Author : Badi'at Ibrahim Category : Top Hausa Novels 2025
Gaskiya matar ta burgeni yanda ta tsaya a kan yaranta, ki gani kuma mijin ya rasu. Dole a buga misali da wannan baiwar Allah, ga masu zagin yaran mace. Ita kam gashi yaranta suna bautama ƙasa. Daga soja sai likita, sai lauya.
"Kai Yahanasu nima labarin matar nan ya burgeni. Dama wanda suka kalla na tabbatar. Mun samu kiraye_ kirayen waya akan labarinta ba adadi." Muna cikin tattaunawa muka iso sabon gari. Sakkowa mu ka yi, ni na biya mai ɗan sahu kuɗinshi muka nufi gidan magajiya. A ɗaki muka same ta a zaune tana ƙirgama wata mata wasu kayan maye masu kama da ganyen shayi. Da ganin matar itama tsohuwar kilaki ce. Magajiya ta kalli Binta tace.
"A Binta mai yar shaye_ shayen ƙwaya kenan baki da aiki sai shan ƙwaya. Nayi miki tayin ganye kinƙi, sai allura kika fi faɗawa dasu. itama ganyen fa duniya ce, sauke nauyin kai take yi sosai. Ja biyu kyawawa in kika yi ya wadatar dake, zaki ji hayaƙin ya wanke miki kwanya. Fatima basu labarin ganye" wannan tsohuwar kilaki ta dube mu ta watsar tace.
"Ai kinsan shaye_shaye ra'ayine. Kuma ganye yafi dacewa da ƴan mata ko masu zaman kansu irinmu. Ihu muka jiyo daga tsakar gidan su magajiya. A guje muka fito dan gane ma idanuwanmu. Wata karuwa ce take wannan ihun, ta faɗa kwata jikinta ya lalace ga ciwuka taji a fuskarta da hannunta. Magajiya tace.
"Nifa na gaji da wannan mahaukaciyar, ina Jumman Lokoja take, ita ta kawo mun yarinyarnan lokacin da hankalinta, amman yanzu tunda ta zama taɓaɓɓiya gara ta tafi titi karta hana kostomominmu shigowa. Jiya ta Hana Bala aci bulus wuce wa, sai zagi da ashariya take yi. Yanzu kuma jibeta. Wacce aka kira da Jumman Lokoja tace.
"Magajiya yarinyar nan, inaga sai dai in sata a mota a yi hanyar barin gari da'ita sai mu saketa, tabi jeji tai ta haukarta. Tun da hankalinta nake jan kunnenta shaye_ shayen da take yi yayi yawa, karta kashe rayuwarta a banza. Da yake ƙadangarun bariki sun ɗaure mata baya, ai banza tayi dani. Ta dinga yin allurai, gashi da ƙuruciyarta zata ƙare a bola. In hankalina dubu ne yau ya tashi, da naji dalilin daya haukata wannan baiwar Allah. Na shiga ruɗani da tashin hankali mai yawan gaske. Hasaso kaina nake yi a cikin irin yanayinta na hauka. Ko wannan dalilinne yake sawa in ban sha kayan maye ba nake jin kamar zan danna ihu, ga wasu surutai da hayaniya da nake ji a kunnena kamar zan zautu" magajiya kamar tasan tunanin abunda nake yi, dafa ni tayi tace.
"Karma ki sama ranki komai. Wannan ɗan kurɓe_ kurɓen da afe_ afen ƙwayoyin da kuke yi, babu abunda zai saki. Ke baki isa ki sha kwatan_ kwatan abinda matsiyaciyar yarinyar nan take sha ba. Har giya da koken sha take, alluran doki take yima kanta, itace shaƙar kashin ƙadangare. Ai wannan naku shaye _shayen na rage matsalolin yau da kullum ne, shi yasa nafi ciniki a wajan matan aure. Dan kaso saba'in bisa ɗari na kostomomina matan aure ne, masu ƙoƙarin cire takaicin mazaje ƴaƴan kunama, sun waye da ciwon zuchiya ko hawan jini ya kashe su, shine sai su kora harka" Ajjiyar zuchiya na sauke ina dafe da ƙirjina nace.
