MAI IDO A TSAKAR KAI BY BADI'AT IBRAHIM.txt

Author :  Badi'at Ibrahim Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   55 / 67

162K to 165K   out of 198.3K words

a bakina cikin tafin hannuna, na kora da ruwan faro dake kusa dani. Na lumshe idanuna ina tsiyayar da ruwan hawaye, zuchiyata da ƙwaƙwalwata sun kasa aika ma da juna sakon komai. Sai jini da zuchiyata take watsawa gangar jikina wanda ya wuce kima. Ina zaune har bayan la'asar ko azahar ban yi ba. Sai ga hon ɗin motar Sani. Na gane hakanne ta dalilin fitowar matarshi cikin sabuwar shiga tana busa ƙamshi tayi waje taran Sani. Ji nayi kamar in jawota in hauta da duka, amman babu ƙarfi a jikina ƙwayoyin dana afa sun soma tasiri a jikina. Ina jingine Sani ya shigo saye da farar shadda, da wani yaro a kafaɗarshi. Idanu na zuba mishi ina karantar yanayinshi. A madadin inga tsoro da firgici a tare dashi, sai naga ganina da Sani yayi bai ɗaga mishi hankali ba.
"Mutan Saudiyya yaushe a gari inji maƙi baƙo?" Da fara'a ya nufoni ya zauna a kujera mai fuskantata.
Saukar kenan nace bari in sauka a gidana, inga mijina da yarana" ƙur nayi mishi inason inji mai zaice. Sai naga yayi murmushi yace.
"Mutan Saudiya kenan, hmmm ke a tunaninki zaki je saudiyya tsawon wannan shekarun ki dawo kuma muci gaba da aure?" Sai ya kalli matarshi yace.
"Honey wannan itace tsohuwar matata, maman su Amira. Maman Amira wannan itace Husna sabuwar matata dana aura bayan na sake ki saki uku" A ruɗe na kalleshi nace.
Saki kuma Sani, giyar wake kasha ko me? Anya a hayyacinka kake?" Dariya yayi yace.
"Wallahi ras nake, ai baki ga halamar hauka tattare dani ba. Cewa nayi na sake ki saki uku, zai fi miki ki tattare ki koma gidan iyayenki." Nan na miƙe dama a buge nake, munci uwar sabada ni da Sani. Dan rufeshi da duka nayi tako ta ina, inayi yana yi. Ihu nake kurmawa dan ƙaramin zaucewa nayi. In muku a gurguje da ƙyar aka fito dani daga gidan Sani. Da ƙyar na gane gidanmu na kai kaina. A cikin kwana goma na haukace tuburan, sai na wayi gari na ganni a gidannan. Ina shirin maka Sani a kotu. Wannan shine labarina, amman kes ɗin yana hannun wata lauya mai zuwa dubani tare da su Mama. Duk abunda na ke turama Sani a lissafe yake, kuma saiya biyani abuna." Rarrashin maman Amira mu ka shiga yi, labarinta ya taɓa mu baki ɗayanmu. A daddafe na basu labarin kab rayuwata da yanda akayi na tsinci kaina a gidannan. Haƙiƙa sun jinjina mun, sun kuma sake jin girman Bulamana a zuchiyarsu, sun tausayama halin dana shiga ainun. Zainura ce tace.
"Labaranmu suna da taɓa zuchiyoyi, ni na haƙura da bada nawa labarin sai zuwa dare in Allah ya nuna mana. Duk sai mu ka tsaya a matsaya ɗaya kan cewar a bari sai da daddaren sai mu ci gaba da jin labarin ɗaya daga cikinmu, ko babu komai zamu rage ma kanmu dare." Misalin ƙarfe taran dare muka sake haɗe kawunanmu domun sauraron labaran ƴan uwanmu. Zainura ce ta soma da cewa.
Ni nawa mijin shi ya sani a cikin masifa da tashin hankalin da nake ciki a yanzu. Auren soyayya mu ka yi, soyayyar da sai da kab dangina suka sanshi. Muna zaune cike da so da Amana, yaranmu biyu. Kwatsam rana tsaka yace shi Aure zaiyo. Har ga Allah a lokacin ni ban ɗaga hankalina ba. Dan bazan mance ba har gidan iyayen yarinyar da zai aura a lokacin ya kaini. Da yamma ina aiki a kitchen ya shigo, yara suka taryeshi, sai da ya gama wasanshi da yara kafin ya same ni a kitchen ɗina a falo.
