MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   42 / 67

123K to 126K   out of 198.3K words

yarannan" Harta miƙe Rashida tace.
"Hajiya barshi, bari inje in same su. Su yi haƙuri komai tsawon zamani Baba dole ya mutu, abunda ya shuka shi zai je ya tarar, mu kuma bai isa ya hana a rabe mana kuɗin lukudin daya tara ba" Miƙewa tayi ta bi bayan su Rauda. Daɓas na zauna zaman ƴan bori akan kujerar tsugunno, domun ƙafafuwanane suka gaza ɗaukata. Ina zancan zuchi ina faman aikin wanke _wanke, hankalina baya ma cikin gidan baki ɗaya. Tuno gidana na Kaduna nayi, da irin tsantsar so, da kulawar da Bulama ya bani a rayuwarshi. Da irin martaba ɗangina da yake yi, da irin sarrafani da yake yi a gado, cike da tsantsar so, da nuna muradinshi a fili. Ohh ya ilahi. Na sake tuno lokacin da nake juyashi sai yanda nayi dashi, da raba shi da iyayenshi, da danginshi da nayi, babu abunda ban tunoshi a yau ɗinnan ba. Ban ankaraba har na gama wanke tulin kwanukannan tas, nasa hannu zan ɗauki kwano naji wayam, ina kallon gabana naga kwanukan sun ƙare, saura ƙatuwar tukunyar tuwo da miya. Kai na girgiza lallai na shafe awanni ina faman aikin tunani. Tashi nayi na dinga kankarar tukunyar tuwonnan, na tara ƙanzon a wani kwandon roba, sama sama na wanke tukwanen, na mammatsar da kwandunan gefe.
"Ki bar sharar yara zasu su fito su yi. Rashida a ba yarannan maganinsu su sha" Cewar Hajiya Kubra kenan, bayan ta mun magana ne, ta juya kan Rashida. Alwala na ɗaura na shige ɗaki, a ledar tsakar ɗakin na yi zaman dirshen dan na gaji ainun, ga zazzaɓi sai sake lulluɓeni yake yi. Kafin la'asar har bana iya gane wanda yake kaina ma, tsabar azaba"








MRS BUKHARI CE
[09/08, 11:40 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: MAI IDO A TSAKAR KA
(DUNIYA)
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B
34


