Da har hankalina ya tashi wallahi, har nake jin kamar bazan sake shan komai ba. Amman wallahi ba iyawa zanyi ba, sai fa na kora nake jin daɗin komai. Siyan abunda ya kawo mu muka yi tare da ficewa a gidan, mun barsu anata dambarwar kama matashiyar mahaukaciyarnan. Kemis na shiga na siyo P T. A wajan mu kai sallama da Binta. Ina zaune shiru a bayan Ɗan sahu nayi mugun zurfi a cikin tunani da tashin hankali. Maganganun Jumman Lokoja dana magajiya sai karakaina suke a kaina. Haka ƙwaƙwalwata sai hasko mun hoton matashiyar mahaukaciyarnan yake yi. Idanuna na lumshe, tare da shafa cikina da nake tunanin kamar jinin Bulamana ya samu wajan zama a mahaifata. Hakan ya sanyaya mun raina, har guntun murmushi ya sufce mun. Amman tunanin wannan yarinyar ya kasa goguwar mun, a haka na shiga gida da sallamata, hannuna riƙe da ledar cefanen dana tsaya a bakin hanya nayi mana. A guje su Bawa da Anisa suka nufoni, maryam na biye dasu itama a guje tana kiran.
"Umma umma umma" Maman Hassan da su Maman Iklima mai kitso sai dariya suke ma Maryam. Tsugunnawa nayi na ɗauketa na rungumeta ina faɗin.
Yarinyar ummanta, kinga su Maman Iklima sai dariya su ke yi miki ko? Maman Sajida ta dubeni tace.
"Umman su Maryam anya ba cikine dake ba kuwa?" Tana gama faɗar haka ta saki kan matar da take ma kitso ta matso kusa dani. Ni dai sai dariya nake yi mata ina jin wani farin ciki.
"Gaskiya cikine dake babu makawa, Allah ya raba lafiya, zamu sha sunan kanurai. Maman Hassan tace.
"Ah za'a gwangwaje sunan kanuri a cikin gidannan. Sai dai wannan ƴa ko ɗa zai zo da baƙi kamar bawa, koma yafi bawa tunda Hajara tace mahaifiyarsu farace kamar tsada. Turus nayi na bi Hajara dake tsintar wake da ido. A tunanina matan gidannan basu da masaniyar bani na haifi su Bawa ba. Ashe aku mai bakin magana tuni ta fesa musu, harda haɗawa da suffanta uwarsu. Ko da yake nima nayi kuskure da nake tunanin Hajara ba zata basu labari ba. Allah kaɗai yasan me suka sani a kaina. Ɗan Murmushi na ƙaƙaro nace.
Kaji mun maman Iklima da gani na sai kice cikine dani? Ke kuma Maman Hassan sannunki da kushe mun mijina. Ko da yake kun saba ai, kullum yazo wuce wa ina ji kuna cewa wannan miji na Yahanasu ba dai baƙi da jan ido ba, ga muni ko? Nagode sosai." Ba da faɗa na faɗa ba, asalima dariya ce a fuskata, amman na ɗauresu da jijiyoyin jikinsune, kuma sunji kunya ainun. Basarwa nayi na dubi Maman Iklima wacce ta juya sum_ sum zata koma bakin aikinta na kitso.
Maman Iklima inna gama girki zan zo ki mun kitso." Cikin dariyar kunya da dibibicewa tace.
"Mu fara kitson mana kafin ki ɗaura sanwar, in dai ba abu mai wahala zaki dafa ba, maman twins" Murmushi nayi nace.
To bari inyi sallah, naji ana kiran sallar la'asar. Bawa muje ko?" Na ja hannun yaran nayi gaba, na barsu da kunya. Itama Hajara da muka haɗa idanu na bita da kallon kin kyauta, sai wani borin kunya take yi, sai labarin yara take bani. Ni kuwa na bagarar da'ita a gefe nayi alwala na ƙule ɗakina. Na daɗe a zaune a kan sallaya ina tunane _tunanen da bansan meye mafita ba, ni dai har ga Allah na kaɗu da ganin wannan yarinyar. Wata zuchiyar tana faɗi mun. "Anya ba zaki dena shaye shayennan ba tun kafin wankin hula ya kai ki dare?" Wata zuchiyar kuma sai zugani take yi da cewa.