"Maman Hafsa baki sauke sanwar ba, bacin tun jiya na sanar dake zamu fita?" Ranshi ya ɓaci sosai. Ni kuma cikin rarrashi nace mishi.
Kayi haƙuri, gas ɗinane ya ƙare, sai da na fita na sawo. Amman abincin yanzu zai tsotse, ni kuma ai kaga a shirye nake tun ɗazu yaranma na shiryasu.
"To kiyi sauri dan Allah." Yace dani. Cikin minti goma abincina ya tsotse, na zuba wanda zamu ci a kula, sauran na barshi a tukunyar. Mayafina da jaka na shiga ciki na ɗakko. A kan mashin ɗin roba robanshi na sameshi. Hafsa na gaba ita dashi. Musina tana tsaye a ƙasa kusa da ƙafarshi. Gidana na kulle kafin na hau mashin ɗin, na ɗaura Musina a cinyata. Ya ja ni fuu sai gidan budurwarshi, bai tashi sanar dani ba sai da muka tsaya a ƙofar gidan, ina gefe ni da yara ina jiranshi. Parking ya gyara kafin ya nufoni.
"Nanne gidansu Nana, ta jima tana mun ƙofarin ita tana son ganinki. Shine fa yau dai nace bari in kawo ki. Dum naji gabana ya faɗi, na bi Sunusi da idanu ina mamakin wulaƙantani da yayi. Tunda itace take son lallai sai ta ganni ina laifin ita ya kawota gida ta ganni? Sai ni ce marainiyar wayonsu. Ban samu zarafin cewa komai ba, domin in nace zanyi magana to zagine zai fito a bakina. Nana ce ta fito cikin kwalliyar kece raini, sai masifaffen ƙamshin Humra take yi, wanda Mrs Bukhari take siyarwa, mai inganci da riƙe jiki. ga me buƙata sai ya neme ni.
"Allah ya taimaki ɗan maraƙin jimina gagara ɗaukar shawo. Barka da zuwa shingena. Cewar Nana wacce ta yi banza dani kamar bata ganni ba. Shi kuwa Sunusi sai wani yashe baki yake yi kamar gonar audiga.
"Barka da fitowa tauraruwa, kai kwalliyarki abun yabawace, ƙamahinki mai daɗin shaƙane" Jikina sai rawa yake yi mun. Zuchiyata na ingizani kamar in jawo Nana inta jibgarta. Sai da Sunusi ya gama dibar albarka kafin ya dubeni yace.
"Maman Hafsa ga Nana, Nana ga Maman Hafsa yau na cika alƙawari dai ko?" Nana ta washe baki tace.
"Barka da zuwa uwargida ran gida. Gaskiya Baby ka cika alƙawari. Maman Hafsa mu shiga ku gaisa dasu Mama." Kamar raƙumi da alaka haka na bi bayan Sunusi dake bayan Nana. Mune har cikin gidansu. Nana ta gabatar dani ga ƴan uwanta. Muka gaggaisa da iyayenta. Kafin muka shiga ɗaki. Hmmmmm nan naga kwanukan abinci da abubbuwan sha ratata wai duk namu ne. Ni dai ruwa kawai na iya kurɓa, wallahi da ƙyar ya wuce. Sunusi da yara dai sai da suka take cikinsu. Har Nana tana ce mai. Baici dayawa ba yau, ko dan ya ganni ne. Ni dai banza nayi dasu. Daya gama taɗinshi da Nana muka kamo hanyar gida. Nana ta cika yara da su sweet da biskit. Ni kuma ta bani takalmi da jaka. Tun daga wannan ranar na soma kwasar baƙin ciki. Ashe banga komai ba. Sai da Nana ta tare ne, na gane waye Sunusi. Ƴan uwa tunda Sunusi ya shiga ɗakin Nana bai sake waiwayena ba. Nayi kukan, nayi zuchiyar, na kai ƙaran amman wallahi sai sabon wulaƙanci kawai da Sunusi yake sake tata mun. A hankali Sunusi ya dena bamu abinci. Sai dai in je inyi aikatau in samo ma yarana abinci. Na nemi ya bani takaddata ni na haƙura da auren. Sunusi ya je ya sanar da iyayena. Mahaifiyata da bulala tazo ta zane ni a gaban Nana. Kuma tace muddin na kashe aurena basu bani. Rayuwa ta yi tsanani, hawan jini na son halakani. Ranar wata maƙociyarmu ƙawatace take bani shawarar in samu ɗan maganin tari in dinga kurɓa, zai mantar dani halin da nake ciki. Ita kanta in takaicin ɗa namiji yai mata yawa, maganin tari take sha tai ta bacci. Kamar wasa na soma sha, sai naji ashe da gaske yana sauke matsaloli, ya rage cunkushewar zuchiya. Wannan dalilin ne yasa na faɗa harkar shaye_shaye haiƙan.shine silar shigowata wannan gida. Bayan na samu taɓin hankalin, ina cikin wannan halin, Sunusi ya aiko mun da takaddata, kuma ya turo su Hafsa suka dawo gidanmu. Wannan shine labarina a taƙaice. Hadiza ta share hawayenta ta kallemu tace.
