta, gashi naga bakinta a kumbure.
"Ƙawata Adam ya yaudareni ace munafukine ban sani ba?" Zama na gyara nace.
Yi mun bayani dan Allah dena kukannan akan wani banzan namiji, wanda ƙila yana can yana sheƙe ayarshi ke kina nan kina kururuwa" Cikin kuka tace.
"Ashe Adam yana kwanciya da Sagira baibai kawai suke ninkeni? Yau naga kilakanci sai ga Sagira da ciki, harya soma fitowa ni banma sani ba. Kuma dan bura ubanci Adam ne yazo yake shaidamun wai zai kaita asibiti zata soma awo. Wallahi ƙawata bansan sanda na cukume Adam na dinga narka ba, na haɗa da makira, kar ki so ganin buyagin da nayi yau. A take Adam ya cikace mun saki, a taƙaice dukka igiyoyin auren sun ƙare" Ido na zare waje nace.
Ya sakiki fa kika ce, kuma kika ce Sagira na da juna biyu, wanne irin sakaci kika yi haka Mabaruka? Kinga irin abubda nake faɗa ko"
"Ke dai bari, tunda na koma gidan Adam, ban sake kaima boka ziyara ya sabunta mun aiki ba. To bani da kuɗin Zubaina, duk kuɗaɗen aikina akan mallakar Adam suke ƙarewa, ban tara komai ba, gashi ya sake ni a banza. Sai dai zan kunna mishi jafa'i da masifar da bazai iya fita a cikinta ba. Dafata nayi.
To meye na kuka ke da kina yin jini uku shikenan, kina da damar da zaki yi aurenki kwaf ɗaya. Ga Alhazai suna shaƙawata a gari. Kinganni fa duk sha'awa sai tsotseni take yi, a hakanma dan nakan ɗan rage ma kaina zafi. Zawarci masifa ne ƙawata, ni da'ace wata uku zanyi da naji daɗi, wani hamshaƙin Alhaji zaki cabke ki shige ki baza mulkinki. Ki duba Asiya yadda take tsula tsiyarta a gidan mijinta, gabaki ɗaya uwar gidan, da yaranta Asiya ta shafe su. Kinga haihuwarnan da tayi? Yanda kika san Asiya ce ta soma yi mishi haihuwa. Suna Umara fa yanzu haka Harda Mama. Me zai dame ki to dan Adam yayi ma Sagira ciki? Su je can su ji da talaucinsu, zaki samu babban rabone, kuma ki bar mata yaranki ta gama shan wahalarsu dan ubanta. Kamar yadda na tafi na barma jakar matar da Bulama ya auro rainon yara"
"Wallahi ƙawata kuma hakane. Wato Mama ana makka? Oh ma'aikin Allah na madina ni Mabaruka. Muma Allah ya koro mana wani ƙusan, ƙawata yayi wuff damu, za'ayi zawarci fa mai lafiya, ko dan samun mai maiƙo ma. Tare da Mabaruka muka wuni a gida,. Sai da yamma lis muka fita nasha wanka da ɗan ƙaramin mayafina, ga Yusuf na riƙeshi a ƙuguna, shima naci mishi ado. Gidansu Mabaruka muka je. Ta zaiyanema mamanta cewar Adam yai mata duka ya sakota. Nan mamansu ta shiga sababi, tana ɗure_ ɗuren ashar manya manya. Duk jirgi ɗaya ne ya kwasosu da su Mama. Zuwa bayan isha na ɗau haramar gida. Ko a haka zawarawa suna latsani, sai dai irin waɗandan nake son su zo basu bane suke zuwa ba. Nakance musu iddata bata ƙare ba, kuma goyo nake yi ɗanye. Haka dai kwanaki su kaita tafiya. A tafiyar su Mama Musa kullum sai ya shigo da ƴan mata a ɓoye sun kwana a gidan, sai da asuba nake ganinsu wani sa'in. Sagiru kuwa, tun kafin Mama ta tafi yayi mata sallamar ya tafi Lagos, zasu bikin wani abokinsu. Tun daga ranar bamu sake sakashi a idanunmu ba. Nafisa kuwa, sai ta ga dama take kwana a gida, in kuwa bata ga dama ba, a waje take kwana abunta, dana yi mata magana ta nemi zagina, sai na fice a harkarsu duka daga ita har Musa. Tunda Mama ma data haifemu babu yadda ta iya damu dukkanmu, kuma ita ta sabar mana duk abinda muke son yi dai dai ne, ita ta koyar damu rashin ganin girman na gaba. Haka dai naci gaba da gwagwuyar zawarcina. Da kuma renon Yusuf. Wata rana in samu dubu ɗaya a hannun Bulama, wata rana ɗari biyar, kuɗaɗen albashina baya isata yima kaina hidima sam, dan duk wata ina sayen sutura kamar biyu, da takalmi da mayafi, harda ɗankunne da sarƙa fashion haka. Gaye nake ɗanɗasawa sosai.