"Amman su ai ba kalar abu ɗaya kuke sha ba, kuma bakya shan giya da koken. Da ana haukacewa da Hajja Fati da Binta sun daɗe da yin hauka tuburan. Ga mata nan birjik da suke shaye shayensu basu haukaceba sai ke?" Da yake aikin shaiɗanne sai naji hankalina yafi rinjaya akan zuchiyar da take ƙoƙarin sake dulmiyar dani. Take na jawo jakata na ɓalle haɗin laka mis ɗina na kwankwaɗi abuna, na miƙe. Kallon ɗakin nayi babu wani gyara da yake buƙata, dan kafin in fita nake gyara ko'ina. Humrar gashi na jawo a gefen katifarmu, na bulbula a gashina, na sake lakutan KULACCHAM na gashi na shafe kaina dashi. Dama kan a tsefe yake tun jiya, ya kuwa sake danƙarewa. Kum na ɗauka, na fice na samu matan gida an kafa daba anata gulmar masu zaman kansu na gidan. Ni dai nawa idanu kawai, Mama Iklima tana kitso tana tofeni da yawu, tsabar gulma na cinta.
Ni kam ki yi sauri ki gama mun kitso, bana son mijina ya shigo ban gama girki ba." Dungure mun kai tayi tana dariya tace.
"Masu miji manya, ai ni nawa mijin ba miji bane ko, sabida baya mun wanki ko?" Nan fa maganar ta dawo kan maza. Maman Nuratu tace.
"Ni ko sanda nake da tsohon ciki ma, Baban Nuratu bai taɓa mun dai_ dai da juye ruwan wanka ba." Maman Hassan tace.
"Hana ƙarya Baban Hassan ya taɓa ninke mun kayan su Hassan sau ɗaya tak, lokacin suna jira jirai" wannan tace wannan, wannan tace wancan. Ni dai sai dariya kawai nake yi, ina ƙara godema Allah daya bani miji irin Bulamana. Alhamdulillah da munin nashi, da baƙin nashi a hakan nake bala'in son shi. Shima duk baƙi da rashin dirina bai hana shi tsantsar sona ba. Babu abinda kyakkyawar mace zata nuna mun, ta fannin soyayyar miji. Wallahi wata kyakkyawar bata samu kwatan son da Bulamana yake yi mun ba, a wajan mijinta. Kuma wata kyakkyawar mai gashi bata fini jin daɗi da kwanciyar hankalin aure ba. Me zan ce ma Ba Bakura? Sai adda'ar gamawa da duniya lafiya. Maman Binta ce ta katsemun tunanina tace.
"Yahanasu a bamu laƙanin muma mana, kinsan fa Kanuri, da Shuwa basa barin mazajensu haka, akwai wasu asiri _asiri da ake haɗa musu a gida" Da sauri na tare ta da cewa."
Wannan duk ƙaryace kawai sauran ƙabilu suke jifan ƙabilarmu da'ita." Hajara tace.
"Umman Maryam kina nufin Kanuri basa asirin mallakar miji?" Na kalleta nace.
Bazan ce muku kanuri basa asiri ba. Kamar yadda bazan ce, fulani, Hausawa, Yarbawa, Inyamurai, Ibira, Igala, arago da sauran ƙabilu da dama basa asiri ba. Ko wacce ƙabila nayi. Ni abinda na sani shine. Tunda na taso ban taɓa ganin wani abu daya jiɓanci asiri ba. Mahaifiyata da dadduma da Qur'ani, da carbi na santa. Kuma nima guzirin data bani kenan. Abunda na sani da matan Kanuri suna da tsantsar biyayyar aure, da tsantsar tausayin miji. Ƙamshinmu da tsabtarmu ke lashe zuchiyar mazajenmu. Amman ba komai ba. Allah yasa kun fahimci bana cikin Kanuri masu mallake miji ta hanyar asiri, kamar yanda kuma bakwa ciki ko?" Ɗankwalina na ɗauka na karkaɗe jikina dashi. Na ajjiye ɗari biyu a cinyar maman iklima.