Ni zafin zawarci, da irin tsangwamar da ƙabilar hausawa ke ma bazawarane yasa na faɗa hidimar shaye_shaye. Amman alhakin mijina ne ya bibiyeni, dan babu irin rashin ɗa'ar da banyi ma Bala ba. Asirceshi nayi, na dinga tamaule da rayuwarshi. Hatta albashinshi in akai musu biya sai dai ya ɗakko A T M card ɗin ya bani. A taƙaice babu irin zaluncin da banyi ma Bala ba. Bayan asirin da nayi mishi ya karyene ya sauwaƙe mun. Ya kuma hanani ɗaukan ko yaro ɗaya. Wannan shine iya abinda ya dace ku sani. Amman ina cike da nadama, da zabarin ganin na roƙi Bala yafiya, ko hakan zai zame mun matattakalar shinfiɗa rayuwa mai kyau a gaba." Ranar a cikinmu banyi tunanin ko akwai wacce ta runtsa ba. Domun cikinmu ko wacce ta fama wani mikine dake zuchiyarta. Ni dai da naga kwanciyar ba zata kaini ba. Sai na tashi na ɗaura alwala na shiga raya daren da nafilfili. Bayan na idar na shiga istigifari domun neman yardar Allah maɗaukakin sarki.


Ghana:




Zubaina:









MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE
[17/08, 12:06 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
49








Zubaina:
Haka rayuwa tai ta shurawa dani. Lalacewar da nayi tafi ƙarfin gaban a kwatanta sai wanda ya gani kawai. Ga Zarah ta sani a gaba zagi da habaici babu irin wanda bata yi mun. Ni in Zarah na tsakar gidan ma shakkar fitowa nake yi, sabida gudun fitina, dan hatta yaran gidan duk rashin kunyarsu Zarah bata ƙyalesu ba. Alh Liti kawai take jin shakka a cikin gidannan. Sati na zagayowa Nabila ta dawo. Watan ta guda da dawowa ta suntulo ɗiyarta mace mai tsananin kama da'ita. Ni dai sai tura nawa cikin nake yi, yau ciwo gobe lafiya, har yanzu hannuna bai idasa warkewa ba, gashi inaji ina gani na zama me giɓi a bakina. Oh duniya mai ido a tsakar ka. Duk wanda yayi sake duniya da abun duniya su ka ruɗeshi, zai mutu a wulaƙance yana cike da dana sanin rayuwa. Cikina watanshi takwas da kwanaki amman ban taɓa zuwa awo ba, ba abinci mai kyau, ba ruwan sha mai kyau, na dawo kamar ƴar lambu. Ƴar babbar wayar da nake ɗan hawa whatapp in rage ma kaina zafi, na siyar a lokacin da nayi wani rashin lafiya, kwanana huɗu a asibiti a kwance. Rashida ce tayi jinyata, Alh Liti baya ma ƙasar ya tafi fataucinshi daya saba, da biye _ biyen matanshi da baya rabo dashi. Dan kullum kaje kwanan turaka ka ji ya raba dare yana hirar soyayya da mace a waya. Ni dai a kullum roƙona shine, Allah ya shiga lamarina ya taɓa ya kawo mun ƙarshen wannan zaman rashin ƴan cin da nake yi. Ina bakin murhu na gama naɗe tuwon dokunu a ɓawon masara kenan na mayar wuta, na ji hon ɗin Alh Liti a get ɗin ɓarayinshi. Da sauri na tafi dan buɗe mishi, da ƙyar nake ɗaga kumburarrun ƙafafuna, amman a hakan har gudu_gudu nake yi, dan kar in yi gagarumin laifi. Ina jin Zarah tana tayi tsaki tace.