YAHANASU:
Daren ba ƙaramin nisa yai mun ba, da ƙyar asuba tayi a wajena, ina kwance lamo, kaina kamar zai fashe tsabaragen ciwo, haka idanuwana in na buɗesu tamkar zasu faɗo ƙasa tsabaragen zafi da zugin da suke yi mun.
"Yahanasu, ki daure ki tashi kiyi sallah, in yaso sai ki koma baccin, ki sanar a wajan aiki baki da lafiya" Da dabara na buɗe idanuna, muna haɗa ido da Bulamana ya sau mun Murmushi, take idanuna su kai ƙwalƙwal. Da taimakonshi na miƙe zaune, kaina na dafe a hannuna na fita a ɗakin. Da dabara nayo alwala na shigo ɗaki. Sallar ma a zaune nayi, ina idarwa na koma na kwanta, take na shiga rawar sanyi. Duk Bulamana ya rikice ya ruɗe, sai da ya lulluɓeni da bargo babba na samu sassauci, shi kuma ya samu zarafin shirya yara zuwa makaranta. A yanzu Bawa da su Anisa da kansu suke zuwa makaranta su dawo da kansu. Bayan sun tafine ya fitar da wanke_wanke da wankin kayanmu, kan kace me ya gama aikace _aikace, shine harda sharar ɗaki.
"Tashi ki je kiyi wanka, in kika fito ga dumame nan ki daure kici. Ni bari inje in siyo miki magani"
Nagode sosai da kulawarka a gare ni. Nace yau baka da jarabawa ne?" Murmushi yayi yace.
"Akwai, saura pepa ɗaya ya rage mana, yau zamu kammalata, ƙarfe biyu zan fita. Kafinnan har abincin rana kinga na gama" Yusuf ya riƙe ma hannu suka fice, nima je bayan gida na watsa ruwa da zafi zafi na fito.
"Umman Maryam jikinne har yanzu dai?" Cewar Maman Gaddafi kenan. Cikin muryar rashin lafiya nace.
Wallahi kuwa, jikin yaƙi daɗi" Maman Hassan tace.
"Bari in ɗan rarrage aiyukana, sai inzo in kama miki wani abun. Naga Baban Maryam ya yi muku wanki sassafe."
Hakane kam. Amman ya gama aiyukan dukka ma, na gode Allah ya bar zumunci" Nan dai su kai ta mun sannu. A bakin ƙofar ɗakina naci karo da Hajara itama tazo yi mun ya jiki. Ahmad ma ya leƙo daga cikin ɗakin nasu yai mun ya jiki. Ina zaune ina ɗan cin abincin kaɗan kaɗan, bulamana suka dawo daga siyo magani. Harda kayan shayi ya siyo mun. A kofin roba ya haɗamin tea mai kauri ya miƙo mun.
"Sha maza sai ki haɗiyi magungunan, ki samu ki rama baccin daren jiya ko? Banyi mishi musu ba na karɓi tea ɗinnan na dinga kurɓa, nasha fin rabin kofon, sannan ya bani magunguna na haɗiya tare da korawa a tean, ragowar kuma na ba Yusuf. Sai da na kwanta na kira ma'aikatarmu na sanar musu ina kwance a gida banda lafiya dan haka bazan samu damar zuwa ba. Abu wasa ne gaske ne, bacci fur yaƙi ɗaukata, har bulamana Ya shirya ya tafi makaranta bayan ya ɓararaka mana taliya. Hajata tayi tayi ya barshi zata ɗaura girki damu, amman fur yaƙi, kasancewar yasan fama suke yi, tunda a hakan mun fisu wadata tunda ni sa'ata ta karɓu ina ciniki sosai. Ita kuma bata daɗe da soma sana'ar siyar da kayan yara ba. Carbin malam, hanjin ligidi, alragis, soyayyar kwakwa da siga, kwakumeti, da dai sauran ƙwalam na yara, ta na ɗan fita dashi ta kai makatantar yara. A mugun galabaice na kai yamma, kaina kuwa ji nake kamar ana tsittsikara mun allura haka nake ji. A ranar Bulamana ya zo mun da kyakkyawan labari mai daɗin sauraro. Bayan ya shigo ya zauna, ya tambayi jikin nawa, sai ya ɗaura da cewa
"Addu'ar da muka daɗe muna yi akan Allah ya bamu aiki. To kusan zan iya ce miki na samu koyarwa a Jami'ar Bayero, kinga a baya na je neman koyarwar a can ban samu ba, da yake ba lokacin rabon yake ba. Amman yanzu da rabon ya tsaga kinga ina dab da haɗa mastas ɗina koma in ce na haɗa tunda mun zana jarabawar ƙarshe sai jiran sakamako, na kuma samu koyarwar. Amman ba yanzu zan soma karantarwar ba,sai lokacin da za'a ɗebi sababbin ɗalibai, a lokacin zan soma koyarwar, wani abokin karatuna ne kamal yai ma mahaifinshi maganata, shine fa aka sama mun koyarwar, kinga ikon Allah ko? Komai na duniya yana da iyakarshi." Cikin murna da zumuɗi na miƙe zaune ina dariya nace.
Wannan babban labarine sosai. Kai Alhamdulillah naji daɗi sosai Bulamana, Allah ubangiji ya taya ka riƙo, ka kula dan Allah da aikinnan naka. Ka sanar ma da Ahmad kuwa?"
"Ahmad baya gida. Amman dama ke ya dace in soma sanarma,tunda su Ba Bakura basu da masaniyar na rasa aikina na gandiroba, da su zasu soma ji, sai ke. kinga da izinin Allah komai zai warware mana, zamu tashi a wannan gidan in kama mana me dama, da zaran na karɓi albashin farko. In sha Allah zan cika miki ɗakinki da kaya. Murmushi kawai nayi mishi, sai na ɗan ji ƙarfin jikina sakamakon wannan kyakkyawan labari mai ɗan karen daɗi. Amman zuwa bayan isha ba sai tashin hankali ya same ni ba, nice harda ihu ina bige_bige. Bulamana ina jinshi yana ta karatu yana tofa mun yana cewa.
"Zaku fita da ƙafafuwanku, domun kuwa kun taɓo gidan rina, ashe ku kuka shafeta ko?" Sai adda'a yake yi yana tofa mun, kaina sai wani zungurata yake yi, jikina kamar ana sossoka mun allurai. ( Subuhanallah shaye_shayen miyagun ƙwayoyi masifa ne mai girma) A hankali naji abun ya na sassauta mun kaɗan kaɗan. Sai kuma na shiga kuka ina mai nadama da dana sanin soma shan miyagun kwayoyi a rayuwata sai nayi kamar in faɗa ma Bulamana halin da nake ciki amman sai tsoro ya hanani. "