Nagode da kitso, bari in je in ɗaura girki" Nan na barsu suna ta tattaunawa. Gaushi na ɗiba a kurfot ɗin Hajara na zuba akan gawayina. Sai na zauna na soma gyara kayan miyana. Farar kuskus na dafa da miyar tankwa, wacce na saka mata ɓararren kifi. Na mitstsike tsamiyar dana dafa tun safe da kayan ƙamshi a ciki. Na tace na zuba ɗan gishiri da suger. A ƙatuwar gora na juye, na miƙa ma maman Kaula ta ɗan samun a gidan ƙanƙara. Abincin kuma na zuba a kula, na ɗaura a faranti da fileti da cokali, da cokalin ɗiban abincin, na shige dashi ɗaki. Na bunke ɗakin da turaren wuta. Sannan na shiga shara, da wanke wanken Kayan dana ɓata. Ina fitowa wanka aka soma kiran sallah. Naga wucewar Ahmad masallaci. Bulamana nasan sai yayi isha zai shigo gidan. A gajiye tulus yake shigowa ga yunwa. Abinci na zuba ma yara, na je na karɓo jus ɗina, na sai ruwa mai sanyi a wajanta. Ina zaune na tuno da P T ɗin dana siya. Ai ba shiri na ɗauka nayi bayan gida. Fitsari na tsula a kanshi bayan na ɓare. Cikin saƙanni sai ga jan layi biyu sun fito ɓaro_ ɓaro. Lumshe idona nayi.
Lallai yau akwai goron albishir kenan Bulamana?"
Ina shiga ɗaki na tarad dashi a zaune a gaban abinci yana ta kiciniyar zubawa. Da sauri na riƙe cokalin zuba abincin na idasa zuba mishi. Sai da na tura mishi abincin da kofin dana tsiyaya mishi jus ɗin gabanshi, sannan nace mishi.
Sannu da shigowa, ka dawo ina bayan gidane" Fuskata ya shafa yace"
"Inata sallama ai, da naji shiru sai na shigo naga bakya nan, nayi tunanin Sallah kike yi. Bari dai inci abinci akwai labari me zafi yau." Yana cin abincin ina mai fifita, nima inaci, muna ɗan taɓa hira jifa jifa. Bayan ya fito wanka ne yake bani labari.
"Ina wajan aiki da safe Wakil ya kira ni. Yana ƙorafi akan matarshi Maman Yahanasu, akan ta fiye ƙazanta, gashi bata yi mishi biyayya kwata_ kwata. A taƙaice dai har tayi zuchiya ta tafi gidansu. Iyayenta basu duba dangantaka ba, tunda duk dangin junane, da ta tafi, mai makon su kira Wakil ɗin suji ta bakinshi. Sai ba su yi hakan ba. Kawai suka turo ƙannenta suka ɗibar mata kayan sawarta da kayan ɗiyarta Yahanasu. Kinji halin da ake ciki yanzu haka, tafiya Damaturu ta kama ni gobennan" Shiru nayi ina tuno Maman Yahanasu.
Zancen gaskiya ƙazama ce, nima na gani, dan ɗakinta har wani tsami yake yi, kaima ai ka shiga ɗakin. Babu ƙamshi irinna matan Kanuri sam. Amman Ba Hamma bai dace ace sun bar Anti Aissa a gida ba. Ya dace su tuntuɓi Wakil ɗin."
"Kinsan wasu iyayen a kwaisu da goyon bayan yaransu. Ba Bakura kuma ya hana Ba Modu zuwa, yace Ba Hamma ya dace ya tuso Aissa a gaba ta dawo ɗakinta, ba wai a turo a ɗebi kayanta ba
Ko kuma ya kirasu a waya, tunda ƙani yake a wajanshi, da kakan Ba Hamma, da Hajja Yahanasu, ƴaƴan wa da ƙani suke, kuma Ba Bakura ya taimaki Ba Hamma sosai a rayuwa. To tunda nine babba shine Wakil ɗin ya kira ni ya faɗa mun halin da ake ciki. Na kira Ba Modu ma a waya mun tattauna. Gobe zamu haɗu da wakil ɗin a Pataskum ɗin, sai mu je tare" Yana gama wannan jawabin ya jawo ni jikinshi, ya kai hancinshi zuwa kaina ya shinshina. Hannu yasa ya zame mun ɗan kwalina, a hankali ya shafa kitson nawa, da ɗan gashina da jelarshi bata wuce kamu ɗaya ba. A kunne ya raɗamun.
"Kitso yayi kyau, mai kitson ma tayi kyau" Bakinshi ya ɗaura akan nawa, lumshe idanuna nayi, tare da cabke leɓenshi. Sai da muka samar ma da juna nutsuwa, sannan na ɗago da kalla na kalleshi, inason yi mishi albishir. Amman ina yayi bacci, sabida a gajiye tulus yake shigowa gidan. Sai da safe bayan ya gama shirin tafiya Tsab na tsaida shi a bakin ƙofa. Sai kuma na shiga kame_kame da ƙyar na faɗa mishi ina da ciki." Murmushi yayi, tare da saurin kamo hannuna ya kafeni da jajayen idandunanshi.