"Aikin ɓur in ji tusa, dan Allah jibabta" Ni kam ban ko saurareta ba, na je na buɗe ma Alh Liti get ya shigo a fusace kamar zai taka ni da mota, sai ƙara raɓewa nayi a jikin get ɗin ina sauke ajjiyar zuchiya. Da ƙyar na mayar da get ɗin na rufe, na nufi Alh Liti da sauri dan karɓar jakar hannunshi. Dawowarshi daga tafiya kenan.
Sannu da dawowa Alh " Kallona yayi a wulaƙance yace.
"Menene haka ya sameki naga kin aune, fuskarki ta kumbura idanuwanki sun nutse kamar an huda saƙwara?"
Ni kaina ban sani ba, wayar gari nayi na ganni na kumbura takota ina, jikina har ƙyalli yake yi. Gashi bani da kuɗin zuwa asibiti" Tsaki yaja yace
"Ku da an magana sai batun asibiti. Ki kwaɓa toka mai zafi ki shafe jikinki dashi, zai saɓe anan gidan haka akeyi. Ko kin ɗauka ni lusarin kanurin mijinki na da ne da kika maidashi soko? To ni ba haka nake ba. Yau ko mutuwa kika yi su Jummai take kowa? Su ke da asara amman ba ni ba. Kafin ki rufa kwana uku zan maye gurbinki da tiya leda. Wuce ni dallah ki shigar mun da jaka" Sum _ sum na wuce ciki ya bi bayana yana faɗin.
"Um um hum su Zubaina wanka, an zama Zubaina ƙazanta. Naga ƙafarki har kaushi ta soma yi. Da an samu dama sai faman damawa akeyi, ana lanƙwasa tamkar ba'a kashi, yanzu jibeki yanda kika dawo guzuma." Hawaye kawai nake yi. Key yasa ya buɗe ɗakin muka shiga. A sama na ajjiye mishi jakar, a kan matattakalar sakkowa muka haɗu dashi, yana haurowa yana waya, sai kalaman ƙauna masu daɗi yake faman zabgawa. Har na wuce yasa hannu ya jawoni baya. Daɓas na zauna akan matattakalar ina haki, dan jawoni da yayi, baya nayi zan faɗi. Numfashi na sauke, ban ko iya tashi ba, ina zaune har ya gama lallaɓa budurwarshi da halama fishi tayi. Nima sai ya tuna mun da fishin da na taɓa yi mishi lokacin bikin Nafeesa, wanda a Wannan ranar ne nace sai ya ƙarashe mun ginin gidana, inason mota, kuma inason zuwa aikin Hajji. Murmushi nayi dana tuno amsar daya bani a wannan lokacin.
"Ke dan bura'ubanci shine zaki wuce ni kamar kinga buhun dawa? To ki hauro sama in murje kuɗaɗena da aka ci mun ko?" Da sauri na kalleshi nace.
Kai mun rai. Wallahi bazan iya ba. Ba daɗi nake ji ba, tun jiya marata take faman ciwo"
"Ni ne zanyi miki rai? Allah ne kaɗai ke ma ɗan Adam rai. Ki taso ni dallah. Ke kin isa kici tuwo ki kwanta getsetse ba tare da an banbasha ki ba." Sahunshi bani da kallo yana haure bene. Da ƙyar na kai kaina ɗakin Alh . Irin wannan kwanciyar dai da hausawa ke mata laƙabi da ( salamatu kwanta ko kuma Ci ka rufe) Ita yai mun. Ya hau yai ta sukuwa tamkar ya samu tsowon jaki. Babu abunda nake ji sai raɗaɗi. Marata kamar zata dare haka nake ji. Dan mugunta Alh sai da ya kai kusan minti ashirin yana ƙurzata. Sai da ya ƙoƙeni tas ya shige ban ɗaki ya barni a yashe a gadon ina cizon yatsana. Da ƙyar na yunƙura na miƙe, na ja zanina ya rufe mun ƙafafuna. Da bin bango, da zaman hutu na sauka ƙasa. Ina komawa cikin gidan naga Nabila na raba ma yara dokunu, harta sauke ta mayar da tukunyar ruwan wankan jegonta. A gidannan ko haihuwa kayi ɗaga ƙafar kwana bakwai akeyi maka. Da kan ka kake yima kan ka komai. Gefe na samu na zauna naci gaba da rabon abincin ina share zufa da bakin zanina. Bangajeni Zarah tayi sai da na kusan faɗuwa ƙasa. Da sauri na ɗago ina kallonta, sai jijjiga take yi a kaina.