Ghana:
Adda'a duk wacce tazo baki na cabkarta nake yi, kafin in kai ƙarshe ta dubce mun, domun asarar kuɗin tara akayi. Sai da aka kira sallar isha na daure na tashi da ƙyar na fita tsakar gidan. Wani irin abinci naga suna ci a cikin ɓawon masara abun yake kamar tuwo mulmulallu. Zakiya tace.
"Zubaina yanzu nake shirin tura yara su kira ki kici abincin dare, kinga shinkafarki ta rana ma tana kitchen baki je kin ɗauka ba" Fuskata a kumbure nace mata.
Bana jin daɗi ne, ko sallar magriba ban yi ba." Nan matan suka shiga yi mun sannu. Yayin da yaran kuma suka bini da idanunsu, Rashida ce kaɗai ta mun sannu. Har samarin gidan ba wanda na isa kallo. Kwata_kwata yaran gidan Alh Liti basu da tarbiyya, kasancewarsu yaran tsakar gida, kuma yaran ido iyayensu mata basa gidan balle su kwaɓesu. Mata_ matan kuma na lura haƙuri akeyi dasu kawai, dan da ƙyar suke aikuwa, aikima ba yi suke ba, in banda ɗebo ruwa da suke yi a gidan. Alwala na ɗaura na koma ciki na yi sallar magriba da isha. Ina idarwa na miƙe dan takwas saura, ina tsoron kar Alh Liti ya dawo bana wajan, dan nasan zan sha tujara." A gurguje nake tafiya har ina harɗewa domun ina jiyo hon ɗin motarshi yanda yake matsawa da mugun ƙarfi. Da ƙyar na buɗe mishi get ɗin ya shigo, yana faka motar ya fito ko rufewa bai yi ba. Cikin jaraba da ƙanƙance idanu yake nunoni da yatsa.
"Wannan bura'ubancin ya isheki haka yarinya. Kar ki ga ina sassauta miki dan ke amarya ce, nan da kwana bakwai in akace miki kiyi hakan ma, sai kin gwammaci mutuwarki, ki kiyaye ni bazan ɗauki sakarci ba" Wani kududune ya tokare mun wuya na, bance komai ba nabi bayanshi, juyowa yayi ya kalleni yace.
"Wa zai rufe miki motar, ni kike jira inje in rufe miki ko, in ubankine zaki bari ya rufe da kanshi ne?" Tsaki yayi ya shige ciki yana sababi.
"Aikin banza aikin wofi yara sai rashin kunya, da rashin sanin darajar aure" Kai na girgiza kawai na je na tura ƙofar motar na bi bayanshi, ina cike da tsantsar zafin zagin ubana da yake yi. Ko da na shiga ɗakin baccin nashi har ya shiga wanka. Layar da boka ya bani na zaro a bireziyata, na jefa ɗaya ƙarƙashin gadon Alh Liti. Ɗayar kuma na ɗauki pillown da yake ta da kai dashi na zare rigar pillown, a ɗinke pillown yake, da baki na dinga cisgar daren ɗinkin har na samu bakinshi. Ɗan waje kaɗan na ɓarka na tura layar nan da sauri. Ina kan mayar da rigar pillown Alh Liti ya fito. Da kallo ya bini yana mun murmushi, take tsoro ya kama ni ina tunanin anya kuwa bai ganni ba. Wata zuchiyar tace mun, ko kuma asirin ya soma aiki ba. Ajjiyar zuchiya na sauke.
"Ya naga baki sake kayan jikin ki ba, ko baki yi wanka bane? Kinsan fa kwalliyarki ba ƙaramin sukurkutani take yi ba. Yana yin magana yana kallon ƙwayar idanuna. A tausashe nace.
Da zazzaɓi na wuni, ban sake wanka ba tun na safe, amman yanzu zanyi" Ina gama faɗar hakan na shige ban ɗakin Alh Liti ina murmushin muguntar yazo hannuna, zanyi tamaule dashi"