"Da gaske ko zolaya Yahanasu na, shine baki faɗa mun tun jiya ba, asibiti kika je ko yaya kika gane kina da ciki?" Wannan tambayoyin nashi a jere su suka sani darawa.
Gwadawa nayi da P T amman inason zani asibiti tunda bamu da aiki yau"
"Alhamdulillah Allah na gode maka. Ki kula sosai Yahanasu, kinsan cikin fari sai da lallaɓawa. Allah ya raba lafiya, Allah ya bamu masu albarka" Da Ameen na amsa mishi. Dubu ɗaya da ɗari biyar ya bani, nasa hannu na karɓa.
"Ga wannan kije asibiti, sauran canjin ki riƙe a hannunki duk abinda kika ga kina son siya sai ki siya. Kuɗin cefanenki na saka miki a bankaɗen katifa, dubu ɗaya ne, ki jalauta zuwa yau ko gobe. Akwai saƙo da Ahmad zai kawo miki da yamma. Ni sai na dawo." Nan mu kai sallama na bishi da fatan alkhairi. Yara sunata ɗaga mishi hannunsu, har yayi mana nisa, sannan muka koma ɗaki. A tsanake na shirya tsab, na fito rataye da ƙaramar jakata. Hajara na miƙa ma Su Bawa, na mata sallama akan zanje kasuwa, dan nasan dana ce mata asibiti zani zata baza ni a wajan matan gidan. Ban wani samu layi sosai ba can, duk da asibitin gwamnati ne. An gwadani, ƙaramin ciki ne har na sati Takwas, wata biyu kenan. Sun ce nan da wata biyu sai in dawo na soma awo. Murna a wajena ba'a magana, ina fitowa na yi ma Bulamana saƙon karta kwana ta wayarshi, na faɗa mishi satittikan yaron nashi. Kai tsaye na wuce sabon gari, a ƙofar gida na samu Magajiya tana faman ciniki. Ga matan aure nan suna ta siyan kayan maye. Wasu ma da goyo a bayansu, wasu kuma masu ciki ne. Sai mamakin yanda shaye_shaye ya zama ruwan dare a wajan matan aure nake yi. Magajiya ta miƙo mun laka mis gora biyu.
Ni kuwa Magajiya ya ku ka yi da wannan matashiyar mahaukaciyar da rannan muka tarar ana artabu?" Shewa tayi tace.
"Tuni Jumman Lokoja tasa manyan maza suka cabketa aka fice da'ita bayan gari aka wullar." Baki na buɗe da mamaki nace.
Kuma iyayenta ba zasu zo nemanta nan ɗin ba?"
"Karuwa ce fa Yahanasu, wa yasan daga inda ma tafito balle har azo wani nemanta. Kai naci gaba da jinjinawa, ina tsaye ina jiran canji na, in yi gaba, dan kullum nazo wajannan bana samun nutsuwa har sai na bar wajan. Sai inga kamar idon sani zai ganni asirina ya tonu. Wata matace tazo itama siyan abun mayen. Ni naga sai wani fisge fisge take faman yi, tana dafe kanta. Kwalba biyu na maganin tari Magajiya ta bata, a take ta shanye. A cikin minti biyar ta sauke ajjiyar zuchiya tace.
"Haba sai yanzu na dawo duniyar mutane. Da ji nake kamar za'a zare mun ƙwaƙwalwata daga ƙoƙon kaina. Wallahi kwana biyu na shiga halin rashin kuɗine Magajiya. Sai da na faɗa ɗakin matar gidanmu na aro kuɗaɗe. Ƙaro kwalba biyu, ki haɗa mun da laka mis gora biyu. Na yi maneji zuwa kwana biyu. Canji Magajiya ta miƙa mun na wuce. Hankalina yafi tashi yau fiye da wannan mahaukaciya dana gani. Dan Magajiya ce mana tayi, har giya da koken take sha, shi yasa ta haukace. Wannan matar da na baro a wajan Magajiya ai naga ita maganin tari da laka mis take sha. Amman jibi yanda ta fice a hayyacinta, wannan babu wani sauran hankali a jikinta, zaucewa