"Malama tun tuni kin tafi wajen miji kin bar mutane da yunwa, dallah ni ki zuba mun abinci." Da yatsa na nuna ta nace.
Kinci alfarmar abunda ke cikina, amman wallahi da yau na nuna miki waye Zubaina. Zarah baki sanni bane, ruwane ya daki babban zakara, kin samu kura tayi lafiya, ni ɓarayi nake masga da manyan ƴan iska wanda suka fiki riƙa da gashin fiffike. Hmmmm Allah ya shirya ni banga abun kishi a cikin gidan da kowa ta kanshi yake yi ba.'" Robar hannunta na fisge na zuba mata dokunu ƙulli biyu da kan kifi ɗaya, na dangwarar mata a gefen ƙafarta. Ai kuwa ashe na taɓo tsuliyar dodo, nan Zarah ta shiga kutuntume_kutuntumen ashar, har su Hajiya Kubra da Rashida suna rirriƙeta wai sai ta tattakani. Ni kuwa sai haɗiɗiyar zuchiya nake yi bakina yana ambaton Allah. Gabana sai faɗuwa yake yi, dan nasan ko lafiyace dani a dake zan sha duka a wajan Zarah, dan hausawa sunce halamar ƙarfi tana ga mai ƙiba. Ana cikin wannan sowar Alh Liti ya shigo cikin gidan buguzun_buguzun da malum_malum yana tafe yana saɓawa.
"Wai menene ne haka gida sai jaraba, sai kace ku kaɗaine kishiyoyi a cikin gidannan?" Ya dubi Zarah da aka rirriƙeta yace.
"Ita kuma wannan mahaukaciyar masifaffiyar meya faru da'ita na kada ta haune ko barhazs?" Hajiya Kubra tace.
"Ba wani na kada. Zarah bata son zaman lafiya sam tunda ka aurota kullum a cikin tarar masifa da bala'i take. Ni bansan me take ma kishi a cikin gidan ba. Koma meye ya kamata ka sanar mata mu tazo ta samu a gidan, Zubaina tana gaba da'ita" Kwafa Alh Liti yayi, ya wuce kamar bazai yi komai ba, ace satar Zarah yake son yi. Ƙafarta ya ja ta faɗi rub da ciki ta saki ƙara. Igiyar shanya a tsinke a bango. Ya hau jibgarmu baki ɗayanmu harda yara da suke faman kallo. Kowa ya watse ya barni da ƙyar nake ɗaga ƙafafuna, ɗakin Hajiya Kubra na kutsa kaina da sauri. Yafi sama da mintuna goma yana bol da kwanuka yana wani irin kutuntume_kutuntumen ashariya. Ajjiyar zuchiya na sauke ina ambaton Allah. Sai da ya gama buyaginshi ya bar tsakar gidan, kana kowa yaci gaba da aikinshi. Ƙarashe rabon abincin nayi. Nabeela na juye ruwan wankan jegonta na mayar da nawa. Kafin magriba nayi wanka Sallah na ɗan gargasa jikin nawa. Ina zaune jigum akan sallaya tunani yabi ya addabeni ƴar Nokia ta raka ni kashi ta soma ruri. Mama ce ke kirana, da sauri na ɗauka.
"Yaya yanayin jikin naki da sauƙi dai ko, ciwon marar fa?" Numfashi naja nace.
Kayya yau kam da ƙyar nake ɗaga ƙafafuna, cikin kuwa a kan guiwata nake jinshi Mama. Haihuwarnan tazo fa, bana tunanin zan wuce gobe ban haihu ba. Mama kiyi mun rai ki taso ki zo, wallahi gani nake yi kamar mutuwa zanyi ma. Bana son in

55 / 67