Bulama Babba:
Muna tafe a cikin mota, jikina na gugar na Yahanasuna, hannuna na kan ƙugunta na tallafota jikina gabaki ɗaya, dan naga bacci take shirin yi. Ahmad ne ya zungureni dake shine a kusa dani
"Wallahi baka da kunya, ji yanda ka ƙwaƙwube ƴar mutane a cikin motar haya, ko kunyar Hajara ba zaka ma ji ba?" Murmushi nayi mishi nace.
Ai ban hana ka ka jawo taka matar ba, kowa ya biya allonshi sai ya wanke" Dariya mu ka yi dukkanmu, Ahmad yace.
"Naji daɗin yanda hankalinka ya koma kan Yahanasu sosai, na kuma ji daɗin yanda kayi fatali da son da kake yima Zubaina. Duk da nasan baka haɗa komai da iyayenka."
Ahmad aini yanzu nake ganin ma nasan meye soyayya, in da na auri Zubaina sabida haskenta, da cikar halittarta. To ita Yahanasu son so tsakani da Allah nake yi mata. Kuma a idanuna ina ganin kyanta fiye da kyan Zubaina, ina son matata sosai" Ni da Ahmad mu kaita tattauna halin rayuwa, a haka har muka iso garin kanon dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika. Bayan mun fito daga tasha, Ahmad ya tare mana ɗan sahu zuwa na'ibawa cikin layin S P. Anguwace wanda kai tsaye zamu kirata da anguwar talakawa, domun masu rufin asirin cikin unguwar baifi a ƙirga ba. Unguwace mai cike da datti, hayaniya, da hargowar yaran geto da ake sakinsu suna damun mutane da fitintuninu.






YAHANASU:
A bakin ƙofar wani kwaraɓaɓɓen gida mai ɗan sahun ya tsayar da ɗan sahunshi. Gidan ko ƙofa babu sai wani cinyayyen labulen buhu fari, wanda tsabar datti ya dawo ruwan ƙasa. Kayayyakinmu muka sakko dashi. Hajara tace.
"Abban Anisa wai wannan ƙazamin gidan shine gidan da kuka kama dama?" Ahmad da gani baiji daɗin maganar Hajara ba sam, shi yasa ya amsa mata a daƙile.
"Shine in baiyi miki ba, sai in mayar dake gidanku tunda yafi wannan tsabta ko?" Bakinta ta tsuke tayi shiru. Ni dai hannun yara na kama nayi gaba. Da sallama a bakina na shiga cikin harabar gidan. Cunkus ɗakin tsumma kenan. Babban gidane sosai mai cike da ɗakuna a jajjere hagu da dama, sai filin tsakar gida, da wata doguwar kwatar data kai tun daga farkon gidan har ƙarshe. Ko wacce mace da kurfot ɗin girkinta a bakin ƙofar ɗakinta, kasancewar yamma ne ko wacce tana bakin ƙofarta tana faman kacaniyar girki. Yayin da yaran cikin gidan wasu ke guje gujensu, wasu ke wasan gare gare abinsu. Datti takota ina a tsakar gidan kamar gidan gwagware.
Assalamu alaikum sannunku da gida" Na faɗa ma matan gidan. Da fara'arsu kuwa suka tarbemu, nace.
Mune sababbin zuwan da muka kama ɗakuna" Hajara tana bayana sai ƙarema gidan kallo take yi. Bulamana da Ahmad kuma bayan sunyi sallama, ko wanne ya nufi ɗakin daya kama da kayayyakinmu. Mu kuma muka tsaya aka gaggaisa da matan gida. Wata mata wacce ake kira maman Sabeer tace.
"Ga can ban ɗakunan gidan, sune daga ƙarshen gidan, na wanka biyu, na ba haya ma biyu. Amman babu kitchen kun dai gani ko wacce dai a ƙofar ɗakinta take girkinta. Mu matan aure dai mun kai mu Ashirin da uku ko Uwa? Ta tambayi matar dake tuƙa tuwon dawa a ƙofar ɗakinta.
"Mu ashirin da biyu dai, kin mance Hauwa zaman idda take yi, data gama zata kwashe kayanta. Sai masu zaman kansu mutum takwas, mu dai talatin ba ɗaya in an cire Hauwa da zata tashi." Mamakine ya kamani da naji sun ambaci masu zaman kansu. Hajara tace.
"Au a cikin gidan harda masu zaman kansu kuma ya kuke ƙarewa da mazajenku?" Matar da aka kira Uwa ta yi shewa tace.
"Waye ma Hajiya Dumba ba zata saka ba a gidanta, matar da bata san mutunci ba, kuɗi kawai ai tasa a gabanta. Ai kuwa da masu zaman kansu muke zaune, amman ai kowa harkar gabanshi yake yi, babu ruwan matan aure da masu zaman kansu. Maman Sabeer tace.
"Abun takaicin ma sai kuna zazzaune, za'a shigo muku da ƙaton gardi, baku da yanda kuka iya, wani ma da wando iya cinya yake shigowa, gida ya kaure da hayaƙin sigari. Gidan haya makaranta." Ni dai jikina a sanyaye na wuce su a tsaye, Hajara na jin kanun labarai. A tsaye na samu Bulamana, da halama jiran shigowata yake yi. Shi nake kallo.
"Kinga irin gidan ko? Kiyi haƙuri mu lallaɓa, in sha Allah ba zamu wuce shekara guda ba. Wallahi rashin kuɗine yasa na kama wannan gidan, bani da kuɗin da zan kama ɗaki in biya shekara, shi kuma wannan duk wata dubu uku ake biya shi yasa.
Idanu na lumshe nace.
Ai ko dokar daji ka kaini ni mai zama ce, ballan tana nan gidan na mutane. Karka damu kanka, Allah ya hore mana sai mu sake gida."
"Ameen Yahanasu na. Inason in fita yanzu zan dawo amman." Tausayinshi ne ya kamani, dana tuna gidanshi na Kaduna, da irin motar da yake hawa, gadon da yake bacci akai ma mai shegen kyau.
Adawo lafiya Allah ya tsare." Da "Ameen" Ya amsa yasa kai ya fita. Ɗakin na ƙarema kallo, ɗakine madaidaici, shi ba babba can ba, amman ba za'a kirashi ƙarami ba. Ga ƴan katifu madaidaita guda biyu ya

30 / 67