Alh Liti:
Zubaina na shigewa Bayi, ya saki murmushi tare da girgiza kanshi. Sai da yaji zubar ruwa halamar wankan ta soma, sannan ya miƙe ya isa bakin gadon. Da wayarshi ya haska ƙarƙashin gadon ya hangon layar bata ma shiga can ciki ba, hannunshi ya zura duka a ƙarƙashin gadon ya zaro layar. Kai ya kuma girgizawa kawai, ya jawo pillown ya cire layar data cusa. A cikin durowarshi ya adana layun, ya dawo ya zauna kamar ba shi ba.
"Yaro baisan wuta ba sai ya taka. Turnuƙu faɗan ibilisai, yarinyarnan ni zata yi ma asiri a wautarta da ace ba da idanu ɗaya nake bacci ba da yanzu ba'a kassarani ba? Ai ko matan da na saka kaɗai sun isa su jefe ni. Zanyi maganinta, ni da ita babu saki, mutuwa ce kaɗai zata raba mu. Hatsabibiya kawai. Miƙewa yayi tare da nufar durowar gefen gadonshi, ya zaro wani magani a baƙar leda. Ya barbaɗa ɗan kaɗan a cikin nama, bayan ya raba naman gida biyu kenan, yasa hannu ya cakuɗa naman yana kwashewa da dariyar mugunta"




ZUBAINA:
Cikin walwala na fito, duk da zazzaɓine kau a jikina. Rigar baccin dana tawo da'ita a leda na zare na zura a jikina, nabi jikina da turare na fesa sama_sama. Kayan dana cire kuma na ninkesu na mayar cikin ledar da na cire rigar baccin. Sai kallona Alh Liti yake yi yana murmushi. Nama ya buɗe cike da takadda ya ji yaji da albasa, take yawu ya soma gudana a bakina, dama banci komai ba tun safe cikin fara'a nace dashi.
Abincinka fa baza kaci ba yauma? Da wai so nake yanzu in je in ɗakko maka ai" Hannuna ya riƙo ya zaunar dani a saman cinyarshi yana shinshinar ƙamshin turarena. Cikin muryarshi ta yaudara yace.
"Ai ko kusa bazan so kiyi nisa dani ba, in ce dai kema baki ci abinci ba ko? Ga nama na kawo mana shi zamu ci mu kwanta. Wannan doguwar rigar taki ta tado mun da sha'awarki ainun" Far nayi da idanuna nace.
Ai kai da kaya duk mallakar wuya ne. Abinci kuma banci ba sabida da zazzaɓi na wuni sosai" Zamewa nayi na zauna a gefenshi. Naman ya soma ci yana kallona.
"Kici nama ga fura in kina son sha ki sha." Zamana na gyara cikin kissa da kisisinar dana ƙware a kai nace
Dama Alh Liti inason muyi magana ne akan inason ka bani jari in soma gudanar da kasuwanci, tunda kaga baka son aikin mace, ni kuma ina kulawa da Mama, da ƴan uwanta. Duk da nasan su Asiya ma suna iyakar iyawarsu." Shiru nayi ina kallonshi tare da karantar yanayinshi. So nake in gani maganin boka ya soma aikinne, duk da na ga halamar ya soma aikin, tunda har yayi mun tayi nama da fura"
"Hmmmm kamar nawa kike ganin zai isheki yin kasuwancin, sannan wacce sana'a kike sha'awar somawa ke da baki san kan Ghana ba tukunna?" Wani sanyin daɗi naji a raina. Lallai duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi bazai hango ba. Wato irin garaɓasar da Mama ta hango mun kenan, shi yasa tafi son in yi haƙuri in kwantar da hankalina in dandali arziki."
Ko miliyan biyar ma in ka bani zan soma juyawa mu gani" Ƙwarewa yayi da nama, take ya shiga tari ƙwatol_ƙwatol. Ruwan roba daya shigo dashi ya ɓalle sai da ya sha rabi sannan ya sauke robar. Ya dubeni ƙur, ni kuma sai sannu nake yi mishi cikin muryar yaudara. Dariya yayi mai ɗan tsayi kafun yace.
"Miliyan biyar zai miki dai ko ai naga kamar ba yawa?" Cike da azarɓaɓi na gyaɗa mishi kaina halamar E zai ishenin"
"To shikenan, in Allah ya kaimu gobe sai in ƙirga in baki. Kinga waccan durowar? Shaƙe take tab da kuɗi harda na amurka" Idanu na zare, na bi durowar da kallo ina murmushi. Muna hira jefi jefi, muna cin namannan, ko wanne cikinmu da abinda yake saƙawa a ranshi. Furarshi yasha ya rage mun nawa, ya dubeni yace.
"In kin gama cin naman sai ki share gidan kiyi mopping ɗinshi. Da safe ya kamata kiyi, ganin ke ɗin amaryace yasa na ɗaga miki ƙafa." Cikin fara'a na amsa mishi da.
Ba matsala dana gama zanyi" Zama na gyara na dinga cin namannan sai da na cinye tas, na kora da fura. Sannan na tashi na shiga aiki. Hmm aikin babu sauƙi domun sai da na share sama da awa biyu ina abu ɗaya, bayana da ƙafafuna duk sun ƙaƙe. Da ƙyar na hauro sama, a zaune a kan gado na samu Alh Liti, yana daddanna waya yana murmushi. Wanka na shiga nayo, a yadda na barshi a haka na fito na same shi. Ina hawa kan gadon, ya murgino ya hayeni kamar doki, nan ya shiga sukuwa yana nishi. Ni kuma wani baƙin ciki ne ya turniƙeni, babu ko ɗigon sha'awar Alh Liti a tattare dani, banjin zan iya sha'awarshi kwata_ kwata. Haka yaita matsata kamar kayan wanki. Yana sauka a kaina ya soma sakin munshari. Kallonshi nayi inaji kamar in shaƙeshi ya mutu kowa ya huta. Da ƙyar bacci ya kwasheni na wahala, dan ko ina a jikina ciwo yake yi mun. Gabana kuwa ina tunanin ya tsagene, dan raɗaɗin da yake yi mun bana wasa bane.






YAHANASU:
A gaba Bulamana ya tusa ni, tare da yin tagumi. Ni kuma ko ina babu daɗi a jikina, ji nake yi kamar mutuwa zanyi. Gashi inason cikin dake Jikina ya zauna, nima ace ga nawa ɗan, shima Bulamana zai ji daɗin faruwar hakan, da ma su Ba Modu baki ɗaya. Idanuna haka su kaita fitar da ruwa. Sai na samu nutsuwa, zuwa can sai in kama kaina ina rishin kuka. Dan ji nake yi tamkar kaina ya ragargajene. A taƙaicen taƙaicewa yadda Muka ga rana haka darennan ya kasance mana. Bulamana idanuwanshi sun ƙanƙance sosai. Ko da asuba tayi sai da ya kira Hajara ta zauna dani kafin suka tafi masallaci. Ni kuma da taimakonta na samu nayi sallah a jingine a kan katifa, dan bazan iya zama akan sallaya ba. Bulamana yana shigowa ya shiga aikin hura wuta, kunu ya dama mana. Ya aiki Bawa ya siyo ƙosai a cikin gidan. Ni dai da ƙyar na yarda na sha kununnan, babu abunda nake son sha sai caka mis. Wannan baiwar Allahn na tuno wacce muka taɓa haɗuwa da'ita a wajan magajiya, tazo a birkice a ruɗe. Idanu na runtse gabana na tsananta faɗuwa, gani nake yi tamkar watan tonon asirinane ya tsaya.
Ka yafe mun Bulamana, ka yafe mun dan Allah. Ko da na mutu ka samu Binta zata nuna maka fili......" Kaina na riƙe ina salati da ƙarfin gaske, a ruɗe Bulamana ya kama kaina ya shiga yi mun tofi.
"Ki zauna bari in ɗakko ɗan sahu muje asibiti, duk da ina ganin ciwon kamar makarai ne suka shafeki, amman muje dai asibitin. Ki kwanta ina zuwa yanzu" Yana

42 / 67